Showing 270001 words to 273000 words out of 296878 words
murya, yasan Akka ita ce nan take da iko da su da iyayensu, yasan idan ta bashi Chuchun to fa babu uban da ya isa ya hana, haka zalika idan ta hana shi, wannan dalilin ma yasa ya biyo ta wajenta kai tsaye bai je wajen daddy ba, dan ko ya je ga daddyn ma zai ce mashi sai abin da Akka ta zartar ne, so shiyasa ya fara bi ta wajenta, kuma Mammaiensu ce ta bashi wannan shawara, ta ce kai tsaye ya tunkari Akka, kuma kada ya wani ɓata lokaci wajen jira, ya yi saurin tunkararta ya gaya mata, hakan yasa ya gaya mata ɗin.........
Lallai da gaske Mammie ta shirya raba Jawad da soyayyar Chuchu karfi da ya ji, domin kuwa hanyar da ta biyo mai karfi ne wanda ya fi na Jawad karfi, tun da Rizwan ya gayawa Akka shikenan kuma, Akkar zata tambayi Chuchun tana son yayan nata ne ko bata sonsa, idan har ta amsa da tana son shi fa shikenan babu wanda ya isa ya sa a fasa wannan aure sai mutuwa sai kuma wani ikon na Allah. Ku ma dai kun san Chuchu dai tana son yayan nata, dan haka da e tana son shi zata amsa. Akwai cakwakiya ba kaɗan ba, akwai tashin hankali.
🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼
ABU ABDUSSALAM EMPIRE 🤍🔥
Nutsuwa sosai Leesharh ta yi tana sauraron abin da yake faɗa. Daga yadda yake fitar da word's ɗinsa kai kasan nutsatsen mutun ne mai ji da izza haɗe da class, ba karya jinin King Zuhair yana gudana a jikinsa.
Magana yake yi a kan lallai a cikin daren nan dole zasu yi wannan meeting ɗin, domin gobe da safe za su wuce ƙasar Tunisia, so ya zama dole a daren nan su haɗu, umarni ya baiwa wanda suke yin wayar da shi a kan lallai karfe takwas ya samesu a wani katafaren luxurious guests house ɗinsa. Ba taro ne da zasu yi a ma'aikatarsu, taro ne na team guda ba na gabaɗaya special weapons and tactics ba, manya manyan zakarun gurayen mazan dake cikin Team na Ramish ɗin su sha biyu ne dai'dai, kowanne daga cikinsu kuma yana da yaran aikinsa a karkashinsa, hakan yasa waɗan da suke a ƙarƙashin Ramish ɗin sun fi mutun 200, waɗan nan maza sha biyun sune jiga jigai masu kula da kannar dake cikin team ɗin, su suke karɓar umarni daga wajen Ramish ɗin su zartar wa da na kasa da su ɗin, so haka suke, team, team, suke, sai dai team na Ramish ya fi na kowa shahara a cikin special weapons and tactics, saboda bashi da wasa, duk kuma wanda za su kasance a cikin team ɗinsa to ba karamar horar wa yake sakawa a basu ba, domin kuwa shi baya ɗaukar faɗuwa, burinsa a kullum cin ma nasara, baya wasa da aikinsa, waɗan nan gurayen maza guda sha biyu na cikin team ɗin nasa ba karamar horar da su ya yi ba kafin su kai matsayin da suke kai a yanzu, ba shi da aboki daga waje sai cikin gida, su ne kuma Bilal, Rizwan and Dr Raj, haka zalika bashi da wani kusanci da wani a wajen aiki, duk da ya kasance cewa ƴan team ɗin nasa horonsa ne, amma baya yarda da kowa, dan yasan farautar rayuwarsa ake yi kamar yadda ake farautar ruwa a sahara mai tsananin zafin rana, yasan komai hakan yasa bashi da wani makusanci biyun Bilal, Rizwan and Dr Raj, a waje baya yarda da kowa, kallo da ido kawai ta raba shi da kai.
A ko da yaushe yana yawan zaman meeting da waɗan nan gurayen mazan ƴan cikin team ɗin nan nasa domin kara karfafa team ɗin nasu ya cigaba da kasancewa shi ne na ɗaya a cikin hukumar special weapons and tactics, yana son ya kasance a sahun gaba kullum....... Yo dama jinin King Zuhair jinin Akka ai dole ya zama haka, su fa basu ɗaukar wasa a lamuransu, wai kun manta me Akka ta ce ne a kan jarumta?..........😅
Sosai Leesharh ta tsumaya da sauraron zazzaƙar muryarsa, tana naɗar duk abin da yake faɗa tana kuma jin daɗin yadda yake yin maganar one by one.
Bata bar wajen ba har sai da ta dai'na jin maganarsa alamar ya bar wajen kenan.
Cikin hanzari ta fito daga in da ta laɓe ɗin ta nufi room nata, jikinta sai kerma yake yi kamar wadda ta aikata wani abin rashin gaskiya....... Ko da yake rashin gaskiyar ai ta aikata tun da ta yi wa wani laɓe ta ji abin da yake faɗa.
Tana shiga ta haye saman gadonta tana sauke nannauyar ajiyar zuciya, kirjinta sai bugawa da sauri sauri yake yi. Zuciyarta sai harbawa pat, pat, pat, yake.
Wani irin razana ta yi jin vibrate na wayar dake ƙarƙashin pillownta, dama can a razane take tsabar rashin gaskiya, da wayar ta fara vuuu kuma sai ta kusa rugawa a guje.
Dafe kirjinta ya yi tana furta Hasbunallahu wani'imal wakil cikin rawar murya. A hankali ta kai kallonta kan pillown, jiki a sanyayye ta janyo pillows tare da ɗauko wayar. Da farko kamar ma ba zata ɗauki wayar ba, amma tuna cewa number ɗaya ce take kirarta a wayar kuma wannan number babban barazanace ga rayuwar mahaifinta yasa ta hakura ta janyo wayar.
Wani irin wahalallen yawu ta haɗiye lokacin da idanunta suka sauka a kan wannan number, ji take yi kamar ta maka wayar da ƙasa ko ta haɗiyi zuciya da mutu kawai huta, ta fara gajiya da fargaba da faɗuwar gabar da suke jefata a ciki, idan ta cigaba a haka wlh faduwar gaba ne zai zama sanadiyar rayuwarta.
Picking ta yi tare da kara wayar a kunnanta jiki kamar wadda aka zarewa laka.
Daga other side ɗin aka fara magana cikin sanyin murya. "A'isha na manta ne ban sanar dake wani abin ba, idan kin je wajen walimar nan ki mayar da hankalinki sosai a kan mutane, babu ruwanki da yin magana da kowa, sannan kada ki manta wajen a cike yake tab da camera's sosai".
A tunanin matar yanzu ne Leesharh zata tafi wajen walimar, bata san ita kam har ta je ta dawo ba abinta, zama ya gagareta a wajen walimar saboda rashin gaskiya.
Da kyar ta ɗan iya saita nutsuwarta tare da fara gayawa matar duk abin da ya faru tun daga zuwan ta wajen walimar har izuwa yanzu da take zaune a bakin bed dinta.
One thing about Leesharh yarinyar nan bata karya, kome zaka yi mata in dai zata buɗi baki ta yi magana to gaskiya zata faɗa, sai dai idan tasan gaskiyar bashi da amfani a wajen ko kuma tana tsoron faɗarsa kada ya zame mata illa to a nan kuma shiru zata yi sai dai a kashe ta, amma ba zata taɓa yin karya ba!!.
Wani irin sautin dariya ne ya fito daga ta cikin wayar, a hankali sautin yake tashi, da alama sun ji matuƙar daɗin news da Leesharh ɗin ta basu.
Shiru baiwar Allah ta yi tana sauraron dariyar matar har na tsawon minti ɗaya. Ɗan taɓe baki ta yi tana mamakin ko me ya sanya matar yin dariya? Ta tambayi kanta.
Ta shagala da tunane tunane ta tsinkayo muryar matar tana faɗin. "A'isha Allah ya yi maki albarka, ashe da rabon kin kusa komawa wajen babanki, yau kin gaya mun labari mai daɗi, amma kin tabbatar a guests house ɗinsa ya ce zasu yi zaman?".
Gyaɗa mata kai Leesharh ta yi tamkar tana a gabanta kafin ta ce e ta tabbatar.
"Good! Kenan Ramish zai fita gida kafin karfe takwas na dare, dan shi baya wasa da lokaci, hakan ma dai'dai ne, yanzu dai abin da nake so da ke shi ne, akwai wata magani da zan sanya a kawo maki, ko in ce ki fita ki je ki nemo wacece zata kai wa Ramish abincin dare? Idan kin dawo zan kiraki karfe 6 dai'dai dan na gaya maki a in da zaki ga wannan maganin, abin da nake so da ke lallai lallai ki shammaci mai kai mashi abincin nan ki zuba mashi wannan maganin a cikin cappuccinonsa, dan na san ko bai ci abinci ba tabbas ba zai fita daga gida ba tare da ya sha cappuccino ba, dan haka zai sha maganin kafin ya halarci wannan taron, idan kika yi komai cikin nuna taka tsantsan da kulawa tabbas gobe zan haɗaki da babanki a waya ku gaisa, idan komai ya tafi yadda muka tsara kam ma a cikin daren nan zaki bar gidan, kina barin gidan kuma sai ƙasarku zaki koma....."
Zubur ta miƙe tsaye tare da zaro idanu tana faɗin. "Aunty da gaske zaki haɗani da babana a waya? Kuma da gaske zan koma ƙasarmu?".
Tabbatar mata da hakan matar ta yi kafin ta katse kiran kit. Wani irin farinciki Leesharh ta ji ya rufeta, nan take ta ji kwarin gwiwa, tabbas in dai zata gaisa da mahaifinta a waya to ba shakka yanzu ba sai anjuma ba zata nemo waye zai kai wa Ramish abincin dare.
Lallai ba shakka matan nan sun san lagon Leesharh, sun san da cewa idan suka ce zasu haɗata da babanta to fa zata yi masu abin da suke so cikin sauri, basu zaɓota a kan wannan aiki haka kawai ba sai da suka tabbatar da lallai tana da jajircewa akan abu idan ta sanya kanta, in dai ta ce zata yi abu fa to wlh sai ta yi shi, haka take, sun san zata iya ne yasa suka fara, da sun san ba zata iya ba ba zasu fara wannan aikin da ita ba.
(Ni kuwa na ce tom Leesharh kada dai ki manta Our twin's Obaid and Omaid na Maman Sultan suna nan😌 ki bi dai a sannu.)
Miƙewa ta yi cikin kwarin gwiwa da azamarta har ta ji karfi ya zo mata ta nufi waje, sai murna take yi zata yi magana da babanta, sam bata san illar da abin da zata aikata zai haifar ba. Kasa ta sauko domin neman wacece zata kai mashi abincin dare kuma da wani lokaci zata kai mashi.
Tsabar rashin tsoron irin na yarinyar nan da muradin cin ma burinta karara a saman fuskarta, ba tare da shakkar komai ba ta tinkari kitchen ɗin dake ƙasa kai tsaye abinta, cikin jajircewa take yin komai tare da burin cinma nasara.......... Akwai kura kuwa ba kaɗan ba, kura mai tashi har sararin samaniya ma kuwa. Leesharh fa tana ganin kamar samun gane mai kaiwa Ramish abinci abu ne mai sauki a gareta! Sannan tana gani aiki mai sauki ne ta iya zuba mashi wani abin a cikin abinci ba tare da an gane ba! Ta manta da cewa a Abu Abdussalam empire take. To wai ma me zata zuba mashi? Me amfanin hakan? Kuma da alama so suke ya ci maganin kafin ya fita! Me suke nufi?.
🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️
GIDANSU KHADIJAH 💔😥
🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
Share fisabilillahi 👏
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍
🔥CROWN OF INJUSTICE🔥
𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡
❤️🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️🔥
(❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)
🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻
❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 11/9/2024.....✍️📚🌹
For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.
🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥
اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️
E____________49🔥
🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️
GIDANSU KHADIJAH 💔😥
Kai tsaye gida Maman Zainab ta nufo, ranta sai tafasa yake yi, tana tunanin hukuncin da ya dace ta yanke wa kanta.
Tun daga ɗan nesa da gate ɗin gidan nasu ta fara jiyo hayaniya a cikin gidan kamar gidan biki, kamar kuma gidan dambe ne ko filin yaki za'a ce ne oho.
Ruwan bala'i take ji ake ta zazzagawa wanda sam ta kasa iya tantance muryoyin su wanene?. Sai da ta shigo cikin gidan ne ta fahimci muryoyin masu yin maganar.
Wani irin sanyi ta ji a ranta jin suna hayaniya. A fili ta furta ku kashe kanku ma idan kun ga dama ƴan iskan kawai. Cikin parlourn ta shigo abinta. Kamar bata gansu ba ta wuce fa nufi saman sofa ta yi zaman, bata son shiga in da su Zainab suke ne, dan tasan ba shakka sai ta samesu suna kuka, Allah sarki bayin Allah, a duk lokacin da suka ji wannan bala'i na familyn baban nasu sai sun shiga cikin ɗaki sun sha kukansu son ransu, suna shiga tashin hankali, sam abin baya yi masu daɗi, ace kullum da familyn babansu da mahaifiyarsu basu shiri, kullum cikin faɗa kamar masu ganin hanjin junansu, abin kam babu daɗi kwata kwata.
Zama maman Zainab ɗin ta yi tare da zuba masu na mujiya tana kallon faɗar tasu, ta mayar da su Tv abinta.
Maman Haidar ce da maman Hanif sai Hajiyarsu suka zo, sun tasa Hauwa a gaba, Hajiyarsu sai tsinewa Hauwar albarka take yi, ita ma Maman Haidar yanzu da yake taga Hajiyarsu ta zo sai ta samu bakin zazzagawa Hauwar rashin kunya dai'dai gwargwado, domin a tunaninta Hajiyar tasu zata tare mata faɗa.
Sai da ina, Hauwa ai ba tayar baya bace, bata da mutunci kuma bata san mutunci ba, ka yi mata halacci ma ta ci amanarka bare kuma ka nuna mata iya shege? Ai wlh tsab zata warware maka zani ta yi maka zigidir a tsakar kasuwa, bata da albarka.
Da farko dai ta yi shiru tana jin Hajiyar tasu tana ta kwashe mata albarka tare da tsine mata bata ce komai ba, ta danne bata tanka ba. Amma da abin ya isheta sai ta fara zazzagawa Hajiyar tasu kwandon bala'in, ta yi wa Maman Haidar zazzajen attarugun masifa, ta haɗesu ta cinye masu mutuncin tas!!. Sai da suka yi tsit kamar waɗan da ruwa ta cinyesu!.
Baban Zainab dai bawan Allah ko sannu bai iya cewa ba, hakan ba ƙaramin konawa Hajiyarsu rai ya yi ba, har ta kusa yi mashi baki saboda bakinciki, ace wai ɗanka yana zaune wata ƴar gantali titi tana zaginka! Ai abin da ciwo over.
Ita kuwa Hauwa yadda kuka san daga tsatson fir'auna ta fito, tsabar rashin tarbiya har da cewa sai ta tsinke Hajiyar da mari har sai ta ga wuta yana bata taurari a face ɗinta.
Maman Zainab dai wannan abin ya sanyaya mata zuciya, duk wani tukukin bakinciki da ta kwaso daga wajen bokan nan sai ta ji ya gudu, ranta ya ɗan yi haske, ai dama maganin shege sai ɗan banza. Ta saki baki tana kallon film abinta, dan wannan bala'in da ake bugawa a cikin wannan gida film ne mai zaman kansa.
Hajiyarsu ce ta tambayi wacece Hauwa?. Baban Zee da bakinsa ya amsa mata da matarsa ce. Ai kuwa idan ran Hajiya ya kai dubu to sai da ya ɓaci a wannan lokaci, cikin fusata tare da bada umarni ta ce maza yanzun nan ba sai anjuma ba ya saki wannan maras albarka!.
Kai tsaye ya ce mata ba zai yiwu ba, babu saki a tsakaninsu, dan haka ba zai saketa ba, su fice su bar mashi gidansa ma tun ransa bai ɓaci ba, sun zo sun ɓatawa matarsa rai sun sa tana ta faɗa a banza.
Saura kaɗan Hajiyarsu ta yanke jiki ta faɗi ƙasa saboda mamaki game da bakinciki, ta san dai tun da take da baban Zee, tun da ya kai shekaru goma a duniya, ya fara mallakar hankalin kansa ba ta taɓa yin magana ya ce a'a ba, komai ta ce mashi da daɗi da ba daɗi hakura yake yi ya amsa mata da to, kuma ya aikata abin da ta ce ɗin cikin biyayya matuƙar bai saɓawa Allah ba, dan ba'a bin umarnin kowa a aikata saɓon Allah, ko alamar ɓacin ran baya so ma ba zaka gani a face ɗinsa ba, kawai zai aikata umarninta, amma yau rana tsaka shi da bakinsa da girmasa yake mayar mata da martani? Abin da bai taɓa yi tun yana yaro ba!.
Wannan abin ya gigitata kuma ya zame mata izina a rayuwarta, yau ta ga ayar Allah ƙarara. Shiru ta yi tana tunani, gani take yi laifinta ne, sam bata kawo a ranta cewa Hauwa ta asirce shi bane, faɗi take a cikin zuciyarta koma me ya yi a halin yanzu laifinta ne, bawan Allah mai biyayya, ta takurawa rayuwarta shi da familynsa, ta hana shi sakat, ta ɓata mashi farincikinsa bayan kuma shi kullum ƙoƙari yake yi ya ga ya sanya ta farinciki, ta cusa mashi damuwa da tunani, duk wani walwala da yake yi sai da ta toshe mashi wannan kofa ya dai'na samun yinta, yanzu ga shi tura ta kai shi bango har ya juyo yana iya kallonta ido cikin ido ya gaya mata ta ɓatawa matarsa rai dan haka ta fita mashi daga gida? Wato ya gaji da irin cin mutuncin da suka rinƙa yi wa Maman Zainab shiyasa yanzu ba zai bari su yi wa amaryarsa ba, yau ga ayar Allah ido da ido ta gani..... Ita fa take wannan tunanin a cikin zuciyarta.
Wannan ba aya ce ga iya Hajiyarsu ba, ina fatan ya zama izina a garemu mata gabakiɗaya, idan yaro yana yi maki biyayya, yana binki sau da kafa, to fa ki yi ƙoƙari kiga kin kyautata mashi kema, kuma ki yi ƙoƙari taya shi neman farincikinsa kamar yadda yake yi maki, in dai ba abin cutarwa kika ga zai aikata ba kada ki matsa mashi wajen ganin kin hana shi yi, zuciya wani lokaci wawan abu ne, kuma wannan ɗabiarmu ce mata, idan munga mutun yana yi mana biyayya yana kyautata mana sai kawai mu yi ta bashi umarni ba kakkautawa, komai sai mu nuna mashi iko, mu hana shi sakat, tabbas wannan ɗabi'ar kaso tamanin cikin ɗari na mata suna aikatata. Ki sani idan kika takura mashi, yana yi maki biyayya kika matsa mashi ke kuma, kika hana shi sakat da wasu umarninki da ba wahayi ne daga