Showing 186001 words to 189000 words out of 296878 words

Chapter 63 - RAWANIN ZALINCI BOOK 1 COMPLETE HAUSA NOVEL

20 Dec 2025

111

ta dawo kwana a ɗakinsu ba, ɗan iska saboda yana kalle kalle batsa kullum yana cikin ɗagawa kansa hankali, dole ya yi ta ƙoƙarin latsa ƴar mutane. A kullum idan Sadiq ya fara yi mashi nasiha a kan ya dai'na kallon film irin haka, to wlh faɗa ne yake biyowa baya, basu wanyewa lafiya, hakan yasa Sadiq ɗin yanzu bai ci bi ta kansa ba, ya sharesa kawai tun da baya ji kuma ai ba yaro bane shi, ya fi Sadiq ɗin shekaru da shekaru biyu, kamata ya yi ace shi yake yi wa su Sadiq ɗin faɗa da nasiha, amma ina, ina ma yaga hankali ne wannan kam, sai dai Allah ya kyauta.

Yanzu ma girgiza kai kawai Sadiq ɗin ya yi tare da nufar nasa gadon, already da alwalar barcinsa a tattare da shi, dan har ma ya kwanta mamarsa ta kirasa ya tashi ya fita, so yanzu yana dawowa addu'ar barci kawai ya yi tare da kashe wayarsa ya kwanta, ba jimawa barci ta yi awon gaba da shi.

A ɓangaren Khadija ita ma bayan ta yi sallar nafila raka'a biyu kamar yadda kawun nata ya ce, sannan ta rufe da shafai da witiri, hankalinta ya kara kwanciya sosai, ta ƙara samun nutsuwa sosai da sosai in da ta zo ta haye gadon ta kwanta, cikin ƙanƙanin lokaci barci ya ɗauketa, dama ita Zee already ta yi barci abinta.

Mamarsu kuwa, cikin kuka ta sanar da Aunty Hauwa halin da ake ciki. Hakuri Aunty Hauwar ta bata tare kuma da ce mata ta kwantar da hankalinta gobe da safe zata zo gidan, kada ta ji ta wani damu zasu yi maganin baban Zainab. Da haka dai ta rinƙa rarrashinta har ta hakura a nan barci ya yi awon gaba da ita, in takaice maku labari dai bata yi sallar mangariba bare isha, a haka barci ya saceta saboda kukan da ta sha.

(A gaskiya ina jin labarin gidansu Khadija tamkar true life story, wato tamkar gaskiya, wlh duk idan na zo rubuta part ɗin ji nake yi kamar gaske, saboda abu ne da yake faruwa yau da gobe a zahiriya sosai da sosai, Allah dai ka ƙara tsaremana imaninmu ka rabamu da ƙawaye jahilai.)

Washegari da safe kamar yadda suka saba haka Maman Zainab ta tashi tare da biyan bashin sallolin da suke a kanta na tun jiya, sannan ta nufi kitchen da nufin ta yi masu girki, kasancewar farar shinkafa da miya ta dafa masu daren jiya wadda basu ci ba, sai ta ɗauko shi ta sake ɗumama masu, saboda bai yi komai ba, kuma yana da yawan da bai kamata su zubar ba, so sai ta sake mayar da shi wuta ta ɗumama, shi ta sanyawa su Khadija a kulolin makarantarsu.

Suma su Khadijah suka yi wanka suka shirya kamar yadda suka saba, baban su ne kawai yaki fitowa, da yake dama sai maman Zainab ta haɗa mashi ruwan wanka sannan take tashinsa daga barci, to jiya dai ya rufe room door ɗinsa da key, koda ta kammala shirya masu komai kamar yadda ta saba ta nufi room ɗin nasa dan ta tashesa, sai ta ji kofar a rufe da key.

Kamar zata yi knocking, sai kuma ta hakura ganin cewa su Khadija suna nan, kuma tasan halinsa tun suna saurayi da budurwa, damone sarkin hakuri over, amma kuma idan ya zuciya wlh abin da zai sanya shi ya sauko ba karamar abu bace, kuma duk yadda yakai ga kawar da kai ga abu idan fa ya zuciya tura ta kai bango to fa mantawa yake yi da wata kawaici ko makamancin haka, yanzu haka a yadda yake cikin fushi sosai ɗin nan yana iya yi mata faɗa tatas sosai koda a gaban su Khadijah ɗin ne, zai manta da wani tarbiya.

Tuna hakan yasa ta fasa yin knocking na kofar ta juya izuwa nata room ɗin, bata sake bi ta kan su Khadijah ɗin bama ita ma. Bayin Allah da suka ga lokaci na ƙurewa zasu yi latti ga Khadijah suna dab da fara rubuta Exams, sai suka fito suka nufi wajen kawunsu Sadiq, dan ya kai su school kamar yadda ya saba, yau dai sun hakura da yin sallama da baban nasu tun da bai fito ba.

Knocking suka yi masu Sadiq a kofar ɗakin, ba'afi second ashirin ba sai ga Sadiq ɗin nan ya buɗe kofar ya fito. Shirye yake cikin dakakkiyar shaddar mai shegiyar kyau, da alama yau ma yana da class.

Har suna haɗa baki wajen cewa Uncle Sadiq ina kwana. Murmushi ya yi yana kallon Zainab sarkin tsiwa kafin ya amsa masu gaisuwar, yarinyar nan Zainab ba dai iyayi ba, haka take zama ta karewa maman Haidar da kakansu zagi fes kamar an aikota, bata da sauki, Khadija kam daga e sai a'a, sai kuma gyaɗa kai kamar ƙadangaruwa.

"Dama na shirya ku nake jira, ina da class karfe 7:30 dai'dai mu je ko?". Sadiq ya faɗa yana kai hannunsa ya ɗan bugi bakin Zee da take aikin turo shi kamar wadda aka zaga.

"Kai kawu Sadiq menayi maka to?". Ta faɗa tana ɗaure fuska.

Khadijah ce ta amsa mata da. "Kwaɗayin duka yake ji yasa ya dake ki, ko dai bai kai bane?".

Wani irin harara ta bi Khadija da shi. Shi dai Sadiq wucewa ya yi izuwa wajen mashin ɗin baban nasu, da yake key na a hannunsa, fito da mashin ɗin ya yi kamar yadda suka saba, ba ɓata lokaci ya ce su yi sauri su hau su tafi lokaci yana ƙurewa. Da sauri suka hau Zainab sai raki take yi. Da haka suka bar gida, shi kuwa Haidar yana can yana barcin asara, wani lokaci ma sai 10 yake tashi ya tafi kasuwa ko kuma wajen mamarsa or kakarsa, kullum aiki ɗaya, ya kusa yin aurema bai canza hali ba, ko waye zai ciyar mashi da matar idan ya yi auren? Shi da kasuwar ma sai yaga dama yake zuwa. Akwai matsala sosai, akwai case ba kaɗan ba.

Misalin karfe 9 dai'dai sai ga Aunty Hauwa ta nufo gidan kamar yadda ta faɗawa maman Zainab zata zo jiya. A lokacin baban Zainab bai fita ba, yana ciki, da alama yau ba zai je kasuwa da wuri ba, ita ma maman Zainab tana cikin ɗakinta ta yi zaman ƴan bori a saman tsakiyar gado, ta haɗa hannayenta ta buga uwar tagumi kamar wadda aka aikowa da wahayin yinsa, ta luluƙa duniyar tunanin ya zata yi da rayuwarta, har yanzu ta kasa iya gane cewa damar da Allah ya bata a baya ne take wasa da shi son ranta, tana yi kuma ba tare da godiya ga Allah ba, to yanzu damar tana neman kubce mata, ta kasa iya gane hakan ma bare ta yi ƙoƙarin dawo da damar izuwa gareta..... Tirƙashi, akwai matsala fa my people's, mu je dai zuwa.

A parlourn Aunty Hauwa ta zauna, ta tsantsara kwalliyarta cikin wata shegiyar lace mai kyan gaske, da alama ma case ɗin maman Zainab ɗin bai wani dameta ba, ta yi ɗaurin ture kaga tsiya a kanta irin yau ba mutuncin nan, sai wani kwaɓe fuska take yi kamar wadda taga kashi.

Fitowa maman Zainab ta yi daga room ɗinta cike da damuwar halin da take a ciki, tsawon shekarun nan da suka yi aure baban Zainab bai taɓa yi mata makamancin haka ba, har ya share tun jiya bai yi mata magana ba har yau, abin dole ya jefata cikin damuwa sosai, a maimakon ta kira mahaifiyarta ta sanar da ita abin da yake faruwa, sai ta sake kirawo Aunty Hauwa kuma.

"Hauwa ki zo mu shiga cikin bedroom, baban Zainab yana nan fa". Maman Zainab ta faɗa murya ƙasa ƙasa.

Okey Aunty Hauwa ta amsa tare da ɗaukar wata ƴar figaggiyar jakarta irin na dillalai, ga gyalenta dama a kafaɗa ta yafo shi kamar ba matar aure ba, burinta kawai su shiga ciki ta tambayi maman Zainab ɗin baban Zainab ya sha maganin? A ƙage take da ta ji ya sha ɗin ko bai sha ba?.
A haka ta miƙe da nufin su shiga cikin bedroom ɗin dan rashin hankali irin na maman Zainab da kuma damuwa da ya rufe mata idanu.

Tana miƙewa tsaye sai ga baban Zainab ya fito cikin shirinsa na shadda mai shegen kyau launin sky blue, ɗinkin manyan kaya ne, so ya ɗaura babbar rigar ma a sama, a takaice dai makurar shigar mutunci ya yi, da alama yau ma ba zai ci abincin maman Zainab ba, kamar dai daren jiya, dan dai ga shi ya kammala shirin fita abinsa.

"Sannu da fitowa, ina kwana?". Aunty Hauwa ta faɗa cikin sanyin murya.

Turus ya ja birki ya tsaya tare da juyo da kallonsa a kanta, wani irin faɗuwar gaba ya ji a lokacin da ya sauke idanunsa a kanta. Da ni da ku duka mun san cewa baban Zainab in ya shigo ya sami maman Zainab da bakuwa wlh ko kallon in da suke baya yi, baƙin suna gaishesa ma baya tsayawa, wani lokaci kafin ya amsa masu gaisuwar nasu ma ya kai bakin kofar ɗakinsa, amma yau sai ya tsaya tare da juyowa yana kallon Aunty Hauwa.

Maman Zainab ta ɗan yi mamaki, amma sai ta ce kila zai tambayi Aunty Hauwa ɗin ina ta je jiya ne, dan haka sai bata wani damu ba.

"Sannunki da zuwa Hauwa ya gida ya yara?". Ya faɗa yana bata full attention ɗinsa.

Murmushi ta sakar mashi kafin ta amsa mashi da komai lafiya lou.

Shiru ya ɗan tsaya tare da zuba mata idanu yana ta kallonta. Maman Zainab kuwa sai ta taɓe baki tana ganin abin kamar a Tv a gabanta, ita kuma Aunty Hauwa sai wani irin murmushi take yi mashi.

"Yanzu zaki tafi ne na kai ki gida?". Baban Zainab ya tambaya.

Wani irin zaro idanu maman Zainab ta yi, abin da bata taɓa ji ba, ba kuma ta taɓa gani a tattare da shi ba, kai ina bata yarda ba, a mafarki ta ɗauki abin, dan haka sai ta kai hannunta saman face ɗinta ta ɗan mari kumatunta wai idan mafarki take yi ma ta farka.

Amma ina sai ma ji da ta yi Aunty Hauwa tana cewa. "E zamu iya tafiya a tare duk da ba yanzu naso tafiya ba, amma tun da zaka mayar dani ai komawa ta kamani".

"To muje ko?". Ya faɗa yana mai cigaba da kallon face ɗinta sosai, sai wani uban murmushi take yi.

Maman Zainab bata ankara ba tana can tana tunanin mafarki take yi ne ko ba mafarki ba kawai sai ganin Aunty Hauwa ta yi sun jera da baban Zainab sun nufi wajen parlourn.

Ai bata san lokacin da ta bi bayansu ba, a harabar gidan ta ce. "Hauwa menene haka kuma?".

Dakatawa daga tafiyar da suke yi Aunty Hauwa ta yi tare da juyowa ga maman Zainab ɗin, ɗaure fuska ta yi sosai kafin ta ce. "Wacece kuma Hauwa? Ni kike kira ko dai wata?". Tashin hankali da ba'a sanya mashi date kenan!!.

Wani irin zaro idanu waje maman Zainab ta yi, tamkar idanunta zasu faɗo ƙasa, cikin tashin hankali ta ce. "Hauwa ban gane me kike faɗa ba? Ban gane me kike nufi ba? Ko dai kunnuwana sun dai'na ji ne? Ko dai har yanzu a cikin mafarki nake ne?".

Kallon baban Zainab Aunty Hauwar ta yi tare da cewa. "Abu Zee mu je ko? Bani da lokacin A'isha ni kam".

Da okey kawai ya amsa mata ba tare da ya kalli in da maman Zainab ɗin take tsaye ba, kamar bai taɓa saninta ba a duniya.... Tashin sense kenan yau ake yinta a wannan gidan.

Gaba Aunty Hauwa ta yi tana wani rangwaɗa tare da kara gaya mashi su je ita fa bata da lokacin maman Zainab a yanzu. Rufa mata baya ya yi da nufin su tafi ɗin.

Ai tsabar kishi da bakin ciki yasa Maman Zainab bata san lokacin da ta yi kukan kura ta damko wuyar Aunty Hauwar ba, idanunta sun rufe, wani irin bakin cikin take ji kamar zata haɗiyi zuciya ta mutu, wani irin cin amana ne wannan mai azaban raɗaɗin zafi haka?.

Cikin sauri baban Zainab ya fara ƙoƙarin kwatar Aunty Hauwar daga shaƙar da maman Zainab ta yi mata, da alama mafa baban Zainab ya manta wacece maman Zainab. Tirƙashi.

Maman Zainab kuwa ta shaƙeta da iya karfinta na karshe tana faɗin wlh sai ta kasheta, azzaluma maciyi amana, su taso a tare su yi karatu a tare, komai a tare suke yi ne zata nemi ta ci amanarta haka? To wlh ba zata barta ba, kasheta zata yi sai dai duk abin da zai faru ya faru.

Wani irin mari da baban Zainab ya sakar mata ne yasa bata san lokacin da ta saki wuyar Aunty Hauwar ba tana zunduma ihu kamar zararriya. Wani irin kukan kura ta sake yi ta................

Tashin hankali, akwai babbar cakwakiya na kin ƙarawa a wannan gidan, kenan Aunty Hauwa amanar maman Zainab ta ci? Ta kaita wajen malami da sunan samun mafita kenan kanta ta shiryawa hanya mai kyau ba maman Zainab ɗin ba?🤔 Ita kuma maman Zainab cikin rashin sani ta bashi maganin kaunar Aunty Hauwar da hannunta ya sha?🤔 Ga shi har da ƴaƴanta su Khadijah ta bawa suka sha dan rashin hankali da rashin tunani? To kenan ya makomarsu take su kuma? Suma zasu bi ayarin Aunty Hauwa kamar babansu kenan? Bala'in nan, wannan shi ne bala'i, akwai yaki gagarumi a cikin wannan gida, ya makomar maman Zainab? Farkoma ya makomar auren Aunty Hauwar? Da ni da ku dai duk mun san tana da aure? Alamu kuma sun nuna baban Zainab dai ya kamu da sonta, kuma ga dukkan alamu ita ma hakan take so, to ya kenan batun nata mijin?🤔 Ina su maman Haidar? Zasu yarda da hakan kuwa? Kada ku manta sun yi mashi mata fa a cikin family, lallai akwai rikici da rikita rikita, yau akan Aunty Hauwa baban Zainab ya mari Maman Zainab, tab duniya kenan, amana ta yi ƙaranci, ni dai PRINCESS TEEMA na haɗa kayana sai mun haɗe daku gobe dan jin yadda wannan bala'in yakin da ta tinkaromu zata kaya!! RAWANIN ZALINCI ya fara ɗaukar tafasa ma ba zafi ba, Zalunci ta ko'ina😥💔

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘



Share fisabilillahi 👏



ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍

🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍


🔥CROWN OF INJUSTICE🔥







𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡

❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥
(❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)






🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻




❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 13/8/2024.....✍️📚🌹




For information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥





اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️








E____________34🔥



Wani irin mari da baban Zainab ya sakar mata ne yasa bata san lokacin da ta saki wuyar Aunty Hauwar ba tana zunduma ihu kamar zararriya. Wani irin kukan kura ta sake yi ta damko wuyar Aunty Hauwar, idanunta sun rufe, ita dai ta kashe Aunty Hauwa kawai hankalinta ya kwanta.

A karo na biyu baban Zainab ya kara mata wani zazzafar mari, sai dai a wannan karon ko da ya mareta bata saki Hauwar ba, sai ma kara ƙanƙame wuyarta da ta yi, yadda ta ji zafin wannan mari haka ta kara shaƙe mata wuya gam.

Kafin baban Zainab ya samu ya kwaceta daga hannunta har Hauwa ta sume, saboda azaba, tasha shaƙar manya, ga shi cikin fushi aka yi mata shaƙar.

Fara ƙoƙarin dukan maman Zainab ɗin ya yi, amma ina, ai bata tsaya ya daketa ba, sai ma kwasawa da ta yi a guje ta nufi cikin kitchen, muciyar tuƙa tuwonta ya je ta ɗauko, hauka hauka ta nunawa baban Zainab a in da ta fara ƙoƙarin dukan Hauwa dake sume yashe a ƙasa da wannan muciya, ta sumar da ita ɗin ma ba zata kyaleta ba.

Da baban Zainab da ya ga haka sai shi ma ya sanya mata karfi da nufi ya yi mata duka ya kuma karewa Hauwa dake sume faɗar. Amma ina maman Zainab taki yarda ta bari ya sake ɗaura hannunsa a jikinta, sai zulle mashi take yi, shi kuma yaki barinta ko sau ɗaya ne ta kwalawa Hauwa wannan muciya da ta ɗauko.

Daga karshe dai ya yi nasarar kwace muciyar tare da kamata ya turata cikin ɗaki, ya kuma rufo kofar ta waje ya barota a ciki. Kamar zararriya haka ta rinƙa dukan kofar nan da iya karfinta na karshe, tamkar zata ɓalle kofar, hakan yasa Haidar ya farka daga barcin asararsa da yake yi.

Shi kuwa baban Zee bai ma sake bi ta kanta ba, ruwa kawai ya ɗebo a kitchen ya zo ya yayyafawa Hauwa ta farfaɗo. A haukace ta farfaɗo tana ambatar ta shiga uku yau zata mutu.

Hakuri ya fara bata kamar wani ɗanta, harda tsugunnawa a gabanta ya fara rarrashinta. Ji maman Zainab take yi zuciyarta zai iya fasa kirjinta ya fito waje, hakan yasa ta fara neman abin da zata karya wannan kofar da shi ta fito waje, yau ji take yi idan bata kashe Hauwa ba ba ita ba zaman lafiya, kada ku manta dama baban Zainab ya ce tana da balai'n kishi na wuce tunani, bare kuma ace irin wannan cin amana mai bala'in zafin da Hauwa ta yi mata ai dole ne ta haukace masu, kawarta ce fa da suka taso tun yarinta, duk da tun suna yara halinsu ya sha banban, amma hakan bai sa sun rabu ba, kawance ta ɗaure har girma izuwa aure, ace rana tsaka ta yi mata irin wannan ɗanyen aiki ɗanyen cin amana, ai dole zuciya ta sosu over.

Fatana a nan dai shi Allah yasa mata kun ɗauki darasi! Duk abin da yake faruwa da maman Zainab ita ta jawa kanta, kama daga abin da su maman Haidar suke yi mata har wadda Hauwa ta yi mata a yau, duk ita ce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login