Showing 189001 words to 192000 words out of 296878 words

Chapter 64 - RAWANIN ZALINCI BOOK 1 COMPLETE HAUSA NOVEL

20 Dec 2025

100

da laifi, ta ya za'ayi ki rinƙa sakin baki kina gayawa wata cewa mijinki yana kula dake hundred over hundred? Kuma sai ma ki rasa wadda zaki rinƙa gayawa hakan sai wadda ita mijin nata baya yi mata hakan, a haka kike tunanin zaki samu zaman lafiya? Ke kina tunanin cewa ai kawarki ce, kun taso tare ba zata ci amanarki ba, to ai ga shi nan kun gani ido da ido, ita tana can tana fama sai ta sha rana ta yi kasuwanci tukun nan ta iya biyawa kanta dukkannin buƙatun da take so, ke kuma kina daga kwance ake yi maki komai, sannan kizo kina bata labarin irin daɗin da kike ji ki ce ba zata yi tunanin ita ma bari ta yi join ɗinki kuci daɗin a tare ba? Waye baya son daɗi? Waye yake son wahala? Kin yi kuskure babba idan ma haka kike tunani, wata ma domin hasada da bakin cikin bata samun abin da kike samu ko ba zata auri mijin naki ta shigo kuci daɗin a tare ba zata yi duk yadda zata yi ta rabaki da mijin, idan kuma hakan bai samu ba to zata yi duk yadda zata yi ta ga ya dai'na kyautata maki kin koma wahala kamar ita.

Ai a zamanin yanzun nan duk yadda kuke tare da mutun da ya tambayeki ya mijinki? Alhdulillah kawai zaki ce mashi, daga wannan Alhdulillah ɗin kada ki kara kada ki rage, bakinki kanin kafarki, idan kuma kin ki ji to fa ba kyaki gani ba.

Idan muka koma muka yi duba da abin da yake a tsakaninta da su maman Haidar nan ma ita ta jawa kanta, domin kuwa ita ce nan tun farko ta sakewa Haidar ya san komai ɗinta da har yake kwasan sirrin gidan yana kaiwa kakarsa da kuma mahaifiyar tasa. Kunga ita ma maman Haidar ɗin ba samun jin daɗin nan wajen mijinta take yi ba, baban Zainab ɗin ne ma mai ciyar da ita, saboda mutuwar zuciya irin na mijinta, ai dole ita ma zata ji haushin bata samun abin da maman Zainab take samu, dole ta yi mata hasada da bakin ciki, shiyasa take zuga kakan su Khadijah dan kawai ta takurawa maman Zainab ɗin kuma ta ƙuntata mata. Yaushe zaki bari har familynsa su san irin kyautatawar da yake yi maki? Ai a irin haka ne ma wata daga cikin family zata maƙale ta ce idan ba shi ba ba zata yi aure ba, haka kina ji kina gani za'a sanya ya aurota kamar dai yadda kuka ga aya a kan maman Zainab. Ai ko mijinki ya ɗauko kaninsa ya kawo maki ki rike, sai ki san ta yadda zaki zauna da shi baki cuce shi ba kuma baki bari ya cuceki ba, kada ki yarda ki bari yasan cewa ga abin da yayansa yake yi maki, ki koyawa mijinki ko abu zai baki to ya baki tun daga cikin bedroom ba sai anzo parlourn bama bare har a kai ga tsakar gida. Fatana dai my people's kun ɗauki darasi na farko a kan maman Zainab?.

Sosai baban Zainab ya rarrashi Hauwa, sai kukan makirci da kisisina take yi, ita kuma maman Zainab tana can tana ƙoƙarin haɗiyar zuciya kofa yaki buɗewa. Tana ji tana gani baban Zainab dai ya saka Hauwa a gaba suka bar gidan, sai lallaɓata yake yi. Dama kun san shi ya iya sosai..........😅

Suna fita gidan Haidar kuma ya fito daga cikin nasu ɗakin, dukar kofar parlourn da maman Zee ke yi ne yasa ya farka, sai dai bai yi nasarar ganin menene ya faru ba, baban Zee ya ja Hauwa sun yi gaba. Ko da ya fito waje bai ga kowa a harabar gidan ba, ita ma Maman Zee a lokacin ta dai'na buga kofar parlourn ta kwasa a guje ta nufi cikin bedroom ɗinta, dan taga tafiyarsu ta window, sun riga sun fita, ko ta buga kofar ba amfani, dan haka sai ta kwasa da gudu ta yi cikin room ɗinta.

Jikinta har wani irin kerma yake yi saboda bakin ciki, wani irin zufar wahala yana tsastsafo mata a gabaɗaya face ɗinta, kuka take yi hawaye bibbiyu, idanunta sun yi jajir kamar wata ƴar shaye shaye. A gigice ta ɗauko wayarta, har wani yana yana take gani a cikin idanunta, bata ganin screen ɗin wayar da kyau saboda kuka.

Number mahaifiyarta ta fara kira a haukace, sai yanzu ta tuna da cewa ta kira mahaifiyar tata, da can duk bata tuna ba, sai da abu ya kwaɓe mata.

Bugu biyu mamar tata ta ɗauka. Cikin kuka ta fara faɗin. "Nashiga uku mama, na mutu na lalace Hauwa ta cuceni".

A gigice ƴar tsohuwa ta ce. "A'isha lafiyarki kuwa? Babu sallama sai ihu haka? Menene yake faruwa? Me Hauwa ɗin ta yi maki?". Da gaji maganar tsohuwar nan kasa ta firgice, baiwar Allah maman Zee ta ɗaga mata hankali babu shiri.

"Mama Hauwa ta cuceni, ta kaini wajen boka, da kai'na kuma tasa na bawa baban Zainab maganin da zai sota, da kuɗina kuma muka karɓo maganin, yanzu shikenan sonta yake, ga shi can ya ɗauketa sun tafi, na shiga ukuna, mama ki taimakeni kada na mutu". Yadda take maganar zaka fahimci cewa tabbas ba'a cikin hayyacinta take ba, bata ma san me bakinta yake faɗa ba, kawai sambatun surutai barkate take yi.

Ƙara rikicewa ƴar tsohuwar nan ta yi, sai cewa take yi. "A'isha ki nutsuwa ki yi mun magana a nutse ta yadda zan fahimta, yanzu ni bana iya gane komai da kike faɗe". Ita ma tana magana tana haɗe words, saboda a rikice take, kun san irin wannan call ɗin ma sai mai dakiyar zuciya yake iya jurewa baya suma, amma a kiraka irin haka ana kuka ga shi ba gari ɗaya kuke ba, baka san halin da ake ciki ba kuma baka san kan zance ba, in fact bata ma taɓa kiranka ta ce maka tana cikin wata damuwa ba, rana tsaka kawai ayi maka irin wannan kira ai dole bawa ya rikice, idan akwai abin da ya fi rikicewa ma yi zai yi.

Sai sambatu maman Zee take yi ta kasa iya nutsuwa, a haka dai ta kwashe duk abin da ya faru tun daga farko kan auren Khadija da Haidar har izuwa yau ta gayawa mamar tata, tana yi tana kuka hawaye bibbiyu.

Cikin tsananin tashin hankali mamar tata ta ce. "A'isha kin tabka baban kuskure da gyara shi zai yi matukar wahala a yanzu, da hankali da tunaninki har wata zata kaiki wajen wani boka? Shin bana duniyar ne da ba zaki kirani ki sanar da ni ga abin da yake faruwa ba? Ga halin da gidanki yake a ciki? Tun farko ma ban hana ki yin shawara da wata ba? Tun kuna yara na yi na yi na rabaki da Hauwar nan, amma kika ki rabuwa da ita, yanzu ba ga shi ta kai ki ta baroki ba, to ita ina ma mijinta yake? Da auren nata ta biyo baban Zainab ɗin kenan ne ko yaya?". Ta yi maganar cikin maƙurar ɓacin rai!.

"Mama bansani ba, ban san ina aurenta yake ba, ni dai kawai nasan dai tana da miji da yara, ni ba zuwa gidanta nake yi ba, nafi wata 8 ban leƙa gidanta da ƙafafuna ba, mama nashiga ukuna".

A ɗan fusace mamar ta ce mata. "Ai baki shiga uku bama tukun nan A'isha, ba dai shirka haɗa Allah da wani kika yi ba, laifi mafi girma a duniya, ai kin rinƙa shiga masifu kala kala kenan Allah ya kiyaye ba baki nake yi maki ba, amma wlh kin tabka baban kuskure, kuma abin da zan gaya maki a nan yanzu shi ne tun wuri ki fara istigifari kafin abin ya yi nisa ki fara fuskantar fushin Ubangiji, kin taɓa ganina da ko da sassaken itace na jiƙa na sha ne da zaki kama hanyar zuwa wajen boka? Wato duk nasihar da nake yi maki kullum abanza yake ko? Kishi haukace? To tun wuri ki yi gaggawar tuba, ki nutsu ki koma ga Allah, hankalinki ya dawo jikinki kafin mu san abin yi". Ta kai karshen maganar ranta a matuƙar ɓace sosai.

Kuka ne da ya ci karfinta yasa ta ƙasa iya amsa maganar maman, danasani ne kawai a cike a cikin ranta, nadamar sanin Hauwa a rayuwarta ne kawai ya cika mata zuciya. Sam bata san lokacin da mahaifiyar tata ta karaci yin faɗarta ta katse kiran ba. Ita dai ta luluƙa duniyar tunani mafita, a wajen ta sulale ƙasa ta kwanta tana mai cigaba da wani irin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro.

Shi kuwa Haidar dama can kun san ba shiri da ita yake yi ba, dan haka ko da ya ji kukanta ma tsaki ya ja ya koma cikin ɗaki abinsa, ya je ya haye gado ya cigaba da yin barcinsa, dama lokacin tashinsa bata yi ba, kawai sun tashesa ne.

Baban Zainab kuwa da yake ba yin kansa bane, abin hawa ya tara masu shi da Hauwa suka nufi gidanta, da alama ya manta da cewa tana da aure.... Tirƙashi, akwai cakwakiya kam ba kaɗan ba wlh.

🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️

🌼DUBAI🌼

Ɗaki mai matuƙar kyau aka kai Leesharh, tamkar ba ɗakin ƴar aiki ba, ya ji komai na more rayuwa, ga bed ɗinta ma katafare da shi, yana shinfiɗe da shinfiɗa ta alfarma, ita kaɗai ce a room ɗin, ba'a haɗata da kowa ba, ta ji matuƙar daɗin kasancewar ita kaɗai ga kuma room ɗin ya ji komai, ga wani haɗaɗɗen sanyin Ac dake ratsa jiki gwanin daɗi.

Ai tana shiga cikin room ɗin bayan Radia da Fadila sun fita, saman gadonta ta kwanta tana mai da numfashi, sai yanzu ta samu damar sauke nannauyar ajiyar zuciya, godiya ta yi wa Allah da ya kawota cikin irin wannan daula, addu'a kawai take yi da Allah ya bata nasara ta kammala aikinta cikin ƙanƙanin lokaci ta koma wajen babanta. Nan take kuma face ɗinta ya canza, tunawa da ta yi da irin aikin da ya kawota, duk sai ta ji ta shiga gagarumin damuwa, yanzu da gaske haka zata yi wannan aiki na leƙan asiri Ramish? Tukun nan ma waye shi? A ina kuma yake? Shi ma a wannan part ɗin yake ko yaya?.

Jin motsin an shigo mata cikin room ɗin nata ne yasa ta yi saurin kai kallonta zuwa bakin kofar shigowa. Fadila ce ta dawo ɗauke da akwatinta, ta je ta ɗauko mata ne.

Sannu da hutawa ta yi mata kafin ta ce mata ga akwatinki nan. Nagode Leesharh ta yi mata tare da binta da kallo, daga haka basu sake ce da juna ko sannu ba har ta ajiye mata akwatin ta fita waje.

Barci mai shegen daɗi ne ya ɗauki Leesharh, ba ita ta farka ba sai wurare karfe 1 na rana, kasancewar yanayin gidan baka iya gane rana ko dare ya yi sai dai ka duba time, sai ya zamana bata iya gane cewa wani lokaci bane a yanzu.

Miƙewa ta yi cikin kasala irin na mai barci ta nufi cikin toilet. Haɗaɗɗene toilet ɗin nata, ita a nata ganin sai take ga kamar wannan room ɗin ai dai'dai yake dana ƴar gida, saboda ta ga ya haɗu ne sosai, da alama ta mance a gidan waye take da har take ƙoƙarin haɗa room ɗinta dana ƴar gida, tab bata san duk wannan haɗuwa na room ɗin nata su shi suke kallo a matsayin na masu aiki ba, kila idan ta shiga bedroom na ƴar gida sumar tsaye zata yi dan haɗuwa.

Akwai komai a cikin toilet ɗin na buƙata, harta su kyawawan towels masu kyau na wanka, ga jacuzzinta ma mai ɗan girma da shi. Wanka ta fara yi kafin ta ɗauro alwala ta fito, tun asali ita Leesharh tana yawan son zama da alwala, shiyasa a duk lokacin da ta shiga toilet bata fitowa sai ta ɗauro alwala ko da ba lokacin yin sallah bane ba.

Akwaitin kayanta ta jawo bayan ta fito daga cikin toilet. Dukka Arabian dressing ne a ciki, daga dogayen riguna, sai riga da sket, riga da wando. Leesharh mayyar son riga da wando ce, tana da son yin gayu sosai, kawai halin babu da suke ciki ne yasa take hakura, amma idan ba haka ba tana da son yin gayu, lokacin da take gaban iyayenta mafiya yawan kayanta riguna da wanduna ne, ta ci gayu gwanin ban sha'awa, ga ta kyakkyawa kuma dirarriyar mace.

A yanzu ma riga da wando ta ɗauko tare da mayar da sauran kayan da ta fitar ciki. Riga da wandon sun haɗu makurar haɗuwa, Arabian dressing ne, wando ne mai kyau dogo har ƙasa, sai rigarsa da ya tsaya mata izuwa gwiwowinta, sannan wani ɗan ƙaramin veils mara girma sosai.

Da alama Leesharh ta jima a tare da larabawa, domin kuwa tsab ta iya dressing nasu ya zauna a jikinta da kyau da kyau, kamar wata balarabiyar gaske, a yanzu ma haka ta shirya cikin wannan kaya ta fita ras abinta, ta yi rolling veil ɗin nan a kanta kamar yadda suke yi, sai kyanta ya kara fitowa sosai.

Wayarta ta ɗauko ta kunna da nufin ta duba time, haka kawai ta tsinci kanta da shiga fargaba da faɗuwar gaba na kunna wayar, sai take jin kamar kada ta kunna wayar ta kyale shi a haka.

Amma haka ta kunna ta duba time. 2:5 pm. Ganin har karfe 2 ta ɗan wuce ne yasa ta zaro waɗan nan manya manyan idanun nata waje. Cikin hanzari ta miƙe tare da fara waige waigen ina ne gabas dan ta yi sallah?.

Sallamar da aka yi daga bayanta ne yasa ta yi saurin juyawa izuwa kofar shigowa room ɗin. Fadila ce ta shigo hannunta ɗauke da abinci a wani katuwar try, ɗazun ma ta kawo mata abincin, sai ta sameta tana barci, shi ne ta koma da abincin, yanzu kuma na rana ne ta kawo mata.

Fadila fa babbar budurwa ce wadda a kallah zata kai 25 year, amma saboda tarbiya irin na gida Abu Abdussalam yasa suma masu yi masu aiki suke ɗaukar kansu kamar dukka ƴan uwa ne, basu nuna banbanci ko fifikon shekaru, suna aiki a tare sun zama kamar ƴan uwan abin gwanin ban sha'awa, yanzu na tabbata kun ji sha'awar yadda Fadila bata nuna cewa ai ta fi Leesharh shekaru dan haka ba zata kawo mata abinci ba, da wasu ne za su ce sai dai ta zo da kanta ta ɗauka, amma a gidan Abu Abdussalam ba'a yin haka, masu yi masu aiki ma suna da tsari na bin doka haka ina kuma ga ƴan gida? Masu aiki ma an koya masu haɗin kai har haka ina kuma ga ƴan gida? Ya kuke tunanin haɗin kan ƴan gidan zai kasance?.

A saman carpet ta ajiye mata abincin tare da sake yi mata sannu da tashi daga barci. Kasancewar ita Leesharh tana under umarni da kashedi na kada ta kula kowa a cikin gidan, sai ya zamana ciki ciki ta amsawa Fadila ɗin, tana yi kuma tana kawar da kanta, dan a wawtarta hakan ce zata sanya ta yi nesa da ƴan aikin kada ta kulla abota da kowa.

Fadila kuwa, ta yi tunanin saboda Leesharh bakuwa ce yasa bata sake da ita ba, ta yi mata wannan uzurin, a in da ta ajiye mata abincin kawai tare da nufar kofar fita waje tana faɗin. "Idan kin kammala cin abincin zanzo na ɗaukeki mu je ki ga wasu gurare a cikin gidan, daga nan sai ki ga parlourn da zaki yi aiki a ciki, sai bedroom ɗin Aunty Sharifat da zaki rinƙa gyara mata, nata ita da Guyson, bedroom biyu ne kawai zaki rinƙa gyarawa, Ummie ta sanar da ni shi ne aikinki".

Nan ma ƙasa ƙasa Leesharh ta amsa mata da. "Okey amma dan Allah ina ce alkibla a wannan gida?".

Da hannu Fadila ta nuna mata gabas tare da sa kai ta fice abinta. Saman carpet ta yi tsaya ta fuskanci alkiblar, sannan ta tada sallah da iya wannan veil na kanta da ta yi rolling.

Bayan ta idar ta yi addu'oi sosai da sosai, lokacin da ta ɗauka tana zuba addu'ar ma ya fi lokacin da ta ɗauka wajen gabatar da sallar. Bayan ta shafa ta matso kusa da abincin nata, dama yunwa take ji, tun safe bata ci komai ba, sai kuka ƴaƴan hanjin cikinta suke yi.

Abincin ta fara zaɓar wanda zata ci, cikin nutsuwa ta zuba a cikin plate, ba ɓata lokaci hannu baka hannu kwarya ta fara cin abincin. Wani tunani ne ya faɗo mata, tunawa da yadda taga yawan Cameras tun daga kan titin da zai kawoka gidan nan har izuwa cikin gidan ta yi. A hanzarce ta ɗaga kanta sama ta fara neman camera a cikin room ɗin nata, dan ta tsorata, a tunaninta akwai camera, kada ya zamana duk abin da take yi masu gidan suna kallonta.

Ganin bata ga alamar camera a room ɗin bane yasa ta cigaba da cin abincinta tana tunanin yadda zata kaya mata a wannan gida.

After some minutes. Ta kammala ci tas, ta ci abincin sosai, sannan ta tattare komai kamar ba'a taɓa cin abinci a wajen ba, ta kwaso kayan abincin ta fito waje. Nan ta bar wayarta a saman bed ɗin tata, ita da aka ce ta ɓoye wannan wayar, kada ta fitar kowa ya gani, ta bari za'a bata wayar amfani a gidan, dan duk masu aikin gidan suna da wayoyi da Ummie ta saya masu wanda zasu iya kiran ƴan uwansu, haka tsarin gidan yake, amma ita Leesharh tun ba'a je ko'ina ba ta baro wayar sirrinta a saman bed wangalam ba sakayawa ta yi waje abinta.... Toh fah, akwai fa ƙura, da alama Leesharh dai ita da kanta zata tonawa kanta asiri a wawtarta da shiriritarta.

Fitowa haɗaɗɗen parlourn nasu ta yi, yadda part na masu aikin gidan yake ma sai ya baka sha'awa, parlourn ne haɗaɗɗe mai cike da komai na more rayuwa, sai bedroom manya manya guda huɗu a cikin parlourn a hawa na farko kenan, a na biyun ma hakan ne har karshe, so ƴan aikin da suke hawa na farko suna amfani da part ɗin, ƴan aiki na hawa na biyu ma haka, in da Leesharh zata yi aiki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login