Showing 12001 words to 15000 words out of 60071 words
yarinya tasa sai nakuma jika jikina wnd ko minti ashirin bankuma yi da wankaba
Muje xuwa BUF yanzu aka fara wasan
WAIWAYEWAIWAYE ADON TAFIYA
yaudai xamuji waye wnn BUF din dashi da DIAMOND'S FAMILY dinnan da ake ta gwagwar maya
BUF FAMILIES
Alhj UMMAR FAROOQ GIANT haifafen garin yola ne,malam musa modibbo shine mahaifinshi cancikin wasu kauyikan yola Wanda fulani ke rayuwa mafi aksarin arear suke.
arxiki ne na kin kari ALLAH ya ma wnn ahalin mlm Modibbo shanu gare shi wanda shi be san iya karsuba ga gidan gona suna noma su tumatir su albasa karas cocumber da sauran kayan lambu ga fannin kiwo kamarsu kaji talotalo jimina agwagi gist da sauransu
sun shahara sosai ta fannin arxiki dan ana shigowa daga can cikin jihar yola ana saran tumatir ana na gwangwani dashi da sauran kayan lambu
Company suka yi yar jejeniya cewa xairuka noma masu tumatir akan sari suna sara suna kaiwa ana saffarashi
dan danan modibbo arxikinshi yakara habbaka akasan MODIBBO ME GIDAN GONA inkashigo jahar yola da ka fadi wnn ahali xa a kaika har wnn kauye nasu
saidai dukkudin wnn bawan ALLAH yaki yashigo burni yayi,acewarshi ai gwamma ya zauna anan mahaifarshi dan birni kana shigarshi duniya xata rudeka kamanta da wani abu waishi xamunci
kusan dayawan yan kauye abun dake rudarsu kenan da sunshigo birni idonsu yabode sai kaga anyi watsi da zumunci duk da dai ba duka akataru akaxama daya ba
shikam gsky gwamma ya xauna cikin danginshi
Mlm musa modibbo yana da mata biyu Aisha da Bilkisu,Aisha ita ce uwar gd,tana da yaya uku biyu maza daya mace,ummar Farooq shine na farko sannan Ahmad na biyu sai karamar su Asiya tundaganan ALLAH be kara sa tasamu cikiba har aka yo mata amarya
sai dakin gwoggwo amarya (Balkisu)
tana da yaya biyar namiji daya Mata hudu Abdul hakeem, Amina,Maryam,fadimatu, Firdausi ,
Gida ne da yaginu cikin zaman lpy sbd me gidan yana da zafi baisan wargi dan duk wnd yace xaimai iya shege tofa xaimai hukunci dai dai da laifinshi
Modibbo mlm ne ta fannin addinin musulunci dan har kartu akanxo dauka wajenshi
ga kyauta da tausayi
dan wata xubin mahaifin BUF yakan ce halinshi kaf irinna mahaifinshi ne saidai shi yasoma yafi mahaifinnashi zafi
duk ya aurar da yn matan sai firdausi da dayake itace karama duk sunyi aure nan cikin yolan sai guda biyu da sukai aure daya a bauchi daya a gombe
Modibbo fa yabar maxan yynshi maza karatu
sbd wani alh dayaketa yi mai bayanin amfanin boko
gashi da arxiki in aka karanta boko zaifi dadi arika juyamai dukiyarshi tunda yagaynd companies ke sarrafa kayan lambun su
hakan yasa MODIBBO ya zage wajen bama yaya mazan ilimin boko amma duk da haka be kyalesu ba ta fannin addini saida ya cusa masu mahimmancin son addininsu fiye da boko karatun dasukayi yakara fito da sunan gdn har akemai lakabi da GIANT sbd gsky zuriar gidan modibbo akwai tsayi shi kanshi modibbo dogone sosaikakkarfa ga su kyawawa kyawu dai na fulanin asali
(Zandanyi bayani takaitacce akan wnn rayuwa da muke ciki wlh ynz anfi fifita ilimin xamani akan na addini.dan abun ynzu yahabbaka yr academy ta islamiyyunnan damuka samu ana ta budewa kirkiri xakaga anki asa yara wai hausawa sunfi yawa kawai ace addini ne yafiyawa amma b hausawa ba xa afake da hausawa.sai kaji uwa tace aiboko dashi xa aci ba da addiniba to ai ba ace kar kanemi duniya ba amma kanemeta daidai misali bawai kafifita bokon ba akan addininka sai kasamu ana biya ma yaro samada 30thousands kudin School fees amma ana biyan kudin isla miyya dari uku shima saikaga har koro yara ake akan dari biyun
Gsky mu gyara idan muna son ALLAH yashiga al al amarinmu shiyasa zakaga sai mutum yana campaign wai alokacin ne zai nemi jawo maka ayoyi tunda sunga kuru in musulmai sunfi yawa tobari ajawo ayoyi Dan ace kai wane ai yasan addininshi to kuma alokacin shima addinin xaitozar taka kamar ynd katozar tashi abaya wlh duk wnd ya toxarta addinin ALLAH bazai taba barinshi ba shima sai ya toxarta shi imma a duniya ne ko alahira YA ALLAH KASA MUDACE)
Ummar Farooq ya karanci fannin bzznss yayi digree dinsa har ya fara aiki awani company da suke sarin tumatir awajensu
gurin zuwa taron branch din company nsu da ke maiduguri anan yahadu da maimuna yarinyar manajan cmpany
Maimuna shuwa arab ce kyakkyawa ce ajinkarshe ga kudi itama da take takama ubanta nadashi
Gidansu suma suna dayawa ba laifi Dan matan babanta hudu
Kuma suna karatun boko sosai Dan yafima ratsa su akanna addinin Dan gdn yn boko ne nakarshe suna dadewa basuyi aure ba
Tunda takyalla ido taga ummar Farooq ai saitaji bawanda takeso sai shi
Kunsan yn boko basu dauki wai cema namiji suna sonshi a matsayin wani abuba
Koda dai addini be haramta hakanba
Shima Alhj UMMAR FAROOQ beyi wata wataba ya amince mata yana komawa gd yatura akai magana
Abu namasu kudi Dan danan akayi buki
Maimunata tare acikin tankamemen gdnta daya ke cikin garin yola
Alhj UMMAR FAROOQ beyi sankai ba duka yn kannanshi maza ya yayyankanmasu fili kusa dashi yace suzo suyi gininsu dmma besan irin tsarin da sukesoba daya Gina masu
Ahmad shikadai yake karantar likita yayin da Abdul yabi bayan babban yaya ummar yakaranci bzznss
Maimuna tana da wani hali na tsanar talakawa ga jarabar kishi kamar takashe ta
Saida xama yayi zama tukunna halinta ya bayyana
Kannenshi mata rannan sunje sugaisa da dan uwansu tamusu ibar albarka
harda zagi wai anzo acika mata gd
Sukan suna komawa suka fadima alhj modibbo dan dukka yn gidan modibbo yakaisu makka hadda asiya datake karama
modibbo fa ya fusata dama gashi da xafi
Gashi dama maimuna ba haihuwa takeba wai family planning tayi sbd karta haihu da wuri megd besaniba
harta kai su Ahmad da Abdul sunyi aure har sun haihu amma ummar shiru kake ji
Anfita dam aimuna kasar waje adubamata mahaifa akace inmbata daina planning ba to fa baxata iya haihuwa ba
cewa tayi kada likitan yagayawa mijinta Dan ALLAH
sunan kasar England din tace sudan huta kafin sukoma
dayake ambata bed rest saiya nema mata me aiki anan wata baturiya itace mom hanifa
Sunana xaune dayake company nin su ya sha hara wajen sarrafa tumatir anaija
dan har sun fara son buda branch akasar waje shine yayi amfani da wnn damar yacigaba da fafutukar bude masu branch din anan England din
abunka da kudi masu gdn rana dandanan akasama masu wani company shima na tomatoes
suka hada suke juyawa
Wnn shine musabbabin Dan xamansu a England Dan ambar ma ummar wnn fannin ya dunga kula dashi anan englan din
ana nan maimuna tasamu ciki saidai batai wani murnava wai ita batason tara yr ynz duk tabi tawani tsofe
Alhj UMMAR FAROOQ yayi farin cikin wnn ciki kamar zaiyi me harsadaka yadungayi
yabuga gida modibbo ma yai farin ciki amma yana mejin haushin maimuna na abin da tayi ma yayanshi ga kuma tsarin iyalin datayi duk yaje kunnanshi
kafewa tayi ita baxata koma naija ba saita haihu shikadai yayi tafiyarshi ganin gida yayin daya bata da mom hanifa
Mom hanifa mata ce mai maatukar hakuri da juriya ga ladabi ga son mutane itama tana da mijinta wanda basu taba haihuwaba gata da jarabar son yr
saidai ita bamasu irin kudinnan bane flawer ma take siyarwa mokotan su Alhj ummarce
tananan mijinta yarasu tayi kuka kamar me harta hakura shine Alhj ya roketa kozata rika taimakawa matarshi da Dan ayyuka ambata bed rest
tace bakomai yahanata saida flawer yana Mata komai wnn shine musabbabin zaman mom hanifa a hannun Alhj UMMAR FAROOQ
maimuna watan haihuwarta yakama ALLAH yataimaketa tahaihu lpy ta haifi danta namiji a babban asibitin dake yankinsu anan England din
farinciki kamar me agurin UMAR FARUK amma ita kadaran kadaham mom hanifa harta fita murna
yarofa kyakkyawa kamar sace shi ganauyi dan da akayi weight dinshi Saida yakai wajen 6kg turawa har daukarshi akai dayake yazo ranar mother's day shima anbuga shi ajarida cikin jariran shekarar
Anfara shirye shiryen komawa gd suna dan. cewa akai kada wnd yazo gasunan dawowa anan xa ayi suna
Mezai faru ai suna dawo wa suka tadda modibbo ya rangadawa Alhj ummar amarya
habawa maimuna hauakane kawai bataiba Dan sunan ma gdnsu akayi
Alhj UMMAR FAROOQ kuwa be wani damu ba bayan kwana biyu aka kaishi gun yr bafullatanan amryarshi me kyau da ita
Maimuna kuwa abun har ya shafi yaron da ta haifa me suna BILAL
ALLAH yaso da mom hanifa aka taho ita taita renonshi wata xubin kinbashi nono ma take saidai tace mom hanifa tabashi madara wai xuwanshi duniya kaddararshi harta fara zuwa mata mara kyau kujihauka
Saida mahaifiyar ta tamata da gsk tukun take kula yaron
mahaifinta ne yadawo daita badan tasoba
Wai ita tafi karfin xama da kishiya
Allah SARKI Rashida amaryar me hankali bata ma kulata intana haukanta kishin saurin ta duk suka komama Rashida sbd mutuncinta
Aiko ina wutar sakasu Wai muna fukaine sun hade Mata kai
dole tasa yaraba masu gd
Tashin farko Rashida tahaifi namiji haihuwarta ta farko kamin shekara biyu tayi yaya biyu nabiyun ma namijine
Bilal ya girma amma yafi sabawa da mom hanifa Dan uwar bata cika kualshi ba
itama maimuna ta kara haihuwa tahaifi namiji aka ma modibbo takwara musa anace mai hibban takuma kara wata haihuwa akasa mai ridwan
nakarshe da tai aka samu mace habawa zokiga doki gurin yarinya kamar xa alasheta
Duk da dai uwar tana nuna tafi son ridwan kirikiri Wai hibban sunan modibo yaci shiyasa bata cika wani sonshiba amma duk da haka tafi sonsu akan Bilal
Naseer shine baban yaron aunty amarya Rashida sai na biyu Hamza itama daganan bawanda yasake haihuawa cikinsu
Anan aka kara replacing din Alhj UMMAR FAROOQ a England amatsayin directo na company sai sukayi parkin suka koma England can duk akasa yaran makaranta Bilal dama yayi nisa saidai akamai transfer
zaman lpy yadan wadatu balaifi sakamakon bore da Alh yayiwa duk wcce takara tada mai hankali agd nan ba naija bane ehe
Saida sukai shekara biyar tukanna suka dawo naija kwata kwata Alhj UMMAR yabude nashi cmpny
Bilal aka bari acan sbd karatunshi yayi nisa gashi likita yake karanta
saidai ak juyo da sauran yaran gd
shikuma aka bash shi da mom hanifarshi dama ita taci fitsarinshi da kashinshi tsakinin shi da uwarshi bawani sabo bane sosai
Saida ya zama kwrren liktan fata tuknn yadiro naija
anyi murnar dawowrshi gd don daddy har walima yamai
Ananan yanemi sojan sama suka bashi short service sbd ganin kwalinshi me tsadane
wata shidda yayi yayi passin out da mukami babba
Maimuna mommy kenan tadan sauya ba kamar daba tunda tana nunamai so yanzu sosai saidai tamakaro sabo ai bawasaba
saidai matsayi na uwa da ba acanxawa kawai
BILAL UMMAR FAROOQ (BUF)
Shine ckakken sunan shi daga baya yashiga wrestling shima sbd tun yaa yaro yake sha awarshi sosai Dan inyau aka fito da wrestling sai yasai plate din
yashiga wrestling ne ta hanyar mom hanifa
Dan da abun yayi kamari har tiket yake yanka yashiga kallon ido da ido
ahaka har yafara wasn shima yakuma shiga da kafar dama Dan Buf ALLAH yamai kirar karfi kamarme ahankali har kugiyar wrestling tasan dashi aka bashi tankamemen fili shine yayi wnn mahaukacin Mansion din
Wnn shine tarihin BUF
________________________
ABIN YABO BOOKSHOP
Kasuwar Rimi Kano
Tel: 07038339244
SANADIN SON BANZA
By:
Shamsiyya Daheeru
(((12)))
ASALIN ABUN DA YA FARU A SABUWAR SHEKARAR
In baku mantaba BUF gidansu duk maza ne mace daya ce aka haifa a gidan kuma mahaifiyar BUF ta haife ta
Sunan ta RUKAYYAH
suna ce mata pretty
Kyakkyawa ce
sai dai duk mazan sunfita kyau
ita fara ce tass sabanin maxan dasuke da surki da jaja jaja
RUKAYYAH tA ta shi cikin gata,kowa gidnn rukayya Buf na kan iya cewa rankatakaf yafi sonta dan dayaji kukanta tofa xaka ganshi a gun
itama harta fara sabawa dashi da mom hanifa
koda zasu dawo naija da kyar tayadda tabiyosu
uwar nason rukayya sosai amma fa bakamar ridwan ba
shiyasa yake tsula tsiyarshi son ranshi
Rukayya tatasa tazama yan mata TUBAR KALLAH
ai sai ta ce atafau tunda yaya BUF dinta yaxo to in zai koma da ita zaikoma
alokacin aka karama Buf girma aka nadashi shugaban sojojin sama
anyi budiri kamar me modibbo shanu yayi ta yankawa kamar me kyauta kam anyita kamar za akarar da dukiya
modibbo ya jinjina ma BUF sosai
gashi da son zumunci dan inyaxo komai saurinshi saiya je kauye ya gaidA modibbo
yayi tafama da modibbo ya maigini yadawo cikin gari amma fur yaki ya dawo
lo kacin daya juya England da akamai karin girma bai fara wrestling ba
kuma baa gina MANSION ba
yadaiyi wani gida mai kyau hawa daya wnd a ynz yazama Guest house din shi
gidan da mahaifinshi suka zauna na company ne
shiyasa ynz ya gina nashi yatashi duk da ba korar shi akai ba
Yadauko mom hanifa yadawo da ita
toynz ga sis rukayya tanace sai ta biyoshi
uwarsu taita balai wai baxata bamma baturiya yaya har biyu ba aiba ita ta haifa mawaba
rukayya ta tabure fa saita bishi uwar ta zugata amma taki
mahaifin yace tsbishi tayi hutun sabuwar shekara da za ai inyaso inzai dawo bikin sabuwar shekarar sai sutaho tare harda mom hanifa
wnn yasa BUF yatafi dA rukayyah
shiru har kusan shekara nawa haryayankan mata form tafara jamia
uwar tayi balain har tagaji
ahaka har yashiga wrestling kowa yasAn Buf yasan rukayys
yana zuwa naija amma rukayya bata binshi gudun kada momy tahanata da wowaa
ginin Mansion da akayi Saida ya gina mata side dinta har biyu
daya a inda yayima iya yenshi acan sama daya akasa
rukayya Buf naji da ita sosai dan wata zubin intace batason abu toko yanaso yabarshi
haka inyace beso to intanaso sai anyi
karatun addini yane man mata malami balarabe
me suna
Sheik abbss ibn abbass
dayake kanin abokinshi ne da suka hadu a makka dayaje
rukayya kuwa tuni ya kaita ta sauke farali
ansa date din taron lunch ing din bude wnn mahaukacin Mansion da yayi
mutane sun halarci taronnan kamar hauka
Yn wrestling ne, sojoji,likitoci kai abun ba a magana
a naija kuwa hardasu MODIBBO da matanshi su Hjy Aisha da balkisu
Yn jarido sai daukar mansion suke anata yayatawa
Rukayya ita tayanka xaren lunching din
akasa mata tafi kai bukin ya kayatar
dama kuma ya gayyoto malamai sunmai addu oi sosai yayi sadaka ya je gdn marayu ya gina masallatai da bohole a naija kamar hauka
duk inda yaje sai yace yana baran addua akan ayyukanshi addua kuwa yana shanta sai dai fatan ALLAH ya karba Alhj BUF
gsky mansion yakeru ko ta ina side din rukayya nasama dana kasa ankasan mai nera dan kuwa tayi kuka
uwar BUF datashiga mansion dinnan ai sai kai ya kara girma
Dan kowa saida ystafi yabarta
Dan cewa tayi saita huta
sai da tayi kusan sati tukun tafara shirin komawa lokacin tadan fara hure ma rukayya kunne tana wai ta gujeta tana matsayin uwarta ynz harta fison baturiya ko akanta
hakan datake fadi yadan karyama rukayya zuciya tace tom xata bita Amma sabuwar shekarar nan da zamu shiga zata dawo uwar tace tom yanda dai kikace
gashi zanje meduguri indauko safna da ummita xasu dawo gurina da zama kwatakwata ai sai takara samata son xuwa
dama duk sa oi ne itada su
to da zasu tafi tacema BUF zata bi Mom bai musa Mata ba
saboda yaga ta da de basuje naijaba
A jirginshi na prvt da ya mallaka da kudinshi ya shirya masu tafiyar da tsaraba niki niki
da zata tafi saida tarike rigar Buf tana wani irin kuka mai ban tausayi Buf shima abun yataba mai xuciya yarungumeta yana sorry rukayya innazo a sabuwar shekarar ba sai mudawoba
Kinga nima ina yawan xuwa akai akai kodannauyin da yake kaina nashuga bancin da ka bani
tace bro wlh gabana fadi yake sai inga kamar bazan sake haduwa dakaiba
shima fa Buf dauriyar kawai yake donshi tun jiya yake jin faduwar gaba mai tsanani
yace inkinji irin haka kidunga addua tace to bro
kayafe mun duk abun da naimaka yai saurin kallonta da idonshi da ya kada yayi ja
yace daina fadin hakamana my pretty keda nakeson kiyi karatu kizama kwararrar lauya
INSHAALLAH
tayi murmushi tace tom bro aikasan ALLAH yace dukkan merai mamacine
tokaga dole karika tunawa da ita ako dayaushe
yace hakane amma bazaki mutu yanzuba INSHAALLAH
murmushi tayi tace nidai kace kayafemun mom hanifa na gefe tsoron mom yahanata karasowa har ita saida suka bata tausayi dayake da turanci suke magna dan zamansu a England
turanci yakama bakinsu kamar dashi aka haifesu
dakyar dai suka rabu saida mom taita sababinta tukunna suka bar juna
sun isa naija da wuri kowa yayi murnar ganin rukayya musamman su ridwan donsuma suna sonta ba laifi
YAU MUKA SHIGA SABUWAR SHEKARA
Ko ina kaduba murna ake musamman gdn da akwai yan boko,boko kuma ta ginu a gdn
gidansu Buf yana daya daga cikin wnd ake murnar zagayowar shekara musamman wnd date of birth dinsu zai ka sance a January
gidan kusan mutane biyar zasuyi birthday a family n a wnn watn na sabuwar shekara
ankama hall babba domin duk an hada birthday din rana daya ga dukkan masuyi
antanaji abubuwan more rayuwa kalakala Buf yace suyi komai duk tsadarshi amai calculation zai turomasu da kudi
mahaifinsu yaso ya hana don gsky yace bidia ne
dan da kyar ya yadda Amma yace banda cakuduwa maza da mata a hall din mata bazasuba
wacce natayakams ranar ta hakuradan baza a mai agd ba
duk da yn matan yaran kannanshine dan shi rukayya kadai ya haifa
sai hakan yaso yazama tsegumi saida aka tsawatar
anyi angama bukukuwan lpy
RUKAYYAH tace xata ta gaida modibbo
yan uwan tai ma magana kowa yace shi yagaji taje kawai su xasu daga baya
haka daddy yamata tsaraba nikiniki tatafi mommy kuwa bakin ciki kamar me Dan me rukayya zatace zata kauye
itadai rukayya bata kulataba sai shirinta take
Saida tagama tace mom kiyi hakuri mana modibbo fa zanje gaisarwa
tace to da sharadi kwana daya zakiyi ta ce to mom ALLAH ya nuna mana goben lpy sai indawo
da xata tafisaida tanemi ya fiyar kowa tukunna takama hny
taduki wayarta da BUF yasaimata SAMSUNG NOTE 9
takira modibbo tana hanya sabis yaki shiga haka ta hakura
tafiyar da dan nisa daga ciki garin yola xuwa kauyen Dan sai anwuwwuce ya kauyi ka kusan biyar ana shidanne zasu je nasu
acikin xauciyarta tace wnn tsohon da kafiya yana da kudin da zaizo yayi gini abirni Amma yaki ai ko sudaddy sa mai ginin amma kirikiri yakafe shi abarshi a mahaifarshi kai wohoho ni modibbo ko
tana ta magana azuciyarta sun