Showing 36001 words to 39000 words out of 39506 words

Chapter 13 - MATAR SO BOOK 2

06 Sep 2025

3200

Murmushi yayi sannan yace.
"Ai abubuwan ne sai a hankali kuma bama son mu dawo da Yunus a yanda muka same shin nan kar Yar uwanku tace batayi."
D'ago kai tayi tana shafa fuskarshi cikin salonta tace.
"A duniya babu namijin da zai iya samun maryam Sajida ta bashi soyayyarda tabawa Yunus ko yaya kuka kawo mata shi zata amshe shi hannu biyu."
Zuge zip ɗinta yayi ta kalli cikin idanunshi, hmm tace a rainta jaraba an dawo.
Shafin soyayyar Aman da Rahilah ai ba sauki.

....... Haka ma ya faru a gidan Ahmad tunda ya shiga ya sami Rahimah, ta bashi abinci yaci kaɗan yace.
"Nifa ba wannan yunwar nake ji ba."
Tun da ya faɗi haka, san abinda yake nufi lallaɓa yaranta tayi Ta kunna musu tap suna game, rufe kofar kitchin tayi sannan ta koma ɗakinta ta gyara jiknta tabi Ahmad. Jirgin soyayyar suma suka haye.

****
Haka kawai aka sani a gaba da maganin mata, tun bayan komawar Aunty Gausiya aka shiga ɗura min magani, ga Mai gyaran jiki, kullum sai tazo an gyara min, kai an buwayi rayuwata gabaki ɗaya.
Kamar na fasa ihu haka nake ji.
Sai da aka samu kusan wata biyu ana abu ɗaya, ranar jumma'a na tafi makaranta, na shigo a gajiye, na shaki kamshin da ya kusan tarwatsa min zuciyata, a hankali na shiga gidan banga alaman komi ba, yaran ma ba ji, hayaniyarsu ba. Ɗakinmu na wucce nayi wanka na kwanta dan yau nake tsamanin bakona zai ɗauke,

Can wajen magarib sai ga yaran a guje sun shiga ɗakin Umma bana nan suka leka na Mama ma haka, shine suka shigo ɗakinmu. Suka zuɓe a kaina kallonsu nayi, nace.
"Yaran Mamansu ina kuka je."
Jan hannuna sukayi da na mike, dole nasaka hijab na bisu, har falon baki.
Anan zuciyata ta tsinke, sabida kamshin Yunus, a hankali na shiga ciki yana tsaye jikin window dake kallon harabar waje. Gani nake kaman gizo yake min, kallon yaran nayi da suka isa gurinshi da gudu suna cewa.
"Dadyy." dan haka nake faɗa musu daddy duk namiji daddyne.
Juyowa yayi, ya durkusa a gabansu yana shafa fuskarsu.
Mutuwar tsaye nayi, ina kallon Yunus,, ɗago kanshi yayi ya kalle ni, murmushi yayi sannan ya mike, tare da ɗaukarsu duk biyu, ya iso gabana. Ja da baya nayi har muka kure bangon ɗakin, rungume mu yayi baki ɗaya.
Muryanshi can kasa yace.
"Duk nawa ne wannan."
Kukan da nake haɗiyewa ne na sake, a hankali tare da gyaɗa mishi kaina nace.
"Duk nakane har da Mahaifiyarsu."
Sauke yaran yayi ya ciro chocolet ya mika musu yace.
"Maxa ku kaiwa Umma tasha."

Suna fita, ya tallabi fuskana da hannunshi, yace.
"Maryam sai kuma kika ji labarin na mutu."
Janye hannunshi nayi, nakifa kaina a kirjinshi ina kuka, bani da wani bakin magana, kallonshi nake ina shafa fuskarshi nace.
"Ai ban yarda ka mutu ba, dan zuciyata bata aminta da haka ba,"
" Nidai abinda nasani shine, na shiga garari adalilin rashinka kuma da nace zaka dawo karyatani akayi ana min kallon na haukace. Daddy kaine cikon rayuwata, bansan ina sonka ba sai da kayi nisa dainda nake nasan cewa kaine rayuwata."
Rungume ni yayi kamar wani zai kwace ni.

Mun jema sosai a haka, kafin yace.
"Maryam zaki iya zama dani kuwa, kinga yanda na koma fa?"
Murmushi nayi nace.
"Yunus nake so ba wani ba, dan haka ni bani da damuwa ina son Haske rayuwata haka."
Haɗa fuskarmu yayi, yana goga hancina da nashi. Yace.
"Maryam zan wucce dake gida, ins kewarki sosai."
ɗaga kaina nayi, ina murmushi nace.
"A'a kabari dai su umma su maidani da kansu."
"Toh ki barni mu gaisa a nan."
"A'a baza'a kuma dani ba ga nifa ma ina hutun sallah."
Na faɗi haka ne dan ya kyale ni wallahi bazan iya jaraba ba.
"Toh taimaka ki min wani abu."
Kaman ban fahimce mi yake nufi ba nace.
"Dame fa, Yunus."
Jan bakina yayi yace.
"Yanzun zaki gani."
Hannunshi ya tura a rigar nayi maza na rike nace.
"Karka taɓa amanar H² kaga babu daɗi na bari a ci amanansu."
Dariya yayi dakyar na lallaɓashi muka rabu lafiya.

.......Tunda ya dawo kullum yana, zarya a gidanmu sannan ya kwashi yaranshi su tafi yawo, ina fama kintsa kayanmu da zan koma, dan yace ya dawo da sauran matanshi Saura nice.
Sosai Umma da Mama da Rahilah suke haɗa min zafi, sai da na fara fita hayacina dan maganin karfine dasu, wasu wanda Rahimah takawo min daga, turaren tsuguno daga India Uwar mijinta ta kawo mata, sai wani na sha, haka kawai suka sani jin desires ɗin dole.

Ranar jumma'a aka mai dani ɗakina nida Yarana,

Bayan tafiyarsu Aunty Hamdiya, shima ya shigo, ya taramu a falo mu huɗu sai Yaran da suka haye mishi jiki, Balkisu da Fareeda na dariya, ina gefen Aneesah wacce har yanzun bata nutsu ba.
Nasiha yayi mana akan zamanmu na baya da kuma kurakuran da ya aikata, ya rokemu da mu yafe mishi. Sannan yace za'a raba kwanaki ɗa'ɗaya, sannan ya kara da cewa.
"Maryam Idan baki manta ba, kinyiwa Fareeda da Balkisu alkawarin basu..."
"Ai dama Yaransu ne, dan ko da ake maganar auren Sulaiman niyyata na yayesu, na mika musu. Sune iyayensu ni bani da haufi na barnusu Yaran duniya da lahira."

"Madalla da samun mace tagari kuma nagartacciya, mai zuciyar zinari, Allah ya albarkaci rayuwarki."
Kallon Fareeda nayi cike da tausayinta, dama kuma yaran sukan je gurinta ko tazo ta ɗaukesu, balkisu kuma bata wata guda, bata zo kaduna dubasu ba,dan haka suna gaba tsalle a jikin Uban suka koma kansu.
Hassan da barna ya tsikawa Balkisu ɗan abin wuyarta ta gwal, murmushi tayi ta sumbaci goshinsa tace.
"Wata rana zaka saya min sama da wanda ka tsinka."
Taɓe bakina nayi na zubawa mijina ido, ina wani lumshe su. Duk abinda nake yana gani, amma dan a zauna lafiya bai wani damu ba asalima jaddada mana zaman lafiya yayi kafin aka kawo abinci wanda Fareeda ta girka, muka ci.

Allah sarki huda na makaranta kamar tayi tsuntsuwa, a wannan shekaran zata gama. Mufeeda kuma tana gabansu hajiya yarinyar ta nutsu.

****
Yau wata biyu kenan da akayi wani kazamin hatsari a hanyar yola, kowa ansami danginshi amma banda sulaiman, karshe saka hotonshi akayi a network news, anan Alhaji yaganshi.

Tunda Mama kilishi ta ganshi zata mike Alhaji ya maida ita, yace.
"Na yarda da tarbiyan da nabawa Yarana shaiɗan ne ya shiga rayuwarshi, ki yafe mishi Allah zai sassauta mishi bari gobe ns kira Yunus da abokanshi su tafi yolan.""

Kuka tasaka tace.
"Wallahi na yafe mishi ina mamakin halayarshine, amma ya wucce."


Lallaɓa ta yayi, har suka kwanta.
.......A bangarenmu kuwa ban san iya adadin lokacin da muka ɓata muna hira inda yske bamu labarin rayuwar gidan kaso ba, sai da na shafa wayata, naga karfe biyu saura, mikewa nayi nace.
"Bayin Allah da alkhairi."
Na wucce sama, dariya Balkisu tayi tace.
"Fareeda nima na gudu, dan nan gaba Maryam kuka da tasaka mana mun riƙe mata miji."

Dukkansu suka miƙe suka hauro sama, shi kuma ya shige ɗakinshi yayi wanka. Sosai sannan yasaka kayan barci ya fito ya kashe komi na gidan, ya hauro sama.
Ya shigo yasame ni, nayi wanka na kwanta, kunna wutar d'akin yayi yazo har inda nake.

"Ya muna hira kika gudu?"
"Hiran ce ba karewa zata yi ba, kuma ai sai a bani mijina, tunda ka jima da dawo dasu, nima sai a barni na mori mijina ko."

Janyoni yayi na shige jikinshi, sumbatar bakina yayi, ya sauko har.....
Daga nan kuma Tsohuwar soyayya da kewar juna, suka motsa..
****
Washi gari Balkisu ce tayi abin karyawa, tare da taimakom Fareeda, suna gamawa suka ajera a falon akan kafet ɗin cin abinci.

Sannan suka koma ɗakinsu sukayi wanka,
Taɓani yayi cikin zolaya yace.
"Keee Harija tashi."
Dariya ya bani har ina rike cikina nace.
"Toh Hariji, ai sunan da ya dace dakai kenan, tunda tun 2:30 ake abu har 4:02,,, kuma tsakaninka da Allah sau nawa ina ce maka na gaji, amma cewa kake Wallahi yanzun kake jin lafiya. Dake kasaba ka moreni kace min Bby."
Daukar pillow yayi ya wurga yana zare ido yace.
"Amma yarinyar nan kin gama dani, zo ki faɗa min, saunawa kika sauya."
Juya idanuna nayi, bayan na zare rigar da nayi sallah dashi nace.
"Oho dai, ko sau dubu na sauya salon tafiyar waye yake riƙe da linzamin, idan ka isa ka kamani, akoma ruwa ni yanzun karfi nake ji kai kuma basir ya cinye ka."

Nayi ban ɗaki a guje. Bai fasa bina ba kuwa, dan sai da ya nuna min yanda basir ta cinye shi, nida cika baki nice da kuka ina bada hakuri, kukan bafa irin na tashin hankali kuka mai tsuma zuciya da ruhi, wanda kana ji kasan kirsa ceda kisisina, sai gashi ya rufta cikin tarkona. Aikuwa muna fitowa wanka nace.
"Daddy ba wai na gaji bane kyaleka nayi sabida kar na tsotse maka ruwan jiki karasa kuzarinka."
Cizon lip ɗinshi yayi yana sauke ajiyar zuciya yace.
"Ni dake ne, zamu haɗe."
Yasaka kayanshi ya sauka kasa, nima kwalliya nayi cikin doguwar riga na material, na sauko kasa dan yunwa nake ji, ina saukowa shima yana fitowa daga ɗakinshi lekani yayi muka haɗa ido na kashe mishi ido ɗaya. Murmushi yayi nima haka.
Har tsakiyar falon na iso na zauna kamar sauran na gaishesu.
"Kai Maryam Sajida, anya kinyi niyyar bamu mijinki kuwa."
Inji Balkisu.
Rike bakina nayi ina dariya nace.
"Allah Mommyn yara kuyi hakuri."
Dariya duk mukayi sannan muka fara cin abinci, yanda naga Yan biyu sunki kulani nima na tarasu a gefe,
........ Bayan ya gama cin abincine yayi mana sallah zai tafi yola shida su Aman Hijab muka ɗauko nidasu balkisu muka rakashi, banda Aneesah wacce tafita gayarta.

Sai da muka ga fitarshi na juya gareta nace.
"Kiyi Hakuri Mamien yara amma fitanki a haka ba mutunci duk masu kuƙa da gidan suna kallonki ai ko ba komi zaki jawa mijinmu daraja, A gurin ma'aikatanshi."

Nan ta rufe idanunta ta gurza min rashin mutunci, riko hannuna balkisu tayi tace.
"Kinfita hakkin zaman tare Allah ya bada lada.".
.......... Koda Suka isa yolan dakyar aka basu shi, bayan an gudanar da bincike, basu tsaya a ko ina ba, sai babban asibitin abuja, acan akayi cuku cuku, aka wucce dashi Germany.

Tafiyar Yunus ne yayi dan ya dawo mana, yayi kwana biyu sannan suka wucce.
*****
Rayuwar gidan Yunus tana da daɗi a yanxun dan mu uku mun haɗe kanmu, inda mukayi kokarin ganin Aneesah ta biyomu amma ina.
Watan shi huɗu suka dawo, tare da sulaimn wanda ya sami matsala a kafarshi, na dama yana ɗingisata.
Bayan dawowarshi muka tafi bikin yaye su Huda, har da mamanta, bayan an gama hidimar muka dawo gidanshi na nan abuja dan zai dawo nan, muna shiga balkisu ta fara sheka mana amai, kafin wani lokaci ta gallaɓaita, asibiti ya kaita a ɗan gaba unguwarsu.
Suna zuwa aka samata ruwa, sabida ko tsayuwa batayi.

Test ɗin jini aka mata dana fitsari, bayan wani lokaci aka kawo anan aka sake mata scanner, abinda likitan ke tsamani ya tabbata cikin wata uku, cif.
Mikawa Yunus hannu yayi yace.
"Ina tayaka murna Madam tana ɗauke da juna biyu har na wata uku."
Murmushi Yunus yayi ya mika mishi hannu suka gaisa yafito,komawa ɗakin yayi yana kallon yanda tayi fayau, wato rabo fitina ce daga dawowanshi har Allah ya nufa balkisu zata haihu.

Zama yayi har ta tashi sannan ya taimaka mata tayi alola da sallah, likitan na ganinta yace taje gida ba wani abu ya rubuta mata magani.

****
Cikin balkisu bayi da wani fitina sai dai warin fentine bata so, haka muka cigaba da kula da ita,

...... Tunda Huda ta dawo take cikin damuwa da yawan kuka, anyi tambayar duniyan nan taki faɗa karshe sakata nayi a ɗaki na tambayeta, bata ɓoye min ba ita Aure take, so.
Kiran Uban nayi muka zauna nace ta maimaita tana kuka ta faɗa mishi.
Koda aka tambayeta waye take dashitace nan duniya bata da wanda take so sai Ya Kabir.

Shi knn nace mata kawai.

....... Wata litinin naje gida na sami Umma da Malam na musu bayani, basu ki ba sai aka kirashi a waya sukayi magana ta fahimtar juna da Iyayenmu, ba tare da wata damuwa ba ya amsa,......
Bayan haihuwar balkisu,akayi bikin Huda da Ya kabir. A lokacin Daddy ya tada zance kai Fareeda kasar waje ko za'a dace tace ita bata so, wanda muka haifa sun isheta.

*****
Hafsa matar Ahmad kuwa wani alhaji ta aura da zumar auren kashe fire, mutumin yace bai san da haka ba, yayita cin Ubanta Matanshi biyu suma suka tasota a gaba, karshe garin faɗa suka tureta cikin mangyaɗa ta kone fuskarta,
Alhaji na ganin fuskarta ta lalace ya saketa, karshe Ahmad neya ɗauki ɗawainiyar mata jinya har Kasar waje, koda ta dawo ta nemi ya dawo da ita yace a'a yayi ne sabida chuchu.

Hindu kan ba laifi ta nutsu sosai, kamar ba ita ba ganin haka Rahilah tasa Aman ya dawo da ita, dan lokacin Hindu ma cikine da ita gana Rahilah da ya tsufa. Zaman gidan ba laifi,

......... Dake an fara azumi, Fareeda da Balkisu ne a kitchrn ina kwance, Yaransu sai lugude suke a kaina. Cikin ɗags murya nace .
"Maman Yara wallahi kizo ki ɗaga min yaranki zasu murkusheni."

Dariya balkisu tayi tace.
"Haba kekuwa Aunty Mom kiji dasu Wallahi muma aiki yaci karfinmu."

Kamar zanyi kuka haka nake kallon yaran, tunda Ubansu ya jika min aiki shikenan na zama lazy, Bana iya komi sai bin kasa. Har shima ynz kallon juna muke dan bana kaunar ya taɓa ni

Shigowa yayi da sallama, tunda na kalleshi sau ɗaya na rufe idona ban kuma buɗewa ba har yakwashe yaranshi ya tafi,

Uzuri yayi min dan cikin wata biyune sai wahalar da yake bani.....
*****
*Bayan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login