Showing 33001 words to 36000 words out of 39506 words

Chapter 12 - MATAR SO BOOK 2

06 Sep 2025

3204

ya ɗauketa.
****
A hankali komi yake tafiya, musaman kwanakinmu kafin kace mi har munyi arba'in. Shiryamu Umma tayi Yayanmu ya kaini na musu kwana biyu. Na dawo,

Al'amarin Ubangiji tare ds niman yardanshi Ummana tasani a gaba da addu'ar dangana da hakuri, dama niɗin ba ma'abociyar kwaranniya ba sai wani nutsuwa ya shigeni da kamala.
Gashi dai ban cika ashirin ba amma, nakoyi wani dattako a gurin Ummana, hakuri yayinda aka zaluncika. Shanye ɓacin rai yayinda aka zageka. Sadaukarwa ga abinda kafi so da bukata.
Jajjarcewa ga niman nasara a rayuwa, wanda haka ce ta faru dani, a cikin shekaru ɗaya da watani nake zaune a gida, dan yarana yanzun suke da shekaransu ɗaya kenan. Masha Allah gasu nan kaman wasu zakuna.
Ga kiriniya da kujiba kujiba,.
A yanzun da Yayanmu ya nima min, N.C E,
Dan shi nace zanyi dukda kowa bai so ba na zaɓi abuna haka dan bana son dogon karatu.

****
"Sun guy, kana nufin wani aikin ne ya faɗo daga sama."
"Zanci kaiii, kaji min shege. Kana wasa da Sunguy ne, nifa ba karamin kwaro bane, dan haka an bani turamol da Emzlin nasaka a jakar Yar gidan Minister tsaro zata tsallaka saudiya."

"Kutt nawa aka biyaka."
Mikewa yayi yace.
"Uwani bata ce jeka ka gani ba."

Tafiya yayi yabar abokin da cizon yatsa.
*****
A cikin yan kwanakin nan Sulaiman ya takura min, sosai dan sakonshi yafi sama da ɗari a wayata, gashi ya shigewa yan gidanmu alkhairi yake musu kamar wani sauna.
Ranar jumma'a na dawo daga makaranta naga baki a cikin falon baki dake kana iya hangosu ra glass ɗin window. Ga takalmansu a zube.
Shiga gida nayi na sami Umma na a ɗakinta zama nayi sai ga H² sun ɗibo jiki da tafiyarsu da bata wani kwari ba, suka zuɓe min a jiki.
"Wash mazaje zaku karyani, ku barni na huta mana."
Dariya Umma tayi mana, musaman yanda taga, Hussain yana tura baki alamun zai sha nono, tasan yanzun zan gudu. Dan yaran suna shan nono sosai ni kaina kamar zan faɗi idan suka zuke ni.
Bata gama dariya ba, na mike zubur ina dariya nace.
"Mazaje tsoro kuke bani, idan kuka fara shan nono baku tuna komi, sai shi. Yawwa ummana nags baki agidan nan lafiya dai ko?"

"Zauna Maryam muyi magana."
Zama nayi a gabanta ina kallonta dan naga babu wasa a fuskarta.
"Dama kakansu H² ne yazo nimawa kanin Yunus aurenki, sai Baban faruq da yazo niman gausiya ta kom.."
Mikewa nayi a kiɗime nace.
"Na shiga uku na lalace, Umma kuna kaunata kuwa, don Allah ku rufa min asiri wallahi bana son Sulaiman, Umma mijina yana raye."

Kuka na saka mata wanda yasa yaran firgita suka fashe da kuka suma,

Sosai nake yi nace.
"Umma ina zan kai Yaran nan, mi zan ce musu? Idan kuma babansu ya dawo a ce nayi hakuri dan na tara wasu Yaran ko Ya-ya kunga gawarshine? Babu wanda yake da yakinin ya mutu akan mi bazaku bani damar kaiwa shekaru huɗu ba."

"Bazamu baki ba, sabida bama kaunarki. Mahaifinshi yace a binneshi a inda ya mutu, wato har kin kai wacce zaki faɗa mana bama kaunarki toh mungode Allah ya shiryeki."

Tana gama faɗar haka ta barnin ɗakin tashin hankalin da na shiga ba iyaka, wani tausayin kaina nake ji,

Gashi abin an saka auren sati biyu, duk na gigice na fita hayyacina sai rama nake.
Aunty gausiya kuwa kanta rawa yake zata koma gidan mijinta.

Matar Sulaiman har sako take turo min na yanda zata wulakantani.

Zafi uku, ga tashin hankalin da nake ciki, ga fushin Umma wanda yake yawo a jinina, ga exam wanda bansan mi nake yi ba.
Nabi umma na bata hakuri taki, kulani sai ma zuba min idanun da tayi, a ɓangaren sulaiman kuwa ya haukace da murna dukda wannan bai taɓa zuwa ba. Sai sako

Ana bikin saura sati guda aka kawo kayan lefe, wanda kallo ɗaya zaka musu kasan aci kaniyar nera, ko kallo basu isheni ba.

.......
A yau kasar saudiya takama wata matashiya ɗauke da muyagun kwayoyi, yar Minister tsaron naija.
Abinda ya ɗauki hankalin ɗinbun alumma, inda akalar duniya ta juya alamarin.

Lokaci guda mahaifinta ya haukace har da yunkurin koran mutane da dama a cikin gidanshi.

Kafin a wani lokaci har an shiga tattaunawa tare da tsanananta bincike, tun daga fitar Yarinyar har zuwa airport.
A nan aka saka idanu akan Cctv nan suka, gano fuskar Sunboy. Da lokacin da ya fakaici jakanta yasaka mata kwayar.

Take akayi copy ɗin hotonshi aka mikawa sojoji da Yan sanda, tun daga abuja har zuwa sauran state ɗin.
Nan aka shiga muhawara, yanayin saka Kwayar irinta Yunus Marafa ne, mi yasa shi ba'yi magana ba kodan an taɓa Yar miniter ai shima mahaifinshi tsohon sakataren gwanatin tarayya ne.

A cikin awa goma sha ɗaya aka kamo Sun boy, wanda kafin akawo shi yaci mugun duka, sabida sojoji ne suka cafke shi a birnin gwari.
Tsabar yaji wahala tun kafin akaisu yace.
"Zan faɗa muku, Nuriya Kishiyar Mamanta ce ta bani kwayar nasaka mata."

Wani soja ya zabga mishi naushi yace.
"Ba yau kasaba ba, zaka faɗa waye da waye kasawa."

..........
Lokacin da Sulaiman Yaji labarin an kama sunboy, haɗa komi nashi yayi yabar garin Zaria baki ɗaya. Inda yayi kokarin barin kasar.

........

"Eh nine nasakawa Yunus Marafa, shi kuma kaninshine ya bani aikin."

Basu kyale shi ba suka mishi lagalaga.
Koda suka isa Abuja, kallon sunboy Minister yayi yace.
"Ku karya min ɗan iska, dan yasani kusan mutuwa da taimakon suwaye kake wannan aikin a filin jirgi."

"Da taimakon ma'aikatan gurin wanda nake sayansu"

"Ku karya min ɗan banza. Yau zamun kaishi kasar saudiya na dawo da ita, sai kuma Maganar Yunus marafa shima yanzun zamu je ofishin jakadancin china mu nime diyyar kashe shi da akayi ba tare da hakkinshi ba."
****
Shekara ɗaya baya........@lalaci ya kamani, 😹
Page.....11
       Shekara ɗaya baya, da alkali ya yanke hukuncinsu Yunus. Za'a kaisu inda ake gabatar da hukuncin. Toh a lokacin kungiyar siyasan da take gudanar da mulki tana fuskarta barazana daga wata kungiya wanda har take zargin party mai mulki tana kashe mutanen da basuji basu gani ba, dan haka suna kira da alummar china su juyawa wancar party mai mulki baya, a zaɓe su.

       Abin da ya kawo ruɗani kenan a ɓangaren siyasar kasar sai aka dakatar da duk wani hukuncin kisaa, aka ajiyesu.
               Toh a cikin haka aka manta da case ɗin Yunus aka kaishi wani mugun gidan Yari, wanda akayi ta axabtar dasu.
   Yafice hayacinshi, ya lalace
Idan ka ganshi matukar baka yi dagske ba toh xaka shiga ruɗani.
        Dan yayi baki ya jeme.
          Kullum kasame shi yana istigifari, dan yasan hakkinmu ke binshi. Matsalar gurin shi baya jin yarensu su basa jin English sai ya ajiye haka A matsayin k'addarar shi. Koda mutuwa yayi yana fata Allah ya yafe mishi hakkinmu.

               *****
    A zaria kuwa Mama kilishi ce ta yanki jiki ta zuɓe sakamakon jin abinda Sulaiman ya aikata, koda ta farka. Zatayi magana hajiya ta rufe mata baki.
    "Haba Rukayya sai kace baki san k'addara ba, wannan aikin shaiɗane, kuma nayi imani da Allah Makahon sone da tausayi yasa Sulaiman ya aikata haka, tunda kowa yasan Yanda Babangida ya zalunci maryam, wallahi bani da haufi akan shi dan nasan duk inda yake nadama yana tare da shi, ki mishi addu'ar niman shirya karki yarda zuciya takaiki ta baroki."

     Mai da kai Mama tayi tare da zubda kwalla sabida bakin cikin abinda ɗanta ya aikata.

                 ****
   A lokacin guda aka kafa kwamintin lura da abinda ya sami Yunus inda suke tattaunawa da jakadar china, kwamitin yar minister aka kafa zuwa saudiya,
        Na Yunus kuwa har da Alhajinshi wanda aka mishi kiran gaggawa. Da zai tafi bai tafi shi ɗaya ba sai da ya ɗauki Aman da Ahmad.

         Sosai maza suka murza gashin baki da tattaunawa mai zafi inda aka koma har kaduna aka duba cameransu,  aka koma samo vedion. Ba'a ɓata lokaci ba aka wucce china.
   
           ****
Ina can hankalina a tashe, bana ko iya magana. Yaran kuwa suma sai abin ya taɓasu basu da kuzari. Suma sai suka koma gefe guda, suna kallona. Sabida rashin walwalana, na kasa basu farin cikinda nake basu kullum. Toh yanzun bana iya basu.
"Wai kina nufin haka zaki shiga hakkin Yaran da basu da laifi, miye laifinsu da baza'a basu abincinsu ba, karfi da yaji zaki maida yara marayun dole, idan kuma kin yayesu ne toh ki faɗa mana." tana gama faɗar haka tayi taficce waje abinta.
Mikawa Hassan hannun nayi idanuna cike da kwalla, nace.
"Ba laifina bane, soyayyar Mahaifinkune bazata taɓa barina na rayu da kowa ba sai, shi."
Ciro mishi nono nayi na mika mishi, kauda kanshi yayi yana kallon ɗan uwanshi, kama bakin nono yayi ya gatsa min cizo, wanda yasani runtsa idanuna sai da kwalla suka zubo dama suna cike a idanun.
Dariya yayi ya kalli ɗan uwan wanda yazo da sauri ya kama rigana, nifa Yarana basu da wayo dan basu iya ciro nono a riga ba sai dai na ɗaga musu.
Ganin zasu zuke ni nayi maza na kwace kaina ina musu dariya nace.
"Bari na baku tea."
Mikewa nayi na ɗauki feeder ɗinsu na wanke sannan na haɗo musu tea ɗinsu na mikawa kowane.
Jifa da feeder Hassan yayi, ya tsalla ihu har sai da Mama ta shigo.
Ganin feeder a kasa yasata ɗaukarshi suka fita, Damo sarkin dawowa jikina yayi ya kwanta ya cigaba da shan abinshi. Ina shafa bayanshi, ni kaɗai ina zancen zuci.
"Ina Yau da Yunus zai dawo, yaga yaranshi ya kaunacesu ya so su kamar Yanda yake fatar samunsu, I love my Man"
A gaskiya Yunus ya shammaci zuciyata, fiyye da kima. Baxan iya son wani namijin bayan shi ba, dan sonshi daban yake, a zuciyata.
"Ya Allah kai kafini sanin sirrin sarari da boye Ubangiji ga shigo Al'amarina."

Haka nayita addu'a....
*****
Kwanansu Alhaji huɗu a china suna bin gidajen Yari, sai da suka kwana goma sha ɗaya sannan sukayi katari da wani gidan yarin dake can iyakar china da Japan.
Anan aka samishi a gigice sai dai Karfin Ibada ya hanashi ɗimauta dan azaba ake musu, cikin dare a sake musu wasu mugayen ɓeraye suyita cizonsu.

Yunu yaga Jarabawa, amma dukda haka yarda da Allah da karfin imani ya hana aga tashin hankali sai dai, a jikinshi wanda ya kare da wasu cututtuka da cizon ɓerayen nan.

Yana sallah walaha, aka buga kofarshi bai amsa ba sai da suka shigo, lokacin yayi sallama, ya kallesu masu tsaron gidan yarine yana da labarin luwaɗi suke da firsunoni, har a kusadashi anyi abun ɗakin dake gabanshi suka shiga sukayi da wani.
Dake Allah ya kare shi, basu taɓa yunkurin taɓashi ba. Saima wani kwarjini da yayi musu, akan wannan abun.

Nuna mishi kofa sukayi ya fita a hankali mutum mai kuzari da haiba ya koma tafiyar kamar ana turashi, har indasu Aman suke jira nan aka kaishi.
Fuskarshi nan ta haɗa, gashi baka ganin komi sai hanci da baki.
Kafin ya iso Ahmad ya tare shi, rungume juna sukayi tare da fashewa da kuka, Alhaji kam bai iya magana ba, sai kallonshi yake yanda ya koma.
Murmushi yayi yana buga Bayan Ahmad yace.
"Haba Mazaje kace yanzun ka koma mataye."
Janye jiki Ahmad yayi Aman ya kalleshi sai kuka komawa gefe yayi, ya zauna yana kuka. Gaban Alhaji yaje ya durkusa tare da dafe gwiwar Alhaji cikin sanyi rai yace.
"Alhaji ! hakkin maryam yaki barina na huta."
Shafa kanshi Alhaji yayi yace.
"Maryam ta yafe maka tuntuni, sai dai kanime Yafiyar Ubangiji, Zamanka a nan k'addara ce, da taimakon ɗan uwanka. Sabida soyayyar dayakewa Maryam wanda kai ka gaza mata, shi kuma yana jin zai iya bata abinda kai kagaza bata shine yasashi aikata haka, amma koma miye Allah ya yafe mana baki ɗaya."

Kuka Yunus yasaka sosai, tare da rike hannun alhaji. Takardu aka kawo Ahmad ya cika komi sannan suka mikar dashi.
Daga nan basu tsaya ko ina ba sai asibiti, nan aka shiga duba shi. Sosai tare da bashi kulawa.

Sai da suka kwashi sati kusan uku, sannan suka tattaro zuwa kaduna. Koda suka iso zaria aka wucce dashi tun a can yake son tambayar maryam amma ya gaza cewa komi, suma kuma sunki ce masa komi.

Sun isa zaria da karfe biyu na rana yan uwanshi da danginshi duk suka mishi kawanya, suna kukan farin ciki murmushi yake ya kalli wannan ya kalli wannan.

Da misalin karfe biyar su Ahmad suka dawo, kaduna.
Ahmad ya ajiye Aman a gida, shima ya wucce gidanshi.
Yana shiga yasami Hindu a falo ta zabga tagumi zama yayi kusada ita yace.
"Lafiya kike tunani."
Mika mishi wayarta tayi tare da fashewa da kuka tace.
"Aman bansan ya akayi ba wasu suka ɗauki hotona suna, rubutun ɓatanci a kaina."

Murmushi yayi sannan yace.
"Toh ai sai ki godewa Allah tunda baki yi abinda ake magana a kai ba, hmm abinda nake gudu kenan kin lalata gidanki kin lalata rayuwarki, idan kinga zaki iya ki gyara idan bai miki ba, kinsan dai bake ɗaya bace."
Yana gama faɗar haka ya mike zuwa ɗakinshi yayi wanka, ya sauya kayanshi ya nufi gidan Mamie dan har yanzun yaki yarda Rahilah ta dawo gidanshi,gani yake hindu zata iya kashe masa mata da ɗanshi.

Koda ya isa gidan yasame su a kitchen suna aiki da mamie sai hira suke, abinsu ga Sayeed da yake fama da kekenshi.

Yaron naganin Baban shi yace.
"Papaaaa"
Da gudu yazo kan uban ya ɗagashi sama. Yana jijjigashi sannan ya sumbaci goshinsa yace.
"Mr Mandara faɗa min, miye Mominka da Mamie suka ce."
Dariya yayi ya shiga shirme abinshi, cikin nutsuwa ya gaida Mamie tayi mishi barka da arzikin dawowan Yunus, wani kallo yabi Rahilah dashi sannan ya wucce falon Mahaifinshi nan suka tattauna sannan yafito ya shige sider ɗinshi. Bayan yabar Sayeed a gurin takwaranshi.

"Tashi kije, kinyi amfani da abubuwan da nabaki ko."
Kan rahilah a sunkuye ta gyaɗa mata.
"Toh maza jeki Allah ya baku xaman lafiya."
Da sauri tafita, tana murmushi.
A ɗakinshi tasame shi ya kwanta, yana ganinta ya mike zaune ya buɗe mata hannunshi.
Shigewa jikinshi tayi, tana sauke a jiyar zuciya tace.
"Papa nayi miss ɗinka, kwanakin da kayi kaman nayi hauka."

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login