Showing 3001 words to 6000 words out of 39506 words
falon yace.
"Maryam Sajida!!! Sabr"
Jini jikina tare da jijiyar jikina naji sun tsaya min cak,, cikin kuka na durkusa a gurin ina gunjin kuka tare sa kifa kaina akan gwiwata,.
"Daga Yau kowacce mace da na aura zamana take, kar na kuma kama ki Aneesah da cin mutuncin Maryam idan kuma nasamu haka toh wallahi zan iya cewa abakin auren Maceeeeee.".
Basu ba hatta ni sai da na ɗago a razane, ina kallonshi.
"Ehhh Na faɗa zan saki mace akanta, Izayar ta isa haka zaman aure ya kawota shi ya kawo ku kuma bazan ɓoye muku ba nafi....."
Haka kawai an sani typing dole,😂😉 Yau fa ranar hutawa tace, fa😬
🌹🌹🍀
*MATAR SO*
🌷🌷🌻
*MAI_DAMBU*
*Wattpad:Mai_Dambu.*
Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai....
Sadaukarwa Ga Mai Nasara Team😂
_Wannan buk ɗin hakk'in masu shine idan kinsan baki saya ba karki karanta, mai fitarwa kuma ki duba girman Alkawarin da kika ɗauka na cewa bazaki fitar ba, tunda nace idan kinsan zaki saya ki fitar na Yafe ba sai kin saya ba_
*BOOK 2👈*
Page...2
"Nafi son zama lafiya da kwanciyar hankali a gida idan kuma naji wani abu ya fito, zan baku mamaki."
Yana gama faɗar haka ya riko hannuna na mike, sama ya jani tun a hawa step yaga zan ɓata masa lokaci sai ya ɗaga ya ɗaura a kafaɗarshi, har ɗakina ya kaini.
A falo ya ajiye ni, sannan ya sauko ya ɗauki ledar da ya shigo da ita, ya ajiye musu nasu sannan ya kawo min,
Magani ne sai. Take away na abinci da farfesu, ko kallonsu banyi ba, na mike zuwa ban ɗaki wanka nayi da alola nazo na samu dakyar na sauke salollin kaina. Ina kuka kan abin sallar tare da Addu'a Allah ya fitar dani gidan Yunus ko ta halin k'ak'a.
Akan abin sallar na kwanta, ya matso yana kallon yanda gabaki ɗaya na sukurkuce, Yau ɗaya ga fiskuna da ta kumbura sosai. Zama yayi ya janyo ledar cikin nutsuwa ya buɗe abinda ke ciki daga magani ne sai abinci. Yace,
"Tashi kici abinci sai kisha magani."
Buɗe idanuna nayi cikin jin haushinsa amma yanda ya narka fuskarshi yasani mikewa, yatsina fuskana nayi nace.
"Bana jin yunwa."
"Plss kici ko kaɗan ne, sai ki kwanta yau fa tun safe baki kai komi bakinki ba don Allah kici wani."
Kallonshi nayi take kuka yazo min nace mishi.
"Baka taɓa sakani a gaba naci abinci ba,sannan baka taɓa sanin ina da kima a idanunka ba. Sai yau ɗaya jal, da kaji banbancin Yarinya da jinjira, don Allah kaje da abincinka gurin matanka ni na koshi dan naga suma suna min kallon ban isa mace ba, koda yake ai ba laifinsu ba. Kaje dan matukar kana takura min zan maka rashin kunya sabida zuciyata ta kuntatta da kinka, ka bani sarari kar zuciya tasani dana sani."
Ina gama faɗar haka na shiga niman mikewa sanya kafarshi yayi ya taɗeni na faɗo jikinshi. Juya fuskana yayi cikin sanyi murya yace.
"Kiyi hakuri kici koda kaɗan ne, Nasan ni mai laifine amna wannan fushin bazai miki komi ba sai ciko zai kara miki don Allah Maryam Sajida kiyi hakuri mana ke baki tausayina ne, yanda naketa baki hakuri."
Dariya nayi tare da janye jikina daga gareshi nace.
"Kana bani hakurine sabida samuna a cikin jerin matan da baka zata zaka samu nutsuwa da ita ba, bari na tuna maka cewa kayi wayyo Allah nakusan yin asara, maryam haka kike da daɗi maryam kicigaba da bani duniyark..."
"Ya isa haka! Waye baifi karfin kuskure ba?"
Cikin matsanancin kunya ya faɗi haka, tare da jin kamar ya muzanta. Dalilin haka nima sai da jikina yayi matukar sanyi cikin kuka na kalli yanda ya sunkuyar da kanshi yana wasa da yatsar hannuna, sai naji raina ya kara ɓaci sabida laifin da yayi na xauna ina faɗar sirrinsa da kuma kin daɗinsa. Komawa jikinshi nayi na kwanta ina kuka sosai, ganin haka yasa hannunshi ya rungume ni,yana shafa kaina jin kamar ɗigan ruwa akafaɗata yasani ɗaga kaina sama, ina kallon fuskarshi hmm hawaye ne ke bin fuskarshi.
Tsura mishi ido nayi, sanya hannuna nayi ina share mishi, cikin sanyi murya nace.
"Wallahi ka cutar dani, amma babban matsalar guda ɗaya ce ka gyara tsarin gidanka ka ɗaurashi turban musulinci ni kuma na maka Alkawarin sadaukar da duk abinda na mallaka, nadaga jikina kalamai na, lokacina da kuma ita kanta rayuwata, amma sai ka gyara gidanka fa."
Rike ni yayi gam yayi, jikinshi na matukar rawa, haɗa fuskana yayi da nashi ya shiga sumbatarsu, ban hanashi ba sabida ko Ubangijin da ya haliccemu kullum muna saɓa mishi wani lokacin cike da iza da jinkai muke aikata laifi dan musan cewa. Shi gafurun rahim ne, wannan kuma ba haka bane, tausayin wasu daga cikin bayinshi nagartattu yasashi mana afuwa....
(Allahumma Gafurni wa Rahamni)
Dakyar na kwaci kaina na koma kirjinshi, ina sauke numfashi shafa baya ya cigaba dayi, abincin ya janyo ya fara banu ina ki ina komi sai da naci kaɗan nasha magani, sannan na koma jikinshi na kwanta wallahi na kewar jikinshi da shi kanshi.
Zame ni yayi daga jikinshi ya mike tare da ɗaga ni, muka wucce cikin ɗakina, kwantar dani yayi yaja min bargo yafita.
A hankali komi da ya faru da rana ya dawo min, kwanciya nayi cikin sanyi murya nace.
"Dama shine yaren novel🙊"
Rufe bakina nayi, ina tuna irin wahalar da nasha a hannun yunus sai da tsigar jikina ya mike, gyara kwanciya yayi, muryanshi na yawo a kunena. Toshe kunena nayi da karfi, amma ina jin kalamar nake, a cikin kunena da cewa.
"Maryam keba jinjira bace, maryam haka kike, na kusan tafka asara, karki ce zaki han..."
Rutsa idanuna nayi da karfi tare da aza hannuna a kunena. A hankali barci yayi gaba dani.
Can cikin barci naji bakon al'amari bansan lokacin da na buɗe ido ba, Yunus ne yake shagalinshi da jikina. Mikewa nayi na zauna cikin tashin hankali nace.
"Wallahi ban dalafiya kabarni haka."
Murmushi yayi sannan yace.
"Karki damu bazan miki komi ba, kawai zan ɗan... Koda yake kwanta abinki."
Kwanciya nayi jikina na rawa, dan bana tunanin zai nime wani abu ashe ba haka bane. Koda na kwanta bai fasa latsani son ranshi ba, sosai yake jagulani. Har barci yayi gaba dani iyakarshi kirjina dan haka ban wani damu ba nabarshi a gurin.
......Washi gari da sauki amma dole sai da nagasa jikina sosai sabida ya matsar da yayi musu, tun da yafita bai shigo ba sai karfe ɗaya da rigar da yafita sallah ya dawo.
Kallonshi nayi sabida yanda fuskarshi yakw cunkushe da tashin hankali nace.
"Lafiya."
"Ki shirya mufita bari nima na sauya kayana......
Kirjina ne ya buga, kallonshi nayi zanyi magana har yafita. "Mike faru?" na tambayi kaina.
Doguwar riga arbi'an gown nasaka, sannan na lulluɓe jikina da wani babban mayafi, ban shafa turare ba. Sai yar kwali da huda na shafa, dan kayan baya rabuwa da kamshi. Kallon kaina nayi a madubi naga fuskana ta faɗa, sai uwar hanci ina tsaye ya shigo sanye da haf jamfa na wani yadi. Lemon green sai trouser black kaftani. Ya gyara fuskarshi sai ta fito sak matashi irin yan 28 ysr ɗin nan, farin agogo ya ɗaura a hannunshi. Sai hular minister dayasaka baka. Ga wani kamshi da yake fitarwa, kallon yanda yar kwata millim ɗin fuskarshi wacce takarawa sajen armashi, na kalla.
D'aga min gira yayi, tsintar kaina nayi da taɓe bakina na kauda kaina,, wani guri daban karasowa yayi ya janyoni na faɗa kirjinshi. Tare da ɗaga kaina, hannuna duk suna dafe da kirjinshi, kurawa juna ido mukayi a nutse nake jin hannunshi ya rike min k'ugu, juyar da kaina nayi sabida karfin sakonshi yana danne min ɓacin ran da ya kunsamin.
Mikewa nayi daga jikinshi tare da tura mishi baki nace.
"don Allah idan bazamu fita ba, ka kyaleni na kwanta dan bana jin daɗi jikina."
"Ayya mi yasami ki?" na fahimci tsokanata yake sai nayi banza dashi na wucce abuna dan ai yafini sanin amsar, kallon yanda tafiya take yayi. Tare da shafa fuskarshi, a ranshi yace.
*Maryam Sajida, kin haɗu.*
(Da aka cuce ta ba)
A falo yasameni na mike a kujera, idanuna a lumshe.
"Tashi muje." yace min, buɗe idanuna nayi na kalleshi. Mikewa nayi dakyar sabida bana jin daɗin jikina har ynx, gaba yayi na rufa mishi baya.
Fareeda tana zaune a tsakiyar falo, tabaza takardu sai lissafi take. "Hajiya Fareedah."
D'ago kanta tayi shekeke ta kallemu sannan ta mayar kan lissafinta, murmushi yayi yace.
"Na leka Balkisu tana barci, zamu tafi asibiti."
Da mugun sauri ta ɗaga kanta, tana kallona abinda ta gaza boyewa tace.
"Har ka ɗirka mata cikin ne daga wasar jiya."
Take naga mood ɗinshi ya sauya, tsuke fuskarshi yayi yaja hannuna muka fita, wata bakuwar mota nagani. Bansan yaushe yasayeta ba amma motar tayi min kyau dan ta haɗu. Buɗe motar yayi ta hanyar latsa keyn motar, sai ga kofar motarta buɗe.
Shiga nayi shima ya shiga sannan motar tarufe kanta. Tada motar yayi yana satar kallon, ni kuwa nayi ciki ciki da fuskana. Ina kallon gefe hanyar jin shu nayi ya riko hannuna ya haɗa da kan motar yana tukawa, kallonshi nayi na kauda kaina, kasa hakuri nayi na janye hannuna tare da fashewa da kuka, niman guri yayi ya tsaya kukana ke tashi a motar, juyawa yayi ya kalle ni cikin damuwa yace..
"Kiyi hakuri mana, nasan nayi kuskure amma aina baki hakuri, kuma na kara baki hakuri."
"Kawai ni bana son ganinka ne."
"Why?"
"Bcos the way that you treat me is hurt me."
"But no one above mistake am sorry." ya faɗa da raunaninyar murya.
"Bance ban hakura ba, but pls stay alway for me." na faɗa mishi cikin kuka, "Ok but"
"Pls free me." zaro ido yayi cikin tashin hankali yace.
"What??"
"Yess Mr Yunus divorce me,?"
"Why you need divorce,"
"Sabida NA biyaka abinda ka kashe a aurena."
"Hmmm is not reason,"
Cikin hasala da fusata nace.
"Toh mi zan maka bayan kasami riba a jiya, kodan rashin wayona da rashin hankalina ai kasami abinda yafi sadakinka ko da wani abu da zan sake fansar kaina bayan kimata da karabani da ita jiya."
Dukar sitiyeri yayi jikinshi na matukar rawa, juyawa yayi ya kalleni, yace.
"Zan baki abinda kike so, amma abisa sharaɗi guda biyu, ko ki kasance dani na tsawon lokacin da zan sakeki dan kaina, ko kuma ki biyani nera millim goma na baki nan da kwana uku kije kiyi nazari kuma ban yarda kiyi shawara da kowa, ba kuma duk zabin da kika ɗauka yana da sharaɗi a kasarshi."
Ba tare da damuwa ba nace.
"Na amince, zan zauna dakai har sai ka sake ni dan kanka, dan basan hanyar da zan sami kuɗin biyanka ba, sai kuma miye a sharaɗin gaba."
Zuba min ido yayi amma bai wani yi mamaki ba, yace.
"Ok, sharaɗin shine a duk lokacinda naji bukatarki a matsayinki na matata zan zo."
Kura mishi ido nayi cikin jin haushi, nace.
"Gaskiya bazai yu ba, kawai zaka lalata min rayuwa ne, dama kuma ka lalata min, idan duniya da gaskiya. Ai kasha cewa ni ban isa mace ba mi zaka nima a gurina dan kamar huda kake kallona. Jiya kuma ka nutsa ni fiyye da kima ka shiga jikina kasanni yanzun kace bazaka rabu dani ba, taɓ nama fasa zama taimakonka dan kowani lokaci gidanmu zan kom, am tired."
Zare hular kanshi yayi ya kwantar da seat ɗin motar ya kwanta tare dafe goshinsa.
Damuwa tayi mishi yawa. Ga abinda ya faru dare jiya, yana son ya kaini dan kar a zargeshi da kin barina fita cikin yan uwana, ga abinda ya faru na kayansu da hukumar shige da ficce takasa ta kama, wato custom.
Wanda shi aka wakilta ya tafi har lagos yaje ayi magana, ga tekun da ya ɓelowa kanshi.
Mikewa yayi ya tadda motar sai asibiti. Fitowa yayi naki fita dan bansan nufinshi na kawo ni asibiti ba,
Buɗe inds nake yayi ya rike kofar cikin sanyi murya yace.
"Kiyi hakuri ki fito, karki tara mana mutane anan."
Aunty Shkura na hango bansan lokacin da nafito ba, na daidaita nutsuwata na, fara sauri amma dan dole na hakura sa saurin sabida yanayina, rufe motar yayi ya iso har inda nake takawa a hankali, sakala hannunshi yayi a k'uguna, ya janyoni jikinshi. Kasanshi ya saka daidai kunena yace.
"Kina tafiya kamar wacce take koyar tete."
Kallonshi nayi, cikin mamaki nace.
"Nikan kabar taɓani idan naso nayi kowacce tafiya ma, aikaine ka sani hk."
Shiru duk mukayi, kuma hakan da yayi min ba karamin rufa min asiri yayi ba, dan baki ɗaya nasami ɗan kwarin takawa a nutse.
Muna shiga naga Yan uwana baki ɗaya, har da Ummana babu mama amarya. Da sauri na isa gurinsu tare da zuɓewa jikin Umma na fashe da kuka, bubuga bayana take har nayi shiru ina jiknta suka gaisa dashi, har da sauran yan uwana.
Jin zafin jikina taji ta kalle ni tace.
"Kee ma baki da lafiyan ne naji jikinki zafi." sake kifa kaina nayi a cinyarta nace.
"Eh zazzaɓi shine yasa aka min allura."
Dafe goshi Aunty shema'u tayi cikin jin haushi tace.
"Auta baki tambaye waye ba lafiya ba?"
Kallon nayi cike da son karin bayani. Nuna min ɗakin tayi a hankali na mike ina kallonsu, jikina ne ya kama rawa. Har na isa bakin window ɗin, a nutse na leka Rahima ce akwance cikin wani irin yanayi,
Baya nayi kamar zan faɗi, naji an tare ni. Kamshin turarenshi yasa na fahimci shine, da sauri na juya na kifa kaina a kirjinshi tare da rike rigarshi jikina na wani irin kerrma, zazzaɓine ya kara rufa min, kuka nake son yi amma nakasa, sai cakume rigarshi nake,
Muryan Malam muka ji yana cewa.
"Ka maida ita gida, idan aka kwana biyu ka dawo da ita dan nasan ynx haka zazzaɓine yake shirin kamata."
Gyaɗa kai yayi, sannan ya rungume ni muka fito fuskana a kirjinshi, Rahima ce na hango naɗe cikin bandaje.
Fuskarta ce kawai bata kone ba, baki ɗaya na firgita na gigice, ina rufe idanuna ita zan gani. Ihu nasaka mishi tare da kama kan motar kamar zan zubar damu akan titi, rungumeni yayi yana tuki da hannu ɗaya, Allah kaɗai ya kaimu gida, kafin ya fito a motar yakira Dr Nafi, ta kofarshi ya fito damu. Ya ɗauke ni sai cikin gidan, ɗakinshi ya wuccw dani. Ko minti ashirin ba'a rufa ba sai gata, nan yayi mata bayani da yanda nake firgita. Drip tasami, sai allura tace.
"Dama akwai sauran zazzaɓi a jikinta, kuma sai akayi dace, ta sake ganin abinda ya firgitata. Amma nayi mata allura zata ji sauki sosai."
Tana gama aikinta tafita, a daren ya shirya mana kayanmu, a haka ya ɗaukeni ya fita dani dan ruwan ya kare, muka nufi lag,
Mun isa goma na dare, eko hotel ya kama dan haka motarsu ce tazo ɗaukarmu, gani na a rabe a jikinshi yasa aketa kallonmu har muka isa ɗakin da ya kama, yana kwantar dani na buɗe idanuna.
Kallon ɗakin nayi sannan na kalleshi shima. Dafe goshina nayi ina kallonshi cikin sanyi murya nace.
"Mi yasami Rahimahta."
Zama yayi a bakin gadon tare da rike hannuna da yake sanye da cannula yace.
"Daren jiya gobara ya tashi a part ɗinta, bata wani ji ciwo sosai ba, hucin wutace ta saɓelar mata da jikinta, amma ɗazun nakira Ahmad wai ta farka."
Lumshe idanuna nayi, na gyara kwanciyana dan bana jin zan iya mikewa, ban ɗaki ya shiga yayi wanka, sannan ya haɗa min ya zo ta taimaka min, ya kaini zai min, ganin zai min iyayi yasani birkicw masa, dole ya kyaleni nayi wankar da alolar, nasamu ya shimfida min abin sallah, banyi azhar ba da la'asar ga magbri da isha,
Gabatar da sallar nayi, sannan na zauna nayi azkar, ina idarwa na tada rigima ya kira min Umma na. Mun daɗe muna hira da ita rabi kuka rabi dariya, sosai na sake mukayi hira da tambayarta jikn Rahimah tace da sauki ta koma barci.
......Ajiye mishi wayarshi nayi na gyara kwanciyata, sai barci dan ko abincin da ya kawo min naki ci, dakyar nasha magani da fresh milk.
.....Satinmu ɗaya dashi kullum yana jelan akan kayansu, duk cikin kayan da ya kwaso min duk babu na gari, tsaki nayi na ɗauki wata shirt ɗinshu nasaka, itama iya cinya, zama nayi a tsakiyar gadon, tare da zabga tagumi. Shigowa yayi a gajiye nace.
"Barka da dawowa."
"Yawwa maryam ya zaman kaɗaici."
Kafaɗa na ɗaga mishi na cigaba da shiruna kallona yayi tare da shafa kanshi.
Cire kayanshi yayi ya nufi ban ɗaki, can sai gashi ya fito, gadon ya hau tare da rungumana tura hannunshi na shiga yi, amna fir yaki kyale ni, asalima cire rigar