Showing 15001 words to 18000 words out of 39506 words
i can't change Ahmad."
Dariya Uwar tayi har da shewa sannan tace.
"But you can change ur destiny."
"Indai akan Ahmad ne baxai canzu ba." ta faɗawa mahaifiyarta cikin kuka,
"Zai canzu idan kikayi auren kisar wuta."
A kiɗime ta ɗago kanta tana girgiza shi, cikin kuka tace.
"Baxan iya ba, ki nima min wata mafita wannan yayi min tsauri da yawa, bazan iya raba shimfiɗa dawani namijin ba, ni ɗin mallaki Ahmad Zailani bature ce bazan iya ba."
"Good Job" Uwar tace mata.
*****
Kwance yake duk jikinshi ciwo yake, toh ba dole ba ya tsangwami kanshi da masifa sai ya cima manufarshi, karan wayarshi yaji ya laluba ya amsa.
"Kai haka ake baka kira Maryam kaji lafiyarta ba sai kayi shiru ka manta da ita, tun jiya tazo ynx haka tana asibiti ba laifi."
"Kar dai Cikin Ya zuɓe?"
Ya tambayi sulaiman da ya kirashi.
"Wani irin zubewa kuma ciki lafiyarshi lau, itace dai ba lafiya, kuma ana kokarin ganin taji sauki."
Shiru yayi ranshi kamar tayi waje ciki ciki yace.
"Ok zanzo next week ina da wani aiki a gabana."
Yana gama faɗar haka yayi jifa da wayar kamar wanda aka faɗa mishi sakon mutuwa.
Wanka yayi ya fito yana nazarin asibitin da Aneesah ta faɗa mishi.
Murmushi yayi ya saka suit ɗinshi, haka kawai sai yaji yana matukar kewata, dan yasan da ina nan da nice zan shirya shi, ina saka mishi kaya yana taɓe taɓe, wani lokacin dakyae nake korashi ya tafi dan manne min yake kaman danko.
Tsaki ya sake sannan yace.
"Maryam ina sonki, amma haka bazai hanani ganin kinyi rayuwa irinta mata masu daraja ba, har nawa kike da zakiyi tunanin ɗaukar ciki."
Haka ya gama surutanshi ya fice a gidan.
*****
Zubawa Dr Fatrick Zubairu ido tayi likita a babban asibitin koyarwa na Ahmadu Bello T.H.
Zare gilashinsa yayi yana sauraronta, cikinta kuka tace.
"Sabida bani da lokacin kaina da kuma ra'ayin mijina, dan shima baya son tara yara,,,!" numfashinta taja sannan ta cigaba da cewa.
"Sai yace na kara koda ɗaya ne, sai na dakatar da haihuwa tunda lokacin ina da cikin yarona da ya rasu, banyi tsamanin namijine ba, sai da na haihu, yaron na da shekara ɗaya na sami wani cikin dukda na ɗauki allura amma sai da cikin ya shiga, ina faɗa mishi yace na cire bayan na cire wani tafiya da zaiyi india tare muka je aka juya mahaifar, muka dawo abin mamaki shekaran yaron biyu sai ga ciki mahaifar ta juya, shima wannan karon cire cikin mukayi."
Kuka ta kara sakawa mai cin rai, buɗe karamin freezer ɗin ke cikin officer ɗin yayi, ya ɗauko mata goran ruwa ya tura mata, gabanta ɗauka tayi ta buɗe ta kafa kai sai da tashan ye tass sannan ta ajiye.
Sannan tace.
"Fatrick nasanka kasan ni, munyi zaman unguwa ɗaya, dukda addininmu ya banbanta nasan zaka fahimci halinda nake ciki. Bayan an zubda cikin kawai sai ya bani shawaran muje a cire mahaifar, da farko naki yarda amma daga baya na amince sabida ni kaina ba zaman gida nake ba, always am busy bana fita ko ina iyakata a kaduna nake kasuwancina, haka na amince mashi muka je aka cire min mahaifa a wani zuwanshi Turkey, gashi an wayi gari bani da mahaifa bani da D'an ina jin ciwon haka a ynz Kishiyata ce ke ɗauke da ciki kuma yana son ya lalata cikin narasa yanda zanyi saving ɗinta da abin cikinta, karkayi mamaki dan har Matarshi ta farko yasa an rufe mata mahaifa."
Gyara zama Dr Fatrick yayi cikin nutsuwa yana kallon Fareedah, yace.
"Fairy(Sunan da yan unguwarsu da frnd ɗinta suke kiranta kenan tsabar kallon cartoon masu ɗan fifike kuma sai yazo dai dai da sunanta, dukda akwai abubuwa masu haɗi da fairy amma haka bai dameta ba) kunyi kuskure kuda annabinku yace ku Haihu dan yayi alfahari daku, shine kuke aikata abinda muma bazamu iya ba, Fairy Allah ya baki haihuwa baki san wanene arzikinki ba kika biyewa son zuciyar mijinki kika saɓawa Allah, nasan ni kiristane amma bazan taɓa aikata abinda kikayi ba, ko nasa matata tayi haka. Tunda nayi aure nake niman haihuwa har kasar waje munje amma babu labarin dan nine mai matsalar karewa dashen ɗan za'ayi mata nace a'a Allah nasane damu ban fasa kai kunans coci ba dan nasan Allah yana tare dani. Alkawari ɗaya zan miki shima bai zama dole hakan ya faru ba sai dai ai kunce Allah mai jin kaine mai rahama ne, zan miki hanyar wani likita a Germany ya iya dashen mahaifa tayu idan Allah ya nufa da rabo ki sake samun ɗanki na kanki idan kuma bai nufa ba sai kiga baki samu ba, da wannan nake kira da kiji tsoron Allah dan hakkin cikin da kuka zubda ba lallai bane ya barku, zai kuma cigaba da bibiyarku dake har shi maigidan naki, kuma kije gurin Malamanku ki tambaya ko abinda kika aikata akwai hukunci a kanki dan ki fara sanin inda zaki dosa, ni nasan zan miki kokarin ganin...........
*Don Allah kuyi hkr zaku ji ni shiru gobe, da jibi sai ranar monday Insha Allah abubuwa sun min yawa kuyi ta maneji* 🙏
🌹🌹🍀
*MATAR SO*
🌷🌷🌻
*MAI_DAMBU*
*Wattpad:Mai_Dambu.*
Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai....
Sadaukarwa Ga Mai Nasara Team😂
_Wannan buk ɗin hakk'in masu shine idan kinsan baki saya ba karki karanta, mai fitarwa kuma ki duba girman Alkawarin da kika ɗauka na cewa bazaki fitar ba, tunda nace idan kinsan zaki saya ki fitar na Yafe ba sai kin saya ba_
*BOOK 2👈*
*Page....6*
Bakinta na rawa jikinta ma, haka ta kalle shi tace.
"Fatric kana nufin zubda cikin ma akwai hakkin Raiiii?."
"Kwarai da gaske ai kunso kankune duk abinda Allah ya baka yasan da zamanshi da wamzuwarshi, mufa bambancin dake tsakaninmu daku shine matukar akace Yesu yace kar muyi kaza bazamu taɓa yi ba, amma ku musulmai idan aka Allah yace Annabi yace sai kiga mutane suka famkama dan ko sunyi laifin sun dogara da Allah na yafe musu dan ku alummar Annabin karshe ne, kuma duk ba haka bane sonkai da son zuciya ke buwayar, karki ce ina ci miki fuska haka bane iyakar gaskiya na faɗa miki, kuma ina jajjanta miki rasuwar ɗanki."
Goge kwallar dake bin fuskarta tayi, sannan ta mike tare da cewa.
"Nagode."
Ta fita a officer ɗin tausayinta ne ya rufe shi, sosai.
****
Ina kwance a falon Hajiya dan tun safe aka sallamo ni,ina bin suratu ankabu naji sallamar Sulaiman, mikewa nayi naja hijab ɗina na rufe, jin na amsa mishi nace.
"Shigo Baban Arif."
Ya shigo fuskar shi a sake, ya nemi kujera ya zauna. Shiru mukayi dan shima ɗin wani miskiline amma ba irin ɗan uwanshi, yace.
"Kina bukatar wani abune?"
Jim nayi ina nazarin abinda raina ke so, zaro wayarshi yayi a aljuhu ya fara latselatse, sake ɗago kai yayi yaga har lokacin kaina a sunkuye, gyara murya yayi. D'aga kaina nayi nace.
"Babu sai ko masara gashashe."
"Bayan shifa?"
"A'a babu komi."
"Ok"
Yasa kai ya fita can bayan wasu mintoti sai gashi da masara har guda hud'u, magarya, kwakwa da dabino, ya ajiye min.
Har zai fita ya tsaya a bakin kofar cikin sanyi murya yace.
"Maryam miye matsalarki da Yayanmu, dan nakirashi nace mishi baki da lafiya kina asibiti yace min cikine ya zube."
Girgiza mishi kai nayi, muryana narawa nace.
"Wallahi babu komi."
Fita yayi kawai, dan yasan waye Yunus.
Bayan fitashi na shiga ruɗani sosai, dan haka kawai zuciyata ke sasasho min wani abu na daban, lalubar wayata nayi na kunnata..
Lambashi na nima, tashiga amma yaki ɗauka, sake kira nayi bai ɗauka ba, sai a na uku ya ɗauka cike da masifa.
"Toh mi zan miki? Dake ke ba matar rufin asiri bane shine kika fita ban sani ba, har zaria wato ni ban isa dake ba? Kinje haɗani da iyayena ko maryam? Shi kenan ban yafe ba."
A sanyayye na kira sunan shi.
"Daddy!!! Kayi hakuri ban kai karanka ba, kawai daddy ina wahala ne da abinda kake min, idan kace yau na dawo zan dawo don Allah ka janye batun Allah ya isa nan, kayi hakuri."
Yanda nayi maganar sai da jikinshi yayi, yace.
"A'a ki zauna ni zanzo ɗaukarki,"
A hankali na shiga jan shi da jira, har yasake damu muka kashe lokaci muna hira, wanda zallar shagwaɓa ce zalla da kiriniya nake mishi.
........Ranar jumma'a sai gashi a zaria ma yayi sallar jumma'a, bayan sun gaisa da iyayenshi nima muka keɓe yayi abinda yasaɓa taɓayya, da dare korani gurinshi Mama kilishi tayi, tabbas nayi kewar mijina, dake bai zo min yanda sai yasha magani ba yau a musulunce ya zomin, amma dake dama can da lafiyarshi sai da na fashe da kuka, sabida gajiya da wahala, kuma yan kwana biyu ba a jone ba, dakyar ya kyaleni yana sauke numfashi.
Tsaki yayi dan gani yake kamar cikin ne ya sani jin gajiya, juya min baya yayi a hankali naje na kwanta a bayanshi cikin sanyin murya nace.
"Kayi hakuri, bazan kuma kuka ba idan mukayi wanka kazo kasake, bazan kara ba."
Juyawa yayi cikin jin daɗi, yace.
"Ok jekiyi wanka ina zuwa."
Mikewa nayi na shiga bayin kamar jirana yake. Ya janyo jakarshi ya ciro maganin yajefa a bakinshi, dake akwai ruwan da na kawo mishi ya ɗauka yasha sannan,ya shigo ban ɗakin.
Wanka mukayi tare sam ban kawo yasha kwayar ba, sai da muka dawo yace zai koma.
Banki ba dan na rigada na amince mishi, hmmm basan mi Yunus ke nufi dani ba, amma dan wahala kan nasha shi, dan ina jinshi ina ganinshi sai da yagama cutar dani sannan ya duba ko abinda yake bukata ya faru, babu komi sai dan abinda ya fitarm daga jikinmu.
Shida kanshi ya shiga dani, kwalla nabin fuskana haka yayi min wanka shima yayi nashi muka fito.
Washi gari dana samu na koma ɗaƙin hajiya ban kuma yarda na haɗu dashi ba, da dare tace naje kuka nasaka mata, nace.
"Hajiya idan naje mutuwa zanyi don Allah ki barni Daddy ya sauya baki ɗaya, baya tausayina duk abinda yasan zai cutar dani shi yake min, don Allah karki mishi magana kawai zan zauna a nan har mu koma gida."
Shiru hajiyarshi tayi tana kallona, gyaɗa min kai tayi cikin sanyin jiki ta nuna ɗakinta na shige ina kuka, wannan wacce irin rayuwa ce. Nake ciki mai nayiwa Yunus yake son kashe ni da sauran numfashina. Kwalla masu zafi suka sauko min, duk yanda nake son shi baya gani bazai tashi wahalar dani ba sai lokacin da nake bukatar kulawarshi. Dakyar barci yayi gaba dani.
Allah yaso shi bai sha maganin ba, tunda ya lura naki musake haɗuwa ya ajiye maganin, burinshi yanzun bai wucce ya kaini gurin liktan a cire cikin ba, dan ya lura cikin ma yana son kawo mishi matsala.
.....Kwanakin da ya ɗiba mukayi sannan na shiga haɗa kayana ins kuka, dan tun ban bar gidan ba jikina ke bani akwai mugun al'amari a gabana, mama tashigo tayi min faɗa. Wai ya kai kara na gurinta bana son zama inda yake.
Kwarai idan ina falo na ganshi guduwa nake, sabida baki ɗaya ya sauya kaman ba yunus ɗin da na da sani ba.
Koda muka fito da kayanmu falon Alhaji muka shiga yayi masa faɗa, sannan Hajiya ma haka sosai tayi masa tijara.
Haka muka fito yana cika yana batsewa.
Ko a motar yaki kulani haka na jingina da kujeran motar ina kuka, gidan mai ya shiga yasha mai abin haushi warin fetir yasani na shiga amai.
Kallona yayi ya kaɗa kanshi ba tare da wani shakku ba, yace.
"Kina wahalar da kanki, sosai daga nan zan kaiki asibiti a cire *Cikin*"
Wani irin faɗuwar gaba naji tare da ɗago kaina, bakina a sake nake kallonshi, Nace.
"Kayi hakuri karka rabani da shi ina son abuna don Allah idan ma nice ka maidani gidanmu wallahi zan zauna a can amma daddy karka rabani yarona."
"Wow kina nufin kin kai ɗaukar yaro a cikinki ne, ke ko tausayin kanki baki ji, dube yanda kika koma kin lalace baki ɗaya ba makeup ba kamshi ba komi a'a zan cire kema ki sami freedom yanda zaki murza rayuwarki kafin ki cika 20yrs sai ki sake ɗaukar wani."
Girgiza mishi kaina nayi cikin kuka nace.
"Ni ynz nake bukatar ɗaukar ɗana, bayan haka bazan iya ɗauka wani lokaci ba, Daddy da iliminka da saninka kake irin wannan maganar don Allah ka barni na ji kaman yanda sauran iyaye keji."
"Ba zaki bi umarnina bake nan?"
Ya jefa min tambayar,
"Eh indai akan sabawa mahaliccena ne na gwammaci ganin kiyayyarka da tsanar cikin amma ba zan saɓawa ubangijina ba, duk halin laulayi da nake ciki ladane dan haka kayi hakuri."
"Maryam ban isa dake bane, da zan bada umarni kice a'a."
A ynx zuciyata tayi tauri, wani masifaffiyar taurin kai nake ji, da tsabar bala'i cikin izza nace.
"Ka isa amma akan zubda cikin baka isa ba, ai shi yasa kake shan kwaya dan ka zubda min ciki, Allah sarki kainuwa dashen Allah ba dashen ɗan mutum ba, ko zaka kashe ni sai na haifa maka cikin. Hhhhhhh"
Na shafa cikin ina dariya nace.
"Magajin Yunus ko magajiyar Yunus, kinji abinda Daddynku yake cewa wai kar......"..
"Keeee kina hauka ne, wacece ke da zakina faɗa min magana.".
Ban barshiya kai aya ba nace.
"Wacce ka iya raba dare gurin rayuwar aure da ita, kuma ka nuna ɗimautarka da gigitarka, akanta, wallahi idan kana son zamanmu ya ɗuri toh karka taɓa min cikina dan zan fito maka sak maryam da baka taɓa sani ba, zan tsaneka tsana mai tsanani, zank'i ka fiyye dakima."
"Har kima kike dashi keda baki da daraja, mi kike dashi na darajar wacce iyayenki ma, badake suka....."..
"Yunus Muh'd Marafa!!!! Karka fara kuma karka sake ka taɓa min iyaye, kai ɗin banza ans canza miji ba'a canza iyaye, ai daraja da kimana yasa ka gaza hakuri akan yar zabarmawa, da zaran ka ganta duk wani jarabarka da fitinarka yake tashi cikine baza'a cire ba naga wanda zai cire min, kuma kasake buɗan baki kazagi iyeyana zan baka mamaki, dan na lura ilimin addininka bai amfanek....."
Gefen hanya ya koma tare da riko hannuna zai murɗa na kalle shi cikn zafin rai har jikina na rawa nace.
"Wanda yayi niyya ya fasa, ya rena mahaliccinsa."
Kallon yanda kwayar idanuna suka koma yayi, dukar kan motar yayi yana cizon bakinshi.
Lokaci ɗaya na tubure mishi da masifa da bala 'i, gyaɗa kanshi yayi cikin ko in kula yace.
"Ok nidake wanda ya fasa."
Banza nayi dashi na kauda kaina, raina na kara ɓaci kuka ne ya tawo min, na kifa kaina akan cinyata. Sosai nake kuka duk abinda mutum zai min a duniya kar ya taɓa kimata, ina jinshi har cikin raina ne. Musaman iyayena lallai Daddy bai sona, dama can abu ya nima kuma ya samu.
Haka na cigaba da kuka, koda nasanin abinda ya aikata baiyi ba saima kokarin ganin ya samawa kanshi mafita.
Karfe goma sha ɗaya har da rabi muka shigo kaduna, ɗago kaina nayi naga ya sake hanya, juyawa nayi na kalle shi cikin tashin hankali nace.
"Kayi hakuri kasake ni, kaga babu wata damuwa iyayena zasu rikemu nida abin cikina."
"Ai bance bazan iya rikeku ba, idan goma ne ma zan iya rikesu sabida Allah ya hore min takowa ni sako da lungu dan haka. Karamar mara kunya bazan sake ki ba, sai nayi niyya cikin jikinki da zan cire gata zan miki dan har ynx baki san ciwon kanki ba balle kisan ciwon wani, dan ina kwanciya dake bashi zai sani kula da lafiyarki ba, idan kika kai lokcin ɗaukar ciki ni da kaina zan kaiki a duba ki, dan matuƙar aka cire wannan cikin toh zan idona akanki yanda bazaki sake ɗaukar ciki ba, sai na shir....."
"Kana da tabbacin zan sake kara wani wa'adine, Don Allah ka bar min cikina kaji zan fanshe shi da komi har da aurena zan fanshi cikina. Daddy ka wulakantani amma karka taɓa lafiyar abin cikina wallahi yanzan nake jin masifar sonshi, idan kace nabar garin kaduna na ɓace na shiga duniya zanyi dan cikina ya rayu, kuma namaka alkawarin bazan taɓa nuna mishi kai ba, don Allah badan nima dan darajar fiyayyen Halitta, ka barshi shima ya rayu kamar kowa, kabarshi shima yayi farin ciki kamar kowa, karka zubda hawayen Mahaifiyar da zata iya mutuwa dan ɗanta ya rayu mana, karka sani jin tsanarka fiye da kima. Wallahi bazan iya jure wannan zaluncin ba."
Wayata na ɗauko a jaka, na shiga niman nomber Ummana.
Yana shiga cikin sauri tare dafashewa da kuka nace.
"Ummana...."
Fincike wayar yayi tare da jifa da ita waje bayan ya buɗe window.
Hannuna nasaka akai sai kuma na tuna akwai Allah, abinda ya fara fitowa a bakina shine innalillahi.... Da wasu addu'o'i har muka isa asibitin. Motar Aneesah ya gani da sauri ya fita, tare da sakawa motar key, dake tasan da