Showing 24001 words to 27000 words out of 39506 words

Chapter 9 - MATAR SO BOOK 2

06 Sep 2025

3196

kimanin sati huɗu knn tun da yake fama da ɗimauta da zaran yaje cire cikin da aka zo zubdawa sai ya saka injin ɗin yayita aiki fiyye da kima yana ganin jini  na gudu a jikin macen.

          Koda su Aneesah suka shiga ɗakin kallonta yayi cikin fara a yace.
"Madam barka da zuwa, ya aiki."
     Yatsina fuska tayi tace.
"Ga aiki nan, amma ina ganin allura za'a mata, dan ni bana son wannan burge cikin allura yafi sauki."
        "Ok ba damuwa bari nakira nurse tayi mata kinsan kuɗin alluran dai 25k ne."

     Kuɗin ri ta ciro tabashi, kiran norse yayi a waya can sai gata. Faɗa mata abinda zatayi yayi taje tazo da alluran, tayiwa rita sannan sukayi godiya suka tafi.

          Babban Rita babban sojane anan kaduna,Yaransa maza huɗu sai rita mace ɗaya tal jida ita yake kamar rai ɗaya.

       Koda ta koma gida, ɗakinta ta shige, takwanta sabida yanda cikinta yake ciwo. Har dare bata fito ba dakanshi ya shiga ɗakin ya sameta kwance cikinta ya kumbura, ga jinin dake fita ta hancinta da bakinta.

     Kiran yayan ritar yayi Nike, yana shigowa ya cincinɓeta sai waje aka fita da ita sai cikin mota, inda suka nufi asibiti.

      Dakyar aka amshesu sai da mahaifinta ya fida id card ɗinsa na babban soja suka karɓeta.
  
           Nan likitoti suka shiga aikinsu tun takwas har karfe biyun dare sannan suka fito da ita, aka kaita ɗakin yan ɓari.
         Bin bayansu Babanta yayi har aka sauya mata gado, kuma zuwa lokacin jini bai daina zuba ba, bayan fitar wanda suka kawota tabuɗe idanunta cikin wahala tace.
"Am sorry Papa, naci amanar tarbiyan da kaimin, gashi nayo ciki a waje wai dan karka sani naje zubdawa ashe nice zan mutu."

    "Wani likitane yayi miki wannan alluran?"
       Dakyar ta iya buɗar bakinta tace.
"Kawata Anee."

    Jinin ne ya fara zuwa ta baki tana amayar dashi, tun tanayi.a hankali yar yaci karfinta karshe dai Rai yayi halinsa.

         A kiɗime Uban ya fasa ihu. Yana kiranta.

         D'ago kanshi yayi idanunshi, yana kallon Yayanta, jikinshi na rawa tsimin sojar ta motsa.  Nurse aka kira suka rufe gawarta, aka kai inda ake ajiye gawa.
 
       Gida suka komo, uwarta da suka faɗa mata mutuwar Rita ihu take tana dukar kirjinta.
                     Washi gari Aneesah ta nufi bankinsu, tun kafin ta isa taga yanda sojoji suke cin uban ma'aikata ana nima Anee. Tana zuwa gurin suka taso mata a gadarance tafito makale da id card ɗinta.

     ...... Tana fitowa suka kalle id card ɗin, aikuwa cikin hargagi suka ce ga Anee ɗin. Wani basamuden cikinsu yace.
"Kece kawar Rita Uchenna."
  Jikinta narawa tace.
"Eh"
  "Ok muje kace ubanka."

Suka tasa keyarta cikin motarsu, sai barrack suna kaita aka turata wani ɗaki inda aka zuba kartin mata sojoji, rufe da fuskarsu aka buɗe mata hayaki maisa tari da kwalla bayan cin ubanta da suke da bulala. Ta ko ina suke zaneta sai da suka mata likis sannan Baban rita ya shigo ya kalli yanda ta koma zama yayi cikin zafin rai yace.
"Zaki faɗa min, inda akawa Yarinyata allura ta mutu."

    A firgice ta mike zaune tare da dafe kirjinta ta fashe da kuka,tace.
"Ritaaaaa! Ce ta mutu, wayyo Allah na shiga uku wallahi bansan zata mutu ba, ce min tayi tana da ciki kuma bata son ta ɓata maka rai shine nace akwai inda nasani ana cire cikin, shiɓe tace na kaita wallahi Papa bansan zata mutu ba,da nasani bazan fara zama sanadin mutuwarta ba."

   Mikewa yayi yace.
"Kufito da ita muje asibitin."
     Kamar kayan wanki aka suka kwasota aka watsata a hilux, har rigasa suka isa, lokacin ana wani tashin hankali, dr yaje cire ciki wata budurwa ta mutu, shine abin ya zama rikici har da yan sanda. Ana cikin wannan sai ga su Aneesah.

                Nuna musu dr tayi gyaɗa kai Baban rita yayi take sojoji suka sauka, har inda yake suka rufeshi da mugun duka, tare da nurse.

          Dukanshi suke tun yana ihu har ya daina, haka suka masa mugun duka suka kuma jefashi cikin mota aka wucce da shi barrack.

        .......
    Duk wanda yaga yanda na koma sai ya sake kallona, dan gyarani mamah amarya take tare da min nasiha akan hakuri nayi kiba daidai misali.
     Kullum sai daddy yazo nikuwa naki zuwa, idan suka ga van fita ba sai su fara min faɗa, ni kuwa sai naje kofar gida nayi zamana a ɗan barandar malam, dake gurin a kewaye yake gurin idan na zauna bana gurin sai naji tashin motarsa nake fitowa.

        ****
  Zaune yake shida Huda ya zuba tagumi, cikin damuwa tace.
"Daddy kayi hakuri, Aunty Mom zata sauko. Dole tayi fushi amma kayi hakuri."

   Murmushi yayi sannan ya mike yace.
"Ba damuwa."

    Haka yabar makarantar zuwa masaukinshi,
          Washi gari ya nufi kaduna inda ya samu muguwar labarin abinda ya sami Aneesah.

      Nan aka tashiga da fita, iyayensu dashi kanshi, da farko sunbi baban rita cikin ruwan sanyi, ya nuna musu karfin kakinshi shine su kuma suka nuna mishi karfin kuɗi da sanaya, inda aka shiga aka fita karshe haka juya case ɗin kan Dr. Ita kuma akace shawara aka nima a gurinta ta bayar kuma bata da laifi.

     Sai dai tunda ta dawo, itama ta shiga firgici sabida mafarkan da take, wani lokacin idanunta biyu zatana ganin jini, yana gudu ko kukan babys. Lokaci guda ta sambatu da ihu.

       "Wayyo dasu nan zasu shige min jiki." sai aka ɗauka ko zafin bugun da tasha ne. Amna da suka sami labarin halin da Yunus yake ciki take suka mike da niman taimako,

           Na yunus ya haɗu masa da zafin tashin hankali da yake ciki. Karshe sai da balkisu tayi magana da su hajiya aka maidashi zaria.
   Dan kamar zai haukace, koda maganar yazo min taɓe bakina nayi nace.
"Allah ya kyauta nima haka suka hanani farin cikina can da yawarsu."

      ......... Dr kuwa asibitinshi ranar gwanati ta kwace, inda aka shiga ciki aka samu abin mamaki, wani gurin da yake tara, ɗiyoyin da yake cirewa a cikin mata, yana bawa wani katon karen tsafinshi yana cinsu. Ganin girman kare, yasa jami'an tsaro suka juya da baya, karshe suka cinnawa asibitin wuta.

         Yana can ya fasa ihu, tare da zabura da karyayyan kafarshi. Yana yaga rigar jikinshi. A bangaren nurse kuwa ba'a cewa komi.
              ****
      Addu'a malam sa'idu yayi ya mikawa Alhaji, aka saka mishi abaki dakyar yasha tare da cewa.
"Don Allah karku rabani da ita."

      "Bazamu rabaka da ita ba, ta lafiyarka muke." Inji Malam.
             
     Shiru sukayi Aman da yazo har zarian ya rikeshi tare da Sulaiman. Kwantae da shi sukayi,
  Ya rike hannun Sulaiman.
    Cikin raunaniyar murya yace.
"Karka rabani da ita don Allah, dan uwana."

     "Bazan rabaka da maryam ba, tunda kana son abarka."

       Yana gama faɗar haka ya fita a gidan, motarshi ya shiga tare da kifa kanshi. A jikin sitiyerin yana magana cikin damuwa. Yace.
"Wannan wata irin kaddara ce haka? Mi yasa suka min haka? Ni na dace da Maryama nina fara ganinta, amma suka ɗauketa suka m bawa wanda bai san kimarta ba mi yasa bazasu min adalci ba, su gane cewa nina dace da ita."

   Haka yayita surutunshi a gurin.

           ****
     Bayan yan kwanaki gane ganen da Yunus yake yanzun ya daina, sai dai damuwar da yake cikin ranshi a kaina, a ynz su Hajiya sun janye maganar saki sunce yayi kokarin mun daidaita.
     A cikin kwanakin ya dawo kaduna, inda ya cigaba da zuwa gidanmu ni kuma ina surfa mishi rashin mutunci dan banajin zan iya hakuri da abinda yayi min, ina zaune a tsakar gida, yaron makotanmu ya shigo wai.
"Baban Huda yana sallama da maryam"

       D'if na ɗauke wuta nayi banza da yaron na cigaba da chtt ɗina, sai da Umma ta leko cikin faɗa tace.
"Allah ya shiryeki ynx mutum yayi magana malam yace ana k'inki toh tashi mara kirki ki shigo dashi falon baki."
  Tura bakina nayi cikin jin haushi nace.
"Wallahi nikam bazan koma gidanshi ba, gwara ya daina zuwa min. Mutum sai kace mayye."

   Kwalllll naji an kwaɗa min abu a goshina aikuwa na fasa ihu wanda sai da Mama ta gintse addu'ar da take tafito ganina dafe da goshina yasata cewa.
"Kaiii Maryam, dalla kimana shiru sai kace an yanki da wuka. Dalla saka hijab kije ki shigo dashi."

    Figar hijab ɗin nayi, cikin kuka na fita. Nafita har waje yana jingine da mota, babu sallama cikin masifa nace mishi.
"Yau zaka sallame ni dan nagaji da zama da aurenka, idan kuma jikina kake bukata toh wallahi sai dai ka mutu, idan yayi maka kashigo dan kasan Iyayena kima ne dasu, da sanin darajan bakonsu tunda sunsan darajar kansu."

       ............Chaiiiiiiiii
🌹🌹🍀
         *MATAR SO*
                 🌷🌷🌻

*MAI_DAMBU*
*Wattpad:Mai_Dambu.*

Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai....

Sadaukarwa Ga Mai Nasara Team😂

     _Wannan buk ɗin hakk'in masu shine idan kinsan baki saya ba karki karanta, mai fitarwa kuma ki duba girman Alkawarin da kika ɗauka na cewa bazaki fitar ba, tunda nace idan kinsan zaki saya ki fitar na Yafe ba sai kin saya ba_

          
         
*BOOK 2👈*
    Page...8
       Cikin gidan nanufa yana biye dani a baya har falon baki, dama banshi gaba na koma cikin gidan na zauna abuna, fitowa Umma tayi ta ganni a zaune ranta ya kara ɓaci, ciki tashige ta ɗauko wyar caja sai ji nayi ta tsulla min da gudu na mike har ina faɗuwa bata fasa bina ba, har kofar falon bakin ihu nake ina kuka,, dakyar na samu na shige falon ashe shi ya buɗe kofar da niyyar kwatata.

               Na faɗa jikinshi ina kuka, mai da kofar yayi ya rufe kuka nake sosai ina jikinshi sam na manta da rigimarmu, shafa inda bulalar suka kwanta a jikina yayi, cikin matsanacin kewata.
               Zaunar dani yayi a kujeran yana kallon kalabar kaina, wanda suka zubo har kirjina dan na wancakalar da ɗan kwalin garin gudu.

        Kuka nake sosai ina mamakin mi yasa umma take tsanata akan yunus.
             Zaman da yayi kusadani yasashi jin bazai iya jure har na dawo gareshi ba, sai jin ya cusa hannunshi a cikin rigana.

          A firgice na dawo hankalina, tare da niman kwace kaina amma ina, ya min mugun riko wanda bazan iya kwatar kaina ba da hannu ɗaya,  ɗayar hannun kuma tana cikin rigana yana shagalinshi da ita.

   Kuka na saka tare da tureshi nace.
"Kyaleni ko natara maka mutane."
  Murmushi yayi sannan yace.
"Nima zanso haka, kinga zasu fahimci matata na biyo."

         Hmm mutumin nan gwanine a rashin kunya lokaci gida Mai nasara ya birkice min, nima kuma bakina bawai ya mutu bane, sai dai nasan zan kwaci kaina.
          Duk yanda nazo dakatar da al'amarin yawucce tunanina dan bai ji a ranshi ya kyaleni ba, sai da yabiya bukatarshi. Kuka nake sosai kamar raina zaifita haka ya jiyarda kanshi daɗi, da farin ciki dakyar na mike. Na ɗaura zanina Allah yaso da under dasu nagoge gurin da muka ɓata, yana magana amma ban saurareshi ba nayi cikin gida kamar munafuka na shige ɗakinmu, dake Aunty na ƙitchen wanka nayi tare da tsarkake jikina, ina kuka.

             Fita yayi a gidan rashin sawai sai wani nishaɗi yake ji a ranshi, gidanshi ya nufa. Ya sami balkisu a falo kallonta yayi yaga ta mike, sai kunyarta ya kamashi. Murmushi yayi sannan yace.
"Yau naje gidansu maryam tana gaisheki."

    Ganin yanda yake farin ciki, yasata fahimta duk yanda akayi Yunus yasami maryam kamar yanda yake so.

     Wanka yashiga yayi, sai murmushi yake dokawa, yana gamawa yafito. Sanye da jallaɓiya ya zuwa falon, abinci ta kawo mishi, aikuwa yaci sosai.

                   **** Bayan kwana biyu, naje gidan Aunty Hamdiya na wuni a gidan sai yamma na dawo ina dawowa nasamshi a kofar gidanmu, dake mangariba tayi shigewa nayi. A bakin mama naji wai tun huɗu yake kofar gidanmu, sallah nayi ina idarwa na mike. Zan fita mika min turara Mama tayi na goga a jikina, sannan tace.
"Don Allah ku fahimci juna dashi, babu daɗi zama haka ace baki da auren da karancin shekarunki ki fahimci Ummarki."

          Shiru nayi ina kuka. Sannan nafita wajen shi, buɗe motar yayi ya shiga. K'in shiga nayi sai da yace.
"Don Allah kishigo, ana kallonmu."

              Kamar na fasa ihu na shiga ko rufe kofar banyi ba, bai damu ba, mikar da hannunshi yayi yaja kofar ya rufe, sannan ya kunna Ac.

    Shiru nayi kaina a sunkuye kirjina kamar zai fita lura nayi da jikin gilashin motar, kamar mai duhune kai kana ganin na waje nawaje bai ganinta, sannan ta gabar motar ma kusan rabinta duhu ce,

       "Malam idan baka da abincewa zan fita."

          Shakar kamshin yayi sannan yace.
"Duk ɗaya ne, nidai kiyi hakuri mu koma gidanmu."

    "Taɓ naje kasa a cire min mahaifa, Allah ya min tsari." na faɗa mishi kamo hannuna yayi tare da kaiwa fuskarshi yace.
"Insha Allah ko yara dubu zaki haifa min ina sonsu."

    "Daga baya knn, wai anyi sadaka da bazawara."
      Na faɗi haka.
   "Ynx kina nufin nasake ki."
          "Yanzun naji batu wai an daki kwarto da buje"
   Zaro idanun yayi yana kallona.
      "Maryam yanzun kinfi sha'awar zawarci da zaman gidan mijinki."
               "Toh miye a cikin zawarcin, ai hannun hagu ba bakon wanke kashi bane."

           Tsura min ido yayi yana al'ajabin yanda nake faɗa mishi magana kai tsaƴe.
       "Yanzun babu ɗan girmamawa nan maryam."
      "Wai yanda baka tausaya min ba akan mi zan tausaya maka, Ina girman take? Hhh wai ancewa akuya sarkin fawa ya mutu' tace ya mutu da wukar yankanshine"

           Jingina yayi da seat ɗin motar yana nazarin yanda zai shawo kaina.
   Ganin babu halin haka ya kai hannunshi kan nawa na janye da sauri, take ya sake maisawa, sannu a hankali komi ya sauya da wayyo da dabara ya cima burinshi a cikin motar nima kamar wawuya bansan ya akayi komi ya faru ba sai da naji yana maida min kayana, sannan na fashe da kuka. Sosai rarrashina ya shiga yi, cikin kuka nace.
"Laifin mi na maka, a cikin gidan ubana da bani da kima da daraja kazo kake kwanciya dani, mi yasa bazaka je kanemi mata masu daraja da kima ba?"

     "Kiyi hakuri mana maryam, Allah ma muna mishi laifi  ya yafe mana sai mune baza mu yafewa juna ba nayi kuskure kiyi hakuri."

             "Bazan iya zama da kai ba, dan nima na rokeka ka juya min fuskarka baka son ganina da abin cikina da yana tare dani da yakai matakin da zanji bugun zuciyarshi, ka kashe min rayuwata ka hanani amsa sunar da kowacce mace take buri Uwa, waya sani ko shi knn bazan kuma haihuwa ba."

  Cikin ɗauki yace.
"Wallahi zaki kuma, ki zo muko ma gidanmu ki gani sai Allah ya bamu wasu."
Harara na ɓala mishi sannan nace.
"Buɗe min kofa nafita."

   Ba musu ya buɗe min nayi waje abina.

         .......Tun daga ranar ban kuma jin ɗuriyarshi ba,sai da muka kusan sati biyu sannan na ganshi, a lokacin yazo zai murjeni  akayi rashin dace nima ina up,  dole ya haɗi maitarshi amma bai ji daɗin haka ba.
     Duk yanda zan kuntatta mishi ina bi dan duk da ina hutun kullum sai yazo ya matseni son rashi.
               Cikin kwanakin nan wani zazzaɓi yake fama dashi, ga meeting da yake zuwa akai akai, wanda dakyar yake fita, karshe Ahmad ne ya amshi zuwa meeting ɗin.
     Shi kuma ya dawo gida ya cigaba da jinya, kiran Dr Nafi Balkisu tayi. Taxo ta sanya mishi ruwa da allura.

           Bayan karewar ruwa daf magrib, Aman ya kirashi yana sanar mishi da cewa.
"Yunus mun gama komi, sai tafiyarka kawai ya rage wanda muka so ɗagawa amma sunce haka ba zai yu ba, ka daure ka tafi idan ba damuwa muma munso zuwa toh a gaskiya baidace mu tafi dukkanmu ba."
         Can kasar makoshinsa ya amsa sannan yace.
"Nagode."

   Kallon Agogon ɗakin yayi, ya mike dakyar ya nufi ban ɗaki wanka yayi da alola, ya fito sanye da rigar wankan sannan ya buɗe gurin kayanshi yasaka kayanshi.

   Wani irin bakon yanayi wanda yake ɗauke da kewata, masalaci ya nufa.
       Bayanan idar da sallah, gida ya dawo ya ɗauki key sai unguwarmu.
         Ina daki nayi wanka kenan zan gabatar da sallah akace wai yana sallama dani, tsuka nayi kasa kasa,
Sannan nayi sallah na, na gyara jikina. Riga da wandon pakistan mai ruwan kwai nasaka sannan na ɗauko hijab ɗina wanda bai kashi haske ba, nasaka.
   Murmushi nayi  a raina nace.
"Gaskiya Rahilah ta kyauta min da ta kwaso min kayana kaf, daga gidanshi."

             D'aga labule Mama tayi tare da mika min kofi tace.
"Sha maza."
     Kaman zan fasa ihu haka na shanye sannan na fita, sai da nashanye naji wani mugun daɗi a maganin har na isa bakin kofa na dawo nace.
"Mama ko zaki kara min wannan maganin daɗinshi yayi yawa."
    Hararata tayi da sauri nafita, oho dai nasan koma ya-ya ne maganin yayi min daɗi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login