Showing 27001 words to 30000 words out of 39506 words
kuma sai na koma ta kara min.
Ina fita nasame shi a cikin mota, shiga nayi nima na zauna. Ko kallonshi banyi ba na juya mishi baya, tada motar yayi kafin nasan abinyi tuni ya cillamu kan titi, shiru nayi ina tuna faɗar da Umma tayi min, yau da safe akan yan unguwa sun fara surutun naki komawa gidan mijina. Kuma muna tanbaɗewa a waje, maganar dai ba daɗi haka na shanye jinsu gidanshine dai bani komawa.
Tsohon gidanshi ya kaini, kafin nan ya tsaya a wani store yasaya mana fresh milk, can gaba kuma yasayi nama.
Har muka shiga cikin gidan, kin fita nayi a motar yazo ya kwashi kayan yayi ciki dasu, dawowa yayi ya buɗe inda nake ya sunkuceni sai cikin gidan.
A falo ya direni sai a lokacin naji jikinshi zafi, ina son tambayarshi amma na kasa, shiru nayi na cigaba da zama a kujeran dake kusada shi, kitchen ya shiga ya duba bai ga komi ba, dakyar ya buɗe dirowar kitchen ɗin. Ya ɗauko kofi da filet, buɗe famfo yayi ya wankensu sannan ya fito.
Juye namar yayi, wai zai bani ko kallo bai isheni ba nace.
"Kasan nafito gidan da aka san darajar ɗiya mace ne kuma Alhamdulillah, talakan mahaifina ya ciyar dani, kaci kayanka kawai."
Lumshe idanunshi yayi yana jin saukar maganar da na faɗa mishi, ajiye namar yayi, sannan ya mike tsaye ban gama tattara nutsuwata nasan mi zaiyi ba sai naji yayi sama dani.
"Dalla ka sauke ni, ka maidani kamar yar babyn wasan yara."
Bai tsaya a ko ina ba sai ɗakinshi, ya ajiye ni sannan ya rufe kofar, zanin gadon ya zo ya cire tare da buɗe gurin da ake adanasu ya ɗauko wani ya shimfiɗa.
"Kazo ka maidani gida, bana son abinda kake min."
Bai kulani ba, sai ma fincikoni da yayi, na fada kanshi zubawa juna ido mukayi,.muna kallon cikin idanun juna.
Sumbatar goshina yayi daga nan ya gangaro wuyana har zuwa kirjina.
Lumo nayi a jikinshi, tsigar jikina na mikewa. Zare min hijab ɗina yayi, ya ajiye a gefe. A hankali ya cigaba da bina har ya zuge zip ɗin rigana ya ajiyeta a gefe, ɓale bra ɗina yayi, sannan ya cigaba da abinda yake yi.
"Maryam!!!"
Ya kira sunana, "Hmmm" nace mishi.
Sabida ni kaina na masifar faɗawa hannunshi.
"Zaki koma gidana? Mu cigaba da rayuwarmu."
"Humhhum."
"Ki min magana mana, wannan humhum yana cutar dani."
Gyara kwanciyana nayi A kirjinsh, ina jin sakonshi na bin jinin jikina. Sonshi da kaunarshi suna ruruta min kwanyana.
Karan zuge zip ɗin wandona naji na ɗago kaina a kasalance ina kallonshi.
Lumshe idanuna nayi sannan nace.
"Yanzun dai kazo ka tasani a gaba, zaka nutsu dani. Sannan kaima kanka baka da lafiya, kuma zakayu aikin karfi, kuma nan gaba nasake dakai ka zageni har da iyay..."
Ban sami damar karasa maganar ba, sabida yanda ya haɗe bakinmu. A zafaffe ga jikinshi zafi yake karayi.
Sannu a hankali yunus yacima matsaya guda, bayan ya ɗauki dogon lokaci yana gurjeni son ranshi tare da sarafani. Tuni zazzaɓin suka fecce, sai gumi dake sauka a jikinshi.
Idan ana kiran jigata toh yau najita a hannun Mai Nasara dan sai da ya min filla filla, sannan ya kyaleni, na koma gefe nasake kuka sosai, sabida bansan yazanyi da raina ba, Yunus yayi min abubuwa dayawa, kuma sai bina yake yana yanda ya gadama dani.
Janyoni yayi jikinshi yana shafa bayana tare da bani hakuri, da rarrashi.
Kwace kaina nayi naje ban ɗaki nayi wanka, ina dab da fitowa ya shigo tare da rufe kofar, wanka yayi shima. Muka fito lura nayi da mutumin nan baisan gajiya ba, dan ina son saka kayana amma ya kwace tare da maidani gado, yayi min rumfa.
Ina ji ina gani, yasake samun nutsuwa dani, kallon a gogon ɗakin nayi naga sha biyu har da rabi, na tashi na faɗa ban ɗaki nayi wanka da alola nazo nagabatar da Isha tare da shafa'i da wutir.
Mikewa yayi shima ya faɗa banɗaki yafi.
Sallah yayi, yana idarwa na fashe da kuka nace.
"Ka maidani kamar inji ka ɗaukoni, ka kawo ni nan. Dan baka san daraj."
Saka hannunshi yayi a bakina yace.
"Maganarki tana min zafi sosai maryam."
D'agani yayi. Sannan ya cire min kayana ya zaro wata shirt ɗinshi yasaka min, muka koma gadon,
Rungume ni yayi barci yayi gaba damu, kiran sallar asuba ya tadamu, mukayo alola shi ya tafi masalaci ni kuma nayi a gida.
Yana dawowa na tada rigima, sai ya maidani gida, lallaɓani yayi cikin dabara da wayo yasake moreni, yana gamawa nasaka kayana dan ko wanka bayi ba, nace gida kawai.
Saka kayanshi yayi, muka fita ɗaukar naman yayi muka bar gidan.
Allah yaso har muka isa gidan malam na masalaci, yana tsayawa ina fita mika min laidar yayi da atm card ɗinshi da pin ɗinshi.
Da sauri na shiga gidanmu, umma da Aunty suna kitchen.
Ummana ce kawai taga shigowats,
Ban ɗakinta na wucce naje nayi wanka, ina fitowa nasameta a bakin gado, kunyace ta kamani. Nace.
"Ina kwana Umma!"
"Kiwa zuciyarki adalci ki bata abinda take so,.yau ce rana na uku da na kamaki kina wanka, maryam ni bazan hanaki farantawa mijinki ba, amma idan yazo kice ya sami Malam.ki koma ɗakinki na gaji da surutun mutane."
Cikin kiɗima nace.
"Wallahi Umma ba wannan wanka da kike tsamani bane."
"Jiya a ina kika kwana?"
Sunkuyar dakaina nayi,
"A gurinshi ko? Karki maidani yarinya maryam, kowa ya bata yasani kowa ya gyara yasani, gyara kayanka bai zama sauke muraba ba, Allah ya kyauta."
Tana fita na fashe da kuka, sosai sabida na mata musu akan gaskiyarta iyakar abinda tagani tayi min faɗa akai amma naki ji,
*****
Zarya yake a ɗakinshi duk yasawa kanshi damuwa akan matar ɗan uwanshi, ajiyar zuciya ya sauke lokacin da ya tsinci sakon karta kwana a wayarshi, dubawa yayi sannan yasake murmushi,
Sake kiran wayar yayi yace.
"Kasa ido akan komi, yau zai bar kasan nabaka wuka da nama."
Kashe kiran yayi sannan ya nemi guri ya kwanta, yana kaɗa kafanshi.
"Maryam Sajida.......Na kusan mallakarki."
Yana faɗan haka ya sake yar karamar murmushi.
****
Koda Daddy ya isa gida, ɗakinshi ya wucce da sauri. Yana rufe kofar shi. balkisu tarda a cikin ɗakin duk sai yaji ya muzanta a gabanta, murmushi tayi sannan tace.
"Daddyn Huda, ya jikin naka."
Kauda kai yayi cike da kunya yace.
"Da sauki."
Yana gama faɗar haka ya shige ban ɗaki. Fita tayi a ɗakin jikinta ba kwari, da ciwo ace mijinka ya kwana a wani gurin, saukin abun tasan duk inda zai kwana toh da Nice ko Fareeda tunda dukkanmu bama gidan...
Abinci ta haɗo mishi tazo tasamu yana shiryawa cikin black suit.
Ajiye mishi tayi sannan ta juya zata fita yayi maza ya riko hannunta, yanjota yayi jikinshi.
Tare da rungumeta kishin mijinta da kaunarshi suka karya mata zuciya, bata sannan sadda ta fashe da kuka ba, bubuga bayanta ya shiga yi har tayi shiru.
Hannunshi nakan kugunta ya kai bakinshi kunnenta yace.
"My Billy am sorry, bazan kuma ba. Amma maganar gaskiya ba halina na sauya ba ina tare da kanwarki maryam ce."
"Dama ni bance komi ba, kawai dai bana jin daɗin haka ne amma zanyi kokarina gurin samun farin cikinka."
Shiru yayi yana kallonta, tausayi ta bashi, sabida yasan bata da damuwa da fitinarshi amma yanda shi kanshi yake mantawa da cewa itama mutunce yasashi nufar gado da ita. Rike shi tayi tare da ware ido tace.
"Mi kuma zakayi."
"Shhiii."
Ya saka yatsarshi a bakinshi, daga nan kuwa lulawa yayi da ita duniyar majidaɗi. Kishi yasa Balkisu kasa ɓoye jin daɗinta har da kuka(😹)
Bayan sun dawo daga duniyarsu yana rungume da ita yace.
"Tayu idan nafita yanzun bazan dawo ba natafi kenan."
"Kamar Ya?"
"A'a nufina idan na fita zan wucce china sai nan da sati biyu zan dawo koma ya-ya ne ki kula min da kanki da kuma Yarana da Fareeda da Maryam, idan na dawo duk zan dawo dasu inyaso fareeda na kaita asibiti a dubata, ko Allah zai sa a dace. Kema sai a duba min ku."
Gyaɗa kai tayi.
Mikewa yayi ya shige ban ɗaki wanka yayi a gurguje yasa kayanshi sannan ya buɗe ma'ajin kayanshi ya ɗiba tare da shiryasu a jakarshi, ya fita.
Addu'a tayi mishi sannan ta gyara kwanciyarta,
****
Ahmad da Aman su suka mishi rakiya, airport. Kafin jirginsu ya tashi ya tura min.
*Zan tafi bamu yi sallama ba koma Ya-ya ne Ina kara baki hakuri da Kuskurena*
🌹🌹🍀
*MATAR SO*
🌷🌷🌻
*MAI_DAMBU*
*Wattpad:Mai_Dambu.*
Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai....
Sadaukarwa Ga Mai Nasara Team😂
_Wannan buk ɗin hakk'in masu shine idan kinsan baki saya ba karki karanta, mai fitarwa kuma ki duba girman Alkawarin da kika ɗauka na cewa bazaki fitar ba, tunda nace idan kinsan zaki saya ki fitar na Yafe ba sai kin saya ba_
*BOOK 2👈*
Page....9
Daga
Masoyinki Mijinkii
Kashe wayar yayi yasaka a aljuhunshi sannan ya mikawa su Ahmad hannu yace.
"Allah ya kaddara saduwarmu."
Rungume shi sukayi kamar zasu fasa kuka, shelar jirginsun zai tashi yasa shi ɗaukar jakarshi ya kai inda ake sakawa kafin a shiga jirgi.
Yana ajiyewa ya juya zai wucce suka bangaji juna da wani matashi, ɗago kai yayi ya kalli Matashi, wanda ya diririce tare da cewa.
"Sannu bansani bane."
Yana faɗar haka ya bar gurin.
Wuccewa shima yayi gurin jirgi, ya shiga jikinshi ba daɗi. Har jirginsu ya tashi ,zuwa abuja daga can zasu wucce.
****
Tunda Umma tayi min faɗa nake kwance, a gadonta jikina ba karfi. Karan wayata naji na mike na duba sakonshi, tsaki nayi nace.
"Ka kware a yaudara."
Kallon sakon nayi musaman kalmomin mijinki Masoyinki. Jifa nayi da wayar na koma na kwanta abuna.
Tuni barci yayi gaba dani sabida gajiyar dake jikina.
.......
Kwana goma da tafiyarshi Malam yakirani wai na bashi wayata, mika mishi nayi ban san mike faruwa ba, sai dai naga Umma ta fara azumi da yawan sallah dare.
Ga saukar alkur'anin da ake akai akai, oho su suka sani, dan i yanzun wani sabon lalaci nake ji. Kwanciyar kasa ya aureni, har da sadaki sakamakon zafin da jikinA yake akai akai, sai shan ruwa.
Abinda na lura an dakatar da koda jin radio ne a cikin gidanmu, sannan an hana yan uwana zuwa.
Nima kuma malam yace kar a barni na fita, abin haushi toh ina ake son naje.
....... Shiru Ilahirin familyn Mai nasara sukayi har da Fareeda da Balkisu, kuka Huda ya cika musu kunne. Cikin karfin hali Balkisu tace.
"Huda ya isa haka, Addu'ace mafita ba kuka ba."
Zaro Manyan idanunta tayi, cikin tashin hankali tace.
"Mommy kinsan halin da yake ciki kuwa? Kinsan hukuncin da zasu yanke mishi kuwa, wallahi a cikin mutane suke fille kan duk wanda aka kamashi ya shigar musu da kwaya, sharri akawa Daddyna ba halinshi bane."
Shiru duk sukayi cike da damuwa, Musaman Hajiyar shi. Mama kilishi tace.
"Allah sai ya saka mishi, duk wanda yayi mishi wannan abun."
Amin kowa yace, banda sulaiman.
****.Abinda ya faru kuwa, lokacin da suka bar naija daga abuja. Suka nufi china har sun isa a babbar birni Behjin anan garin screen aka samu hodar ibilis a jakarshi, an buɗe gefen jakar aka saka, ba'a ma rufe jakar ba.
Cikin abinda baifi dakika ba yan sanda suka tisa keyarshi zuwa ofishinsu. Nuna mishi abinda aka samu a jakarshi sukayi rantsuwa yayi musu bai dan da zancen ba, asalima shi ba bakon kasar bane.
Nan dai aka shiga musaya yana cewa bana shi bane suma suka kafe, Abokan kasuwancinsa suma suka zo aka tai gumurzu da jami'an tsaro.
Cikin awa guda har an watsa a kafar sadarwa,
*Ankama Attajirin ɗan kasuwan nan Yunus Marafa a filin jirgin Sama na kasar china sabida zargin da ake mishi na shigowa da hodar ibilis*
Take ko ina ya amsa, ya kuma yaɗu,
Gidajen talabijin na kasashen duniya suka haska, gidajen radio suma suka ɗauka.
Mr Huchug shi ya kira Aman ya fada mishi halin da ake ciki.
A kwana na biyu suka isa can har da Alhajinsu Yunus, da kuma Ammbassy na naija, abin fa ba karamin ɗaga hankalin mutane yayi ba, duk yanda akazo ayi abin cikin sauki da niman alfarma Kasar china taki amincewa sai dai ta basu wa'adin shigar da kara.
*****
Kusan wata guda kenan da faruwan al'amarin tun suna samun ganinshi yanzun an chanza mishi wani state, dole suka hakura.
Ni kuwa ina nan ina fama da kaina, da yawan zazzaɓi da amai. Ga kwanciyar kasa, tuni Umma ta gano al'amarina, cikin sanyin jiki take min sannu.
Dan tausayi na bata. Koya zanji idan naji labarin abinda yasami yunus.
Mikar dani tayi ta zaunar dani, sannan ta haɗa min tea mai zafi wanda tasaka na'an'an da citta, sai zuma da ta ɗiga a ciki.
A hankali na kurɓa jikina ba kwari, nace.
"Ummana!!"
"Na'am Maryam" tace min.
"Ummana har yanzun baidawo ba, kuma malam ya kwace min Wayana ina son naji muryanshi, na faɗa mishi bani da lafiya."
Rungumeni tayi tare da shafa kaina idanunta na cikowa da kwalla, Cike da tausayina tace.
"Insha Allah zai dawo, nan kusa ki daina damuwa bake ɗaya bace yanzun kina da lalura a tare dake."
D'ago kaina nayi cikin sanyi murya nace.
"Ummana dagske abinda nake tunanine.".
Murmushi tayi wanda yasa kwallar zuba, tace.
"Wannan watar kinyi wankinkine?"
Girgiza mata kai nayi. Alamun a'a.
"Kinga cikine dake." kuka na saka mata ina kara riƙeta nace.
"Ummana ki yafe min, wallahi cikinshine ba'....."
"Ya isa Maryam waye faɗa miki ina zarginki, ai nasan komi. Autana tayi rashin kunya bata da aji da zaran miji yayi mata daɗin baki zata bashi haɗinkai, koda yake ai da taimakon Mamankune tunda ita ke baki kayan mata."
Kukan jin kunyarta nake tare da ɓoye fuskana a jikinta.
Umma da Mama sun ɗauki kulawar duniya sun aza bisa cikin jikina bana komi sai wanka da sallah, sai azkar.
....... A yau tashin hankalin da familyn Yunus suke dashi yafi na koda yaushe, dan jiya aka yanke mishi hukuncin kisa, a jahar Huj.
Kuka da tashin hankali babu wanda basu shiga ba. Haka ya taɓa zuciyar sulaiman amma idan ya tuna yayi hakane dan kudirinshi sai yaji hankalinshi ya kwanta.
Sunso amso gawarshi amma Alhaji yace a bar musu shi a can dama can ne kasarshi yake.
........Ina kwance naga cin ɗan malele, har da kwanciyana dan ya faɗa. Kukan da salati naji, kamar bazan fito ba na mike nafito Rahilah na gani Mama tana mata fada sun ɗauka ina barcine.
Jina da gani na ne, suka tsaya cak, sakamakon jin mugun labarin Wai mijina babu.
Dafe kirjina nayi tare da fasa kara na zube a gurin, a ɗimauce suka yo kaina. Tare da ɗaga ni.
Jinin dake bin kafafunq yasake ɗaga musu hankali, Jakar Rahila da yake yashe taja takira Aman cikin tashin hankali take labarta mishi.
Kamar zautacce haka yajuyo zuwa gidan. Ko parkin mai kyau bayi ba, yafito a guje. Yana shigowa bai ɓata lokaci ba ya ɗaukeni suka nufi asibiti dani.
A gaggauce aka amsheni inda aka shiga kokarin tare cikin.
Cikin Ikon Allah jinin ya tsaya, shame shame suka maidani wani ɗakin, shi kuma Aman yaje ya biya duk wani bill.
Umma da bata gidan tana dawowa Gausiya