Showing 30001 words to 33000 words out of 39506 words
ke faɗa mata abinda ya faru, cikin juriya da hakuri tace.
"Toh Allah ya kyauta, nima naje Makarantane munyi meeting zamuje zaria ta'aziya."
Shiru sukayi, can dai Umma tace.
"Bari nakira Rahilah naji a wani asibiti suke."
Kiran Rahilah tayi, tambayeta. Tana faɗa mata ta kira Malam wanda tun safe yake zaria.
Komawa kusada Alhjnsu Daddy yayi ya faɗa mishi halin da nake ciki. Ba tare da ɓata lokaci ba, yayi musu sallama.
........Kwana na biyu a kwance na farka, buɗe idanuna nayi na sauke shi akan Hajiyar Daddy nayi bansan lokacin da na fashe da kuka ba, tare da mikewa nace.
"Wallahi bai mutu ba, Mijina na raye ya za'ace ma kowa mijinshi bai mutu ba, sai nawa."
Ban san iya adadin abinda nake faɗa ba, ni dai surutu nake tare da yunkurin mikewa, shigowar likita da nurse suka min allura yasani barcin dole.
Wani irin tashin hankaline ya shigo rayuwata kamar mahaukaciya, bana hmm bana humm. Idan kuma zanyi magana toh ba tada daɗi.
Ga jinina da yayi mugun hawa yaki sauka, cikin jikina kuma ko kuda ba'a kaunar ya kusanceshi balle wani tashin hankali, ga baki ɗaya na birkice na susuce.
Hauce ta sameni dan idan na fara sumbatu, sai kowa ya zubda kwalla ga shi nayita faɗar irin sonda nake mishi.
Lokaci guda Sulaiman ya tattara son duniya da kulawa ya ɗaura mana, nida abincikina.
Azbtuwa akan mijina nayi shikan dan gani nake nima mutuwar zanyi.
Addu'a akace makamin mumuni dashi Iyayena suka dogara dan ba dare ba rana, ga wanda ake bani nake sha sabida cikin jikina ga kuma na nima min lafiya.
**** Lokaci ya tafi sosai dan har an sami watanin da faruwar Al'amarin kusan wata shida, sai girman da cikina yayi sosai zama nake na shafa cikin ina musu sambatu. Inda ya juya ,
"Yawwa babyn Daddy yau kuma wani labari kake so nabaka, ko na daddy kake so."
Haka zanyi shiru dazaran ya motsa dan sake dariya nace.
"Kafin nan zamu fara karatu dan ina son kazama malami ba ɗan kasuwa ko me dukiya ba, wanda alumma zasu amfana da kai dan bana son narasaka yanda narasa mijina Masoyina ba,
Haka zan ɓata lokaci indai ba sallah bane zanyi toh ina zaune muna hiran daddy da halinshi.
Sai da nasami wata goma cif, kafin wata jumma'a ns tashi da ciwon nakuda.
Tun asuba nake fama dashi. Har akayi azhar. Ina fama dashi ban faɗawa kowa ba, sai da Mama ta fahimci walwalana yayi kasa yau, sai kuma zaryan da nake daga cikin ɗaki zuwa, waje.
Shine ta sami Umma.
"Yaya Maryam fa kamar haihuwa ce."
"Eh nima na fahimci haka tun safe, bari tasake ɗaukar lokaci sai kuwucce asibiti."
"Allah yaraba lafiya.". "Amin."
Tabbas naci wuya kafin la'asar nayi laushi, haka suka shirya kayan da sulaiman ya kawo, muka wucce asibiti.
Muna zuwa suka amsheni, inda suka duba, ina mataki na takwai 8cm.
Nan ma wani gumurzun nasha dan ban haihu ba sai karfe biyar na asuba, bayan anfito masalaci.
Yaron farko ya diro, biyar da talatin da ɗaya, tsakaninsu da ɗan uwanshi mintina uku, take kukansu ya ciks ɗakin.
Ajiyar zuciya na sauke. Kalmarshi tana yawo a kunnena lokacin da nace. Na koma gidanka kasa a cire min mahaifa.
Cikin rawan jiki yace..
"Wallahi bazan taɓa aikata haka ba ni ko yara dubune ina sonsu. Ki haifa minsu kiga soyayyar da zan musu."
Kuka nake sosai Allah sarki Ya tafi yabarni da marayu.
Ganin ɗago kaina nayi naga yanda Nurse ɗin take wani dangware min yara, kamar ranta a ɓace yake dan an tasota ta gyara musu jiki. Basan lokacin da nace.
"Keeee ki bi min yara a hankali idan bazaki gyara su ba, ki bar min su kifita ki kara min Mamana a waje, banza dake kina dungure min yara dan baki da imani, sake min yarana kifita."
Masifa yasa wacce take kula dani tashiga bani hakuri ni kuma nace tabar min yarana dole aks kira Babbansu, ita tazo ta amshi aikin wancar kuma aka ce tafita zasu ji da ita.
Ajiyar xuciya na sauke, lokacin da aka miko min Hassan, karɓanshi nayi na kifashi a kirjina, sannan na amshi hussain na kifashi akan cikina, ina jin sautin bugun zuciyarsu da yar kiriniyar da suke irinta niman abinci.
D'aga Hassana nayi nace.
"Barka da zuwa Mai Nasarama ka dawo min ko."
Ajiyeshi nayi bayan na sumbaci goshinsa. Na ɗaga Hussain nace.
"My Sameer kaima kadawo min ina sonku dayawa sosai ynz zamu cigaba da hiranmu tunda kunzo duniya zan nuna muku hoton daddynku, da Aunty Huda da Aunty Mufeedah da kakaninku."..
Kasake Nurse ɗin sukayi suna mamakina, karɓan yaran sukayi aka sakasu a wani gadon ni kuma aka bani kayana na sauya min wani gadon suka taimaka min na hau aka fita dani.
Ga yarana a gefena, idanuna na cigaba da zubda kwallar kewar mahaifinsu, farin cikin da Mama tashiga ba'a magana zatq kira malam sai gasu tare da Umma, ɗakin da aka kaini suka nufa.
Gyara min kwanciya nurse ɗin sukayi tare da saka min yarana a gadon yara da aka tanadar,
Kallona Umma tayi, tana murmushi, shafa kaina tayi, tace.
"Masha Allah, Uwata har yara biyu."
Daukar ɗaya Mama tayi Malam ya ɗauki ɗaya addu'a suka musu, sannan aka ajiyesu Malam yace.
"Mata nayi ko abokaine?"
Kauda kaina nayi tare da fashewa da kuka, nace.
"Malam Yunus ne da Muh'd, ku gafarceni da rashin ɗa'ar da na muku bani da zaɓine shi yasa har naji na kirasu haka."
Murmushi Malam yayi sannan yace.
"Toh Madalla aikinyi dai dai, uwata amma kafin nan zanbi kasuwa na sayo bulala sabida sun gajiyar min da uwata, kinga yands kika koma kuwa."
Kin juyawa nayi ina dariya, sabida soyayyar da nagani a idanun iyayena suka farawa yarana yasani jin kwarin gwiwa..
Barcine yayi gaba dani......
........"Ai nasan baka mutu ba kana raye kazo ka amshi yaranka..."
Kuyi maneji, saura kirsss.
Akwai uzurin da ya kutso min Insha Allah an kusa zuwa Iyaka nagode.
🌹🌹🍀
*MATAR SO*
🌷🌷🌻
*MAI_DAMBU*
*Wattpad:Mai_Dambu.*
Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai....
Sadaukarwa Ga Mai Nasara Team😂
_Wannan buk ɗin hakk'in masu shine idan kinsan baki saya ba karki karanta, mai fitarwa kuma ki duba girman Alkawarin da kika ɗauka na cewa bazaki fitar ba, tunda nace idan kinsan zaki saya ki fitar na Yafe ba sai kin saya ba_
*BOOK 2👈*
Page....10
Cikin kuka nake mika mishi yaran, amma ya gaza amsa sabida mawuyacin halin da yake ciki.
Ajiyesu nayi na isa gareshi na zuɓe a jikinshi nace.
"Yunus Yaranka ne fa, kazo ka amshesu."
Kallon yayi cikin tsananin azabtuwa yace.
"Ban chanchanci zama mahaifinsu ba, sabida ɓarnan da nayi Maryam. Hakkinki yaki barina gashi an mana katanga a tsakaninmu, ki rike min amanar kanki da Yarana, karki...."
Rike shi nayi sakamakon ganin ana janshi ina ihu. " kusake min Mijina....."
Jin ana danne ni yasani buɗe idanuna ashe tun fara mafarkin aka kira likita, mikewa zanyi suka tsira min alluran barci tuni na koma sabida karfinshi.
Karfe uku na farka naga ɗakin ya cika da mutane, dafe goshina nayi ina kallonsu. Hajiyarsu Daddy tace.
"Sannu Maryam, Barka da arziki Allah yabaki lafiya, su kuma ya rayasu tafarkin Sunnah."
Lumshe idanuna nayi na kalli Mama Amarya nace.
"Mama ina son gyara jikina."
Ita da Aunty Hamdiya suka zo kaina, ɗagani sukayi Mama ta samin Hijab, na sauka a hankali a jingina nayi da jikin Aunty Hamdiya, ta rungume ni sosai muka shige ban ɗakin. Kafin su fito Rahimah ta cire zanin gadon ta shimfiɗa wanda Umma tabawa Matar Yayanmu.
Dake Asibitin na kuɗine har da room heater, ruwan wanka Mama ta haɗa min nayi da kaina, kallona tayi cikin tausayawa tace.
"An miki ɗinki ne."
"A'a"
Fita tayi bayan tace na shiga cikin ruwan idan nagama. Watsa ruwan yayi min daɗi nusaman da na shiga ciki, saka kunne nayi naji yaran na kuka, da sauri na watsa ruwan, riga da zanin da aka kawo min nasaka tare da hijab ɗina nafito.
Raba idanuna nake, ina kallon waye ke kuka a cikinsu.
" Zauna mana Maryam! Wannan mai gidan da alamu bazai iya azumi ba, dubi yanda yake niman abinci kamar wanda aka masa yasa a cikinshi."
Zama nayi bakin gado, Mama ta miko min katon Cup da Tea, kasa karɓa nayi sai da ta sake mika min na amsa zuciyata na gurin Yarona.
Kurɓa nayi naji yaron ya callara kara, irinta jarirai. Bansan lokacin da na haɗiye tea ɗinba har da kwarewana. Sannu suka min, burina su bani Yaran amma na lura bazasu bani ba,
Ni kuma kunya tasa naki kallon inda yaran suke, kaɗan nasha tea ɗin na ajiye filet ɗin farfesun kayan ciki Mama ta mika min kamar magani haka nake ci. Shima banci dayawa ba na ajiye.
Sai a lokacin Hajiyarshi ta mike ta kawo min Yaron da yake rigiman ta ɗaura min akan cinyata, kallonta nayi idanuna cike da kwalla nace.
"Hajiya ya zanyi dashi."
Murmushi tayi sannan ta gyara min rikon yaron tace.
"Yanzun ki ciro mamar ki bashi da bismillah."
Sake kallonta nayi zan tambayeta an musu huɗuba ne, tare da basu dabino.
"Ki shayar dasu an gama komi."
A hankali na mai dashi cikin hijab ɗina, na ciro nono ta kasar rigar jikina nasaka mishi a baki. Sai naji kunya ta kamani naki kallon kowa.
Kama nono da yaron yayi yasani cewa.
"Ya Salam."
Da ɗan karfi, sannu suka ce min. Tare da karfafa min gwiwa. Gaskiya shayarwan farko ba daɗi. Dariya Rahilah tai min tace.
"Sannu Uwar two, akwai zafi ko."
Tura baki nayi cikin rigima nace.
"Mama kinjita ko."
"Eh mana don Allah ki ɗaga hijab ɗin nan dan ba mamaki iska yaron yake ja,nd ki kalli yaronki for first time."
Inji Aunty Hamdiya dakyar na zare hijab ɗin, na kalle yanda yake tsotson nono. Haka kawai sai tausayinsu ya kamani, da kuma tuno mafarkina.
"Hajiya Daddy yana raye fa."
Shiru suka min tare da zuba min ido,
Ganin zasu maidani mahaukaciya nace musu.
"Yana raye bai mutu ba, wallahi da gaske nake faɗa muku, ku tsananta addu'a yana bukatar addu'armu."
"A ina kika ganshi?"
Muryan Sulaiman yayi min bazata,
Janyo hijab ɗina nayi na kalli cikin idanunshi nace.
"Mafarkinshi nayi, kuma jikina na bani yana raye."
"Ki daina damun kanki ki kula da Yaranki, har Allah ya kawo miki miji nagari, kiyi aure."
"Wannan kuma ai zance banzane babu auren da zanyi ina nan ina jiran mijina ko shekara dubu zaiyi zan jirashi, duk wanda zamana ya takura mishi sai yasan nayi dani Amma ni matar Yunus ne."
Ina gama faɗar haka na fashe da kuka. Mi yasa komi sai nice na rasa cikina a farko, Yanzun narasa mijina, "Ya Allah na tuba indan laifi nayi Ubangiji ka yafe min, ka sassauta min Ina son Uban Y'ayana"
Shiru ɗakin yayi aka rasa mai magani, jikin Sulaiman yayi matuƙar sanyi, fita yayi daga asibitin yana kalubalantar kanshi da rashin adalci.
Wani irin son kai da zuciya ne suka kaishi da aikata abinda bazai yafewa kanshi ba.
Kifa kanshi yayi da a cikin mota ya fashe da kuka, sosai dan yana hango. Rashin amincewa da buƙatarshi kawai yake,
Haka yayi kukan mai isarshi, ga wutar kaunarta dake kararu mishi zuciyarshi tare da shaiɗanin zuciyarshi dake bashi shawaran banza.
....... Bayan awa shida aka sallame mu, su hajiya suka koma zaria.
Tunda muka koma gida, Umma da kula da yaran Mama kuma dani, wanka sau biyu muke samu. Ga abinci mai kyau wanda sulaiman ya kawo ya jibge.
Ga hidimar da Fareeda take kullum tana hanya, itace kawai bana iya ɗaga ido na kalli yaran a hannunta, amma ko wanka umma ce ke musu wanka sai nace ummana abi a hankali kar su fasa auren.
Zan iya cewa wani mahaukacin son Yarana ya rufe min ido ko barshi nake naji ɗan kukansu a gigice nake farkawa. Sune abu mafiya soyuwa da nasamu bayan rasa mahaifinsu shi yasa ko tari sukayi bana iya hakuri akan haka.
Iyayena sun min uzuri basu taɓa jin zafina ba asalima sake koya min yanda zan kara son Yarana.
Duk wani al'adar bahaushe sai da Familyn Daddy sukayi min, abinda ya matuƙar sani zubda kwalla kenan domin ji nake ina da yana tare damu da munga zallar so da kulawa.
Haka zan zauna ina tausayin yarana, sabida bansan mi zance musu ba idan sun girma, ajiyar zuciya na sauke idan na tuna amsar a bayyane take.
Yan uwana sun zage sosai gurin hidimar suna, wanda baya cikin lissafina. Sai da Mams tayi min faɗa sannan na yarda aka wanke min kaina inda suka kawo kayan gyaran gashin har gida, ana jibi suna Aunty Asma'u tazo daga Abia.
Washi garin zuwanta suka shiga aiki dan buhu uku Ahmad ya kawo na fulawa da Mangyaɗa, da duk wani abin bukata na kayan suya, Aman kuwa ya ajiye mana kayan abincine suna, Alhajinsu Daddy Raguna biyu ya kawona sai gana Fareeda da akwatinta guda uku, tsabar sonkai nawa ne karami, duk sauran na yaran ne,
Ta ɓangaren Sulaiman kuwa duk abinda Uba yakeyi yayi mana, komi har pampers laida sha biyu ne, duk wannan hidimar da yake mana ni haushinsa nake ji, wallahi dan haka kawai zuciyata ke sani jin zafinshi. .
Balkisu akwatina biyu tayi mana.
Banda nasu Hajiya da kanen Yunus, da sauran dangi sai da Umma tayi ta faɗa, Yaseen ko a jikinsu.
Anzo za'a min lalle nace ni bana so, Rahilah tace.
"Baki isa ba Maryam wallahi sai anyi miki."
Dole suka min, aka zana min lalle ja da baki, ina gamawa na kalli yatsin hannuna, yarrrr naji tsigar jikina ya mike.
"Yunus"
Zuba min ido sukayi dan bani mantawa ranar da nayi lalle ja a hannu, kamar ya cinye hannun tsabar abinsun mishi. Kuka nasa musu sosai.
Sam yanzun bani da juriya da hakuri dan na lura kamar Yunus ya tafi min dasune, yabar fanko mara juriya.
......Ranar suna anyi hidima sosai wanda sai da akayi da gaske dani na iya sake jikina, yan zaria kuwa kamar su ɗauke Hassan da Hussain. Haka aka bar musu bayan hassan yaci sunan Yunus Hussain kuma Sameer.
Bayan an watse Yan uwana suka shiga duba kayan da aka mana, cike da mamaki. Suna faɗa min, murmushi nayi dan fitowana kenan daga wanka na samesu sun baza kayan.
"Yanda ya tafi da fatan nasake samun wani cikin da yana nan, ai wannan wasane dan nafi kowa sanin waye Yunus ko Matanshi da nasamu basu sanshi kamar yanda nasanshi ba."
Duka Rahilah ta kaimin cikin tsokana tace.
"Yarinya taji Yaren novel,"
Tsaki na mata, dan nasan fassarani tayi ta other sider.
.....Haka suka gama ganin kayan, har kowacce mijinta yazo