Showing 9001 words to 12000 words out of 39506 words
sosai, kanta take niman ɗaura min akan boons ɗinta, basan lokacin da na injizata ba. A tsorace ta kalle ni cikin ɓacin rai nace.
"mi kika zo yi nan, kuma ga fili a ko ina bai isheki ba, sai gadona.". "Kiyi hakuri Aunty Mafarki nayi shine naji tsoron kar wani abu yasame ni.".
Ciki ciki nayi da fuskana nace.
"Zaki iya fita min a ɗaki."
Da sauri ta sauka a gadon, dan ban sake da ita ba har ynx,
Tun daga lokacin na fita harkanta, na cigaba da hidimar gabana, ni a nawa tsarin bana zuwa ɗakin Mai nasara. Shi yake biyo ni kamar yanda yake bin balkisu su kuma sauran basu damu yazo ko su je ba.
... Toh duk ranar girkina biyo ni yake, sai dai wani halittar da Allah yayi min, guda ɗaya ce shine Allah ya ɗaura min jin kara ko motsi, duk yanda akayi akan kunena ne. Koma gana ake toh ina jinshi amma dake ban cika damuwa da bin didigi ba, sai na ke sharewa nayi uzirin gaba.
Wani lokaci idan dare yayi, zan ji an buɗe kofar ɗakina an shigo musaman idan aka lura yana ɗakina. Sai na ɗauka ko dan ina da yawan jine yasa haka, abinda na fara fahimta shine idan aka shigo, ana ɗaga labulen window ɗakina wanda yake falon, Allah yasa bama barin wuta a kunne, kuma duk abinda yake yi irinsu surutu da wani abubuwa bana barinshi musaman da yake ɗakina yafi kusa dana Aneesah, nakanyi kokarin rufe bakinshi da nawa.
Washi gari da safe kuma sai naga Mufeeda tana kallon cikin kwayar idanuna, sai da na shiga zabga mata harara nasami lafiya.
Ana gobe xata tafi makaranta, sun tafi zaria da Uwarta. Sai naji matan Uban suna hira Aneesah take cewa.
"Fareeda baki san mike faruwa bane a gidan nan."
D'ago kantq tayi ranta a ɓace dan duk abinda zaka mata karka shigo cikin lissafinta, cikin hasala tace.
"Hmm ai yarinyar nan mufeeda ce wallahi ta lalace, kamata nayi ranar tana saka hannunta cikin pant ɗinta, da nayi mata tace ta daina."
Ina daga sama ina jinsu kasa tayi da murya tacigaba da cewa.
"Wallahi sai ga yarinyar ta fito min da vedion Ubanta da Matarshi, sun........."
Daga ni har su Babu wanda yasa Yunus na gidan, dan nasan ya shigo yace min zai fita amma bansan ya dawo ba. Suma kuma dake asabar ce sunsan baya cika zaman gida da lahadine, toh baxata fara wannan haukar ba.
"Keeeee" Ya daka musu tsawa. Sannan ya fito tare da naɗe hannun rigarshi yace.
"Bani videon kuma ki fita ki bar min gidana."
Allah yaso Fareeda bata tanka ba, da natane yafi muni.
Mika mishi wayar tayi ya buɗe sai ga Videon da surutan da yake. Fasa wayar yayi baki ɗaya ya kwace komi nata, ya kaɗata gidansu.
Zaman jiran dawowarsu Balkisu yayi, can yamma suka dawo. Nan taramu afalo ya shiga tambayar mufeeda videon da farko ta musa, ranshi ya kara ɓaci zaro wayar chajin Destop ɗinshi yayi ya cigaba da zuba mata tace yana tap ɗinta, dakanshi ya ɗauko ya buɗe, Video ne na mata masu niman mata wato lesb, sai namu da take ɗauka. Ranar yarinyar taci bugu kamar jaka inda ya rusa tafiyarta makaranta.
Washi gari da safe ya tattara nata yana ta, ya kaita gurinsu Hajiya ya mika musu ita, bai ɓoye musu ba, nan ma sakata sukayi a gaba da tambaya dakyar ta faɗa musu, take mai nasara ya dawo kaduna ya tafi har makarantarsu, yasa aka duba mishi nomber da address ɗin bonke.
Yaje har Hukumar bautar kasa, abu ya zama rikice sai gashi har Indo aka bi, didiginta yasa aka kamata dakyar ya saketa kowa yayi mishi magana yaki, sabida an taɓa yar shi.
Karshe ni Hajiya tayiwa Magana, yana zaune ya zuba tagumi. Zama nayi kusa dashi na ɗaura kaina a jikinshi nace.
"Dalilai guda uku suka jefa mufeeda a wannan rayuwar, dalilina farko rashin cusa mata Allah a zuciyarta, Na biyu rashin janta a jiki, na uku rashin addu'a da nimawa Yaranku kariyar Ubangiji, ranar da ka daketa naki baka hakurine sabida ba jina zakayi ba, amma a ynzu da aka kai matakin dole sai nashiga aigashi na cusa kaina Daddy baka kyautawa bakasan hakkin Yaranka akanka ba, baka damu da su ba, sabida kana niman duniya dansu amma bakasan tarbiyansu ba, ai gwara kai da Mommynsu dan ita tafi kowa laifi. Taya zaka haifi ɗa kabarshi duniya ta biyar dashi Daddy gabaki ɗaya rayuwarku akwai gyara, yaranka suna da hakkin ta shiga alamarinsu ka binciki suwaye abokanansu. Ka kuma saka ido akansu, babu tsoron Allah a zukatarsu wanda zaisa idan suke je aikata wani abu karfin iklas da imani tare tsoron haɗuwarsu da Allah ka taɓa duba ta tayi sallah ko batayi ba, sannan basu damu da islamiyya ba sai boko, Anya kana tunanin tsaywarka a gaban Ubangiji. Ka bar yara kara zuɓe, daga kai har mahaifiyarsu. Toh bari na faɗa maka wani abu, A sanadin Mufeeda idan bakayi da gaske ba sai ka shiga gidan Wuta."
. A razane yakalle ni nace.
"Yes da gaske nake, sabida yazo a cikin alkur'ani, yaranku da dukiyarku, zasu kaiku ga hallaka. Karka ka rikesu a hujja akanka su zama hujja gareka, kuma."
Shiru yayi a hankali na warware mishi hakkinsu dake kanshi da, kuma mahaifiyars sannan nace.
"Ni banga dalilin da zaka rufe musu yar mutane ba ka kyaleta ta tafi, idan duniya da gaskiya ni da ka min shegen duka, kuma ummana tasani tace miye kasan ciwon da taji lokacin, Mama Amarya tace min sai da tayi kwana bakwai tana azumi da sallar dare dan Allah ya kaɗe fitinarda zaisa ka bugeni da zara zatasha ruwa sai tayi mana addu'a,, sannan da kata kunsamin bakin ciki ka hanani zuwa gidan Rahilah, ga abubuwan da matanka suka min, da nakirata ina kuka. Mi tace ce min tayi nayi hakuri wata rana zai hucce, kasan ciwon da take ji idan taji ina kuka, duk haihuwanta uku lafiya tayi sai da tazokaina ta haifeni seven month sabida bata da lafiya kasan wahalar da tasha akaina ga ciwo aikin da aka mata, ga ni kuma ko wanka an hana ayi min, haka tayita fama dani, amma bawan Allah kada belt ka zuge mata Auta ita kuma ta faɗi ta mutu, misali nayi maka, toh ita Bonke take banke ita tayi muku hannunka mai sandane,, idan lalacewa kake tunanin Mufeeda tayi ai a cikin gidan nan tayi tunda tana jin maganar da ya girmi kunenta, tana zaune cikin uwayen mata, dama da abinta Corp tasameta kaga knn, babu amfanin tsare mata. Tunda a cikin gidan nan ka fara turata taje ɗaukarmu vedio my dear ka sake musu Yar mutane ta tafi, kuskurene ba ita ɗaya tayi ba, har daku...............
Yaseen na gaji.....😂
🌹🌹🍀
*MATAR SO*
🌷🌷🌻
*MAI_DAMBU*
*Wattpad:Mai_Dambu.*
Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai....
Sadaukarwa Ga Mai Nasara Team😂
_Wannan buk ɗin hakk'in masu shine idan kinsan baki saya ba karki karanta, mai fitarwa kuma ki duba girman Alkawarin da kika ɗauka na cewa bazaki fitar ba, tunda nace idan kinsan zaki saya ki fitar na Yafe ba sai kin saya ba_
*Page..4*
"Ko Ubangijin da ya haliccemu muna masa laifi kuma haka yake hakuri damu ya tanadama a lahiranmu tazo bata amfanemu ba, bandan wasu bayin Allah da yara kananu da tsofai da tuni Ubangiji yasa mala'iku sun turmushemu.
Don Allah ka kyale musu yar mutane ta tafi, kaima kacigaba da istigifari. Zaka sha mamaki kaji My sugar daddy."
Rungumeni yayi yace.
"Shi knn amma sai kin biyani ladan amincewa."
Zaro ido nayi tare da ɓata rai nace.
"Wallahi kai kam, anshiga uku dakai zan gudu gidane abuna"
"Haba dagske Yan mata. Har nafi keda kike ririkeni tare da kuka faɗa min miye sirrin kukanki nan ne."
"Ai kaima kanayi, ranar har ce min kai na faɗi nawa nake so kabani, ka bani sabuwar motarka da kasaya. Ka ban...."
"Hmmm karya dai haramune."
"Eh nasan haka zaka ce"
Daga nan kuma yaren ya sauya irin wanda ya ɗaurani akai, toh mi zance mi kuma zan iya nima karamar munafuka, son mijina nake wanda yasani gaza fahimtar yana cutar dani ko baya cutar dani burina kawai na faranta mishi koda ni zan kuntatta kaina.......
*Bayan wata hudu*
Wanda ya haɗa da watanin baya muna da shekara kusan ɗaya da aure dan ga shi mun fara hango watar azumi. Haihuwar Rahimah yasa Yan uwana suka tasoni a gaba ko bani da lafiya ne.
Nace lau nake lokacine baiyi ba. Bayan suna dake, Y'a mace ta haifa aka samata suna Mama Amarya Atika, sai muna kiranta Hibbatu.
......Muna zaune a falonshi kaina bisa cinyarshi kallonshi nayi cikin damuwa nace.
"Daddy kasan an dame nida maganar rashin haihuwa."
A tsorace ya kalleni cikin yace.
"Toh miye dan baki haihu dawuri ba."
"A'a Ya hayat da Aunty Hamdiyya sunce na sami lokaci nazo asibiti a dubani kasan Ya Hayat likitane, Aunty kuma Nurse....."
"Babu inda zaki, indai ba shishigi zakiyiwa Ubangiji ba miye sai kinje asibiti nidai abinda nasani, ki kara kaimi gurin kwanciyarmu sai kiga kin sami baby ko Jinjirar mata na."
Da wannan muka rufe hiran dan take ya shagalatar dani, wani batu dakyar muka shige ɗakinshi.
Haka rayuwarmu tacigaba da tafiya cike da abubuwan al'ajabi, kwatsam daf da azumi sai ga tafiya ta kamashi zuwa canada, duk ya haɗamu ya tambaya wacce zata rakashi, Fareeda takawo uzurinta, Aneesah ma haka, karshe balkisu tace.
"Kaima dason ɓatawa kai lokaci ka ɗauki maryam kayi tafiyar da ita, ba ɗa ba ciki mi kuma zaka damu kanka da nimar yar rakiya. A dawo lafiya Allah yasa ayi farar tafiya a tafi babu a dawo da..".
Dariya suka saka, irinta shakiyanci. Dukda ba wani shiri muke ba amma ynz babu wani tashin hankalia zamanmu, wani lokacin duk ranar girkin balkisu ce mishi take bata dalafiya yaje gurina kawai. Kuma hk zai zo.
Wannan tafiyar ta gaggawace, dan haka nice na shirya masa kaya, na haɗa da nawa.
Washi gari muka bar kaduna zuwa abuja acan muka tashi.
Mun isa lafiya, sai dai bai da nutsuwa kullum yana waje gurin kanfanin da zasu haɗa gwiwa da wasu mutane, sai da mukayi kwana uku ranar ya dawo a ɗimauce, sakamakon ganin wata shaiɗaniyar budurwa a gurin meeting ɗin, ko kallo bata isheshi ba. Ya dawo gida sai da yayi wnka ya huta sannan ya fara niman huccw gajiyarshi ta asali. Sai da yazo kan point ɗin ya shiga niman maganinshi bai samu ba kamar zaiyi hauka gashi yana bukace, dan dole yayi haka zuciyarshi cike da wasi wasi.
Koda ya gama kallona yayi yace.
"Maryam yaushe kika gama period ɗinki."
Kallonshi nayi nace.
"Da sauran lokaci banyi ba tukun."
Gyaɗa kanshi yayi ya faɗa wanka, tun daga lokacin ya rage fitinar da yake, sai kuma ya shiga taka tsantsar gurin mu'amalarmu.
Har ya tambaye ni banga cream ɗinshi ba, nace a'a.
Haka kawai naji ina zargin amfanin cream din, haka muka gama abinda ya kawomu.
Muka dawo gida, ni da muka dawo sai na ɗauki hoton kwalin abu a wayata zan turawa Ya Hayat ta tambayeshi sai na manta.
A haka mukayi azumi, inda na tsananta Addu'a Allah ya bani haihuwar nima na huta.
Kwatsam ranar muna hira a grp ɗinmu na yan yan uwa, na tura musu hoton da tambaya cewa wata kawata ce take son sanin miye amfaninshi kuma.
Dogon sharhi Ya Hayat ya turo min da cewa ai cream ɗin na hana ɗaukar cikine, da kuma bayanai da Aunty Hamdiya tayi min, ajiye wayar nayi na koma ɗakinshi na shiga duba kwalin nasamu yasaya dayawa. Kaɗa kaina nayi nabar ɗakin zuciyata na zafi. Wato burin Daddy ya cutar dani bayan yana kasancewa dani.
Ban nuna mishi komi ba sai dai gabaki ɗaya na kauracewa bukatar shi, dake azumi ake kuma farkonta sai na tsananta addu'a baji ba gani.
Ana cikin haka yayi tafiyar kwana huɗu, a cikin kwanaki nayi period ɗina nayi har nagama. Ranar da ya dawo ya nemi ne ni kuwa fir naki dama kuma girkin Balkisu ce furrr naki amince masa jin haushi haka yassashi fita zuwa ɗakinta nan yasamu tana up, dole nice yazo min. Nan kuwa nace.
"Ni nagaji bazan iya ba."
"Kamar ya bazaki iya ba?"
Share shi nayi na shige ban ɗaki, nayi wanka sannan nafito. Duk yanda yaso na bashi hakkinshi ki nayi karshe yaci da zuciya, inda ya murɗeni ya biya bukatarshi, sai da ya gama ya koma gefe. Na fashe da kuka nace.
"Dole kayi rape ɗina mana, ga sexer machine kasamu. Bayan ha'intata da kake wai nikam miye na tare maka ne, da ka tsane ni ove kana amfani da cream dan kar na ɗauki ciki ka maidani gidahuma mara lissafi bansan mi nake ba, Allah zai min sakayya."
Shiru yayi cike da mamaki ya akayi nasan da haka. Kai hannunshi yayi zai taɓani na buge na bar kan gadon na shiga bayi nayi wanka.
Tun daga ranar, muka shiga takun saka dashi dan yana taɓa ni zai ji magana marasa daɗi, tun yana jurewa har ya fusata.
Koda aka kusan gama azumi yace na shirya muje zaria kamar bazani ba, haka nashirya muka tafi.
Can mukayi sallah dakyar ya shawo kaina muka dawo kamar da, satinmu ɗaya muka dawo gida, a hankali al'amuranmu suka sauya a cikin gidan dan balkisu ta shigo jikina munayi da ita, har su karatu. A binda batq sani ba zata tambaye ni na bata amsa.
Anyi sallah har da wata guda, a cikin wani dare muka tashi Sameer ba lafiya ciwon ciki da amai, ko kafin su isa asibiti Allah ya amshi rayuwar Yaron,
Tashin hankalin da muka shiga ba iyaka, dan Fareeda har da suma ga sambatu, shima Uban na tausaya mishi.
Yanda mutuwar ta girgizamu yasani na fara wani zazzaɓi da ciwon kai gabaki ɗaya na fita hankalina, a gida Dr Nafi tasami ruwa. Sannan ta ɗiba jinina taje tayi text, sannan ta kawo cikin ikon Allah sakon ya faɗa hannun Balkisu. Dake gidan da mutane har ɗakinmu ina kwance ta shigo ta zauna a bakin gadon ta mika min, takardan kallonta nayi cike da son karin bayani, itama kallon takardan tayi sannan tace.
"Inji Dr Nafi"
Mik'a mata nayi nace.
"Hmm mommy ki buɗe mana."
Kura min ido tayi ganin yanda ta ko ina ya nuna akwai dashen Mai nasara yasata murmushi tace.
"Idan naga sakon ciki mi xaki bani."
"Komi mommy kika gani kina so zan baki."
Sai muka burge yan uwana da wasu mutanen.
Tace.
"Ok nidai abinda tunani na yake hasasho min za'a bani, idan ban son kaina ba."
"Ba batun sonka da kai da kaya mallakar wuya ce."
Buɗewa tayi a hankali ta warware takardan, tana bi a sannu har takai kan gwajin. Cikin sati bakwai cik.
Murmushi take tare da zubdar kwalla tace.
"Koda banyi ɗawainiya dasu huda ba don Allah idan kika haife abin cikinki ki bani shi nima na gwada tawa tarbiyan mana, Allah mai iko Sameer ya tafi Allah ya kawo mana wani Allah yasa sameer ɗin ne."
Da sauri tafita zuwa ɗakin Fareeda da take kwance, zama tayi a bakin gadonta tace.
"Karɓa ki gani."
karɓa Fareeda tayi ta duba, ai bata san lokacin da ta hantsilo ba, tafita da gudu zuwa ɗakina ina kwance ina, kwalla nabi fuskana rike hannuna tayi tace.
"Maryam cikine dake? Alhamdulillah Sameer ya tafi Sameer ya dawo, kaiii Allah nagode maka daka sake azurtamu ta wani hanya."
Fita tayi sai gata da key kamar ba mutuwa aka mata ake zaman makoki ba, tashigo " faɗa min mike so, a sayowa Lil Sameer."
Shiru nayi ina kallonta ta bani tausayi nace.
"Maman Sameer zauna, baki da