Showing 21001 words to 24000 words out of 39506 words

Chapter 8 - MATAR SO BOOK 2

06 Sep 2025

3194

nake ciki, bazata taɓa hakuri da abinda yake min ba.

Dafa goshina Aunty Hamdiya tayi, tace.
"Sannu Auta."
Sake buɗe idanuna nayi sabida duhun da nake gani. Ina kallon inda tanake jin muryanta.

Shigowar dr Nafi yasa duk suks fito sai shi ɗaya da ya rage a ɗakinki, dubani tayi sosai sannan tace min.
"Maryam Ina ke miki ciwo?"
"Babu, cikin yafita ko?"
Rike hannuna tayi cikin tausayawa tace.
"Allah zai baki sama da wanda ya fita. Ki yarda da K'addara mai kyau ko mara kyau."

"Dr kenan! Ai tunda na kasance musulmai na amshi k'addarata hannu bibiyu, tun daga ranar da aka halicceni har zuwa ranar da zan koma ga Ubangijina, akwai kurakuran da sai mun gyara da kanmu kafin musamu rabauta."

Ina gama faɗar haka na juya mata kaina ina jin ciwo a cikin zuciyata fiye da kima, runtsa idanuna nayi dan naji fitarta. Jin kamshinsa yasani kara jin wutar tsanarshi.
Shafa kaina yayi zuwa fuskana nayi maza na rike hannun, na kalleshi cikin ido nace.
"Kasanyawa zuciyarka, cewa tankar bamu taɓa zama a inuwa ɗaya ba, ka ji aranka ni mafarkice nazama wata shuɗaɗɗiyar karni da aka jima da yinta, ka janye tunaninka akaina dan haka shi zai tsiratar da kimarka da Mutuncinka da iyayena suke gani, Kace bani da dajara ynx zamu fara wasan. Kamar yanda ka azbatar da zuciyata da ruhina, ka sani kuka ka kuma katngeni da farin cikina. Ka maida min zuciya wata iri na daban kasani tsanar ka, idan baka manta ba kace min zaka rabu dani sai lokacin da kayi niyya, toh ynx kabani idan kuma ka k'i kuma tabbas duniya zata jimu daka kafita dan bana kaunar ganin fuskar, idan ka takura min toh kasan suwaye iyayena da kuma abinda suka sani akan addini toh zan faɗa musu susan yanda zasuyi dakai ko su kaika kotu ko kuma su nuna maka cewa ni nafi zinari da azurfa daraja da kima kuma wallahi Ubangiji sai yayi min sakayya dan ban yafe maka ba"

"Kiyi hakuri Maryam wall"
"Bazaka kafita bane?"
Na tambayeshi a hasale.
Zai sake magana nace.
"Waje"
Jikinshi babu kwari ya fita, tun daga ranar ya shiga sintiri. Ga mugayen mafarkan da suka sakashi a gaba.

Ni kuma naki kula al'amarinshi. Hajiyarshi da tasan komi bata taɓa damuwa ba, sai ma nuna min, kulawa na musaman fareeda da balkisu kullum suna asibiti. Sau ɗaya Aneesah tazo.

Kwana na goma sha biyar, suka bani sallama koda aka haɗa kayana. Na kalli Umma nace.
"Gidanmu zaki wucce dani."

Cike da mamaki umma ta zuba min ido.
"Kiyi hakuri muje gidana."
Kai tsaye nace mishi.
"Lallai ma kuwa, kaje akwai mata masu daraja da kima, kana da kuɗin da zaka iya auren Yar shugabar kasa, ni Yar malamai ce bamu da kuɗi sai yarda da Allah."

Duka Umma takai min ranta a ɓace tace.
"Wallahi ki wucce kibi mijinki."
"Babu inda zan bishi."
Na faɗa kaina a sunkuye.
"Toh wallahi zan kira Malam."
"Umma sai dai kuyi min duk abinda zaku min amma badai gidan Yunus ba."

Ga baki ɗaya ɗakinmu ya hautsine da tashin hankali sun kafe nima kuma wani mugun taurin kai ya kafar dani.

Har Malam yazo shima yayi juyi duniyar nan naki har da barazana yayi min idan ban koma gidan yunus ba toh zasu zareni a cikin yaransu.
Kallon Yunus nayi cikin.muryan kuka nace.
"Mai nasara, kayi nasara rabani da farin cikina, Yanzun kuma da iyayena ko? Toh wallahi da na zauna da kai gwaara nafita, duniya ka zauna kai da naka iyayen lafiya hakkina sai ya kama kowa dan a dake ni an hanani kuka."

Ina faɗar haka nasa kai zan fita, kusan yanayin ɓari, ban kai bakin kofa ba jini ya sake ɓale min, a gurin na yanki jiki na suma.
Tashin hankalin da na shiga Allah kaɗai ya sani, dan sabon jinya ce tasake dawowa.
Ga jinina da yayi mugun hawa........

Fatan alkhairi gareku......Masoyan Yunus naso kai typing ɗin irin 6k....Amma iya kanshi...5.440k....Nagode



🤭🤭🤭🤭🤭
🌹🌹🍀
         *MATAR SO*
                 🌷🌷🌻

*MAI_DAMBU*
*Wattpad:Mai_Dambu.*

Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai....

Sadaukarwa Ga Mai Nasara Team😂

     _Wannan buk ɗin hakk'in masu shine idan kinsan baki saya ba karki karanta, mai fitarwa kuma ki duba girman Alkawarin da kika ɗauka na cewa bazaki fitar ba, tunda nace idan kinsan zaki saya ki fitar na Yafe ba sai kin saya ba_

          

*BOOK 2👈*
*Page...7*
      Fushi Umma tayi taki zama a jikina, Hajiyarshi ce ta zauna min, kullum sai yazo kamar maraya, ga tashin hankalin da yake ciki na mugayen mafarkai.

    A haka muka ɗibe kwanaki, sannan aka sallameni. Gidanmu Hajiya ta kawoni. Dan tana son magana da su Umma, amma dole sai Alhajinsu Daddy yazo dashi da Sulaiman.

                Karfe biyu suka iso, harda shima daddyn. Ina kwance a ɗakin Mama Aunty gausiya tazo kirana, mikewa nayi na fito. A nutse har falon baki, da sallama na shiga na gaida kowa na falon sannan na koma gefen Malam na raɓe, dan umma taki sake min fushi take dani.

        Da sallama Alhaji ya buɗe taron da Addu'a sannan, yace.
"Da farko kafin nace wani abu ina bawa Maryam hakuri abinda abinda Yunus ya aikata mata, munyi haka ne dan kuma iyayenta kusan halin da take ciki, nayi bakin ciki da alhinin abinda Yunus ya aikata, amma ba komi kanshi yayiwa. Sannan abinda ya kawo mu anan shine.."
          Har yakai aya, sannan ya ɗago kanshi yana duban malam da umma, wnda mamaki ya kusan sambaɗesu zuwa lahira, cigaba yayi da cewa.
"Allah ya gani nafita hakkinshi na masa komi da uba yakewa ɗa nayi na fita hakkin Yunus, amma idan bazaku damu ba zanso naji Ra'ayinku akan abinda ya aikata muku." 

      Sunkuyar da kai Malam yayi yana girmama al'amarin, shiru yayi sannan ya kalleni cikin sanyi murya mai bayyana tsantsar hakurinshi yace.
"Tabbas anyi kuskure, sai dai mu bamu da ikon hukunta mijin maryam, kuma idan muka ce zamu ɗauki mataki ai kimar zata iya zuɓewa, mi kike gani Hasina."
   Kallon Malam Umma tayi cikin mamaki tabbas ranshi ya ɓaci, girgiza kai tayi, sannan tace.
"Malam!!! Kaine mahaifinta duk abinda kace ai duk ɗaya ne."

     Kallonta Malam yayi tare da kallon Alhaji yace.
"Mu dai a matsayinmu na iyayenta, munyi hakuri babu wanda yafi karfin laifi, sai dai bazamu tauyeta ba gata nan idan ta hakura shiknn."

               D'ago kaina nayi cikin matsanancin kuka ina kallon Malam bakina narawa.
     Alhaji yace.
"Mun gode sosai da wannan dattakon, maryam muna jiranki."
    Kallon Umma nayi na kalli hajiyarshi kauda kanta hajiya tayi, sannan na kalli Mama amarya gyaɗa min kai tayi, cikin murmushi umma kuwa bata iya kallona ba, shi nakalla. Ya gama zuba min ido, girgiza kaina nayi yanda nake tuna rashin imanin da yayita min, cikin wani irin murya nace.
"Bazan yafe ba, ya cutar dani, ya dakeni ya tunkuɗeni."
  Dafani malam yayi na ɗago kai cikin kuka nace.
"Kabarni na faɗa dan idan na cigaba da rike haka mutuwa zanyi, malam zuciyata kamar zata kama da wuta, ya sani kuka amma wancan ba komi bane, idan  na tuna tsantsar rashin imanin da nagani a cikin kwayar idanunshi,  bazan iya zama dashi ba, Umma kin koya min hakuri da yarda da kaddara, umma kin koya min abubuwa umma miyasa baki koya min fitar da damuwata zuwa gareki ba, umma na haɗiye bakin ciki dayawa. Don Allah ki kwatar min yancina, karki juyawa al'amarina baya, ki kwatar min yancina."

      "Maryam!!! Mi kike bukata daga yunus?"

          D'ago kaina nayi ina kallon hajiya cikin zubda kwalla nace.
"Hajiya kiyi hakuri,,, zama dashine bana so."
     "Miye ne na bada hakuri, ai hakkinki ne. Yunus ka sawwake mata."
Tace mishi.
       A gigice ya ɗago kanshi yana girgizawa cikin tashin hankali yace.
"Hajiya don Allah, kuyi hakuri ina son matata, maryam kiyi hakuri na sauya halina karki rabu dani wallahi ina sonki sosai."
     Girgiza kai nayi cikin kuka nace.
"Ai nima haka na rokeka da karka zubda min farin cikina, wayasani ko shiknn bazan kuma samun wani ba, ka zubda min shi. Kaje mun barka da Ubangij...."

   "Maryam!!!"
   Umma ta buga min tsawa.
      Tsabar tashin hankali baka hangi komi a idanun Yunus.
   Kuka na fashe mata dashi nace.
"Ni..."

      Gaban Umma yazo ya dukar da kanshi cikim mugun yanayi yace.
"Kiyi hakuri, ku bani damar karshe."

   "Abaka damar kashe musu y'a ƙo  wacce irin dama kake bukata." Inji Alhaji.
         Hannuna na ɗaura akaina ina kuka nace.
"Umma!!! Cewa yayi fa bani da daraja da kima, sabida an bashini a banza ko?"
  
   Cikin ko in kula tace.
"Eh toh nima dai naga rashin kimarki da darajar, ina suke? Ina darajarki take? Ina kimarkin take?"
          Rike bakina nayi tare da kallon Umma, wani irin ajiyar zuciya nake saukewa tsabar tashin hankali da ɗimauta.
    
Murmushi tayi sannan tace.
"Idan D'iya ta garice ko tari bazatayi ba, sai dai tajira hukuncin da zamu yanke mata. Ina guje miki aikin danasani ne kar wata rana ki zubda kwallar da tafi wanda kike zubdawa, ita rayuwa ba'a binta a guje. A nutse ake binta tafi daɗin ganuwa."
      Mikewa nayi tsabar bakin ciki in dakeni an hanani kuka. Ko gani banayi. Nasa kai zan fita ji nayi an rukoni,
    "Dawo nan Mamana."
    Inji Malam zuɓewa nayi ina wani irin haki, hawayen ya kafe sai zuciya zalla da take aikinta.
       Kwantar da kaina yayi akan kafarshi yana shafa kaina tare da tofa min addu'a. Sai da yaji numfashina ya daidaita sannan ya ɗago kanshi ya kalle Yunus cikin damuwa tace.
   "Wallahi baka kyauta min ba, dan tunda nake ban taɓa jin an rabata faɗa da kowa ba, bata taɓa kawo min karan wani ba nasan halin duk Yarana amma nata halin dabane, hakurinta daban ne, adalci ɗaya zan iya maka nabaka dama ka gyara tsakaninku, idan haka bai samu ba toh zan iya baka hakuri ka sallam...."

     "Malam..." Mama ta kirashi raunane.
  Dakatar da ita yayi, cikin murmushin ya cigaba da cewa.
"Ban goyi bayan Maryam ba, sai da na fahimci har ynx hasina bata kaunarta, kiga yanda take numfashi, idan ita bata son Maryama ni ina sonta, kuma zan tsaya mata, ai duk sauran mazajen ba haka suke ba, haka mijin Rahilah yake? Yaron da ko gidan nan Rahilah tazo yana makale a kofar gidan nan, Mijin Rahimah nine nan nasanya shi yajanye ɗaure da yayiwa uwargidanshi, sabida kimar da muke dashi a idanunshi."

   Murmushi Malam yayi sannan ya kalli Alhaji yace.
"Manyan mutane irin Yunus, basu san darajar mace ba, sabida cuɗanya da turawa. Zuciyarshi ta girmama alamarinsu, kayi hakuri Alhaji Y'ata Lu'ulu'u ce, kima take dashi da daraja, yaje ya shawo kanta idan ya samu damar haka zan iya duba al'amrin da idon basira amma bazan miki mishi maryam ba, dan tana da kima. Duk laifin da yayi bai basu kai wannan muni ba. Ku gafarceni banyi haka akan zubda cikin ba nayi ne sabida kalmar bata da kima da daraja, ka duba yanda take bana son na zama silar lalacewarta, nafi son ta koma rayuwarshi dan kanta badan mun tirsassata ba da fatan kun fahimceni."

       "Wallahi babu komi, malam ai kun mana dattako, tunda baku dubi girman laifin zubda ciki ba, wanda nake jin abun har cikin zuciyata, Insha Allah zan sashi ya sawwake mata, itama tasamu ingantacciyyar rayuwa ina kara baku hakuri da abinda ya faru."

       Gyara zama sulaiman yayi wanda yake zaune cike da damuwa tunda aka fara rikicin yake kallonmu,*Allah kaga zuciyata ɗaya nake son Maryam Allah nagode maka gwara akashe auren nina sameta.* Ya faɗa a ranshi kallon Alhajinsu yayi cikin zakuwa yace.
"Hmm Alhaji, idan bazaka damu ba kasashi ya sauwake mata da wuri, in yaso ni sai na shiga niman aurenta, kuma zan riketa da kima, zan ɗaga darajarta a idanun duniya, Wallahi zan riketa fiyye da ruk....."

  Tauuu.Yunus ya tsinke shi da mari, bai damu ba yace.
"Wllahi sai ka saketa na aureta, kasan kana kishinta da sonta ka zubda mata da cikinta, kai d kanka kace min, idan ka tuna yanda take rokonka sai hankalinka ya tashi, kayi biriss da ita zuciyarka tana ingiz...."

   "Sulaiman zan kasheka."
   Ya riko wuyar Baban arif, mikewa iyayenmu maza sukayi ran hajiya ya ɓaci, aikuwa tana mikewa ta shiga kifawa daddy mari takowani fuska, sabida bacin rai, tace.
"Sake shi, kuma sai ka rabu da maryam, Insha Allah sulaiman sai ka auri maryam."

      Kallon hajiyarshi yayi tare da sake baki hawaye na sauka daga cikin idanunshi ya sauke kanshi kasa yace.
"Hajiya ina raye zaki rabani da farin cikin rayuwata, itace mafarkina fa, duniyata rayuwata hajiya karki min sassarin da bazan iya kwacewa ba."
     "Allah sai ka rabu da ita, azzalimi, mugu maha'inci. Ina tsoron ganinka cikin sakayyar Ubangiji dan hakkin rayuka bazasu barka."

........Dakyar aka shawo kan hajiya, faɗa Alhaji yayiwa sulaiman da kar ya sake abinda yayi.

        Rufe taron akayi da addu'a sannan suka fita daga ɗakin aka barni dashi ina kife a kujeran da Malam ya tashi, da sauri yayo kaina zai taɓa ni nace.
"Koda wasa! Karka fara taɓa ni, dan zan maka wulakancin da baka taɓa tsamanin ba, mi yasa bazaka rabu dani ba? Mi yasa bazaka fita a rayuwata ba? Nifa bana sonka bana kaunarka, don Allah ka kyaleni."

Ina gama faɗar haka na mike nabarshi a gurin ko magana naki bashi damar yi min.

               Zaman dirshan yayi ya kama kanshi da hannunsa duk biyu. Ina fita ɗakin Mama na wacce, na kwanta har lokacin jikina da numfashi na basu daidaita ba.
           Dakyar yaja kafarshi ya fita a gidanmu duk sun tafi, koda ya shiga motarshi kifa kanshi yayi tare da sauke kwalla masu zafi. Mi ya aikeshi aikata abinda zai zame mashi tashin hankali.

            Kamfaninsu ya wucce a gigice, yayi parking. Yana shiga gurinsu Ahmad ya zube musu akan kujera tare da dafe goshinsa yace.
"Ku taimaka min, zasu rabani da matata."
     A tsorace suka ɗago kai tare da cewa "kamar Ya?"

       Zama yayi ya shiga basu labarin abinda ya aikata da irin hukuncin da...

         "Alhamdulillah, karshen tafiyarmu tazo yunus, nasan ban kaika samu da kuma buɗi ba, amma na hakura duk wani haɗakar dake tsakaninmu zan cire kaje ka zauna da Aneesah da ta baka shawaran sannan ita kuma maryam Allah yakarɓa mata sakinta a hannunka taje ta auri wani, ashe duk hiran da mukayi ka zauna kabugi cikina ne, lallai kayi kuskure ni ko sau dubu Rahilah zata haifa min yarana ina so, kuma bazan taɓa gajiya da ita ba, ada dan matsalata na aureta a yanzun kuma dan ta zame min wani yankin rayuwata ce, koda wasa bazanyi kuskure rabuwa da ita ba ko kuma naja dalilin da zasu rabani da ita ba, yayi maka kyau."

Inji Aman, yana gama faɗar haka ya tattara kayanshi yabar ofishinsu baki ɗaya.
       Bakin ciki ya hana Ahmad magana, kayanshi ya haɗa ya bar Yunus shi ɗaya. A ofishin duniya tayi mishi zafi kowa ya juya mishi baya, ji yake kaman ya haɗiye ranshi ya huta amma ba halin haka..

                Daga zaria kullum sai Alhaji ya buga mishi waya akan sakin, ga Hajiya ma da ta sakashi gaba. Mama kilishi ce take kulawa da lamarinshi idan akwai.
         Idan yaje gurin aiki ba kowa a ofishinsu sai shi ɗaya, duk su Aman sun daina zuwa, sai dai yaje shashin ma'aikata yayita kallon yanda kowa ke farin ciki, da walwala, toh.mi yasa shi baida farin cikin mi yasa ya rusa nashi farin cikin. Yana cikin ɗimuwa,

               ****
Tsautsayi ya rufta da Aneesah, suna cikin aikinsu tare da abokiyar aikinta wacce take cikin damuwa, kallonta Aneesah tayi sannan tace.
"Rita mike damunki, naga kwanan nan kina shiga damuwa."
    Juya kujeranta rita tayi cikin cunkushewar fuska, tace.
"Bari kawai Neesah, kinsan mahaifina sojane toh burinshi na auri soja irinshi, ba'a bukatar naja miki labarin. Yanzun dai sojan da ya nima min, zan aura shine muka ɗanyi making love da shi, tsautsayi yasa bamu saka goldenring ba, yanzun ina da cikin 2month na rasa yanda zanyi da cikin dan a coci ɗinsu Papa ba'ayarda da ka amshi cikin da za'ayishi daga waje ba yankan zama masifa da bala'i a cikin family da society."

    Dariya Aneesah tayi sosai, sannan ta kalleta tace.
"Yanzun sabida Allah sabida ɗan karamin cikin da kika ɗauka shine kika jefa kanki cikin damuwa yo Allah na tuba ina zan saka damuwa a raina, ciki ko na wata nawa ne zan iya cire shi ba tare da nayi nazarin ya zanyi dashi ba, idan kin shirya muje na kaiki a cire miki."

         Kamar rita ta fasa ihu dan murna, ana tashi a bankinsu suka suri jakarsu sai Rigasa.

        Koda suka isa, dr nacan yana aikiwa wata sai ihu take sabida burge mata cikin da yake.
         Suna zaune yafito sharfan da zuba hankalinshi tashe, ya nufi ofishinsa ya kira nurse aka fito da Yarinyar da aka burge mata ciki kamar matacciya, dake da uwarta suka zo nan ta riƙeta suka fita,
              Yana zaune ya dae goshinsa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login