Showing 1 words to 3000 words out of 40600 words
AISHATUL___HUMAIRAH
..... Labarin Indo .....
❤️💚❤️💚❤️💚❤️💚❤️💚❤️
=Na=
A'ishatu Bint Muhammad
(MATAR UNCLE)
🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀
The Story of life childhood, Entertainment, And Love.
. SADAUKARWA GA YAN UWANA.
Kauyen wakaza dake garin dustinma karkashin katsina state, a yau kuma can naje domin dakko muku wani muhimmun labari, ku biyoni dan jin ina zamu kwana, mai rubutu taku MATAR UNCLE.
KAUYEN WAKAZA
KATSINA STATE
🌺1&2🌺
Tafe take rungume da allo a hannunta, da ka ganta kasan daga makaranta ta dawo,cikin tsakar rana take tafiya yayin da kafarta ko takalmi babu, tayi wani bututu da jikinta,can nesa kadan naga tana wangale baki tare da bude baki tana fadin "Salame Salame, wadda aka kira da wannan sunan ne naga ta juyo take ta zuba na kare.
Ganin ta fara gudu ne yasa yarinyar binta, cikin lokaci kankane ta kamota tare da bugata da kasa, ta kuma haye kan ruwan cikinta, tana zuba mata kasa a baki, can kuma ta saki dariya tace "wai da ke salame kinci bati kenan ko, har ni zaki sa malam Dahe ya dakeni ko,tashi tayi daga kanta bayan ta cika bakin da kasa, ga jini yana zuba ta hancinta amma bata raga mata ba, bishiyar darbejiyan dake wajen tai tsalle ta dane tare da fizgota, lokaci guda ta dawo hannunta, bata wani ji tausayinta ba ta fara zabga mata, salame ba damar ihu.
Dik yawan mutanen da suka taru an kasa samun wani yayi mata magana, domin kana mata magana kanka zata dawo, kamar daga sama taji wata murya, lokaci guda ta yarda bulalan, tana kallonsa cike da tsantsar tsoro,wani saurayi ne cike da karfi ya fara jan hannunta suka bar wajen cikin lokaci kankane, mutanen dake wajen ne suka kama salame ta mike daganan kuma kowa ya watse ya kama gabansa.
Tafiya suke a daidai lokacin suka shiga cikin wani gida, na jar kasa ne, shigarsu ke da wuya na hangi wasu bukkoki guda 3 da suke a jere sai daga baya can na hangi wani abu kamar rumbu. Shigowarsa ne ya kalli tsohuwar dake gidan tana kokarin hada itace, domin ta dora sanwar abincinta, juyowar da zatayi ne ta ga mutum tare da yarinya, cikin hausanta irin ta fulani tace "to garba kace yarinyar yau ma tayi halin nata, kallon yarinyar tayi tace" wai ke indo yaushe zakiyi hankali ne iye, ke gaba daya bakya girma, rigima yau daban ta gobe daban, kafin ta rufe bakinta aka rangwada sallama a kofar gidan,garba ne yaja tsaki sannan ya saketa ya fita dan yasan kiran mai gari ne.
Fitarsa ne yasa indo ta kalli tsohuwar tace "to ke kuma ina ruwanki, mata sai sa'idon jaraba, malama ki kyaleni naci zamani na, ke wayasan ma me kikayi da kika tashi yin taki kuruciyar, kawai dan nazo a hannunki shikenan sai ki fara min jaraba, na rantse da allah kuma kema kin jawa kanki, a lokacin data rufe baki ne muryar garba ta fara tashi, alamun shigowar sa kenan,"zaki tashi mu wuce wajen mai gari ko sai na bata miki, yarinya mara mutunci, narantse da allah muka dawo daga wajen mai gari inaga sai na targadaki tsaki yaja ya tashi yayi waje, ba shiri ta tashi ta bishi tana kunkuni kamar wani sa'anta.
Iyalle bayan fitarta kuwa rike baki tayi tana fadin "kai wannan yarinya allah ubangiji ya shiryeki, yarinya karama sai wulakanci da rashin kunya, ga shegiyar fitsara, yarinyar kamar yarinyar aljanu, mayafinta dake jikin igiya taja sannan ta fice ta nufi wajen mai gari dan jin ina za a kwana a wannan lamari na indo.
A wajen mai gari kuwa, salame ce da mahaifiyarta sai mahaifinta a zaune a wajen mai gari, yayin da kallo daya zakayi mata kasan ta daku ba karya, shigowar indo da garba ne yasa taja tsaki, kallonta indo tayi take a wajen ta fara babbaka dariya kamar wata sabon kamu,dik yawan mutanen wajen sakin baki sukayi suna kallonta kamar wata sabuwar kamu, tsawar da garba ya daka mata ne yasa ta yin shiru, salame ta kalleta cike da kuluwa, mai gari sanin halin indo ne yasashi fara magana a hankali.
"ke indo me ya hadaki da salame ne, cike da tsiwa tace" yo baba me gari kaji min wani batu dana kasa gane ina ka dosa, salame ce a makarantar kan tudu tasa malam iliya dan me karfi ya dakeni, ni kuma wallahi tinda ya dakeni nace a kanta zan rama, shisa na kamata na jibgi abar banza, mai gari ne yayi gyaran murya yace "ke bakisan a inda kike ba har kike wannan lafazin, kallon salame yayi yace ke salame meyasa kikasa malam ya daketa.
Cikin kuka da sharbar majina, salame tace" baba mai gari wallahi ita ce ta samu allo na ta wanke min hi a kogin dan marka dayake kan hanya, shi ne ni kuma da muka je makaranta na fadawa malam, yace sai ta bada kudi an min wani rubuta, da tace bazata biya ba shine yayi mata bulala goma, sannan yace ta bani hakuri amma sai taki.
Mai gari ne ya kalli indo yace ke indo haka akayi"dariya ta kyalkyale da ita tace eaa haka akayi mana mai garin garinmu.
Mai gari ne yayi nuni take wani dogari ya fito da wata zabgegiyar dorina mai baki biyu, indo idanunta idan dorina ai tini ta tattara ya nata ya nata tai waje ta bar wajen, yayin da mai gari yace a bita a kamota dik inda taje.
Gudu take suna binta, ta kasuwar garin ta biyo, tana yi tana waiwaye, a lokaci daya ta bace musu, sunyi nema sunyi nema har sun gaji abin har ba'a magana, haka suka hakura suka dawo domin fadawa mai gari.
Indo kuwa samu tayi ta shiga rumfar idi mai shayi cikin inda ake ajiye bread nan ta samu ta rakube, idi shi tsoransa allah kada ma ta dauki wani abun, sai da ta dauki wajen mint 30 sannan ta fito, a lokacin rana ta take, kallon biredin idi tayi ta hadiye yawu, kallonsa tayi tana daukar daya, cike da bacin rai idi yace ke wallahi ajiye min biredi tinda ba ubanki bane ya siya min, wani kallo tsyi masa kallon baka da wayo, tare da fadin zo ka kwata, nufota yayi cikin sa'a kuwa ta tsugunna kasa ta debo ta watsa masa a ido,ta runtua na kare.
Tafiya take tana yagar biredin dake hannunta, a lokaci guda ta cinye hade da sakin wata gyatsa, shafa cikin tayi sannan ta fara magana, amma gaskiya ban koshi ba, kuma ni bazan koma wannan gidan ba indai garba baya nan, kara na bari sai can anjima, tafiya take tana watsa kasa, can gaba kadan tazo shigewa ta hango tukunya a wani gida, murmushi ta saki tana dariya, shiga tayi tana zazzare idanu,
Faranti ta hango da ludayi hakan yasa ta bude tukunyar, dafaffiyar shinkafa ce jellof taji alayyahu da manja, diba tayi sannan ta koma gefe ta fara ci hankali kwance, har ta gama cinyewa tasha ruwa sannan taji alamun mutum zai fito, da gudu ta fice daga gidan tana waiwaye.
Haka tai ta gantali a cikin kauyen wakaza ganin dare yakiyi ne yasa ta tafiya gonar wuro tare da danewa bishiya, can kusan la'asar sannan ta sakko tai hanyar rafi.
Sai can wajen magariba sannan ta fara kokarin shiga gidan nasu, ba kowa a tsakar gidan hakan yasa fa shige madafa, tuwon da iyalle ta gama ta kwasa ta fara ci kamar jaka, sannan ta shige makewayi daga baya kuma ta fito, a dai dai lokacin iyalle tafito, kallon ta take cike da mamaki, "ke yanzu indo haka kika zaba ko, wallahi ke da mai gari domin yanzun nan zan kira garba yazo yayi miki maganin abinda yake damunki, yarinya sai iskanci, murguda baki indo tayi" ke wallahi iyalle kin cika jaraba, kin san allah kika sake kika kira garba wallahi ai bata rufe bakinta ba taji shigowarsa, kallin kallo aka fara, a wani gudu tai tsalle ta dare katangar gidan ta gudu.
Sai wajen 10 ta dawo daga dandali a lokacin bakajin sautin komai sai na tsuntsaye,mainakon tayo hanyar gida sai tayi hanyar gidsn mai gari, cikin sa'a kuwa fa dare katangar gidsn ta fada cikin gidan, turakar mai gari ta karasa, sai kuma ta juyo ta dawo zuwa tsakar gidan, wani mulmulallen icce ta dauko tare da burshi ne fuskarta da toka kamar fatalwa,dakin mai gari ta shiga shi kuwa sai shara bacci yake, kamar xaga sama ta daga wannan iccen ta rabka masa a kafa, a fisrgice ya tashi zaune yana fadin nashiga3, fitilar gefe ta kunna a lokacin ya ganta fara fat abinka da me bacci.
Mai gari ne ya fara magana "dan allah kuyi hakuri ku Kuke ganinku ba mu muke ganinku ba, ku taimaka dan allah ku kyaleni, a lokacin da indo ta fahimci ya dauka cewa ita din aljana ce, sai ta babbake da dariya.
AISHATUL___HUMAIRAH
..... Labarin Indo .....
❤️💚❤️💚❤️💚❤️💚❤️💚❤️
=Na=
A'ishatu Bint Muhammad
(MATAR UNCLE)
🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀
The Story of life childhood, Entertainment, And Love.
2🌱3
"Kai mai gari rufe mini baki, kasani daga yau sai yau karka kuskura koda wasa a kara kawo maka karar indo yar wajen iyalle ka karba har kai tinanin zakai mata hukunci, idan kuma ka kuskura ka aikata wannan hukuncin to na rantse da sarkin aljannu sai na kwakule maka idanu, na cire maka hanci, sannan na rabaka gida 6 naba yaran sarkin aljannu su gama min da kai,"
Mai gari kusan fitsari ya kusa saki da toh toh yake amsawa, tsabar firgicin da yake ciki ya rasa ta ina zai fara,cikin kakkausar murya indo tace" zan tafi amma ka tabbatar da cewa zan dawo da zarar kayi kokarin taba ta, sannan bazan barka haka ba, koma kai bacci, cike da jin tsoro ya kwanta yana raba idanu, daga iccen tayi ta kara sauke masa a kafa, bayan data toshe masa baki, daga nan ta fice daga dakin ta inda ta biyo ta nan ta koma, sannan ta tafi makwancinta, tana ta kalle kalle.
WASHE GARI
Tin wuri ta tashi ba abinda tayi sai jikin bishiyar darbejiyan dake tsakar gidan taje ta zauna tana kallon giccin iyalle, Garba ne ya shigo yana kallonta cike da bacin rai amma ko kallonsa batayi ba, matsawa yayi kusa da ita yana fadin "ke baki iya gaisuwa bane, indo tana jinsa amma tai banza dashi domin yau yanda takejin kanta wallahi zata iya koma menene amma bazata yi masa kuka ba.
Kafcecen hannunsa ya daga ya shara mata mari, dagowa tayi tana kallonsa, fada ya fara yi mata ta inda ya shiga ba tanan yake fita ba, ganin kamar ya tsai da ta ne yasa ta mikewa ta fice daga gidan, cike da mamaki yake kallonta domin tabbas yanzu indo ta daina tsoron ko wane abin halitta.
Tafiya take daidai kofar gidan su salame ta tsaya, kanta tsaye ta shiga a zaune ta tarar da salame, zama tayi kusa da ita da wani mugun tsoro salame take kallon indo, domin ita har ga allah ta tsorata da lamarin indo, katse tinanin indo tayi tace "ki tashi mutafi kinsan dai habi tana can tana jiran mu saboda kinsan mu ne kawayen amarya ko, dai dai lokacin mahaifiyar salame ta fito daga bayi," ke kuma annoba me kika dswo kiyi mana a gida wallahi indo idan baki fita narantse sai na lahanta ki, indo cike da tsiwa tace" karki fasa kuma ai ba wajenki nazo ba wajen 'yar ki nazo, ke salame taso mutafi, ba yanda salame ta iya dole ta mike tabi bayan indo, domin idan ta kuskura tayi mata gardama tsabb zata kara dankara mata duka ba abinda ya dameta.
Gidan su habi suka tsaya a lokacin tana cin kosai da kunu, ko gaisawa basuyi ba indo ta dauke kosan da kofin kunun ta koma gefe, tana ci tana jiran idan akwai wani mai magana a cikinsu, har tayi ta gama sannan ta ce "ke habi taso muje a karbo kudin, kuma na rantse harda ubana dik yar bura'ubar da bata bada ba, ba wanda zai bata abin ajo, ke habi kuma wannan ba ruwanki ki barni da su kawai, ita dai habi tasan hali shisa take ta daga kai kamar wata kadangaruwa.
Tafiya suke dai dai gidan mai gari suka tsaya, suna kokarin shiga, indo a gaba tin daga bakin kofa take fadin gafaranku dai masu gida, wuri suka samu suka zauna, indo ce ta kalli matar mai gari tace lafiya dai laure naga dik kin wani chanja, ke tsaya ina barki take,"laure tace ai bata nan tana makaranta, ba wanda ya kara magana tashi sukayi zasu tafi, indo ce tace suyi gaba ita kuma tai bangaren mai gari.
A zaune yake yana firfita, idanunsaa ya dora kan indo take ya kau da kai yana kallin gefe, daga can yace" hajiya indo barkanki da hutawa ya mutanen gidan naku dan allah a gaishe min da iyalle, dariya ce taso kwace mata dan haka ba ta tsaya ko ina ba sai kofar gidan a lokacin ta saki dariya harda rike ciki. "habi ce tace yadai indo me ya faru tsaki indo tayi" to ke kuma yar sa'idon jaraba, wallahi habi ki fita daga idona kuma muje wajen idi ya bamu rabonmu, daga nan sai mu biya shagunan kasuwa kowanne dan iskan ya bamu kudin ajo.
Haka kuwa sukayi dan ko wane shago daga mai 20 sai mai hamsin, kafin wani lokaci salame da habi sai washe baki sukeyi, daga nan suka fara bin gidan kawaye suna karbar kudin, dik wadda bata bada ba ita da indo, dayake sun san halin indo sai su kwammace su basu kawai.
Indo tin sanda ta fito daga gida har akai sallar laasar amma bata koma ba tana nan tana gantali da su habi, gaba daya kudinne da aka samo indo tace ita za'a bawa, dole sunaji suna gani suka bar mata akan gobe da sassafe za a fara rabon kayan ajo, al'adar kauyen kenan.
Tafiya takeda dan karanta tanayi tana wakarta ta karkara, Kabiru ne ya hango ta a take ya fara yankare hakora, tin daga nesa ta hangosa tassn me yake nufi, karasa wa tayi tana tsalle tana dariya tace "aa kabiru sannunka wannnan kajinfa, mika mata yayi yace" dama na inna ne zanje na saida mata su a kasuwa, karba tayi ta duba sai da ta samu katuwar ciki sannan ta karbe ta tace "to maza jeka na karbi wannan, dole yanaji yana gani indo ta karbe kazar ba damar yayi magana ta dankara masa wulakanci, shikuma gashi yana son indo bazai iya hana ta ba.
Kofar gidan su salame ta tsaya, sai kuma ta shiga ba wanda tayiwa magana ta tafi neman wuka, sai da tasha fama sannan ta samo wukan, tare da danne kazar ta yankata,dik wannan dramer a gaban uwar salame da salame domin su yanzu tsoron indo sukeji, sun kaita kara amma mai gari ya tashi kafa da targade, idan ba sa'a ba aljanun indo ne suka ligudesa, salame ce ke magana kasa², juyowa tayi tana kallon salame, sai kuma taga tayi tsitt.
Tana gama yankawa ta bar musu wukar anan ta tafi abinta, gida ta shiga tana wakar samun nasara, iyalle ce ita kadai tana jan carbi, muryar indo ce ta katse ta, da take fadin ina Kawu garba ne iyalle, amsa ta bata da "ya tafi birni sai gobe zai dawo, bata kara magana ba sai madafa ta shige, ruwan zafin dake tukunya ta juyo ta zauna ta fige kazarta, sai kuma ta zabura ta mike, iyalle ki karasa min wannan aikin ki dafa min ita, ki tabbata taji daddawa yanzun nan zan dawo da gudu ta fice daga gidan.
Iyalle ce ta bita da addua'ar samun shiriya, domin ita abin ma damunta yake, ta rasa yadda zatayi da indo, kwata kwata bata biyo mai halin nata ba, amma zan san yadda zanyi, mikewa tayi ta fara kokarin aikin dan ta riga da tasan halin indo ba mutunci gareta ba, yanzu sai taja za mata asara.
Fitarta da tayi tinawa da tayi da gidan su dije da yake sunje karbar kudin ajo, taga suna dafa taliya da manja, gidan ta shiga tana haki tana kallonsu, cikin bacin rai ta fara fadin na rantse m
da allah dik wanda ya cinye taliyar nan bai bani ba wallahi wallahi yau sai na muku bakin aiki, yayan dije ne ya fito daga daki yana fadin ke"oh wai taliya to mun cinye kiyi dik abinda zakayi, cike da fada tace kai "katon banza badakai nake ba, duka ya kai mata ta goce ta nufi randar dake karkashin bishiya, wani katon icce ta daga ta sauke musu a lokacin suka tarwatse, wannan karar ce yayi sanadiyyar fitowar dije daga daki dauke da kwanon taliya.
Indo ce ta kalle tace "wato tsabar mugunta da ga taliyar amma kika hanani ko, wartar kwanon tayi tana zama akan kujerar katako, ta fara zuba taliyar, yayan dije ne yayo kanta, ya sakar mata dundu, amma ko a jikinta, ci gaba tayi da cin taliyarta, sai da ta gama sannan ta dago tace ka tabbata sai na rama. Ke kuma dije "wallahi sai na ci mutuncin ki da kin rage taliyar amma shi ne kika barni nazo ina hayaniya, maza samomin ruwa nasha, dije ta rasa ya zatayi sai can ta nemo wani a kofi ta bata tana sha ta mike tabar gidan.
Ganin ta cika cikinta ne yasata yin hanyar gida domin zuwa ta cinye sauran kazar da iyalle ta dafa mata, tin daga kofar gida ta ke jiyo hayaniya, hakan ya tabbatar mata da muryar innar kabiru data kwacewa kaza, hakan yasata kama katanga tabi ta wajen rumbu, iyalle na can tana bata baki ta zagayo ta juye kazarta a roba ta mai da tukunyar, fakar idanunsu tai ta shige bukkarta.
Iyalle da kyar ta bata baki akan a bata kazarta, tana dakko tukunyar kazar taji ba kaza ba alamunta, inna ce ke banbami akan a fito mata da kazarta, indo na daki tana jinsu.
💋💋MU💞💋🌺💚
AISHATUL___HUMAIRAH
..... Labarin Indo .....
❤️💚❤️💚❤️💚❤️💚❤️💚❤️
=Na=
A'ishatu Bint Muhammad
(MATAR UNCLE)
🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀
The Story of life childhood, Entertainment, And Love.
4❤️5
Sai da ta tabbatar da tafiyar inna tana ta zuba allah ya isa sannan ta fito da robar, abin mamaki gaba daya ta cinye naman saura tsoka daya data rage, mikawa iyalle tayi sannan ta fice daga gidan tana wakarta.
Dandali ta tafi a can taga tarin yammata da samari,