Showing 9001 words to 12000 words out of 40600 words
wani abokin malam ali yace yana sonta da aure, batayi wata wata ba kuwa ta auresa, domin zaman bazai mata, kasancewar bata da 'yan uwa, kuma su din yan gudun hijira ne, auren aka daura da malam sale, malam sale yana kulawa da ita sosai daga ita har yaranta.
Bayan wasu shekaru ne yara sun tasa sun zama samari, shi nura sai ya gaji sana' ar mahaifinsa, shi kuma baffa yace ai shi bazai iya kiwo ba, dan haka yake zuwa kasuwa cikin gari kullun ba ranar fashi,kwanci tashi ba wuya a wajen allah, a inda yara suka girma ali tin a wajen sana'arsa ya samu 'yar gidan wani mai gidansa, ai kuw aya aura masa ita tin daga nan baya zuwa wakaza sai karshen wata.
Sai bayan da ali yayi shekara 3 da aure sannan nura yayi, a lokacin ma ali yana da da 1 mai suna Ahmad,nura ya auri wata yar garin bauchi ce,dayake yana zuwa kasuwanni, anan ne aka dauro musu aure, suna zaune lafiya da iyalle.
Kwatsam wata ranar jumua aka tashi da mutuwar malam sale, sakamakon yar karamar jinyar da yayi a daren, cikinsa ya yi ciwo, washe gari ne kuma aka kaisa gidansa na gaskia,bayan barmata dan sa daya tilo daya mallaka a dunia, bayan sadakr 7 kowaa ya watse daga nura sai iyalle sai aminatu matar nura.
Shekarar su 2 da aure amma sam allah bai basu haihuwa, sunyi magani amma maganin kamar baya musu aiki shisa suka hakura suka fawwalawa allah, ana cikin wannan yanayin ne kuma, matar ali ta kara haifo yara 'yan biyu, zo kuga murna wajen iyalensa da kuma mahaifiyarsu, ranar suna kuwa macen taci sunan A'ishatu wato iyalle, sai kuma namijin ne wanda aka sa masa sunan nura,haka akyi suna kowa na farinciki haka kowa ya dawo gida.
Ana cikin wannan lamari ne ali ya tattara ya tashi ya koma kano da zama, domin yanzu ya samu cigaba, daga nan sukayi nisa da iyyale, basa samun ganin juna, dan ma tana da garba da nura a kusa da ita, idan tanason tayi magana da shi sai dai su fita gari su kirasa.
Bayan shekara 1 da komawar ali kano, allah ya bawa aminatu ciki, zo kaga murna wajen aminatu da iyalle, a haka iyalle taci gaba da kulawa da ita har allah yasa ta haifi cikin nata, lafiya lau ta haifi yarinya mace santaleliya, amma da dare yayi danda nan jiki ya rikice kafin kace wani abu, tini amina tace ga garinku nan, ba iyalle kadai ba hatta mutanen garin sunji mutuwar aminatu domin mutuniyar kirki ce.
A ranar da aka kai amina gidanta na gaskia ne, bayan sun dawo jaririya tace batasan batu ba domin ita yunwa takeji, wata daga mutanen kauyen ce ta dauki indo, kasantuwar tana da jariri itama, ta hadasu tana shayar dasu, bayan sadakar 7 anan aka sanar da mutanen wajen sunan yarinya aisha amma za a na kiranta da indo, haka kowa ya watse yana jimamin wannan yarinya.
Sai bayan sadakar 7 ali ya samu labarin mutuwar aminatu,zuwa sukayi a lokacin ahmad yayi wayo sosai, sai kuma yan biyunta da take goyo, bakin ciki wajen salma matar ali, iyalle kuwa zuwansu ya dawo musu da mutuwar aminatu sabuwa, salma ce ta kalli iyalle tace "iyalle dan allah ki bani indo na hada da ita, iyalle ce tace" kul salma baki ga yan 2 kike goyo ba, dan allah kibarta anan kinji.
Nura ma yayi farin cikin zuwan ali da iyalinsa, ali ne suna zaune a farfajiyar gidan, sai indo datake hannun iyalle, ahmad ne ya matsa ya fara yi mata wasa, salma ta lura da yanayin ahmad, dik lokacin da aka dakko indo hankalinsa na kanta a yan kwanakin nan.
Da daddare salma ta kalli mijinta ali tace "daddyn ahmad, juyowa yayi yace na'am, dama nace me zai hana a hada ahmad da aisha aure saboda naga yana kaunarta, ka duba ka gani yadda kullun yake kusa da ita, ko maidata za'ayi ya dinga kuka kenan, shiru ali yayi sai kuma yace" tabbas wannan shawarar taki tayi min yadda ya dace, dama inason wannnan zumunci namu ya dore har abada.
Washe gari bayan sun shirya, kowa ya fito su ali zasu tafi, ali ya sanar da iyalle da nura wannan batun kuma sunyi matukar farinciki, zo kaga iyalle baki har kunne, daga baya kuma ta fara zuba musu addua.
BAYAN SHEKARA 5
Abubuwa da yawa sun faru,a ciki har da girman indo wanda gaba daya idan ka ganta bazaka ce itace ba, ta zama wata "yar karama bazaka ce indo bace, sai dai dsn banzan rashin ji kamar rainon aljaan.
Yauma iyalle bata nan ta tafi daji tayo icce saboda garba baya nan, indo ce ta shigo gidan allon hannunta ta ajiye, ganin ba kowa a gidan yasa ta kai ta fice, gidan matar data shayar da ita ta tafi, tin daga kofar gids take sallama, tana zuwa ta ganta tana hada kaya, zama tayi tana goge hawayen fuskarta, yanzu shikenan inna tafiya birni zakiyi, wadda aka kira inna ce tace "allah sarki indo tafiya zanyi ban ga ta zama ai, amma dan allah indo kibi a hankali ki tsaya ki maida hankali kiyi karatu kinji saboda wataran idan banzo ba ke ma zakizo.
A haka sukayi sallama, a wannan ranar ta bar kauyen a wannan ranar mahaifin indo ya kaita makarantar boko, da farko dai haka sukace bazasu dauketa ba, amma kuma da sukaga tana da konanne wayo yasa suka dauketa shi kuma ya dawo gida.
Yauma makarantar ta shiga ajinsu ta shiga inda take, wajen maza ta je zata zauna wani yaro ne ya bige ta cikin gwarancinsa yace "ke dallah matsa daga nan ki tafi can nan ne wajenki, cike da bacin rai ta daga hannu ta zabga masa mari, kuka ya saka amma ita ko a jikinta.
Dawowarta ne ta hango mota, tana ganinta ta ruga ta shigo gidan ko sallama babu,nura ne a gefe a zaune kusa dashi tazo ta zauna tana kallonsu, ganin ba ahmad yasa ta kalli nura tace "baffa ai banga yaya ahmd ba, sai 'yan biyun mama, dikansu dariya sukayi, nura ne yace mata" ke baki iya gaisuwa ba, sai a lokacin ta gaishe su.
Kwanansu 1 suka tafi a lokacin indo ji tayi dama ta bisu amma ba dama dan haka ta zauna, bayan shekaru 4 anan hatsabibancin indo ya kara bayyana, gaba daya ta takura kkwa bata kallon kowa da gashi, barna kuwa har da wadda ba ai zato ba, mai gari ba yadda baiyi ba da indo amma ina.
Ko a makarantar bokon ma korarta sukayi saboda ta samu wani dan aji 5 ta masa duka harda fasa masa goshi, da yayarsa tazo shiga ta hada dasu ta doka, shi ne dalilin korarta, taji dadin hakan daganan ta koma yawon allah rufa asiri.
A cikin wannan shekara ne mal nura rana 1 ya tashi da matsanancin ciwon ciki kwanan 2 yace ga garinku nan, ali ne ya yazo shi da iyalinsa a lokacin harda ahmad.
Bayan sadakar 7 ahmad ne rike da hannun indo sai surutu take masa, murmushi yayi yana kallinta yace to "humaira ni zan tafi kinji amma dai zakizo ko, kinga da iyalle zata bani ke da tini mun tafi, indo ce tace" to ai yaya amad bazata bari kawai ka bari idan na girma zanzo, murmushi yayi yace "allah to tsaya anan na miki hoto ko, yadda idan kikazo zanga kin girma ko baki girma ba, tsayawa tayi yana zuwa zai dauko ta sa dsriya, hoton yayi kyau sosai, daga haka sukai sallama indo harda kukanta, wannan shi ne karo na farko da naga indo tayi kuka.
💘💘💘CIGABAN LABARIN❤️💘?
?AISHATUL___HUMAIRAH
..... Labarin Indo .....
❤️💚❤️💚❤️💚❤️💚❤️💚❤️
=Na=
WALEEDAH MUHAMMAD
(Auntymu)
🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀
The Story of life childhood, Entertainment, And Love.
MARUBUCIYAR
A sanadin kishiyar uwa
Jannat
Kawancen mu.
And Now
AISHATULHUMAIRAH
12💗13
Haka dai sukaci gaba da zama da indo, indo bata zuwa makaranta kullun ko ka ganta a daki ko kuma kullun tana dawan makaranta a haka dai har aka debi sati 6.
Iyalle tana zaune a tsakar gida tana tankaden masara domin samu zatayi tayi musu tuwo, garba ne ya shigo yana sallama, da sauri ya taho yana fara'a yawwa iyalle kinga yayan birni ne yake kirana, shi ne yace na kawo miki, dik wannan maganar da yake bai tsaya ba sai da ya kai aya.
Karbar wayar iyalle tayi tana fara'ah allah sarki aliyu, gaisawa sukayi da ali sannan kuma suka dakko wata hirar daban ta yaushe gamo, iyalle ce tace "wai ke yaushe zakazo ne, yaushe rabanka da garin wakaza ali, banji me aka ce va sai murmushi da iyalle tayi kawai tana sanya masa albarka, yayin da shi kuma ko me yake ce mata allahu aalamu.
Yau ta kama monday ilahirin student din na gaban assembly din da ake gabatarwa, ba akan komai bane illa akan tsafta, zuwa da cikakkun kayan aiki, da sauransu.
Bangaren indo kuwa tana ta shirga bacci, tashi tayi ta duba hostel din ba kowa kowa ya tafi class, tsaki taja tace "aikin banza kawai kowacce yar banzar ta shige ta tafi wata boko, suna ji ana cewa boko a wuta amma suna zuwa, bahol din makarantar ta tafi tana wakarta, kamar daga sama ta hangi wata dattijuwar mata, kwala mata kira tayi maimakon ta amsa, aa sai tafiya tayi taci gaba da wakarta tana karkada kai kamar kadangaruwa.
Dattijuwar ce ta biyota zata rikota, ai tana ganin haka ta sa gudu kamar zata tashi sama, bin ta tsohuwar take ganin tayi mata fintinkau ne yasa ta hakura tana fadin ai na ganeki zaci ci ubanki, yar banza.
Indo kam sai da tayi nisa, kamar wadda aka mintsina naga ta tsaya tana daroya sai kuma tace "da an gaya miki nidin ta wasa ce har da zaki biyoni, kamar wadda akayi wa allura naga ta zabura ta ruga,sai da taje katangar karshe sannan ta fara kokarin hawa, bata wani bata lokaci ba tai tsalle ta dare, wani tsalle tayi sai gata a wajen gari, murmushin samun nasara tayi sannan tace, "wo ni, ni indo, ni indon iyalle, indon garin wakaza.
A wunin ranar haka tai ta gantali, ganin tana jin yunwa ne yasata zuwa wajen mai. Abinci, zuba mata tayi sai da ta tabbatar ta koshi, sannan ta silale ta gudu,sai da ta narki yawonta, sannan ta fara kokarin komawa makaranta, kasancewar la'asar tayi.
Haka aka shafe sati indo bata je class ba, wata ranar alhamis ne ta shirya, dik da sai wajen 9 ta fito ta wuce ta gaban mai gadin, amma sanin tana basa 'yan chanji ne yasa bai mata magana ba, shiga makarantar tayi, ba kowa a makaranta, kowane dalibi yana class, ajinsu ta nufa tin daga nesa ta hango malam a ciki, kanta tsaye ta shige, sa' arta 1 shi ne bai ganta ba, domin hankalinsa na kan board din da yake rubuta test.
Zama tayi a inda ta saba zama, kallin ta kusa da ita tayi tace "ke sammin paper, ba yanda ta iya haka ta gutsuro mata ta bata, abin mamaki sunanta ta rubuta sannan ta rubuta na class, sai kuma kai tsaye ta fara answering questions din, ta kusa da ita ce ta kalleta tace" ke bai ce a fara ba, maimakon ta bata amsa sai kallon baki da wayo data bita da shi, sanann taci gaba da abinda yake.
Yana gama rubutawa yace a fara ko 5mint bai ba, ta mike tana zuwa ta mika masa, kallonta yake domin bai taba ganinta a class din ba, da mamaki yake kallon paper domin wannan tsattsauran question din dole ne mutum ya dau lokaci bai gama ba, amma ace ko 5mint batayi ba ta gama.
Tsayar da ita yayi yace "ke kallonsa tayi sai kuma yace" dama anan class din kike, eaa kawai tace ta wuce, bude paper yayi abinda ya basa mamaki ne yasa ya karasa gabanta, ke a ina kika yi copy na wannan answer, bata bashi amsa ba, jakanta ya janyo sai dai me dik littafin daya dakko sai dai yaga empty domin ba komai a ciki, ganin bashi da wata hujja ne yasa ya kyaleta kawai domin abin nata yafara basa mamaki.
Haka yau ta kasance,bayan an tashi daga school ne na hangi malamar ta dawo cikin su fauzah na ganta suna tafe suna hira kamar ba indo ba, daidai wajen wasu senior suka zo wucewa, dayarce katuwa tana zaune a karkashin bishiya tana zaune kan benci, gani tayi su fauzah sun tsugunna sin gaisheta, maimakon ita ma tayi hakan sai tsaki da taja ta wuce, katuwar ce tace "kai ku bita ku kamota kuma kuzo min da ita, binta sukayi.
A lokacin indo tana hostel har ta cirekaya, shigowar su fauzah ne suke ce mata" ke indo waya ce baki gai da aunty babba ba, to wallahi kin jawa kanki dan na rantse sai kin daku, kallonsu tayi taja tsaki,aikin banza ku kuka ga zaku iya badai ni ba, zama tayi ta fito da gurasa ta fara turata da ruwa, tana yi tana balbalin Masifa.
Shigowar yaran aunty babbane suka hango indo sai cin gurasa take, sai kuma wata takardar tsire a kusa da ita fall da naman, kusa da ita sukazo, dayar ce tace "ke taso mu tafi anty babba na nemanki, maomakon ta tafi sai babbakewa da tayi da dariya, tace" amma ku dai anyi shashashu wata can katuwa ba kanwar uwarku ba, bata ubanku ba ku kirata da aunty,to kuje kuce mata nace banzuwa,ganin zasu bata mata lokaci ne yasa dayar tace larai janyota mu tafi.
[10/12, 3:49 PM] Waleedah Muhammad 😍❤️: Tafiya tayi gadan gadan domin ta janyo indo, amma abun da yabawa kowa mamaki bar da ni kaina dana tsaya dakko rahotan, ko kadan indo batayi motsi ba, bare a saka ran za a iya motsata, jan ta takeyi amma ina, juyowa tayi tana fadin suwaiba taimakamin, tahowa tayi suka fara kokarin janta, indo tana jinsu amma taci gaba da cin gurasarta hade da tsiren da ni kaina bansan a inda ta samo ba.
Ganin taki tahowa ne yasa suwaiba kallon larai tace "kinga muje mu fadawa aunty yadda komai ya faru, tafiya sukai suna haki gaba daya sun jigata, suna fita ta mike tana kallon 'yan hostel din tace" to munafukai ku kuma kun tsaya kuna wani kallo na, narantse dik yaron da yace ga inda na tafi sai na tura masa aljanu guda dari 500 sunyu min maganin sa saboda naga kamar kanku rawa yake.
Haka ta fice daga hostel din, hanyar fitarta daga makaranta tayi tana tafe tana waka, dai dai bakin katanga tai tsalle ta dane ta fito, kallon garin tayi tace "aikin banza ashe ma, azo a wani kulle mutum a makaranta, maimakon ta tafi cikin gari kamar yadda ta saba aa sai naga ta yanki daji ta fara tafiya, sai da tai nisa ta tsaya.
Aunty babba ce ta shigo tana wani bubbudawa tsabar kitse yayi mata yawa, shigowarta ne yasa kowa yayi shiru yana kallonta, dube duben neman indo take amma ko sama ko kasa ta rasa indo, dan karamin tsaki taja tace "ku fada mini inda ta tafi ko kuma yanzu na muku punishment, jin shirun da sukayi yasa tace" gaba dayanku ku fito dan bura'ubanku, ba wanda ya mata magana fitowa sukayi, kallonsu tayi tace "oya knell down ba wanda zai he islamiyya a yau din nan wallahi har sai indo ta dawo.
Haka bayin allah suka jeru a rana, sai kyalli sukeyi, ga yunwa suna jinta, ga kuma wannan hukunci na indo sai ta dawo za a sakesu.
Tofa masu karatu ku biyoni.
😍❤️: ALLAH YANA SON ME ƊABI'U UKU.
-
"Wato wasu ɗabi'u ne guda uku, ba wai don su kenan ba, amma su aka lissafa cewa lallai ne Allah yana son duk mutumin da ya siffantu da waɗannan halaye guda uku don muhimmancin dake tattare dasu".
-
Manzon Allah ﷺ yace: lallai Allah yana son bawa, me taƙawa, me ƙana'a, kuma wanda baya nuna cewa shi wani ne fiye da kowa.
-
▪️Me jin tsoron azabar Allah.
▪️Me gamsuwa da abinda Allah ya bashi.
▪️Me ɓoye aikin alkhairinsa daga barin yin riya.
AISHATUL___HUMAIRAH
..... Labarin Indo .....
❤️💚❤️💚❤️💚❤️💚❤️💚❤️
=Na=
WALEEDAH MUHAMMAD
(Auntymu)
🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀
The Story of life childhood, Entertainment, And Love.
KING AND QUEEN WRITERS ASSOCIATION
MARUBUCIYAR
A sanadin kishiyar uwa
Jannat
Kawancen mu.
And Now
AISHATULHUMAIRAH
14💗15
Can bayan awa 1 naga indo ta fito tana tafe tana murmushi, irin murmushin samun nasarar nan, maimakon ta kkma ta inda ta biyo aa sai ta juye ta nufi hanyar cikin gari, yawonta take hankalinta kwance,dai dai wajen wani makaho ta tsaya, dariya ce ta kwace mata yayin da ta hangi wani ya basa kudi yana lalubawa, da gudunta ta karasa inda yake wuff tayi ta dauke sabuwar 500din tana fadin allah ne ya bani, kafin makahon yayi wani yunkuri ai tuni tasa ta.
Haka tayi ta bin unguwa unguwa, daidai wani katon gida naga ta tsaya tana daroya ita kadai, sai kuma tace "aradun allaj yau sai na shiga gidan nan domin da gani gidan nan ana cin dadi, kai tsaye tafiya tayi, tin a bakin gate suka fara tataburza da mai gadi, fakar idonsa tayi ta shige gidan, wuff ta fada falo mai gadin ne ya biyo ta da sauri domin yasan zata iya ja ya rasa aikinsa.
A zazzaune ta tarar da mutanen su 4 suna cin abinci, kamar doluwa haka ta tsaya tana kallonsu, sai kuma ta shige wajen abincin, ganin jello din shinkafa ne yasata zaro ido tana fadin " ahayye wallahi yau zanci dadin da nadade banci ba, al kir'ani rabona da abincin nan tin a gidan mai gari, abincin gaban wata budurwa ta dauke ta fara ci kamar kura.
Mutanen gidan ne suka tashi, dayar ce ta kalli dayar tayi mata sign, cikin dan kankanin lokaci ta samo madoki, indo bata ankare ba taji saukar karfe a bayanta, abinda ya bani mamaki masu sauraro, karfen lankwashe wa yayi amma ita ko gizau batayi ba, kallon kallo ne ya shigo tsakanin wadan nan yammata, sai wani namiji.
Namijinne ya karasa gabanta, ya rike ta yana fadin "dan allah am sorry please what do yiu want in my house, dariya ta babbake da ita tace, kai jan banza, kayi min hausa, dan aradu banajin wannan yaren, kallon kallo sukayi, bai kara magana ba da saurinsa ya mike