Showing 6001 words to 9000 words out of 40600 words
ba wani excuse ta danna kai tana muzurai, wasu kwanika ne guda 3, zama tayi tana baje baki yayin da lawan ke kallonta a fusace, ko kallonsa batayi ba ta fara kokarin aikin budewa, daya naman data baro ne, daya kuma garau garau sai ruwa, ba abinda ya fito daga bakinta sai "Alhamdulillah amma dai lawan ka koshi da wannan abincin naka shisa kakeso na maka aiki, lawan kasa magana yayi ya tsaya yana kallonta.
Kofar gidan mai gari ne taff da mutane, kowa yana tofa albarkacin bakinsa kuma ba komai bane maganar tasu sai indo,ita wadda akeyin maganar dominta ma bata wajen bare tasan ma da ita akeyi, garba ne ya mike yace "to jama'a ku saurara dik wannan jawabin ba akan indo bane to insha allahu nan da gobe war haka tana makaranta, domin kuwa zata koma makarantar kwana ta baku waje ku huta, kowa na wajen ba abinda yake fadi sai Alhamdulillah, kara ma haka.
Mai gari ne ya katsesu yace "to ku sani dai wallahi dik mai so ya rabu da indo lafiya to ya zama tabbas ya bata wani abin, idan ba haka ba wallahi kunsan sauran, liman ne ya kallesa da mamaki yace" amma me gari yadai me ya faru, murmushi mai gari yayi yace "bazaka gane ba liman wallahi aljanun indo su suka targadi ni kwanaki, kowa na wajen shiru yayi domin kuwa idan haka ne tabbas indo nada aljanu masu karfi.Da wannan shawarar aka watse akan gobe karfe 8 na safe kowa zai je domin suyi sallama da indo.
Indo sai wajen karfe 9 ta isa kofar gidan habi, kallon gidan tayi tace "shegiya wato ke ga aljana, ai wallahi yau sai kin tumurmusu, idsn kuma ba haka ba ina nan dake sai na dauki fansa, kokarin tura kofar take amma gam taki motsi, kasantuwar an saka mata kyaure mai kwari, tsalle tayi ta dare katangar ta shige gidan, a hankali kamar wata barauniya, shiga take sai da tazo dai dai kofar dakin sannan ta tsaya.
Shiga dakin tayi tana murmushin samun nasara,habi ta tarar tana ta sharar bacci, da dsriyar mugunta tace "shisa na baro wancan sokon mijin naki a wajen zaman majalissa,daure fuskarta tayi sannan ta dankara mata wani kulli a gadon baya, firgigit ta mike tana sosa wajen, tana kalle kalle, mata ta gani zaune a kan gado.
Indo ce ta ce ai sai nayi maganinki, tashi tayi tsaye, ta fita can kuma ta dawo da ruwan sanyi a bukiti,dagashi tayi ta juye akan gadon take dakin ya jike, maimakon ta tafi aa sai da ta cika dakin da ruwa, sannan ta sami habi, wata leda naga ta zaro sai kuma ta bude, wani abu ta fito dashi a dunkule, habi bata ankara ba ta tura mata a baki, sannan ta fito kullota tayi ta inda tabi ta nan ta koma.
Gida ta tafi tana shiga taci karo da garba yana mitar ina indo, sadaf sadaf ta fice domin tasan gamonsu da garba ba kyau, ganin ta shi ma yasaka shi yin shiru yana hira da inna, tinda ta shiga bukkarta, ba abinda takeyi sai bincike, kafin wani lokaci kuma ta debo tulin kudade, zama tayi ta shirya su, sai tayi dariya lokacin amfaninku ya zo.
"Amma kuma ya kamata ace na tafi da wani abu na musamman, zama tayi a gadon sai da taji batajin motsin kowa, sannan ta fito,ta rasa ya zatayi domin tanason guzuri, kasan cewar makotansu ana siyar da gurasa ne yasa ta haurawa, wani katon buhu ta ciko da gurasa, sannan ta dawo tana dariya.
๐บ Washe Gari๐บ
Tin karfe 7 mutane suka fara halarta kofar gidan su indo, ba yanda indo ta iya dole wajen takwas ta fito daga gida, dik da yar karamar dramer da akayi a cikin gida, fitowarta ne yasa mutanen kauyen tururuwar bata kyauta, daga mai soyayyen nama, sai kudi abu dai na buqata.
Indo cikin ranta fadi take aikin banza dan zasu rabu dani har da wani murna, ai dai zan dawo dan allah a can ma ba bari zan ba, domin ni katseta iyalle tayi tana cewa ki kula sosai indo, ubangiji allah yasa ki tafi cikin sa'a indo.
Da haka kuma mai machine yazo ya daukesu, tafiya akeyi akan kwazazzaben kauyen, sun dan jima sannan suka isa, saboda hanyar ba kyau, suna isa suka shiga makarantar, kasancewar garba ya gama komai yana kaita ya juyo ya dawo, bayan ya bada kwakkwaran umarni cewa dik abinda ta aikata, to ai mata hukunci dai dai da abinda ta aikata.
Pc ne ya fara kokarin yi mata register, kallonta yayi tana da harare harare, yace "what is your name, bata bashi amsa ba saboda ta kasa gane me yake nufi, sai da yace ya sunanki, amsa ta bashi da INDO, Aa ba wannan ba sunan da ake kiranki a makaranta, AISHATU NURADDEEN ALI ta fada masa a takaice.
Bayan wasu cike cike ne yakira wata dattijuwar mata, bayanan komai ya bata anan aka kaita hostel, aka bata gado, kallon 'yan hostel din tayi ta gansu kanana kamar ita, ba wanda tayiwa magana sai tabe baki da tayi ta dane gado,jin cikinta na buqata ne yasata tashi ta bude buhun gurasar data debo, zama tayi taci tai nak, ta kora da ruwa sannan ta dane gado.
Garba a lokacin daya koma al'ummar wannan kauyen kowa na harkokinsa yadda ya kamata, ba wta kuma fargaba da suke ji domin su ai damuwar su ta riga data tafi, indo ce, a ranar kowa ka kalla zakaga yana cikin farin ciki, wanann kenan a kauyen wakaza.
Baccin datake sharawa ne, kawai taji saukar ruwa a fuskanta, wata uwar ashar ta saki lokaci guda ta mike tana wartsake wa, wata gandamemiya ta gani rike da cup ๐ฅค, indo ce tace ke kuma dallah ina ruwanki da ni har zaki zo ki zuba min ruwa a jiki na, budurwar bata ankara ba taji ta watsa mata ruwan itama, ke abinda ya fito daga bakin ta, indo ce tace "ki min shiru kawai tinda ai jiki ba fin jiki yayi va, cike da zafin nama ta janyo gashin kan indo ta fara janyota har sai da ta fito da ita daga dakin, indo mikewa tayi tana daga hannu ta zabga mata mari tare da kamata da kokawa,fada suke sosai har sai da security suka rabasu daga nan sai wajen pc domin wannan case din sa ne.
WACECE AISHATU NURADDEEN ALI (INDON IYALLE TA KAUYEN WAKAZA) ku biyoni tare da alkalamina.
Karku manta kuna tare da๐ MATAR UNCLE๐
FALALAR ZIKIRI
Allah Madaukakin Sarki ya ce:
ููุงุฐูููุฑููููู ุฃูุฐูููุฑูููู
ู ููุงุดูููุฑููุงู ููู ูููุงู ุชูููููุฑูููู
Fazkuriniy Azkurkum Washkuruliy Wala Takfuruni.
Ku ambace ni zan ambace ku, ku gode mini kada ku butulce mini" [Bakara, aya ta 152].
ููุง ุฃููููููุง ุงูููุฐูููู ุขู
ููููุง ุงุฐูููุฑููุง ุงูููููู ุฐูููุฑุงู ููุซููุฑุงู
Ya'ayyuhallazina Amanuzkurullaha Zikran Kathiran.
Ya ku wadanda suka yi imani ku ambaci Allah ambato mai yawa". (Ahzab aya ta 41).
ููุงูุฐููุงููุฑูููู ุงูููููู ููุซููุฑุงู ููุงูุฐููุงููุฑูุงุชู ุฃูุนูุฏูู ุงูููููู ููููู
ู
ููุบูููุฑูุฉู ููุฃูุฌูุฑุงู ุนูุธููู
ุงู
Wazzakirinallaha Kathiyran Wazzakirati A'addanlahu Lahum magfiratan Wa'ajran Aziyman.
Da masu ambaton Allah da yawa maza, da masu ambatonsa mata, Allah ya tanadar musu gafara da lada mai girma". [Ahzab, aya ta 35]
ููุงุฐูููุฑ ุฑููุจูููู ููู ููููุณููู ุชูุถูุฑููุนุงู ููุฎููููุฉู ููุฏูููู ุงููุฌูููุฑู ู
ููู ุงูููููููู ุจูุงููุบูุฏูููู ููุงูุขุตูุงูู ูููุงู ุชูููู ู
ูููู ุงููุบูุงููููููู
Wazkurrabbaka Fiy Nafsika Tadarru'an Wakhiyfatan waduwanaljahri Minal kawli Bil'guduwi Wal'asali Walatakun Minalgafiliyna.
Kuma ka ambaci Ubangijinka a cikin zuciyarka, kana mai kankan da kai da tsoro, ba da daukaka murya ba (saka-tsaki) tsakanin asirtawa, da bayyanawa, da safe da marece, kuma kada ka zamo daga cikin gafalallu". [A'araf, aya ta 205].
Kuma Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce; "Misalin wanda yake ambaton Ubangijinsa da wanda ba ya ambaton Ubangijinsa, kamar misalin rayayye da matacce ne". (Duba Sahihul Bukhari tare da Sharhinsa Fat'hul Bari (11/208). Muslim ya rawaito shi da lafazin; 'Misalin gida da ake ambaton Allah a cikinsa, da wanda ba a ambaton Allah a cikinsa kamar misalin rayayye ne da matacce". (1/539).)
Kuma ya ce: "Shin ba na ba ku labarin mafi alherin ayyukanku ba, kuma mafi tsarkinsu a wajen Srkin da yake mallakar ku, kuma mafi daukakarsu ga darajojinku, kuma mafi alheri gare ku daga ciyar da zinariya da azurfa kuma mafi alheri gare ku da ku hadu da abokan gabanku ku rika dukan wuyayinsu, suna dukan wuyayinku? Suka ce ka ba mu labari. Ya ce: Ambaton Allah Madaukaki". (Tirmizi (5/459), da Ibn Majah (2/1245). Duba Sahih Ibn Majah (2/316). Da Sahihul Tirmizi (3/139).)
AISHATUL___HUMAIRAH
ย ย ย ย ย ย ..... Labarin Indo .....
โค๏ธ๐โค๏ธ๐โค๏ธ๐โค๏ธ๐โค๏ธ๐โค๏ธ
ย ย ย =Na=
ย AISHATU BINT MUHAMMAD
ย ย ย ย ย ย (Matar Uncle)
๐๐ท๐ธ๐ท๐๐ท๐ธ๐ท๐๐ท๐ธ๐ท๐๐ท๐ธ๐ท๐
The Story of life childhood,
Entertainment,
And Love.
DASHEN ALLAH WRITERS ASSOCIATION
10๐11
ASALIN LABARIN..
Malam nura ya kasance da ne ga, malam ali da aishatu, wanda ya kasance mutum ne bafula tani, kuma makiyayi, wanda yake sana'ar kiwo, matarsa ta kasance aisha ana kiranta da iyalle, ita ce ta haifi nuradden.
Nura ya kasance ya taso da gata da kuma kaunarsa da iyayensa suke yi, bayan shekara 2 da haihuwar sa ne ta samu wani cikin, zo kaga murna wajen iyalle, a lokacin malam ali ya tafi kasuwa sai da akuyoyi, a hanyarsa ta hanyar dawowa ne, allah yayi masa rasuwa sakamakon hadarin da suka samu a hanyarsu, da kyar aka nemo gawarsa ma.
Bakin ciki a wajen mutanen wakaza ba'a maganarsa, bayan mutuwarsa da wata 9 ta haifi yaronta santalellen saurayi, kyakkyawa dan har yafi nura kyau ma, haka ranar suna ta zagayo aka saka wa yaro sunan mahaifinsa, amma suna kiran sa da baffa, sunan mahaifin su nura da suke fada masa.
Haka iyalle taci gaba da rainon yaranta, bayan ta gama iddarta ne, wani abokin malam ali yace yana sonta da aure, batayi wata wata ba kuwa ta auresa, domin zaman bazai mata, kasancewar bata da 'yan uwa, kuma su din yan gudun hijira ne, auren aka daura da malam sale, malam sale yana kulawa da ita sosai daga ita har yaranta.
Bayan wasu shekaru ne yara sun tasa sun zama samari, shi nura sai ya gaji sana' ar mahaifinsa, shi kuma baffa yace ai shi bazai iya kiwo ba, dan haka yake zuwa kasuwa cikin gari kullun ba ranar fashi,kwanci tashi ba wuya a wajen allah, a inda yara suka girma ali tin a wajen sana'arsa ya samu 'yar gidan wani mai gidansa, ai kuw aya aura masa ita tin daga nan baya zuwa wakaza sai karshen wata.
Sai bayan da ali yayi shekara 3 da aure sannan nura yayi, a lokacin ma ali yana da da 1 mai suna Ahmad,nura ya auri wata yar garin bauchi ce,dayake yana zuwa kasuwanni, anan ne aka dauro musu aure, suna zaune lafiya da iyalle.
Kwatsam wata ranar jumua aka tashi da mutuwar malam sale, sakamakon yar karamar jinyar da yayi a daren, cikinsa ya yi ciwo, washe gari ne kuma aka kaisa gidansa na gaskia,bayan barmata dan sa daya tilo daya mallaka a dunia, bayan sadakr 7 kowaa ya watse daga nura sai iyalle sai aminatu matar nura.
Shekarar su 2 da aure amma sam allah bai basu haihuwa, sunyi magani amma maganin kamar baya musu aiki shisa suka hakura suka fawwalawa allah, ana cikin wannan yanayin ne kuma, matar ali ta kara haifo yara 'yan biyu, zo kuga murna wajen iyalensa da kuma mahaifiyarsu, ranar suna kuwa macen taci sunan A'ishatu wato iyalle, sai kuma namijin ne wanda aka sa masa sunan nura,haka akyi suna kowa na farinciki haka kowa ya dawo gida.
Ana cikin wannan lamari ne ali ya tattara ya tashi ya koma kano da zama, domin yanzu ya samu cigaba, daga nan sukayi nisa da iyyale, basa samun ganin juna, dan ma tana da garba da nura a kusa da ita, idan tanason tayi magana da shi sai dai su fita gari su kirasa.
Bayan shekara 1 da komawar ali kano, allah ya bawa aminatu ciki, zo kaga murna wajen aminatu da iyalle, a haka iyalle taci gaba da kulawa da ita har allah yasa ta haifi cikin nata, lafiya lau ta haifi yarinya mace santaleliya, amma da dare yayi danda nan jiki ya rikice kafin kace wani abu, tini amina tace ga garinku nan, ba iyalle kadai ba hatta mutanen garin sunji mutuwar aminatu domin mutuniyar kirki ce.
A ranar da aka kai amina gidanta na gaskia ne, bayan sun dawo jaririya tace batasan batu ba domin ita yunwa takeji, wata daga mutanen kauyen ce ta dauki indo, kasantuwar tana da jariri itama, ta hadasu tana shayar dasu, bayan sadakar 7 anan aka sanar da mutanen wajen sunan yarinya aisha amma za a na kiranta da indo, haka kowa ya watse yana jimamin wannan yarinya.
Sai bayan sadakar 7 ali ya samu labarin mutuwar aminatu,zuwa sukayi a lokacin ahmad yayi wayo sosai, sai kuma yan biyunta da take goyo, bakin ciki wajen salma matar ali, iyalle kuwa zuwansu ya dawo musu da mutuwar aminatu sabuwa, salma ce ta kalli iyalle tace "iyalle dan allah ki bani indo na hada da ita, iyalle ce tace" kul salma baki ga yan 2 kike goyo ba, dan allah kibarta anan kinji.
Nura ma yayi farin cikin zuwan ali da iyalinsa, ali ne suna zaune a farfajiyar gidan, sai indo datake hannun iyalle, ahmad ne ya matsa ya fara yi mata wasa, salma ta lura da yanayin ahmad, dik lokacin da aka dakko indo hankalinsa na kanta a yan kwanakin nan.
Da daddare salma ta kalli mijinta ali tace "daddyn ahmad, juyowa yayi yace na'am, dama nace me zai hana a hada ahmad da aisha aure saboda naga yana kaunarta, ka duba ka gani yadda kullun yake kusa da ita, ko maidata za'ayi ya dinga kuka kenan, shiru ali yayi sai kuma yace" tabbas wannan shawarar taki tayi min yadda ya dace, dama inason wannnan zumunci namu ya dore har abada.
Washe gari bayan sun shirya, kowa ya fito su ali zasu tafi, ali ya sanar da iyalle da nura wannan batun kuma sunyi matukar farinciki, zo kaga iyalle baki har kunne, daga baya kuma ta fara zuba musu addua.
BAYAN SHEKARA 5
Abubuwa da yawa sun faru,a ciki har da girman indo wanda gaba daya idan ka ganta bazaka ce itace ba, ta zama wata "yar karama bazaka ce indo bace, sai dai dsn banzan rashin ji kamar rainon aljaan.
Yauma iyalle bata nan ta tafi daji tayo icce saboda garba baya nan, indo ce ta shigo gidan allon hannunta ta ajiye, ganin ba kowa a gidan yasa ta kai ta fice, gidan matar data shayar da ita ta tafi, tin daga kofar gids take sallama, tana zuwa ta ganta tana hada kaya, zama tayi tana goge hawayen fuskarta, yanzu shikenan inna tafiya birni zakiyi, wadda aka kira inna ce tace "allah sarki indo tafiya zanyi ban ga ta zama ai, amma dan allah indo kibi a hankali ki tsaya ki maida hankali kiyi karatu kinji saboda wataran idan banzo ba ke ma zakizo.
A haka sukayi sallama, a wannan ranar ta bar kauyen a wannan ranar mahaifin indo ya kaita makarantar boko, da farko dai haka sukace bazasu dauketa ba, amma kuma da sukaga tana da konanne wayo yasa suka dauketa shi kuma ya dawo gida.
Yauma makarantar ta shiga ajinsu ta shiga inda take, wajen maza ta je zata zauna wani yaro ne ya bige ta cikin gwarancinsa yace "ke dallah matsa daga nan ki tafi can nan ne wajenki, cike da bacin rai ta daga hannu ta zabga masa mari, kuka ya saka amma ita ko a jikinta.
Dawowarta ne ta hango mota, tana ganinta ta ruga ta shigo gidan ko sallama babu,nura ne a gefe a zaune kusa dashi tazo ta zauna tana kallonsu, ganin ba ahmad yasa ta kalli nura tace "baffa ai banga yaya ahmd ba, sai 'yan biyun mama, dikansu dariya sukayi, nura ne yace mata" ke baki iya gaisuwa ba, sai a lokacin ta gaishe su.
Kwanansu 1 suka tafi a lokacin indo ji tayi dama ta bisu amma ba dama dan haka ta zauna, bayan shekaru 4 anan hatsabibancin indo ya kara bayyana, gaba daya ta takura kkwa bata kallon kowa da gashi, barna kuwa har da wadda ba ai zato ba, mai gari ba yadda baiyi ba da indo amma ina.
Ko a makarantar bokon ma korarta sukayi saboda ta samu wani dan aji 5 ta masa duka harda fasa masa goshi, da yayarsa tazo shiga ta hada dasu ta doka, shi ne dalilin korarta, taji dadin hakan daganan ta koma yawon allah rufa asiri.
A cikin wannan shekara ne mal nura rana 1 ya tashi da matsanancin ciwon ciki kwanan 2 yace ga garinku nan, ali ne ya yazo shi da iyalinsa a lokacin harda ahmad.
Bayan sadakar 7 ahmad ne rike da hannun indo sai surutu take masa, murmushi yayi yana kallinta yace to "humaira ni zan tafi kinji amma dai zakizo ko, kinga da iyalle zata bani ke da tini mun tafi, indo ce tace" to ai yaya amad bazata bari kawai ka bari idan na girma zanzo, murmushi yayi yace "allah to tsaya anan na miki hoto ko, yadda idan kikazo zanga kin girma ko baki girma ba, tsayawa tayi yana zuwa zai dauko ta sa dsriya, hoton yayi kyau sosai, daga haka sukai sallama indo harda kukanta, wannan shi ne karo na farko da naga indo tayi kuka.
๐๐๐CIGABAN LABARINโค๏ธ๐
๐
AISHATUL___HUMAIRAH
ย ย ย ย ย ย ..... Labarin Indo .....
โค๏ธ๐โค๏ธ๐โค๏ธ๐โค๏ธ๐โค๏ธ๐โค๏ธ
ย ย ย =Na=
ย AISHATU BINT MUHAMMAD
ย ย ย ย ย ย (Matar Uncle)
๐๐ท๐ธ๐ท๐๐ท๐ธ๐ท๐๐ท๐ธ๐ท๐๐ท๐ธ๐ท๐
The Story of life childhood,
Entertainment,
And Love.
DASHEN ALLAH WRITERS ASSOCIATION
10๐11
ASALIN LABARIN..
Malam nura ya kasance da ne ga, malam ali da aishatu, wanda ya kasance mutum ne bafula tani, kuma makiyayi, wanda yake sana'ar kiwo, matarsa ta kasance aisha ana kiranta da iyalle, ita ce ta haifi nuradden.
Nura ya kasance ya taso da gata da kuma kaunarsa da iyayensa suke yi, bayan shekara 2 da haihuwar sa ne ta samu wani cikin, zo kaga murna wajen iyalle, a lokacin malam ali ya tafi kasuwa sai da akuyoyi, a hanyarsa ta hanyar dawowa ne, allah yayi masa rasuwa sakamakon hadarin da suka samu a hanyarsu, da kyar aka nemo gawarsa ma.
Bakin ciki a wajen mutanen wakaza ba'a maganarsa, bayan mutuwarsa da wata 9 ta haifi yaronta santalellen saurayi, kyakkyawa dan har yafi nura kyau ma, haka ranar suna ta zagayo aka saka wa yaro sunan mahaifinsa, amma suna kiran sa da baffa, sunan mahaifin su nura da suke fada masa.
Haka iyalle taci gaba da rainon yaranta, bayan ta gama iddarta ne,