Showing 27001 words to 30000 words out of 40600 words

Chapter 10 - AISHATUL_HUMAIRAH (Labarin Indo) HAUSA NOVEL

08 Nov 2024

4920

mayafin kanta, da murmushi yace "farhana yadai, cikin sunkuyar da kai tace yaah Muhammad ina wuni, da lafiya ya amsa ya fara tambayarta ina mutanen gidan.

Bata bashi amsa ba indo ta shigo tana sallama, bai juya ba itama idon bata damu da ko waye ba, farhana ce tace" humaira ina kika tafi nake ta nemanki, maimakon ta bata amsa daidai sai tace"yoo aunty farhana bakiga uniform a jikina ba, makaranta naje kuma nadawo, sakkowar mama yasa fa fadin "rabu da ita humaira wuce kije ki shirya kizo kinji, batayi magana ba sai jijjiga kai ta wuce.

Sai da tai sallar magariba sannan ta fito, abinda ya bata mamaki shi ne ganin dik mutanen gidan a zaune, can gefe daya taje ta zauna ita ma, mama ce tace "humaira bakyajin yunwa ne, naga yau baki ci abinci ba ko," mama na koshi ta bata amsa kawai.

Muhammad anas ne yace "daddy yau kimanin wata 5 kenan da faruwar wannan al'amari da shi yayi sanadiyyar chajawar ahmad, wata ranar laraba a bakin wani eatery, mun fito daga eatery anan muka ga wasu yammata, a tsaye suke, zuwanmu ne yasa daya daga cikinsu ta karaso wajen ahmad tana masa murmushi, to daddy kasan halin ahmad ga miskilanci, ga rashin magana, hadi da ga shi yace bayasan kowa idan ba AISHATUL HUMAIRAH ba.


Tin daga wannan lokacin na kasa gane kan ahmad dady, koda na kirasa baya dagawa, haka zalika koda haduwa zamuyi bayaso, tin daga nan narasa gane mai ke damun ahmad, jiya da na kira wayarsa ba 'a daga ba, amma bara na kara kira yau.

Wayar ya fito da ita daga aljihu ya fara kokarin kira, sai da ta kusa katsewa sannan aka katse, kara kira yayi sai da ya kira kusan sau 4 sai a na 5 aka daga, a handsfree ya saka wayar, "muryar mace ce tace" kai wane irin maye ne, haba mutum sai jaraba, sai kira kake anki dagawa amma sai da kai ka kara kira ko, to kasani idan ahmad kake nema, to ya bata, idan kuma kunason ganinsa zaku gansa amma ba asalin ahmad din ba, kai idan ma zan baku asalin ahmad din to tabbas sai na juyar da kwakwalwarsa, sannan kuma ba dauke garkuwar tasa don haka abinda kuka zaba, ga zabi na nan, ko ku bani matar ahmad wato aysha, ko kuma na batar da ahmad, idan kukaban aysha zan dawo dashi lafiya qalau, idan kuma kukace aa to wallahi sai na dauke ta ta karfi da yaji, kittt kiran ya katse.

AISHATUL HUMAIRAH
       ..... Labarin Indo .....
❤️💚❤️💚❤️💚❤️💚❤️💚❤️
    =Na=
 AISHATU BINT MUHAMMAD
       (Matar Uncle)
🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀
The Story of life childhood,
Entertainment,
And Love.

DASHEN ALLAH WRITERS ASSOCIATION

40&41

Gaba daya falon kowa hankalinsa antashe yake idan ka cire indo da ko a jikinta, ganin ba wanda yayi magana ne yasata mikewa ta nufi dakinta, gaba daya falon binta sujayi da kallo, farhana bata san lokacin da tace "lalle humaira na cikin matsala, ga matsalar bata karasa ba tai maza ta rufe bakinta.

Indo ce ta fito sanye da riga da wando sai dan karamin veil, kallonsu tayi yayin da suma din ita suke kallo, indo ce tace" kuzo mu wuce indai har zata saki yaya ahmad to wallahi ku kaini, kowa a falon sai da kirjinsa ya buga, kallin kallo ne ya fara shiga tsakani, kamar daga sama suka kara jin maganar ta ta, again ba wanda ya bata amsa, ganin sunyi banza da ita ne yasa ta zama a wajen, sai kuma ta fashe da kuka, "allah sarki yaya ahmad ko yana lafiya yanzu, ko yaci abinci waya sani, ma ko har yanzu bai, bata karasa ba iyalle tace shikenan indo tashi, dagowar da zatayi ne fararen idanunta suka rine zuwa ja jawur,ganin haka yasa salma iyalle da garba kama indo, da kyar suka samu suka sakata a dakinta tare da sakawa dakin lock,suka dawo suka zaun asuna huci.

Parlorn ba wanda yayi magana, nin sgurun yayi yawa yasa Muhammad anas mikewa yaxe "daddy ni zan tafi ga dare yayi kuma jirana ake a gida amma insha allahu zan dawo nan da gobe, dan jin ina aka kwana, daga haka ya mike yabarsu, dsddy girgiza masa kai kawai ya iya yi.

Gaba daya gidan ya cika da ihun indo, sai doke doke takeyi, sai da suka tabbatar da tayi bacci sannan suka fara kokarin tashi, sai dai abinda basuyi zato ba, wasu muta ne ne, suka shigo sanye da fuskar fuska, ba abinda kake gani nasu sai idanunsu da suka kasance jawur, gaba daya sun zagaye falon, kallon kallo ya shiga tsakanin daddy, salma, farhana,garba da iyalle, kowa ka gansa kasan a tsorace yake..

Babban su ne yace"ina matar ahmad take, anan kowa ya fara raba ido domin kuwa tabbas aikin budurwar ahmad ne da ko sunanta basu sani ba, jin shiru yasa shi saita bindigarsa akan goshin farhana data hada uban gumi.

Da kyar iyalle tace dan allah yallabai ku kyalemu, indo bata gidan nan tin dazu mu ma muke nemanta, wata kwakkwarar tsawa ya daka mata, a take ta hadiye maganar tana raba ido.

Kallon sauran guys din yayi yace maza a bincikemin gidan nan kuma tabbas a tabbatar an fito min da indo, gaba dsya bazuwa sukayi, checking room suke sai da suka kusa gamawa, daya ne yace oga wannan dakin a rufe yake, sauke bindigar kan iyalle yayi ya nufi wajen dakin, sai da ya saita sannan ya harba ta, anan kofar ta bude, indo sharar bacci take batasan meke faruwa ba, dagota daya yayi cakk sannan yayi waje can inda suka ajiye motarsu.

Kokarin tashi suke amma sun hana su kowa ka kalli idanunsa hawaye suke zubarwa, daddy ne yace "dan allah zan baku dik abinda kuke so amma dan allah ku kyaleta, dariya ya saki yace" kai tsoho tinaninka ba 'a biya mu ba, sai da akayi mana kyakkyawan biya sannan mukazo dan haka sai anjima, daga haka yasa kai ya fice yana dariya, tafiyarsu yasa su mikewa suka fita amma kafin suje tini motar ta dade da barin gidan, zama sukai a farfajiyar iyalle sai kuka takeyi domin tabbas wadan nan mutanen anyi shegu.

Haka suka zauna anan basu farga ba sukaji kiraye kirayen sallar asubahi, hakan yasa su komawa falo, mama ta rasa ya zatayi da wannan abu, ta rasa da me zataji, haka sukai alwala daddy da garba suka wuce masallaci su kuma suka bi a gida, mama ce ke sallah tana mika matsalolinta a wajen mai kowa mai komai, mai badawa mai hanawa.

Daddy dawowar su daga masallaci ne suka ci karo da mutum kwance a bakin gate, wayar jikinsa ya fara lalubawa, yana fito da ita ya haska, ba fuskar kowa bace sai ahmad, da in ba wanda ya sanshi ba zai ce ba shi ba ne.

Shigowar su yaga falon bakowa, bai bi ta kansu ba sai dora ahmad sukai akan kujera, sannan ya fara kwala kira, kafin wani lokaci gaba daya sun hallara a falo, mamaki fall taya akai ya dawo, idan kuwa hakane to ta tabbata indo ce a hannunta.

Mama ce ta debo ruwa tare da shafa masa a face,amma shiru, hakan yasa aka kure gudun ac dakin, sai can kuma ya farka, da fuskar mama yayi tozali abinda ya daure musu kai shi ne yana kallonsu ya fara zabura alamun guduwa zaiyi.

Daddy ne ya rikesa ya na fadin "ahmad menene hakan ka nutsu mana, amma inaa ganin yaki tsayawa ne kuma kamar bayajin abinda suke cewa ne yasa su yin shiru, sakinsa sukai sai gani sukai yayi hanyar kitchen, binsa sukai amma kafin su isa ya fito, sun rasa gane kan ahmad, mama ce ta share hawayen fuskanta tayi tace "allah sarki wallahi ta haukata mun shi, ta lalata masa kwakwalwa kamar yadda ta alkawarta.

Da kyar suka kamasa mota suka sakashi daganan suka nufi asbiti, suna zuwa a lokacin dama sunyu waya da doctor, dan haka a office suja samesa, zama sukai yayin da doctor ke kallon yanayin jikinsa da kuma irin motsinsa, kafin daga bisa ni yace"gaskia da alamun sai an masa gwaji, domin ga dukkan alama akwai matsala, amma kuma abin da ya dauremin kai shi ne, tayaya akai kuma ya manta komai, kuma ka riga ka fadan ba accidents yayi sannan ba buguwar kai ya samu ba.

Daddy ne yace "eaa doctor ba wani abu ya samu ba, kawai munga yanayinsa haka, allah sarki shi wanda ake magana akan sa ma bai ma san anayi ba.

Haka dai aka shiga dashi gwaji, salma ce ta zauna tana share hawaye, farhana ce taxmce" mama dan allah jiyi hakuri kinji insha allahu zai samu lafiya, wani hawaye ta goge tace "farhana bazaki gane ba, yanzu ga ahmad amma ina aisha ina marainiyar allah take, ko kinsan a halin da take yanzu, baki sani ba, allah sarki aishatu, wani kukan ne ya kara kufce mata, daddy ne ya zagayo wajen ta ganin haka yasa farhana mikewa tabar wajen.

Barin wajenta kenan taji wayarta tana kara, dubawa tayi ganin ba suna yasa ta sharewa, bata daga ba, sai dai wayar tana katsewa wata ta shigo, dagawa tayi tace "hello, banji me akace daga daya bangaren ba, da sauri ta tafi ta kaiwa daddy, daddy yana zaune farhana ta mika masa waya tace ana kira, daddy ne yace hello,muryar mace ce tace" kaga dattijo gargadi zan maka wallahi idan ko da wasa ka sake kasaka police acikin wannan maganar to narantse da allah sai kashe aisha, na gama magana, daga haka kitt alamun jiran ya katse, daddy dik dauriyarsa sai da ya zubar da hawaye.

Fitowar doctor ne yasa su daidaituwa, kallon yayi yace "ku biyoni office, zama sukayi sanann ya kallesu yace" mun gano matsalar ahmad, abu na farko anyi masa wasu allurai ne da zasu zautasa, su saka ya mance da kowa, ganin allurar taki aiki hakan yasaka an masa ita tafi ta wata 2,sanan kuma daga baya aka buga masa kansa, a gaskia abinda zan iya fada muku shi ne da wuya ahmad ya dawo da tinaninsa na baya, idan kuwa hakan ta yiwu, to tabbas sai dai idan akwai abinda yake tsananin so kuma ya gansa shima ba dika zai dawo ba sai dai ya fara dawowa a hankali, zo kaga tashin hankali wajen mama, wasu magunguna ya rubuta musu sannan ya sallamesu, ahmad suka dauka suka tafi, allah sarki gashi nna kamar yaro.

Ina labarin AISHATULHUMAIRAH wato indo.

Ku biyo alkalami na
Wasa farin girki...
Yanzu aka take lavarin.
AISHATUL HUMAIRAH
       ..... Labarin Indo .....
❤️💚❤️💚❤️💚❤️💚❤️💚❤️
    =Na=
 AISHATU BINT MUHAMMAD
       (Matar Uncle)
          🤗 Zinariyar Nazari WRITERS association 🤗


🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀
The Story of life childhood,
Entertainment,
And Love.

NAZARI WRITERS ASSOCIATION

42✍️43

Baccinta take shara abinta, can kuma ta farka, ganin ta a bakon guri yasata mikewa, ganin kofa tayi guda 2 daya ta shiga ta gabatar da alwala ta dawo tai sallah, sannan ta nufi dayar hanyar inda take tunanin kofar falo ce, hakanne kuwa ta kasance ganin ta tayi a wani katon falo, kalkon kofofi tayi tace "ohhh ni indo yau kuma ina nazo nan, bata damu ba tai wata hanyar, tsintar tayi a kitchen, shiga tayi ta fara kokarin hada breakfast allah ya taimake ta ta samu indomie, dafata tayi ta dawo tana ci taji alamun motsi za a shigo, rasa yadda zatayi tai, dan haka ta mike ta maida indomie ta boye ta koma dakin da aka ajiyeta ta kwanta kamar mai baccin gaske.


Jin kamar muryar data sani ne yasata yin kasake tana kara sauraren muryar, a zuciyarta ta furta "wannan muryar kam tabbas na santa nasan ko ta wacece, amma na manta a ina na santa.

A hankali tai open eyes dinta, abinda yayi matukar girgixa ta ba komai bane face Muhammad anas data gani a gabanta yana kallonta, kallonsa tayi tace" kai ne. Da murmushin mugunta yace "da a tinaninki wanene, zama yayi a gadon ds take hakan yasata ja da yana fadin" kinyi mamaki ko ayshatu karki damu ba wanda zai cutar dake, jin alamun shigowa ne yasa ta kakkon door din,wata budurwa ce sanye da riga da wando sun wani kamata dammm, indo sai da ta kare mata kallo sannan ta tabe baki tace "gaskia ranar lahira akwai kallo, kedai wannan baki da maraba da yan wuta.

Kallonta tayi tace" me kike cewa,indo maimakon tai shiru aa kara maimaitawa tayi, cikin fishi ta ce ke din banza har kina da bakin da zaki ce wani dan wuta, Wayuya mara hankali, jaka kawai, indo ce ta mike tace "kan bala'i wallahi wallahi bazan yadda ba ni zaki kira da jaka, ke dallah tsaya jaka ma ta wuce ke mai suffar maza kawai, ke wai da ga yar iska kin wani taho kina karkada kirji, to tsaya kiji sai nayi maganinki nan da kwanaki 3 masu zuwa, falmata da tagaji da cin mutuncin indo, mikewa tayi ta karaso kusa da ita batayi aune ba ta daga hannu ta sharara mata mari, maimakon indo ta hakura aa tsalle tayi ta haye wuyanta ta fara yakushinta, da cizo.

Gaba daya fada ne ya kaure, kokarin rabasu suke amma abin ya citira da kyar aka samu suka rabu, anas ne ya ciro bulala ya fara zabga mata, ganin haka yasa falmata fita ita ma ta samo dorina, sai da sukai mata lilis sannan suka fi ce.

Ahmad tin da suka dawo daga asibiti tin daga wannan lokacin yana kan kujera, ya taba wannan ya ajiye ya dau wannan kafin wani lokaci ya hautsina dakin, komai na dakin ya lalace, farhana ce ta fito tana kwala kiran mama, ko a jikinsa haka yaci gaba da abinda yake, da sauri salma da iyalle suka fito daga tattaunawar, iyalle ce tace "dama na fada muku a san yadda za'ai da ahmad wallahi domin ahmad na buqatar kulawa,gaba dayansu kowa na dakin ya yadda da zancen iyalle dan haka yasa daddy ya juya ya koma room din sa.

Mama rasa abinda zatayi tai, zama kawai tayi ta fara share hawaye, farhana ce ta matsa kusa da ahmad ta kamosa, juyowa yayi sai kuma ya fisge hannunsa yana kallonta, sallamar da akayi ce yasa gaba dayansu kallon hanya, ba kowa bane gace malam adam, malaminsu, mama ganinsa yasata mikewa tana gyara mayafinta, tana zama daddy ya shigo falon bayan gabatar da gaisuwa da komai, anan malam ya fara duba jikin

Jikin nasa ya kalla yace "ina aisha take, kallon kallo ne ya fara shiga tsakanin mama da daddy, da kyar iyalle tace" malam ai bata nan, malam ne ya ce "shikenan tohm bakomai idan ta dawo zan mata bayanin komai, idan har bada aisha ba to tabbas ahmad bazai samu sauki ba, idan har bada taimakonta ba to tabbas akwai matsala, amma ga shawarwarin da zan baku.

Ya kamata ace koda yaushe kuna kunna karatun alkur'ani a gidan nan, domin kuwa shi ma magani ne mai matukar amfani wanda bashi da algus, alkir'ani haske ne a rayuwar mu, sannan kuma alkur'ani jigo ne, abu na biyu y akasance dik wayewar sa safiya da kuma maraice, anan karanta masa zikirin safiya da maraice, manzon allah sallalahu alaihi wassalm yace" ya ce: “Misalin gidan da ake ambaton Allaah a cikinsa da gidan da ba a ambaton Allaah a cikinsa, kamar misalin rayayye ne da matacce.”_

Ayoyi da dama da kuma Sunnar Annabi (ﷺ) suna karfafa mana tare da ingiza mu zuwa ga yin zikiri da ambato da tuna Allaah. Kuma suna umartar mu a kan yin zikirin da yawa tare da yi mana bayanin irin ladaddakin da masu yawaita zikiri suke samu a cikin ayoyi masu yawa da hadisai da dama.

Allaah Madaukaki Yana cewa:

يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اذْكُرُوا اللَّهَ ذِكْرًا كَثِيرًا

*(“Ya ku wadanda suka yi imani!  Ku ambaci Allaah, ambato mai yawa.)*

وَسَبِّحُوهُ بُكْرَةً وَأَصِيلًا

*_Kuma ku tsarkake Shi a safiya da maraice._*

هُوَ الَّذِي يُصَلِّي عَلَيْكُمْ وَمَلَائِكَتُهُ

*_Allaah Shi ne Wanda Yake yi muku salati (tsarkake ku) da mala’ikunSa (su ma suna yi muku addu’a)_*

لِيُخْرِجَكُم مِّنَ الظُّلُمَاتِ إِلَى النُّورِ

*domin Allaah Ya fitar da ku daga duffai (na kafirci da gafala) zuwa ga haske (na imani da tsarkaka).*

وَكَانَ بِالْمُؤْمِنِينَ رَحِيمًا

*_Kuma Allaah Ya kasance Mai jin kai ga muminai.”_*

_Ibn Abbas (RA)_ ya ce: “Idan kuka aikata haka – ma’ana kuka yawaita zikiri ko ambaton Allah Madaukaki – Sai Allah Ya yi muku salati (addu’ah, Shi) da mala’ikunSa.”

Kuma Allaah Madaukaki Ya sake cewa:

وَالذَّاكِرِينَ اللَّهَ كَثِيرًا وَالذَّاكِرَاتِ أَعَدَّ اللَّهُ لَهُم مَّغْفِرَةً وَأَجْرًا عَظِيمًا

*(“Masu ambaton Allaah da yawa maza da masu ambaton Allaah da yawa mata, Allah Ya yi musu tattalin wata gafara da wani sakamako mai girma.”)*

Kuma Ya sake cewa:

وَاذْكُرُوا اللَّهَ كَثِيرًا لَّعَلَّكُمْ تُفْلِحُونَ

*( “Kuma ku ambaci Allaah da yawa, tabbas za ku samu nasara.”)* Da sauran ayoyi da hadisai masu yawa da suke kwadaitarwa da karfafa Musulmi su yawaita ambaton Allaah kuma suke umartarsu da ambatonSa da yawa.

Ina roqon Allaah dacewa da shiriya zuwa kowane alheri, ga kaina da ku, lallai shi Allaah  mai iko ne a bisa kowane abu. Allaah ya albarkace ni tare da ku da abin da muka ji na Alqur’ani ya gafarta mana zunubbanmu, lalle shi mai yawan gafara ne mai jin qai

*الله تعالى أعلم*

_*ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.​​*_

To allah ya basa lafia, mikewa yayi ya t


AISHATUL HUMAIRAH
       ..... Labarin Indo .....
❤️💚❤️💚❤️💚❤️💚❤️💚❤️
    =Na=
 AISHATU BINT MUHAMMAD
       (Matar Uncle)
          🤗 Zinariyar Nazari WRITERS association 🤗


🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀
The Story of life childhood,
Entertainment,
And Love.

NAZARI WRITERS ASSOCIATION

44😶45

Falmata ce ta nufo dakin domin kuwa jin tayi shirun yayi yawa, knocking ta fara yi jin shiruYa sa ta kutsa kai dakin, sai dai mai ba kowa ta gani, dubawa take amma ta rasa ina indo ta shige, juyawar da zatayi ne ta nemi hanyar ta rasa, wata kara ta kwalla tana kiran na shiga 3 ni falmata, wata dariya ta jiyo daga sama, hakan ya sata saurin daga kai, ba komai bane ya bata mamaki irin yadda ta hangi indo a sama, ba abinda jikinta yake sai rawa kamar ana doka mata ganga.

Wata lalatacciyar murya ce tace "ke ya sunanki?, cikin rawar murya tace" sunana falmata wallahi, indo wani tsalle tayi ta diro kasa, tace "wato ke ce lalatacciyar da kika lalatawa ahmad ali kwakwalwa ko, to kisani yau kin shiga komar aljanu, batayi aune ba taji ta an damfarata da kasa, a lokaci guda dik hasken da ta ke gani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login