Showing 15001 words to 18000 words out of 40600 words

Chapter 6 - AISHATUL_HUMAIRAH (Labarin Indo) HAUSA NOVEL

08 Nov 2024

4915

sai yankan kabewa da hadin kayan miya akeyi, kafin wani lokaci tini an tuka tuwo da miyan taushe.

Indo ce taja tsaki, ta kalli dije tace "wallahi baki isa ba ina salamen take ina take, aradun allah sai naci uwarta, tinda ita shegiya ce, da gudu ta fita dije ta bita a baya, farhana ce ta shigo bukkar ganin kayanta a gefe ne yasa ta fara nemanta.

Indo kuwa a gidan su salame tai rebos, kam bala'i shi ne sallamarta, sai kuma ta fara fadin, wallahi salame baki isa ba, salame ta zaune ta hango indo, take hantar cikinta ta kada,indo ta shigo, "wallahi salame karyarki goma, dan kinga kawai yanzu na rage jan bala'i shi ne kike tinanin zaki iya takani ki zauna lafia, to wallahi baki isa dan ba'a haifeki ba, bata ankara ta rufeta da duka, sai da ta lugideta sannan ta fito daga gidan tana huci.

A can masalaci kuma alumma sun taru, bayan idar da sallah mai gari ya dakatar da kowa akan auren indo da za a daura. Liman ne ya fata addua anan garba ya zama wakilin indo shi kuma daddy ya wakilci ahmad, bayan wasu mintuna anan liman yake sanar da auren AISHA NURADDEN ALI DA AHMAD ALIYU ALI Bisa sadaki naira dubu 100 lakadan ba ajalan ba.

Kusan kowa na  gari ka kalli fuskarsa zakaga tsantsar farinciki domin kuwa tabbas ko ba komai zasu rabu da indon iyalle.

Tafiya take daidai kofar gidan su ne take jin buda, ba wanda ta kuka bukkarta ta shige a zaune taga farhana, hade rai farhana tayi tace "gidan uwarwa kika tafi bayan na gayamiki karki sake ki fita,kallinta tayi taga ta hade rai, sai kuma ta saki dariya tace" yo dama ai naji kince karna fita amma wallahi salame ce ta rai namin hankali, ni zata daukarwa mangoro da tsamiyar da nace dije ta ciro min, shi ne naje na samu yar abu takazan uba na zaneta,zaro ido farhana tayi tace 'yanzu akan mangon kika jibgi yar mutane, amsa ta bata tana cire kayanta a gabanta,ko a jikinta, farhana ganin abinda take shirin yi ne yasa ta fita, tana mamakin halin indo, idan kuwa hakane tabbas akwai kallo a gidan mu.

Tana saka kayan ta fito, farhana ce tace qai ke indo ina zaki ne, amsa ta vata "abinci nake nema, dan wallahi cikina baya jurar yunwa, kafin farhana tace wani abu tuni ta ware ta je ta kwaso tuwo.

Farhan kuwa yana masallaci shi da daddy, sai bayan da kowa ya watse, da mai gari suka gaisa, sukai sallama bayan ya bashi kudi masu yawa,sannan suka taho gidan iyalle,shigowar su ya kalli iyalle yace "ai andaura auren iyalle sai shirye shiryen tafiya saboda kar muyi dare, iyalle da to ta amsa, sannan tace" sai a kira ta ta kimtsa dan kasan indo da fitina, kuma ga nawa kamar jaraba, baya idan taga ana jiranta, dan ma doki take, da murmushi a fuskarsa ya wuce.


Wajen salma yayo yan fadin "amarya an daura ai ganin ba kowa a bayansa yasa tayi murmushi tace" aa daddy uwargida dai ni da nake da sirika yanzu, gata sirikata gata diyata kuma, shima dariyar yayi yace to mu fatmra shirye shirye kada muyi dare ko.

Farhan ne ya tsaya a gaban indo ita dai sai danna tuwo take, farhana ce tace "wallahi farhan ina fadamaka akwai kallo a gabanmu, akwai kallo kuma farhana me ya faru, murmushi yayi yace" ai yanzu ma muka fara gani.

Garba ne zaune da iyalle sai indo a bukkarta, garba ne yace "to indk kinga dai birni zaki koma kince bakison zama anan ko, kibi umarninsu, karki yadda ki bari ki batamusu rai, wallahi dik ranar da kika yadda kika bata misu ko kika ketare umarninsu to karshen zamanki yazo.

Iyalle ce tace" shikenan indo kibi umarnin mijinki kinji, kibisa sau da kafa yi nayi, bari na bari karki yadda ki bari ya kawo min kararki, idan ba haka ba wallahi sai na karyaki.

Indo tanaso tayi magana amma kuma ba baki, domin tinda ta dawo daga gidan su salame take jinta wani iri, dole taja bakinta tayi shiru.

Haka kowa ya fito a bakin mota ta tsaya, dik wani fada da akai mata take ranta yayi fess, murmushi tayi tace "aradun allah yau sai na hau motar nan, ai iyalle kui zamanku a inda kuke zanje naci kayan dadi.

Ba a wani bata lokaci ba, suka dau hanya iyalle harda yar kwallarta, saboda sabo, mutanen kauye kuwa sai murna suke allah ubangiji ya rabasu da indon iyalle.

AISHATUL___HUMAIRAH
       ..... Labarin Indo .....
❤️💚❤️💚❤️💚❤️💚❤️💚❤️
    =Na=
 AISHATU BINT MUHAMMAD
       (Matar Uncle)
🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀
The Story of life childhood,
Entertainment,
And Love.

DASHEN ALLAH WRITERS ASSOCIATION

20💎21

Tafiya suke indo sai murna take, tin tana ganin hanya har bacci ya dauketa tana can bacci, karfe 5 suka shigo KANO TA DABO TUMBIN GIWA KODA ME KAZO AN FIKA inji 'yan magana ba.

Tafiya suke daidai jerin Jerin gidajen unguwar tudun yola suka shiga, ganin haka yasa farhana saka hannu ta mitsini indo, kamar a mafarki tajisa bata san lokacin da yace kan uban can, bide idon da tayi ne ysata saurin rufe bakinta, kafin ta rufe farhan ya kai mata duka, salma ce tace "ya isa haka kar na kara ganin hannunka yana dukan mace ke kuma, bata karasa ba daddy yayi horn, anan indo ta zama 'yar kauye domin bude vaki tayi tana kallo.

Janyo farha tayi tace" kenan anan gidan zan zauna oh ni indo, yanzu dana akwai irin gidan nan a duniya, aradu bani ba komawa kauye, farhana ce ta kalleta tace "to sai ki shirya tafiya domin gobe da wuri zamu wuce abuja, ke bakisan a abuja muke zaune ba ko, dariya ta ski sai kuma tace" wallahi abunku ga ku ga shugaban kasa, amma dan allah idan mukaje zaki barni naje na gansa, farhana bata bi ta kanta ba sai wucewa tayi.

Gaba dayansu shiga sukayi, salma ce ta juya ta kalli farhana, ganin ba indo ne yasa ta fadin ke ina kika baro humairar, juyawa tayi tace kai amma mama tare muka shigo, fita tayi tana kwala kiranta, salma ce ta girgiza kai tace"ai dama indai humaira ce sai hakura.

A waje kuwa indo tana kan bencin mai gadi, hira suke zubawa, shima ya samu abokin zance, tin daga nesa farhana take kiran humaira, amma tana ji tai kunnen uwar shegu da ita, tsauawa tayi a gabanta tace "ke yanzu ba kiranki nake ba, taso muje mama na kiranki, tashi tayi ko magana tmbatayi mata ba suka shiga falon, kallon kujerar tayi taga television amma kuma kasa ta samu ta zauna, saboda acewarta farhana ta mata fada a wajen mai gadi, ai sai ta jaza mata raini, ita da takeson ta zama babba.

Daddy ne ya fito har ya sake wanka, ganin indo yasa ya fadada fara'ar sa yace "humaira ke kadai anan ina farhana, ko kallonsa batayi ba tace munyi fada da ita ai, farhan ne ya fito a lokacin shi ma har ya shirya,daddy ya kalla yace" ni zanje amma kuma naga ita bata shirya ba.

Daddy ne yace "ai farhan kuyi hakuri zamu tafi ni da salma, ku bari kwa taho gobe kasan ai humaira bata da passport, farhan ba yadfa ya iya fole yace to, dan haka ya huce masjid, shima sai da yayi sallar sannan suka fara kokarin tafiya, domin flight dinsu na gab da tashi.

Dawowarsa daga sallar isha'i ne ya fara kokarin tada inji, ganin ya kasa yasaka mai gadi, sai gashi kuwa ya tashi.

A lokacin indo tana kwance akan kujera taga haske, wani tsalle tayi tace "yeeh wallahi an kawota, shisa aka ce a birni kullun ana kawo wuta, yana daya daga cikin dalilin dayasaka na gudo kauye, saboda nasan zan shiga talabijin naga yan film nima su gyarani na zama kamarsu, dik wannan budirina gaban farhan take, kasa rike dariyar sa yayi sai da ya saketa, jin dariya ne yasa ta jiyowa maimakon taji haushin dariyar, sai cewa tayi wai dan allah ina mutanen talabijin din nan suke a nuna min su.

Fitowar farhana ne yasa ta fadin ke humaira kinyi sallah, aa ta bata amsa, to huce jeki alwala ki sallah kidawo kizo nan, tashi tayi dakin data fito nan ta shiga, tana shiga wani katon bed yayi mata maraba, tsalle tayi ta dare har da ihunta, sai da ta gama haukanta, sannan ta fara neman inda zatayi alwala, wata kofa ta gani bidewa tayi ta shige, anan taga shower, famfo, kallin komai take tace to nan kuma inane bata ganin ta rasa inda zatasa ruwa ya kawo ne yasata fara saka kafarta a sauran ruwan wankan bayan ta gama alwala ta fito.

Batayi sallar ba ta fito, farhan ne a zaune akan kujera, ya kunna talabijin saurin karasawa tayi, har bakin talabijin taje ta zauna kamar zata shiga ciki, farhan hankalinsa na kan wayatsa, kamar haka akace dago ya hango indo na kalle kalle tasa hannu a jikin television din.

Humaira farhaan ya furta, da sauri ta kallesa tace "dama yaya farhaan so nake na shiga ciki nima naji me ake ji, dan allah budemin na shiga, farham dmaai da ya dara, sannan yace ai bata nan ake shiga ba, ki bari idan munje abuja zan kaiki inda ake saka mutane shikenan, da yar daria tace" eaa na gane wallahi kuwa ya zaka ganni.

Farhana ce ta fito da plate a hannunta, bayan ta ajiye wa farhaan nasa, ta janyo nasu, humaira zo muci abinci, batayi musu ba karasa, ba komai bane taliyar yara ce, ci sukayi bayan sun cinye indo ce tace "aunty farhan wallahi ban koshi ba, zaro ido tayi tace" aa humaira kina sassautawa cikinki mana, tashi tayi ta bude fridge, l&z ta miko mata, vatayi wata wata ba ta kunce.

Sai da ta shanyesa tsaff,sannan tai gyatsa, farhana ce taja hannunta, sannan tace farhaan sai da safe, daga haka suka wuce, indo ce tace" amma kuma kallon fa, bata bi ta kanta ba.

Suna shiga tace ki shiga kiyi wanka, kallonta tayi tace wallahi aunty farhana bayin ne kamar daki, ni fa na kasa gane komai a bayin, bata mata mgana ba, shigewa tayi ta hada mata ruwan wankan sannan ta fito tace jeki kiyi, sai ki fito ko kuma idan kin gama ki kwalan kira amma ki tabbatar kin daura towel, dariya tayi tace to ta shige.

Lekowa tayi ganin ba kowa a dakin ysata fitowa da guntun towel din, wayar farhana ce a kan gado ita ta dauka, dannawa take amma kai da gani kasan ba a saba ba, kallonta tayi tace "yee nima zan siya waya na ringa kallon kaina a ciki, farhana ce ta turo kofar saurin ajiye wayar tayi tace" aunty farhana na fito tin dazu ke nake jira, murmushhi tayi mata tace to muje ki wanke bakinki ko, xaga haka sukai toilet.

Washe gari tin sassafe suka fito, farhana ce ta kalli farhan tace "farhan  humaira fa bata da kayan da zata chanja, farhan ne ya kalleta yace" shikenan bara mu fita sai mu tsaya a siya mata ko a boutique ne, daga haka suka bar gidan, tin kafin su fita indo tace "aradu anty farhana yunwa nakeji, cikina kamar zai mutu, bude fridge tayi ganin ba komai yasata karasawa kitchen, tea ta hado mata mai kauri ta mika mata, zuwa daya tayi masa ta ajiye kofin, badan ta koshi ba sai dai tasan idan tayi magana yanzu farhana ta bigeta, sabkds sanin halin farhana yasa ta bisu suka fice.

Tafiya suke daidai wani boutique ya tsaya fjta yayi yace "farhana muje a siya mata kayan, shiga sukayi wasu eiga da wando maroon colour ta dauka, zuwa tayi ta saka sannan ta fito, basu dade anan ba suka fito bayan ya siya mata wasu kayan, tafiya sukayi farhana ce tace" please farhan ka tsaya muyi break yunwa nakeji kuma kasan tafiyarmu bata karewa bace, indo har ranta taji dadi domin ko ba komai cikinta ya fara kiran babu. AISHATUL___HUMAIRAH
       ..... Labarin Indo .....
❤️💚❤️💚❤️💚❤️💚❤️💚❤️
    =Na=
 AISHATU BINT MUHAMMAD
       (Matar Uncle)
🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀
The Story of life childhood,
Entertainment,
And Love.

DASHEN ALLAH WRITERS ASSOCIATION

22💐23

Sun dade suna tafiya sannan suka isa garin abuja, garin shugaban kasa ba, tafiya suke yayin da indo ta dade da yin bacci, farhana ce tace "dan allah farhan karbi driving din nan wallahi na gaji na gaji, murmushin gefen baki yayi yace" wallahi bazan karba ba kasan allah sai dai ki tuka tun daga kano fa sai da nazo zaria amma kice kin gaji, yanzu da na kyaleki da tini kina nan kina faman danna waya.

Farhana ce ta murguda baki ta kalkesa, tafiya suke a saman titi wani titin suka hau wanda ya sadasu da wani tangamemen gida mai matukar girma, tin daga bakin gate farhana ta saki horn da shi yayi sanadiyyar tashin indo, farhan hannu yasaka a kunnensa domin karar tayi yawa, cike da bacin rai ya fito daga motar, knocking yaje, mai gadin ne ya leko, kawai sai bige sa ya wuce cike da bacin rai.

Farhana tana sane tayi hakan domin tasan farhaan baya san kara, shisa da mugunta ta kure karar horn din, indo kuwa tsalle tayi ta dawo gaba tana kallon farhana tana dariya, tafawa sukayi tace "humaira ki ready yanzu zamu shiga dake daga haka mai gadi ya bude suka shiga.

Wayyo allah wannan shi ake kira da aljannar duniya wannan gida haka, abinda ya fito daga bakin indo, fitowa tayi tana dube dube, a wajen motoci ta tsaya, kokarin kirgawa take amma data fara zata bace, farhana ce tace muje, jan hannunta tayi suka tafi.

Indo kallo take wani katon falo suka shiga wanda ya kasance komai na dakin green ne da white, farhan ta gani a zaune salma ce ta kalleta tace "farhana wai yaushe zaku girma yanzu dawowar ta kuma da fada zaku fara, wai dan allah yaushe zakuyi hankali ne, yaushe zakuyi hankali farhana kinsan farhaan baya san kara ko, shi ne da sanenki kika saka masa ko, shikenan sai kuyi tayi ai yanda kuka zaba.

Humaira zo indo karasawa tayi, lokaci guda tace "mama ina wuni dan murmushi tayi tace lafia lou humaira ya hanya, wangale dafaffun hakoranta tayi tace ai hanya har mun zo, farhan ne ya mike yana yi wa farhana gwalo, kallon mama tayi tace" mama wallahi ki masa magana kinga yana min gwalo ko, mama batayi musu magana ba hakan yasa farhana bindmsa da gudu,daga nan sukai ciki, mama ce tace "yawwa humaira tashi muje kina jin yunwa ko, daga kai tayi sai kuma tace" aradun allah mama ko wata yunwa nakeji, dika fa shayi ta bani sai wani abu kamar dankali naji dai yaya farhan yace masa irishiy, murmushi salma tayi tace "lalle da aiki a gabana humaira.

Abinci aka zubo mata, dakko abincin tayi ta dawo gaban salma haka kawai tace ai mama ko bazan iya cin wannan abincin akan wancan teburin ba, haka abu kamar bencin makaranta, amma kinga mama na taba ganin wanann abun, mama ce ta katseta tace "ya isa please kici abincinki mana kintsaya kina surutu, idan ana cin abinci ba'a magana, shiru tayi can kuma tace" wai mama ina daddyn naga ban gansa ba, rike kai salma tayi tace "wai humaira ba yanzu naga ma miki magana ba, nace miki idan ana cin abinci ba'a magana ko, daddyn baya nan yau asubanci yayi ya tafi Italy 🇮🇹 zai kai kaya.

Sai da ta gama sannan ta dawo ta zauna nan fa tafara zuba mata zance, salma tin tana bata amsa yasa ta fara sauraronta idan na dariya ne tayi idan kuma na haushi ne sai dai kawai tace "allah ya kyauta.

Haka wannan rananta kare dare yayi, salma ce taja humaira zasu tafi, farhana ce tace" aa mama ki bari mana basai mu kwana tare ba dama ai daki na zata dawo da zama, salma ce tace "aa wallahi dakinta zan bata vazaiyu ki hana ta sakata ta wala, kallin indo tayi tace" humaira ko kinason zama a wajen farhana, indo ce tace "aa mama kawai a bani dakina kinga da ina kauye bukkata daban yanzu ma gaskia nawa nakeso, da mamaki take kallonta, domin humaira tana burgeta bata iya boye abinda yake ranta, amma tabbas ya zama dole ta koya mata abubuwa saboda halin rayuwa.

Washe gari ta riga kowa tashi fitowa tayi tana raba ido, ganin gidan tsitt yasata fadin ai yanzu da a kauye ne da tuni na tafi yawon, amma anan ba damar fita, kallon falon take wani katon hoto ta gani,wani saurayi ne kyakkyawa sanye yake da riga da wando, ga wata lallausar suma mai kama da sumar indiyawa, ta kwanta tayi luff kai da gani kasan taji mayuka kala kala, murmushi indo tayi tace "wayyo allah wannan kamar bature, anya wannan na tabasa jini bazai fito ba, kai da kamar wuya kuwa, wannan idan sauro ya cijeshi ai aradu sai jini ya fantsama, zama tayi tana kara kallonsa, jin har yanzu shiru yasa ta tashi ta fito waje.

Ko ina shiru wajen motocin gidan ta nufa, kallonsu take ta shafa wannan ta huce wannan, can ta hangi wata brown kusa da ita ta karasa tana leka glass din amma ba abinda ta gani, kokarin budeta take amma ta kasa dan haka taja tsaki"wai shikenan komai a kulle kamar sai kuma tai shiru.

Hanyar fita tayi sai dai ta kasa bude gate, ganin ba wani wajen zuwa yasata koma gidan, jin motsi tayi a kitchen karasawa tayi ta leka, farhana ta hango, dariya tayi ta shiga tace "anti farhana dama wallahi kamar kinsan yunwa nakeji, wani kallo ta bisa dashi tace" wai ke yaushe zakiyi hankali, kin tashi da safe ba wata gaisuwa sai dai kizo kice min yunwa kikeji, me yake damun ki ne, indo ce tace "to anti yazanyi kinsan dai yunwa ba a ja mata lahaula ko bare na mata, farhana ce taja tsaki tace" see uh common aunty bazaki iya fada ba amma a haka kike tinanin zama 'yar birni, ai kuwa indai haka zakiyi zaki ta zama a haka a' yar kauye kawai.

Salma ce ta katse ta tace "aa farhana banason rashin kunya mana, idan bazaki jata a jikinki ba bai kamata kina fada mata wannan maganar ba, kuma duba iya kokarinta yi take wajen ta faranta miki, amma ke bakya gani ko, to ita din ai matar yayanki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login