Showing 33001 words to 36000 words out of 40600 words

Chapter 12 - AISHATUL_HUMAIRAH (Labarin Indo) HAUSA NOVEL

08 Nov 2024

4913

ne zaku zo ku dameni, sannan kuma idan magana zakuyi da shi sai na sakar miki shi kuyi tayi aikin banza kawai.

Cigaba tayi da fadin "idan kunason karin bayani ai wajen dr farhaana zaku tafi, itace dr data dubasa, kuma ita ce wadda zata fada muku abinda binciken ya fada mana, daga haka wucewa sukayi suna kallon su cike da bacin rai.

Hajia dina idan ranta yayi dubu yayi kololuwar tashi, dan haka yasata bin office din farhana.

Farhana na zaune tana video call da farhan, farhan ne ke tambayarta yaushe zasu zo masa, dariya kawai ta yi masa tace "haba bro karka wani damu zamu zo very soon, idan ma su mama basu zo ba toh ni xanzo, dan murmushi yayi wanda ya fito masa da dimple yace" but please ki taho min da humaira, ko kuma ki bata mugaisa, kallonsa ta kuma yi tace "kai farhan na fada maka ina hospital, doko kofar da akayi ne yasata kallon kofar cike da bacin rai, tanaji farhan na tambayarta menene amma tsabar zuciyarta ta dau zafi shi ne dalilin dayasa ta katse kiran da yake mata.

Dr ne ya fito hannunsa rike da na ahmad, suna zuwa kusa da indo ya zauna, dr ne ya zauna shi ma a chair din sa, doctor ne yace "a gaskia magana alhaji sai dai ka mikasa zuwa india, domin kamar ydda na fada maka kullin ciwon maimaikon ya ragu saj karuwa yake, sannan kuma idan hakan ta ci gaba da faruwa zai iga jawo masa mituwar kwakwalwa, daga haka kuma zaku nemesa ku rasa domin zai iya rasa ransa.


Shiru kowa yaui yana sauraren dr, alhaji ne yace "to yanzu zamu iya tafiya nan da wani week din, dr ne yace" aa alhaji sai dai nan da gobe, domin anan ba abinda zamu iya yi masa, alhaji ne yace "to shikenan ba matsala, allah ya kaimu goben, sauran suka amsa da ameen, ddr ne yace" ni kuma zan hada dik wasu documents zan tura a yau din nan.


Hey madam lafiya abinda ya fito daga bakin Farhana kenan, wani kululun bakin ciki ne ya cika zuciyar hajia deena, wata fitsararriyar yarinya ce tace "ke dallah doctor karki rainamin hankali mana, how dare you da zaki na fadawa mahaifiya ta wannan maganar, farhana ce tace" ke dallah rufemin baki, wawiya mara tinani, wallahi idan baku fita daga wannan office din ba sai na saka securities sun zo sun fitar min daku, kallonta suke wai farhana ce wannan.

Budurwar ce tace "nagode allah da yaya kabeer bai auro mana kayan jaraba da bala'i ba, wannan ai kina ganinta kinga yar duniya shegiya mai suffar mayu, cike da bakin ciki farhana ta daga hannu ta sharara mata mari, sannan tace" kadan daga hukuncin da zan miki a yanzu.

Budurwar ce yace "wallahi idan har na cika zeey sai na dau mummunan mataki akan wannan marin zaki gane cewa kin daki zainab, farhana ce taja wani dogon tsaki sannan tace" eaa ai akwai lafiya fada amma ba cikawa,fita sukayi farhana ce ta hada kayanta sannan ta dauki wayarta ta fito, ta reception ta biya, kallon nurse din tayi tace"sis grace karki bari kowa ya shiga room 17,cike da girmamawa tace "to madam daga haka ta wuce zuwa moto.

AISHATUL HUMAIRAH
       ..... Labarin Indo .....
❤️💚❤️💚❤️💚❤️💚❤️💚❤️
    =Na=
 AISHATU BINT MUHAMMAD
       (Matar Uncle)
          🤗 Zinariyar Nazari WRITERS association 🤗


🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀
The Story of life childhood,
Entertainment,
And Love.

NAZARI WRITERS ASSOCIATION


50💮51


DINNER
a lokacin kowa na cin abinci, indo hankalinta na kan na yaya ahmad, sai farhana da ake ta jera mata call amma ta saka wayar a silent, saboda bazata daga ba, ko ta daga ma bazai huce zancen kin barin kabeer da tayi a gani.

Daddy ne yace "farhana a hankali ta dago kai tace" naam daddy, gobe zamuje india 🇮🇳 ni da mahaifiyarki sai yayanki,saboda doctor yace ciwon nasa gaba yake shi ne zamu fara zuwa, zuwa nan da wani week din zan dawo sai ku tafi ke da iyalle da indo, farhana ce tace "to daddy dama ya kamata ya samu sauki allah ubangiji ya bashi lafiya, yasa ayi masa a sa'a, gaba xaya falon kowa ameen yace.

Sai da kowa ya gama dinner sannan suka koma falo amma daddy ya fita ita kuma salma ta haura sama, saboda ta hada kaya, iyalle kuma na kishingide na bacci, farhana ce taja tsaki, indo ce ta kalleta tace "dan allah aunty farhana karki bari su ganshi tinda su yan iska ne, farhana cikin dauriya tace" wa kenan wa kike nifi humairah, dan murmushi tayi irin na manya tace "shi kabeer din mana, zaro ido tayi ta fara furta la haula, domin lamarin indo ya bata mamaki, wata zuciyar ce ta katse ta tace" ke ma kike abinki dama indo zatayi abinda yafi haka ma, domin dama can na da aljanu.

WASHE GARI

Gaba daya ilahirin gidan kowa na bakin gate, indo ce ma sanye da uniform din boko tana jiran bus, sai mama da alhaji da suka hau mota, bayan sunyi kowa sallama suka tafi, basu dade da fita ba school bus tazo, indo har ta shiga ta fito da sauri, kallon drivern tayi tace "kaje kawai kaga nayi mantuwa ne, driver ya kawoni.

Gidan ta shiga ba kowa hakan yasata shiga dakin ta, kayan ta ta cire ta sako wani wani harder, sai wata top riga, ta bazo da gashin kanta, dakin ahmad ta shiga ta fara gyara masa, tana yi tana rera wakar ta na dan maliyo maliyo.

Baya da kamar 20 mint, kamar wata hayaniya ce take jiyowa, saurin leka kasa tayi ganin wasu mutane da suka cika kofar falon gidan nasu.

Fita tayi gaban mutanen taje ta janye farhana ta tsaya a gabansu, cike da tsiwa tace kai alhaji wa kake da suna, mahaifin dan iska dan tasha, mara mammora kawai, jin zafin zagin yayi shiyasa ya janyo hannunta ya rike gamm, kallon farhana yayi yace "ki tabbata sai ta biya wadannan maganganun da tayi,farhana ce ta sunkuyar da kai ta fashe da kuka tace" aa alhaji ka saketa indai kabeer ne yanzu zan kira a baku shi amma dan allah ka kyale humaira ba abinda ta sani.

Indo ce tace "cabb aunty farhana kyalesa ya tafi dani, wallahi ya sake ya tafi dani sai na ballasa gida dari 9 na bawa jikokin aljanu sun cinyesa, saurin sakinta yayi yana zare idanu jin furucinta.

Farhana ce tace "humaira idan har baki rufe min baki ba wallahi sai na zane ki haba, iyalle ce taja hannun indo, sannan farhana ta wuce suka tafi zuwa hospital din, bayan tafiyarsu indo ce ta kwalla kara tace"wallahi iyalle da aunty farhana bata hana ni ba wallabi da sai na balla sa din gida dari 9 na bawa jikokin aljanu, kuma fa yanzun ma iyalle ba sha yayi domin ina sane na hukunta kabeer, iyalle kinsan wani abu ni ce fa na saka shi yayi hadari, yoo to iyalle hauka ake na kyalesu.

Gaba daya jikin iyalle karkarwa yake, indo ce ta lura da hakan sai kuma naga ta shafeta take ta dawo dai dai, falon suka wuce, ita kuma indo tai dakin ya ahmad.

Indo tin tana saka ran farhana har taji shiru, ba ita ba alamunta, dakinta ta shiga ta fito sanye da abaya black, tayi matukar kyau, dakin farhana ta shiga, side drawer ta bude kudi ta dauka ta fito, har taje bakin gate sai kuma ta tsaya kallon gate man tayi taga yana bacci, hannunta ta daga take wani hayaki ya fito ya mamaye ilahirin gidan, murmushi tayi sannan ta fito.

Abin mamaki nemanta nayi na rasa, ganin haka yasa na tafi hospital din su farhana, ban dauki lokaci ba na isa, ofdice din farhana naje anan na hangota ta rufe idanu tana karkarwa, cike da wata sarkakkiyar murya naji tace "lalle alhaji sani ka taro bala'i da masifa, domin tabbas sai na hukunta ka, kamar yadda nai niyya a baya.


Bude idanunta ne yasa naga ta fito, bayan asibitin naga ta nufa, kamar daga sama wani hayaki yake fita daga bakinta, cikin kankanin lokaci naga kabeer a kwance a gadon asibiti, kallonsa tayi tace "kai ne makami na, da kai da zeey kanwarka, tashi sama tayi anan naga gadon shi ma yabi bayanta.

Iyalle na zaune taga fitowar indo,da kallo ta bita tace" indo ki ga har yanzu farhana bata dawo ba, cikin sanyin mirya tace "karki damu iyalle ai nasan ma tana hanya, dik inda take, iyalle a jikinta sai da taji ta tsargu, karo na farko da ta fara jin maganar humaira, wani sanyi irin maganar mahaifiyarta.

Indo ce tace" iyalle dan allah muje ki min tatsuniya, da mamaki iyalle take kallonta domin tabbas tasan yau din nan ita kadai ce, da ace da mutanen da dik wannan maganar da take mata to a buntsire zata na mata, jin tayi shiru ne yasata kara maimaitawa, da rawar murya tace "eaa indo taho mana.

Cikin wani duhun daji ta tsaya, wata irin kururuwa aljanar indo ta saki, cikin wata siga mai matukar razana.

Alhaji sani na zaune yaji wannan kururuwar, cike da fargaba ya daga kansa yana kallon farhana da take kwalla, cikin karar ne yaji ana magana cike da hargitsewa ya fara dube dube.

Muryar ce tace "idan har baka dauki farhana ka maidata gidan su ba wallahi sai na kashe kabeer, take talabijin dinsa ta kawo, wani tsoro ne da razana suka sauka ganin wannan yarinyar wato indo, ita da kabeer dinsa sai zeey da take kulle a jikin bishiyar dajin, kusa da ita zaki ne ya taho.

Cikin dauriya yace "kiyi hakuri zan maidata, wallabi zan maidata amma ki kyale mini yarana, dan allah ki kyale minsu, su ne farin cikina, kuma daga yau bazan kara kokarin taba farhana ba har abada, aljanar indo ce tace" bazan maido maka da su ba  sai ka maida ta sannan kayi alkawarin cewa zaka cire hannunka daga kan rayuwar iyalan gidan nan, cikin hanzari yace" eaa nayi alkawari madam please.


AISHATUL HUMAIRAH
       ..... Labarin Indo .....
❤️💚❤️💚❤️💚❤️💚❤️💚❤️
    =Na=
 AISHATU BINT MUHAMMAD
       (Matar Uncle)
          🤗 Zinariyar Nazari WRITERS association 🤗


🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀
The Story of life childhood,
Entertainment,
And Love.

NAZARI WRITERS ASSOCIATION


52-----53

Tuki yake cike da mugun sauri domin burinsa yaje ya maida ta gida, wayarsa ce take ruri ganin haka yasa dagawa, bai ma kula da sunan da ke kai ba.

Muryar deena ce take KUKA, cikin kukan tace "wayyo allah na alhaji wallahi kabeer ya bata, alhaji kabeer ba tafiya yake ba bare a ce yana tafiya, wallahi alhaji saurin katsewa yayi.

Daidai kofar gidan ya tsaya, yana tsayawa ya sauke ta yana fadin sai anjima farhana, saka kofarta a gidan take ta manta da komai, komai da ya faru ya huce sai fitarta da ta tina da kuma shigowarta yanzu,tin daga kofar falon ta hangi iyalle da indo, da sauri ta karasa tana zubewa akan kujera.

Kafin ya koma komai ya dawo yadda yake, hospital ya koma yana shiga ya huce dakin Kabeer shi da jama'ar wajen, ganinsa sukayi a kwance wanda yasa alhaji sauke ajiyar zuciya yana fadin "nagode allah tinda ta dawo min da 'ya' yana.

Hajiya deena ce tace" darling me ya faru ne, menene cikin saukin murya yace "dan allah kiyi hakuri zan miki bayani amma ki bari mu samu waje mu zauna idan kabeer ya farfado, domin maganar ta ahali ce, daga haka yahuce.

Indo na kwance ta zabura ta mike, kallon iyalle tayi tace "ke wallahi iyalle ki ta maimaita tatsuniya, ni fa wannan tatsuniyar tin ina yarinya kike min gashi yanzu na zama yammata, har da aure, tsaki iyalle taja a zuciyarta ta furta" dama nasan za ai hakan domin indai indo ce bazata gode min ba, cikin karaji tace "wai iyalle me kike tinani firgigit ta dawo tana murmushin yake.

Juyawa tayi ta koma kusa da farhana tana raba ido yana mummunar kare, farhana ce tace" humaira me kuka dafa iyalle zatayi magana ta katse ta tace "aunty farhana favorite food dinki mna, da mamaki ta kalleta tace" amma humaira tayaya waya girka miki, murmushi tayi tace "kai aunty farhana kamar ba mace ba, wallahi da kai na na miki bara na jera miki a dining ke dai yanzu kije ki wanka sai kizo ki ci.

Da mamaki iyalle ke kallinta, domin ita ta sani tin tafiyarta suna nan zaune, to sai dai idan dazu data tafi barci tayi mata, amma dai indo bata iya girki ba, juyawa tayi ta kalleta tace wallahi iyalle karki kara magana domin naga kanki na rawa wani time din.

Fitowar farhana daga room taji karar waya,da murmushi tai picking daddy ne yace "ki tabbatar da humairah ta tafi makaranta gobe karfe 10 zasu fara exam ni narasa gane kan humaira wallahi, murmushi farhana tayi tace" dto daddy insha allah yau ma abinda yasa bata je ba ta tashi ne da ciwon kai, amma zataje dama gobe zasu fara exam din waec ko, da eaa ya bita sannan ya gaisa da iyalle da sauran mutanen, iyalle ta tambauesa jikin ahmad inda ya tabbatar mata da cewa gove za'a fara gwaje gwaje jibi kuma a fara kokarin yi masa aikin.

Gaba daya falon kowa addua' yake masa da fatan alkhairy, bayan katse wayar ne indo tace "wallahi yaya ahmad ya samu sai naci uwar falmata da Muhammad saurin kallon iyalle da farhana tayi da suke kallonta, cikin bagarar da zancen tace" aunty farhana muje kici abincin ko, saboda naga kinajin yunwa, daga nan ba wanda ya sake magana.

*Washe gari*
Karfe 10 kowa ya ware sai iyalle kadai da take kwance tana kallo, ba kowa a gidan, cikin ranta tace "kai ina dalili ni gida zan koma wannan zaman birni bada ni ba wallahi, duba min kaga ba kowa a gida kowa ya tafi uzurin gabansa sai ni kadai tall kamar mayya, haka dai tai ta zantukanta.

Tana zuwa makaranta tai tsalle ta fito, class ta shiga kowa ya ganta sara mata yake, domin tabbas sun riga da sun san halin aisha nuradeen hatsabibiya.

Can back bench taje ta samu waje ta zauna tana tauna chewing gum, wasa take da biron hannunta tana karkada hannunta, wata yar karamar yarinya ce ta tsaya kanta tana kare mata kallo, cikin bacin rai tace" ke dan ubanki mai naci ban baki ba har kike min irin wannan kallon, cikin basarwa tace "aa humaira bakomai kawai nazo mu gaisa ne, zama tayi tana tinanin yadda za a kaya, domin bata manta dukan da ta sha a wajen ta ba, ga wanda uncle james yayi mata.

Haka rayuwa taci gaba da tafiya a haka har aka cinye tsawon mako guda wato 1 week, daddy ne ya dawo anan yake shirye shiryen tafiyar su farhana da indo, amma indo tace bazata ba, dole badan taso ba sai dan exam dinta datake yi, daddy yace ta bari sai ta gama sai suje, daddy ne zai koma italy domin kirga kaya, farhana kuma zata tafi India, zo kaga bakin ciki gurin indo kamar ta fasa wannan exam din amma ba izini, dan tasan tana fasawa ta taro ta.

Haka tanaji tana gani farhana ta bi suka tafi aka barta daga ita sai iyalle da take shirin komawa da zarar sun dawo.

Alhaji sani ne a falo gaba daya taron gidan kowa na nan sai kabeer da ya gama warkewa, domin da sauki har sun dawo gida, sani ne yayi gyaran murya yace "daga yau ba ruwanku da ahalin ali aliyu, domin ni naga abinda na gani, idan kuma kuna ganin zaku iya sai kuyi amma ni dai ba ruwa, komai zakuyi karku dawo kuce kun sanni. Kabeer ne yace" wallahi daddy nima haka nakeso na fada, domin wannan accident ba kowa bace sila illa wannan shgiyar yarinyar mai aljanu, kaga daddy nasha azaba, kuma abin takaici ita ta dauke ni ta kaini asibiti, dama wannan yarinya shiru yayi yana tinani, deena da zeey gaab daya cikinsu ya duru ruwa, domin zeey komai na ranar nan bai goge ba, tabbas ita ta shaida da cewa aljanu sun sata a turu, saura kadan rai yayi halinsa.

*BAYAN WATA DAYA*
Haka dai rayuwa taci gaba da tafiya tin wannan tafiyar har yau ba labarin su, gashi su ba waya ba bare a kirasu, gida daga iyalle sai indo, indo har ta gama waec tana jiran azo a tafi india amma shiru ba labari.

Haka suke zaune a wannan gidan ba rashin ci ba na sha amma kuma shiru, hakan yasa iyalle tattarawa domin su koma kauye, ita ma indo ta yadda da wannan shawarar domin zaman gidan ya isheta, wata ranar alhamis ne suka fito, bayan sunyi sallama da mai gadi, daga nan kuma suka wuce.

KAUYEN WAKAZA
Shigowar su ne yasa mutanen kauyen ganin iyalle, indo tin a bakin gari take ganin yara na wasa, cike da bacin rai ta kawar da kanta, su kuwa ganin indo yasa su runtumuwa a guje suna ihun cewa indo ta dawo, indo tinda suka shiga gidansu, garba baya nan dan haka taja trolley bags din ta zuwa bukkarta, kallon bukkar tayi a zuciyar ta ta furta "ohh ni indo gaskia na zuba kazanta ta inanalaha, kara kallo tayi tace ya zama dole kuwa na tsaftace ta, can jikin bango ta komar da kayan, kafin wani lokaci ta gyara, harda fesa air freshner, take bukkar ta fara fito da wani sabon kamshi.


AISHATUL HUMAIRAH
       ..... Labarin Indo .....
❤️💚❤️💚❤️💚❤️💚❤️💚❤️
    =Na=
 AISHATU BINT MUHAMMAD
       (Matar Uncle)
          🤗 Zinariyar Nazari WRITERS association 🤗


🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀
The Story of life childhood,
Entertainment,
And Love.

NAZARI WRITERS ASSOCIATION

*🎀HIJABI🎀*

_🎀An shar'anta hijabi ne domin kawar da idanuwan maza daga kallon mata, idan har hijabin ki ya kasance mai kwalliya mai d'aukan hankali toh hakika kin sa'bawa mafunar data sanya aka shar'anta hijabi!._

*🎀Allah yayi Albarka ga macen data fahimci hakan kuma tayi aiki dashi.*

54-----55


BAYAN KWANA 2
Tin da indo ta shigo kauye ko da wasa bata fito, domin ita bata amfanin fitowarta ba, fitowarta daga bati taga yara da yawa suna lekowa, kamar daga sama taji daya yana cewa"laa wallahi indo ce indo dai ta iyalle kai ka duba kaga yadda indo ta koma, lalle indo aure ya karbeta, jin haka yasata shiga bukkarta, wasu riga da skirt ta saka wanda yayi matukar fito mata da shape sannan ta yana veil wani takalmi ta saka ta fito tana ta zuba kamshin turare, bukkar iyalle taje

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login