Showing 36001 words to 39000 words out of 40600 words

Chapter 13 - AISHATUL_HUMAIRAH (Labarin Indo) HAUSA NOVEL

08 Nov 2024

4925

tace "iyalle dan allah zan je gidan su dije, iyalle na daki tace karki dade indo kinji, kuma banda yawan surutu, daga haka ta fita tana tina rayuwar abuja.

Tafiya take dik ta inda ta huce kallonta ake ana mamakin wannan girma na indo, domin idan ba mutanen gari da suka santa samm ba wanda yake ganeta.

A hankali take sallama kasa kasa, dije ta hango tana wanki karasawa tayi dije jin wani turare yasata dagowa, sororo tayi tana kallonta, murmushin da tayi ne ya bayyaanr da hakoranta hakan yasa ta ganeta, cikin dariya tace "laaa indo ashe da gaske kinzo, wallahi nayi tinanin mutane gari karya suke mini.

Zama tayi suna kara gaisawa suna hirar yaushe gamo, ta dan dade dan har saida mahaifiyarta ta dawo suka gaisa, sannan ta tafi kusan sai da ta yawace garin kowa na sha'awar chanjawar indo, domin kuwa indon indo ce ta chaja ta zama wata silent kamar ba ita ba.

A gaskia ilimi yayi a rayuwa domin ilimi shi ne ya chanja rayuwar indo, ya chanja ta daga abinda yake damunta, ilimi shi ne hasken dayasa take tantace fari da baki, ilimi shi ne yasa ta dai na dik wata barna da takeyi a baya, domin yanzu ga indo ta zama wata silent haka kamar ba aisha indo ba.

Nikam ina labarin ahmad.... Amma kafin nan ga wani topics

      *GYARAN FATA:*

zaki tanadi ababe:

kamar haka:

1. Man Zaitun
2. Lalle
3. Kur-kur
4. Madarar ruwa (peak)

*Za ku hade wadannan* *kayan hadin guri guda* *sai ku kwaba su ku shafe jikinku da fuskar ku, za ku yi wannan hadin kafin ku shiga wanka idan ya bushe a jikin ku sai ku murje sannan sai ku shiga* *wanka,*
*wannan hadin ya na sa* *jiki yayi kyau da sheki* *insha Allahu.*
*Za ku iyayin wannan ma wanda ake hada:*

1. Kur-kur
2. Dilka
3. Zuma kwai
4. Lemon tsami.   
*Za ku hade su a guri* *guda ku samu ruwan*
*ku kwaba kamar yadda* *ake kwaba lalle, amma* *ya fi kwabin lallen ruwa, *sai ku shafe fuskanku,* *idan kuma har da jiki* *kuke so, sai ku shafa* *harada jiki bayan awa daya sai ku shiga wanka* *za k ga yadda* *jikinku*
*zai goge. Das da izinin Allah.*

*MAGANIN NI'IMA NA MATAN AURE:*

*INA MASU FAMA DA KOWANNE IRIN MATSALAR RASHIN NI'IMA:*

*To wannan matsalar tazo qarshe da ikon Allahu.*

*A nemi wannan mahaden kamar haka:*

1* kwakwa 🥥
2* Danyar Aya
3* Dabino
4* Danyar Gyada
5* zuma 🍯

*A hada wadannan Abu hudun a blender a markade su, su zama ruwa sannan a sa zuma sai mace tasha tun kamar qarfe uku 3:00pm kafin lokacin kwanciya yabi jiki ki tsumu  to NI'IMA zata sakko Miki sosai Yata Mai gida ya daina zaman majalisa Kullum kuna tare yayana a gwada za'a yi Farin ciki.*

*MAGANIN SANYI NE SADIDAN.*

*1. Citta danya*🪴
*2. Tafarnuwa* 🧄
*3. Kurkum* 🌿
*4. Lemon tsami* 🍋
*5. Zuma* 🍯

🍵🍵🍵
*Ake hadawa a dafa a rika.sha sau 2 a rana*

🍉🥥 *NI'IMARKI SIRRINKI🍌🍍*
          *SIRRIN NI'IMA*
*(1) kwai da lifton akada ashan ye hmmm*
*(2) kuka da madara sha yanzu magani yanzu*
*(3) ganyen ugu,kawi,madara,zuma :ganyen ugu azuba ruwa misalin rabin kofi amutsukeshi ataceshi azuba kwai guda daya azuba zuma cokali* *(3) madara tagari cokali 2asha kwana uku*
*(4) kankana ayaba ayi blanding dinsu azuba zuma ko madara asha*
*(5) ayaba zallah kafin kici komai ki karya da ita*

GYARAN FUSKA DA FATA,CIKIN SAUKI.

a yau zamuyi bayani game da gyarna fata, musamman masu fama da yawan kananan kuaraje da yawan gumin fuska da maiko na fuska.

Ga duk mai son rabuwa da wandan nan matsalolo ga hanya ingantacciya,wacce bata da wata illa,kuma ba tare da kashe wasu kudade ba,domin wasu masu son gyaran fuska da fata suna amfani da mayukan da suke dade fata wadan kuma suna da illoli sosai ga lafiyar fata.

Ga wasu hanyoyi Guda 3 wadda kowacce idan akai amfani da ita za'a samu Nasara.

HANYA TA FAFKO.

ZA'A NEMI.
1. Lemon tsami
2. Zuma
Da farko za'a matse lemon tsamin a cikin wani abu kamar roba,sai a zuba Zumar a ciki a cakuda sosai sai a shafe fuska da shi na tsawon minti 15 kafain wanka,sannan a wanke da ruwan dumi a shafa man Zaitun a fuskar.

HANYA TA BIYU.

ZA'A NEMI.
1. Danyen kwai
2. Zuma
Da farko zaa fasa kwan amma iya farin ruwan kwan banda kwandowar,sai a kawo Zuma a zuba a cakuda sosai a shafe fuska na tsawon minti 15 kafain wanka sai a wanke da ruwan dumi.

HANYA TA UKU.

ZA'A NEMI.
1. Tumatur(Tomato)
2. Lemon tsami
3. Zuma.

Da farko zaa matse lemon tsamin a runa, sannan a matse Tumatur shima a ciki sai a kawo Zuma azuba a ciki a huya sosai sannan a shafe fuska da shi na na tsawon minti 10 kafun wanka sanan a wanke da ruwan duni.

Dukkan kowacce hanya da zaka gwada zakayi na tsawon sati daya ko biyu gwargwadon yadda kake son fatar taka tayi kya

..... To mudawo kan labari.....

   Queen 👑 waleeiii🌹🌹🌹

AISHATUL HUMAIRAH
       ..... Labarin Indo .....
❤️💚❤️💚❤️💚❤️💚❤️💚❤️
    =Na=
 AISHATU BINT MUHAMMAD
       (Matar Uncle)
          🤗 Zinariyar Nazari WRITERS association 🤗


🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀
The Story of life childhood,
Entertainment,
And Love.

NAZARI WRITERS ASSOCIATION

57++++++58

Sai can wajen la'asar ta shigo gidan, iyalle ta fara tozali da ita sai kuma ta wuce bukkarta, gaba daya ni kaina na shaida indo anyi hankali nitsuwa ta saukar mata.

Iyalle ce ta leko hangota tana rubutu yasa ta kwala mata kira, a hankali ta dago tace "na'am iyalle, yawwa indo zo kije wajen Salisu mai kifi ki siyo min kifin miya kinji, kamar bazata ba sai kuma ta mike ta fito, tana tafe tana hada hanya tana hada rai kamar hadari.

Fitowarta ne tai kicibus da dije, washe baki dije tayi tace" wallahi dama indo wajenki zanzo saboda muje gidan jaru sai nemanki take, bata kula ta ba da farko sai a karshe tace "zo muje ki rakani wajen salisu mai kifi, daga haka suka kara gaba.

Haka dai suke zaune tsawon kwana 20 ba labarin su ahmad, indo dik ta matsu sugo tin tana saka ransu har ta cire ta daina tinanin su ma, kullin suna tare da dije.

Yau ma kamar kullun da kur'ani a hannunta ita da dije sun dawo daga makaranta,dije ce tace "wai dama indo idan mutum yaje birni dama haka yake, ke ki dube ki da indo kinfi kowa tsula tsiyarki amma yanzu kin zama wata salaha, murmushi indo tayi wanda ya fito da ainahin dimple din gefen bakinta tace" bazaki gane ba dije kawai ki rabu da wannan zancen please.

Tafiya suke daidai gidan su dije ta tsaya sukai sallama sannan ta taho gida, tin daga nesa ta hango wata bakar corolla l.e sai daukar ido take sai kuma baya wata jibgegiyar jeep ce ota ma dik sunyi parking.

Dan karamin tsaki taja sannan tace "to kuma su waye auka zo gidan namu bayan mu bamu da yan uwa masu wannan motar.

Ta bakin motar taje tana lekawa amma dayake tint xe ba abinda ta gano sai bakin glass, kamar wadda ake gani tsayawa tayi ta murguda baki sai kuma tayi murmushi tace" waiii ashe nidin beautiful ce, washa raban dana ga kyau na haka, tin ina birni ta bawa kanta amsa, wucewa tayi taci gaba da tafiyarta.

Da sallama ta shiga gidan, ganin mutane tirus yasata fara kallonsu, idanunta take ya sauka akan na farhaan da yake kallonta cike da mamaki, ita ma din da murmushi ta nufi wajensu, sai kuma naga ta juya ta tafi bukkarta, kowa na wajen yayi mamaki wannan lamari na indo, amma ita ko a jikinta, iyalle ce tace "to fa yau kuma da wannan  daru aka sauka da alama bata san tare kuke da ahmad ba, farhana ce tace" aa iyalle ki kyaleta dama nasan za ai haka saboda kinsan ai tafiya mukai muka barta, kuma ba wanda ya kara dawowa tin tafiyarmu, gaba daya shiru sukayi daddy ne yace "to allah ubangiji ya kyauta, dikansu suka ce ameen.

Salma ce ma mike tace "tinda ba wanda zaije wajen 'yar tawa ya lallashe ta ni bara naje, saboda gaskia nasan nidai nayi laifi, hanyar bukkarta tayi tin daga bakin kofar ta hangota tana rubutu, nikam indo ko mai take yawan rubutawa allahu a alamu.

Sallama tayi saurin boye littafin tayi tana kallon gefe, mama ce ta matso kusa da kta tace "haba humairah kiyi hakuri mana nasan ai mun miki laifi amma ai kinga bazamu kara ba, again ko jiyowa batayi ba, mama ce take mata magana amma still ko kallo, mama xe taxe" humaira harda fa ahmad dunki muka dawo, dan karamin tsaki taja tace "to wai mama meyasa baku dawo da wuri ba.

Indo ce tace" wai yaya ahmad din yaji sauki mama, mama ce ta shafa kanta tace "eaa mana humaira yaji sauki sosai, kingansa kamar zaki, dariya tayi sosai tace" allah mama lokaci daya ta hada rai yayin da idanunta suka sauya kala, cikin muryar ta ta aljanar indo tace "tabbas lokacin bayyanar falmata da Muhammad anas yayi, jijjigata taji anayi, firgigit ta dawo daga wannan duniyar.

Mama ce tace" ke indo mennene, me naji kina cewa ne, me naji kince kamar Muhammad anas, ko dama kina da sa hannu a batansa, kinsan yadda ake nemansa ne, tave baki tayi tace "to mama sai me kuma ni ki kyaleni ni nakusa dawo dasu, domin dik bala'in da ya ahmad ya shiga wallahi muhammad ans ne sila, tashi tayi ta fice ta bar mama na mamakin wannan maganar ta indo.

Fitowa tayi tana wakarta farhaan na hango ta ya taso yana dariya, basarwa tayi wajen daddy ta karasa ta tsugunna bayan ta gaishe sa, sannan ta duba lafiyar ahmad, farhana ce tace "wato ni kuma fushi kike dani shisa bazaki min magana ba, dariya tayi tace" eaa ai ke amarya ce ina yaya Ramadan din, allah sarki amma da bikinki sai munje shiru tayi sakamakon kiran da farhaan ke jera mata.

Da gudu ta karasa saboda kallin hannunsa da tayi da wani kwali mai kyau, da fara'arta tace "laaa ya farhann wannan gift di na ce, dan murmushi yayi mata yace" eaa mana gift din ki ce.

Laaa ni yar gatan yaya farhaan, abin da tace kenan, farhana ce tace "ke wai humaira yaushe zakiyi hankali, yaushe zaki daina wannan shiriritar, oho ta bata amsa, kamar daga sama taji daddadan kamshin da take burin shaka a kowane lokaci, kalle kalle take domin jin a inda kamshin yake, daga idanunta ne sukai arba da ahmad sanye da 7stars light blue yayi matukar amsar jikinsa, kallonta yake yana murmushi.

Indo ce ta ce "yaya ahmad ina wuni, gimtse fuska yayi yace aishatul humairah kayan rashin ji, lafiya lau yagida, ya jikin ta fuurta, bai bata amsa ba yace" kin gana murguda bakin a jikin glass din motar, saurin rufe idanu tayi tana dariya, kowa na wajen na murmushi.

Iyalle ce tace "ke indo kizo kije ki amso min gishirin kinga ya kare, ahmad ne yace" aa iyalle gaskia a kyale min mata ta huta, shekara da shekaru ina cewa ki bamu ita amma kika hana, dan haka a kyale ta kawai, humaira ya furta, zo muje ki rakani unguwa, da sauri ta karasa kusa da shi tana dariya, juyowa tayi tare da cewa "iyalle ki bari idan na dawo zan siyo miki, suna fita maimakon suyi cikin kauyen, mota ya shiga ganin haka yasata ita ma shiga tana ta fara'a, daga nan sukai cikin garin dutsin-ma.

Bangare kabeer dai komai yayi sanyi domin kuwa yanzu ya daina dik abinda yake ya kuma shiryu, baya zuwa ko ina daga massalaci sai gida, sai makarantar malam da yake zuwa ake masa dori.
AISHATUL HUMAIRAH
       ..... Labarin Indo .....
❤️💚❤️💚❤️💚❤️💚❤️💚❤️
    =Na=
 AISHATU BINT MUHAMMAD
       (Matar Uncle)
          🤗 _Zinariyar Nazari WRITERS association_ 🤗


🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀
The Story of life childhood,
Entertainment,
And Love.

NAZARI WRITERS ASSOCIATION

59++++++60

_Washe gari_
Tin da sassafe suka fara shirye shiryen tafiya abuja, dik da flight zasu bi, niko nace ina indo taga passport.

Ahmad ne yake driving a motar daga shi sai indo, sai kuma farhaan da yake uzurin gabansa, indo naga ta janyo book din ta ta fara rubutu kamar yadda takeyi kullun.

Tafiya suke sai da suka isa Airport sannan dik suka firfito, indo kallo kawai take tana fadin "to ni ta ina zan hau jirgi bayan ance bani da takarda, jin anja hannunta ne yasata dariya domin tasan tabbas yaya ahmad ne, shiga suka yi bayan an tantance su suka wuce, indo tin daga nesa ta hangi jirgi amma bakinta yaki rufuwa daga nan suka shiga flight sai birnin abuja.

Haka akai kuwa bayan kwana 2 da dawowarsu, indo ta koma islamiyya yau da yamma liss ta shigo gidan, samm ta manta yaya ahmd yana nan tin daga falo take kwala kira, mama aunty farhaan ahayyye wo ni indon iyalle, wallahi nayi kokari kunsan menene kuwa, ahayye jin gyaran murya a kusa da ita yasata zaro ido tana kallon yaya ahmad, cikin hade rai yace "wuce kije ki hado min coffee yanzu ki kawo min, batai magana ba ta karasa, bayan wasu mintuna ta fito baya falo hakan yasata tafiya daki, knocking take daga can yace" come in,shiga tayi kallon dakin take komai ya chanja, dan murmushi tayi ta karasa.

Ajiyewa tayi sai kuma yace "wuce kije ki wanke min toilet, dan zumburo baki tayi tana kallon gefe, sai kuma yace" ke bazaki wuce ba ne, shiga tayi ta dan dade ta fito tace "nagama ai, ok ya furta ihun mai kikeyi ne, kin manta gidan bakowa ne sun tafi dubai hado lefe, kuma farhana bata nan, dan harhada magana tayi tace" dama sunana ya fito ne a cikin zaka kurai wadanda zasuyi saukar alkur'ani mai girmaa, sai a lokacin yayi mata murmushi yace "masha allah ashe malama matar tawa ta zama.

Karar waya ce ta katse musu hirar, dauka yayi yace hello daddy, a'a daddy ba wani labari har yanzu wallai, mun nemesa har mungaji, amma insha allah yana cikin aminci, indo na jin haka ta tabe baki tai kalli gefe, a hankali ta mike ta bar dakin tai dakin farhana, domin kar ma ya je nemanta dakinta.

A wannan lokaci ana shirye shiryen bikin farhana, komai ya tfai dai dai inda ya ahmad yayi wa aisha siyayya ta biki gaba daya, to dama ita ba kawa ba dan ita batasan raini a yadda ta fadamin a baya, a wannan sati ne ranar jumu'ah aka daura auren AMINATU ALIYU ALI da anginta RAMADHAN HASSAN DAHEER Bisa sadaki naira dubu 100, to farhana sai dai muce allah ya kawo kazantar daki, a wannan daren aka kai amarya gidanta, daga nan kuma kowa ya watse, gida ya kuma yin shiru.

Ganin haka daddy yabawa ahmad shi ma gida da mota akan zasu tare a gidan sa nan da kwana 3.

Tin bikin farhana indo ke harhada rai, yau suna zaune a falo suna hirarsu, indo ce ta shigo ran nan a hade yayi murtik, idanunta sun wani zazzago kamar zasu tashi, cikin rashin kunya tace "kai ni dallah ku kyaleni, kowa kallinta yake ahmad ne yayi kokarin zuwa wajenta, mama ce ta dakatar da shi tace" aa ahmad karka kuskura ka karasa akwai abinda zai faru a ayanzu, ina tinanin dawowar Muhammad anas yayi, kowa na falon kallonta yake, amma tsamm na hangi firgici a fuskar farhaan.

Jijjiga ta fara yi sai gata a tsaye ta mike, cijin muryar ihu tace "ya iska ku kawo su nan, sannan su bayyana a wannan falon, bata rufe bakinta ba sai ga Muhammad anas, hijjah, falmata, malama, gaba daya jikinsu ciwuka ne wasu sabbi wasu tsoffi, ga wani uban baki da sukayi, dariya indo tayi tace" yayi kyau wuntsil aikin ku yana kyau, indo ce ta kalli mutanen falon, tace "ni ni ce aljanar indo ina da yara na dika muna rayuwa a anikinta domin bata kariya, amma tinda yanzu komai yazo karshe zamu tafi, sannan kuma baza mu kara dawowa ba, abinda nakeso da ku shi ne karku cutar da indo, domin indo ita ce ta zame muku jigo, ita ce ta taimake ku, sannan kuma kai aliyu ka tabbatar ka kula da ita, kai kuma ahmad mijinta ne dan haka alhakin kulawar ka na kanta, kasan cewa ita din marainiya ce dan haka gata nan.

Sannan karka kara yadda da aboki domin akwai abokai da yawa amma wannan Muhammad ans din nemanka yake da sharri, wani tafi tayo sai ga wata takarda ta bayyana fara soll, ka duba wannan takardar akwai wani sako na musamman da yake cikinta ina mai fatan zaku duba zaku ma kuyi aiki da shi da hankali yadda ya kamata, wai hayaki ne ya bayyana ya fara tashi sama, kafin wani lokaci ya gama fita, indo ce ta zube a kasa, yayin da kowa na falon ke mamakin wannan abin da ya faru da bayyanar Muhammad anas da tafiya da aljanun indo sukayi.

Kowa na dakin mamaki ya cikasa amma banda mama dan dama tasan hakan zata faru, mama ce ta mike kallon ahmad tayi tace "dauki indo ka kaita dakinta sannan ka dawo,daukar ta yayi ya tafi dakinta, ajiyeta yayi zai fito yaga wani diary a ajiye, bude shafin farko yayi yaga ta rubuta labari na ni aishatu, dauka yayi ya fice daga dakin.

Falon ya dawo yana kallin falmata, hijjah, Muhammad ans sai bokansu da suke ta raba idanu wahala ta saka su suna kifkifta idanu kamar na birrai.
AISHATUL HUMAIRAH
       ..... Labarin Indo .....
❤️💚❤️💚❤️💚❤️💚❤️💚❤️
    =Na=
 AISHATU BINT MUHAMMAD
       (Matar Uncle)
          🤗 _Zinariyar Nazari WRITERS association_ 🤗


🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀
The Story of life childhood,
Entertainment,
And Love.

NAZARI WRITERS ASSOCIATION

61++++++62

Mikewa yayi sai kuma ya zauna yana girgiza kai, kallonsa yayi yace "daddy meye kuma hakan dama Muhammad anas, daddy ne ya katsesa yace" ka rufemin baki ahmad, su da kansu zasu bada labarin abinda ya faru da kai daga haka ya kalli Muhammad anas cikin bacin rai yace "kai ka fadamin menene ya faru ko kuma wallahi na saba maka.

Muhammad anas ne yace" ba dole na fada ba idan har an fada ba wallahi baza su kyaleni ba, zan fada muku wallahi tsawon watanni 9 kenan ina wannan aikin sai da aikin yazo gab da cika wannan yarinyar indo ta baygana.


A rayuwa ta tin san da na hadu da ahmad gaskia naji inason abota dashi amma badan komai ba saboda daddy ya fimu kudi, sannan kuma ni gaskia inaso naga faduwarsa, sakamakon kullin kara daukaka yake, duba da yadda ya tafi exam din pilot kuma yaci, ni kuma tin daga bakin kofar gate din aka koreni

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login