Showing 3001 words to 6000 words out of 40600 words

Chapter 2 - AISHATUL_HUMAIRAH (Labarin Indo) HAUSA NOVEL

08 Nov 2024

4923

wata kawar habi amarya ce da batasan halin indo ba ta matso kusa da ita tare da shako wuyanta, "ke uban waye yace ki karbi kudin ajo. Kuma kice bazakiyi a yau ba sai gobe, kallon ta tayi sororo tana mata dariya, yayin da dsukacin mutanen wajen ke cewa ki saketa, tsaki taja tana fadin aikin banza ni har wannan zanji tsoro, yarinya yar ficika da ita sai iskancin,bata karasa va taji wani shahararren mari akan kuncinta, wanda ya dauke mata gani na wani. Lokaci.

Indo ce ta kalleta tace ubanki ne mana shegiya mai siffar aljanu kawai, kuma wallahi bazan bayar da kudin ajon ba, ke kuma habi kisan yadda zakiyi dasu, kinsan hali na ko to na cinye bazan badaba, habi ce ta durkusa a kasa tana rokon indo akan ta taimaka ta bata kudin amma ina fafur ta hana.

Kabiru ta hango take ta tino da abinda ya faru a gida, karasawa tayi tana masa kallon sai naci ubanka, cike da fishi tace"kai kabiru wato baka da mutunci ko kai ga gagararre, to tsugunna anan ko kuma wallahi yanzu na shemar da kai, ba yanda ya iya dole haka ya tsugguna yana jiran hukuncinsa, dan ya tabbatar inna taje gidan su indo,"dan allah indo kiyi hakuri, tsaki taja tace kai dallah rufemin baki shashasha kawai maza ci gaba da tsugunno.

Ke kuma maai suffar Aljanu me kike cewa, kodan dik ba wannan ba idan kina da karfi, zoki kwata, daga haka ta juya, domin jinta take kamar zata iya dukan mutum 30 dan fishin da take ciki, kamar abin arziki ta je gida, bokiti ta dsuka ta tafi rafin dan marka, debo ruwa ta farayi tana zubawa a gida, sai da ta cika ko'ina sannan ta koma rafin, wani dan kulli naga ta fito dashi daga jikin skirt dinta da daita da buje dik daya, cikin dan lokaci ta watsa shi dika.

Tashi tayi maimakon ta tafi gida sai ta nufi bayan gidan su habi, shukar masara ce a wajen ta fara fitowa, cikin dan lokaci ta gama cireta tsabb, sannan tabi gonakin dake kauyen dik ta ciccire shukokin harda ta gidansu ma kuwa, maimakon ta tafi gida ta kwanta dan 11 ai ta riga datayi, aa sai tai hanyar gidan su dije, dakin yayan dije ta shiga wanda yayi mata rashin mutunci dazu lawan, ganin yana sharar bacci ne yasa ta janyo wani kyalle ta rufe masa baki, wata bulalace da bansan a inda ta samota ba ne ta fito da ita, lokaci kankane ta fara sharba masa, ihu yake amma bakajin komai sai guri, sai wasu uban hawaye dake zuba a idanunsa, wani kullin kuma naga ta fito da shi, debowa tayi ta watsa masa a ido, sannan tai sadaf sadaf ta fice daga gidan ba wanda ya jita.

Safiyar yau bata tashi da wuri ba, tana tashi makewayi ta shiga, ruwa ta diba a baho tana shiga ta watsa ta fito, bukkarta ta koma ta dauki kayanta da dik sunyi ja ta saka, sanan ta zauna ta janyo kayan kwalliyarta, kallon mudubi tayi yayin data dakko wata uwar hoda ta fara shafawa a take fuskarta ta rine ta koma jawur kamar me, kwalli ta saka hade da jagira, kallon kanta tayi a mudubi tace "oh ashe nima dai kyakkyawace, fara ce tarr ko duhu batayi ba, ga wani uban gashi tuli guda a kanta, da farko na dauka na doki ne sai daga baya nai tinanin gashin fulani, siririn hanci ne da ita sai dan karamin baki, kallo daya ya ishi ka gane cewa eaa lalle wannan jinin fulani ce.

Bakin kwallin ta dauka ta shafa a bakinta, sannan ta fito ta tarar da iyalle, bani abinci na, abinda ta furta kenan, iyalle ce tace "ke kika debo ruwa jiya indo, aa tace sai kuma tace anya iyalle ba aljanun bishiyar nan bane, zama tayi ta cinye tass ta sha ruwa, allonta t adauka tace 'iyalle na tafi makaranta daga nan ta fice.

Tafiya take tin fitowarta take jin ana maganar rafin dan marka ya baci amma ita kam ko a jikinta, dariya takeyi tana tafiya, tana zuwa makaranta gaban malamin taje ta tsugunna ta gaisheshi"malam iliya dan me karfi ina kwana da lafiya ya amsa yaci gaba da karatu, tashi tayi ta nemi wajen zama.

Abinda yake kawota makaranta kenan kullun ranar laraba da sassafe, saboda gidan malam ana suyan kaji, kuma ana raba naira hamsin, gashi ita har dana malam take hadawa ta debe bai sani ba, idan yara sun kawo na laraba.

Sallama take rafakawa a gidan malam iliya, amaryar malam iliya tana jinta ta fara kokarin boye soyayyin kajin, amma ina indo ta riga data gani, "amarya malam yace ki dakko mishi tawada a daki, amaryal malam bata fahimci komai ba dan haka ta mike ta tafi, indo ganin ta wice ne yasata sakin wata kafirar dariya, leda ta samo karama sai da ta cika ta da naman kajin sannan ta baro gidan tana fitowa bata jira dawowar malam ba tai hanyar gidansu.

Gaba a ya kauyen ya rikice, sakamakon ciccire misu shukoki da akayi, kowa zargin indo yake amma baka da ikon kayi magana, da kyar aka samu wani mutum da shi da samari 4 suka isa gidan su indo a lokacin ta dawo daga makaranta tana zaune tana yagar kajinta tana dariya, sallama ake tafkawa ba abinda tace illa "ku shigo, shigowa sukayi basu jira iyalle ba suka damki indo sai kofar gidsn mai gari.

Indo ana zuwa suka saketa ta zauna taci gaba da cin namanta, mai gari dik a tsure yake domin bai manta karonsa da aljanun indo ba,iyalle ce ta karaso tana fadin" dan allah kuyi hakuri ku kyaleta, babban ciki ne yace "aa ba wanda zai kyaleta wallahi sai ta biyamu, wani ne ya falfalo da gudu kamar yaci babu yace" ba indo bace ta aikata domin ita ma gonar gidansu sai da aka cire ta tsaff.

Indo sai da ta cinye tsabb sannan tasha ruwa tai hamdala, kallon mai gari tayi daya kasa magana, sai kuma tacw "ni fa bani bace sarkin aljanu ne da tawagarsaya, domin jiya wajen karfe 2 na dare naji suna cewa a nome gonakin kowa, anan fa kowa idonsa ya duri ruwa, indo kuwa tashi tayi ma ta kara gaba ta barsu da zance da girgiza kai.

Gidan su dije ta wuce dan ganin ya lawan din, da sallama ta shiga tana yi tana wakar ta data zamar mata sabo, a kwance ta gansa ya mimmike kafa ga wasu uban shatin bulalu da sukayi masa rudu rudu, indo tana ganinsa take taji sanyi a ranta, karasowa tayi ta zauna tana fadin "sannu lawan me ya sameka haka, bai iya bata amsa ba saboda matsananciyar wahalar da ya sha a hannun aljanu.

Dije ce ta shigo tana kiran, wallahi kogin dan marka ya lalace domin kuwa ruwan baya iya sha yiwa yayi jajawur, ya koma kamar jini inna, bata tsaya ba tace, kuma mai gari yace yana neman dik wani saurayi a kofar gidansa domin za'ayi bincike ne, kuma inna lawan ba yaji aljanun ba dan haka kawai ya tashi yaje.

Indo ce ta hankada ta take taji ta a kasa, sai kuma tace "ke dallah shashasha mara hankali, lawan ya kuskura yace eyaga aljanu to wallahi kashinsa ya bushe domin suna dawowa a karo na gaba kashesa zasuyi, jin ance kisa ne yasa ta fara zaro ido tana fadin inalillahi, inna wai da gaske, innar ma taa yadda dan haka tace to yanzu ya zamuyi indo, dariya indo tayi tace "koda wasa karkuce aljanu ne suka kirbesa daga haka ta fice zuwa gidsn su habi.

Tin daga kofar gidan take kiran mai suffar aljanu fito mana ga kawaarkj, yarinyar tanaji tasan itace amma sai tayi banza da ita, a zaune ta tarardasu ita da habi, habi na ganinta ta fara magana "dan allah indo ki taimaka ki bani kudin ajon nan dsn allah, indo ce ta kyalkyaale da daria tace" ke din banza ba kin turo mai suffar aljanu ta karbar miki ba jira nke tazo naga zata iya kwata, wadda aka kira da mai suffar aljanu a fusace ta tashi ta kama indo da fada, amma sai da indo ta mata duka, jin kamar tudu a kirjin budurwar ne yass indo lekawa ai kuwa idanunta suka hadu da nono, dariya ta kuma yi tace shegiya, wadannan yayan kwallon fa.

Ai da su kike gadara ko, ke habi dakko min wuka na yanke yan iska, ba habin ba hatta budurwar ta riga datasan ta gama yawo, habi hannu na raws ta mika mata, yaga rigar tayi tana saita wukar.

AISHATUL___HUMAIRAH
       ..... Labarin Indo .....
❤️💚❤️💚❤️💚❤️💚❤️💚❤️
    =Na=
   A'ishatu Bint Muhammad
           (MATAR UNCLE)
🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀
The Story of life childhood, Entertainment, And Love.

6🐰7

Kafin ta kai ga sa wukar tini taji saukar icce a kanta, a take a wajen ta sume, ba kowa bace illa salame data kwada mata icce, kallinta habi tayi sai kuma, lantana mai suffar aljanu inji indo amma ta fara lalubeta, anan taji kudin dakkosu tayi tace wannan ne da alama, ku huce mutafi mu kaso su, habi dai a tsure take dan haka tace aa kuzo mu kama mu wullarda shegiya domin wallahi idan ta tashi tasan a gidan nan akayi mata.

Kakkamata sukayi suka kaita lungun gidansu suka ajiyeta anan sannan suka tafi.
Iyalle ce ta dawo daga bakin dandali tayi karo da indo, da sallallami ta tsugunna, daukar ta tayi sannan kuma tatafi gida, harda yar kwallarta, shinfida tayi mata ta kwantar da ita akan tabarma.

Indo tin safe har la'asar bata farka ba hakan yasa iyalle jin tsoro, ruwa ta debo ta fara zuba mata akan ta tashi amma ko motsi batayi ba, dan haka ta fara jijjigata, tasan indo da nauyin bacci acewar iyallee wai indo bacci take, dan haka ta kara mata lokaci.

Gaba daya yau kauyen kuwa kowa yau lafiya yake harkokinsa ba wanda ya tambayi ina indo.
Indo ana kiran sallar magariba ta mike tace "kutumar uba ai da gudu ta fita, gidan su habi taje basa nan, zama tayi a kofar gidan tana tinanin me ya kamata tayi ne.

Gidan su dije da salame ta yashi taje amma babu su babu alamun su, hakan yasa tace" da ni kuke zancen, baku kadai ba harda iyayenku sai sun san wacece indo, tashi tayi tana gantalinta har magariba tayi, hakan yasa ta nufar dandali, anan ne ta hadu da barki, indo ce ta karasa kusa da ita tace "ke barki ina su habi ne, washe baki tayi da dik hakoran sun dafe tace," suna gidan su lantana wata uwar ashar ta saki tana girgiza kai, kafin kace me tini ta bar dandalin da wani mugun gudu.

A daidai kofar gidan su lantana ta tsaya tana tinani me zatayi, hakan ne yasa kallon kasa, wata leda ta hango can nesa, zuwa tayi sannan ta tsugunna ta fara debo kasa a hankali, sai da ta cika ledar sannan ta karasa gidan, abinda take tinani ne kuwa ya auku, domin tukunya ce suka dora gefe kuma ga dije a zaune da lantana, shigowarta yasa lantana mikewa ta zuba da gudu tai dakin iyarta, dije ce tace sannu indo, bani banzan kallo ta wulla mata sannan ta bide tukunyar ta juye wannan yashin, kallon dijen tayi tace, "wato ke ga mayya ko, sai kici mugani kuma wallahi na kama habi da salame da lantana sai naci bura'ubansu, daga haka ta fice tana wakarta.

Ganin kowa na tafiya kofar gidan mai gari hakan yasa indo tafiya tana cewa" kara naje ayi komai a gabana ko kuma a samu wani makiyin nawa ya aibata ni, tana zuwa ta zauna daga can nesa ba wanda ya hangota,mai gari ne yayi gyaran murya yace "mutanen wannan kauye ina fatan dik kun wuni lafiya, a gaskia muna cikin tashin hankali domin kogin dan marka, ruwan ya daina sha wuwa, hadi kuma ga gonakin mu da aljannu suka ciccire mana ciyawa,amma ina mai bada shawarar a kara hakuri komai zai daidai ta.

Wani na kusa da maigari ne yace "aa mai gari bazaiyu muci gaba da zama a haka ba, kasancewar mu mutane ne kuma muna buqatar ruwa da sauran abubuwa, amma yanzu meye mafita, dikkanin mutanen wajen tsitt sukayi suna tinani, wani ne ya Mike yace" to allah gafarta malam mudai bamu da abinyi sai abinda kafada.

Indo jin kowa yayi shiru yasa ta yin wuff ta dare gaban mutane, kafin kace me kowa ya fara tofa albarkacin bakinsa da zagin indo, shi dai mai gari yasan gamon ba dadi shisa ma a take yayi tsitt, tsawa ta daka musu tace idan kuka bani abinda nakeso, ina tabbatar muku da cewa zan sa aljanu su dawo da kogin dan marka, jin haka yasa suka hada baki wajen furta me kike buqata ne indo, dariya tayi ta buga kafa tace wannan kuma ni zan yanke, dan haka a yau dik wanda ya shiga gidansa karka kuskura ka bude ko su dawo jikinka.

A haka kowa ya yadda da abinda ta fada, sannan kuma kowa ya watse, indo dariya ta saka tana tafawa, tace "lalle wadannan anyi jahilai yoo inba jahilci ba ai daga jin wannan batu kasan karya nake, wohoho yo ni indo, daga haka ta shige ta fice.

Kamar yadda indo ta umarce su haka kowannensu ya shiga gida ya kulle, direct kasuwa tayi tana tafe tana wakarta, daidai wajen mai chaji ta tsaya,wani katon dutse tasaka ta balle mabudin, shiga tayi ta dakko wata speaker kunna tatayi ta saka wani kida mara dadin saurare, ta kore, abinka da dan karamin kauye take ko ina wannan karar ta wanzu, tana kara gaba, gida taje ta bude kayanta, wani katon abu naga ta dauka fari tass, rafin dan marka taje, bata bata lokaci ba ta cilla sannan ta tafi, speaker ta dauka taita gantalli, ta hana kowa bacci, ko wane gida tazo wucewa sai taji kukan yaro.

Dandali ta koma ta nufi rumfar idi, zama tayi ta fara cin breadi, sai da ta koshi ta fito, mai tukubar tsire, kai in takai ce muku labari sai da ta aikatawa mutanen kauyen nan barna mai yawa, sai wajen 3 sannan ta koma ta maida speaker tai gida, tana zuwa ta kwanta ta fara sheka bacci.

WASHE GARI

Tin aasuba al'ummar kauyen ke tafiya debo ruwan, abin mamaki jan ya ragu dan za a iya sha ma.

Indo sai can wajen tara ta tashi, ba sallah ba salati ta fito daga bukkarta, gaban iyalle taje ta zauna,kallonta tayi tace "tashi kije kiyi sallah, ko kallonta batayi ba tace bazanyi ba alkur"an kuma ki bani abinci na, iyalle ce tace shikenan ke da allah ai, zo kije ki kaimini nika, da har zatace bazata ba amma sai tayi tinanin yau garba zai dawo tsabb zai casata shisa ma ta kwammace gara ta kai.

Nikan ta dakko ta fito, daga wajen ba inda taje sai nika tana shiga taga wani dan masifan layi, tana shiga ta ture na kowa ta saka na nata a gaba, wata budurwa ce ta mike tafi indo girman jiki, tazo kanta tace'ke indo kinga dai na rigaki dan allah ki bari a nika min, indo bata kula ta ba, mai nikan yana gaam wanda yakeyi ta kwatsa nata akai, a lokacin aka nika mata sannan ta dakko tayo gaba.

Fitowarta ne yasa ta hango lantana ta dakko nika, cike da zafin nama ta karasa ta hankade nikan ya zube, kafin ma kayi wani kwakkwaran tinani taji saukar kulli a cikinta, danneta tayi tana kirba, sai huci take kamar wata macijiya, badai ran nan kin gudu ba, bara yanzu naje na samo wukar, tashi tayi ta shige gida, da kyar lantana ta mike ta fara kokarin ceton rayuwarta.

Koda ta fito bata ganta ba hakan yasa ta kara maj sai gidan su salame, salame ta juya baya tana wanke wanke taji saukar icce, juyowa tayi cike da masifa, idanunta ne suka sauka akan na indo, cike da jin tsoro yasa ta fara jan baya, amma ina kafin tai motsi indo ta cafki wuyanta ta fara dukanta,sai da ta jigata ta sannan ta fito tana huci.

Hango fadawan mai gari tayi, take ta kwala musu kira tace nasan ni kuke nema muje, basu san taya akai ta sani ba, dan haka suka tafi, tafiya sukeyi a kofar gidan mai gari ta tsaya, idanunta idanun malam iliya, ai tana ganinsa tasha jinin jikinta, dan haka ta tsaya tana raba ido.

Malam iliya ne yace "mai gari kayi sheda daga yau na sallami indo daga makaranta ta, bana buqatar ta kara zuwa domin indo ta zame min jaraba, ina iyawa da kowa amma banda indo, dan haka a nema mata wani malamin amma badai ni ba yallabai, mai gari ne ya kalli indo yace" kinji dai me ya fada miki ko, mai makon tayi magana sai murguda baki tayi tana kunkuni.

Koda ta koma gida garba ne zaune akan tabarmar kabar da iyalle ta shinfida masa, gefe ta samu ta rakube kamar wata ta kirki, kallonsa take ganinsa da litattafai, pen, biro, uniform, takalmi, zaro ido tayi tana fadin shikenan na shiga 3 yanzu kawu garba sai ya kaini wannan makarantaar, tinaninta ya katse da fadin"ke ki tabbatar yau baki fita ba domin gibe da sassafe zamu wuce zuwa dutsinma, saboda naga alamun lamarinki har da jahilci,tashi yayi ya tafi ya bar wajen.

TOFAH GA INDO ZA A BOARDING SCHOOL
ALLAH YASA AYI ABINDA YA DACE.



AISHATUL___HUMAIRAH
       ..... Labarin Indo .....
❤️💚❤️💚❤️💚❤️💚❤️💚❤️
    =Na=
   A'ishatu Bint Muhammad
           (MATAR UNCLE)
🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀
The Story of life childhood, Entertainment, And Love.

8🤩9

Tin fitar garba ba wanda tayiwa magana sai tashi tayi ta tafi dakinta, zama tayi tana tinanin meye mafita, domin batason wannan makarantar, kuma tasan saboda wannan gantalin nata ne yasa za a kaita, ganin bata da wata mafita ne yasa ta mike tace "bara naje na karasa aikina dan wallahi habi sai jikinki ya gaya maki, fitatayi tana tsallenta.

Direct gidan su dije taje, tana shiga ta hango suna cin nama, ai wani tsalle tayi ta sako hannu, ci takeyi amma fadi takeyi" amma tsabar rashin mutunci dije kuna cin wannan dadin shi ne kika ki kirana, yanzu da ni ce da tini na nemoki, shegiya kawai, "wai dije a ina kika samo wannan naman, dariya tayi tace a dakin lawan saboda kinsan aljanu sun masa duka.

Mikewa tayi tsamm ta nufi bakin kofar dakin,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login