Showing 30001 words to 33000 words out of 40600 words

Chapter 11 - AISHATUL_HUMAIRAH (Labarin Indo) HAUSA NOVEL

08 Nov 2024

4916

ya dauke, wani marayan kuka ta saki, cikin jin zafi tace" wallahi ranki ya dade ba ni bace ba, wannan aikin anas ne shi ne ya sakani nayi komai, kuma idan kinaso wallahi zan iya kiran sa kiji ta bakinsa, indo ce ta doke bakin take jini ya fara zuba tace "ke har ni zaki kirawa anas to kisani idan nayi niyya yanzu zaki gansa a gabanki, amma banason hakan, nafiso ki fara laushi ta inda da kanki zaki warware kullin da kikayiwa ahamd, karkarwa take har yanzu ga wani jini dake zuba daga bakinta, wata kara indo tayi tace "wuntsil ka zane min ita har sai ta kasa motsi,rufe bakinta kenan ta fara jin ruwan bulalu, tin tana ihu har bakin nata ya mutu.

Yau ma dai gasu nan sunyu jungun jugun a falo dika ba mai magana, mama ce tace farhana taso na aike ki, da toh ta amsa, mikewa tayi taje dakinta bata wani 'bata lokaci ba ta fito da veil sai mukullin car din motarta,banji dai me mama ta gaya mata ba, sakamakon daga dakin maman ta fito, ganin falon ba kowa hakan yasaka ta wucewa.

Bayan fitarta, wata murya ce take wani irin gunji mai matukar tsoratarwa, muryar ce ta fara magana, "ku fito, nace mutanen gidan nan ku fito ga indo tazo, gaba dayansu tattaruwa sukai a falo, daddy baya nan daga iyalle sai mama, muryarce tace" mama ki kwantar da hankalinki ina lafiya kuma na tabbatar da cewa yanzu falmata ta gane kuranta, afff mmaa ashe fa bakisan wacece falmata ba ko, to falmata ita ce wadda ta lalata rayuwar yaya ahmad, kuma nima ina daf da lalata ta ta rayuwar, sannan kuma ki dauki wannan, wani kulli ne ya fado daga sama tikk, ki turarashi, amma iya dakin yaya ahmad kawai, na barki lafiya mama, iyalle zan dawo amma sai na gama da lamarin falmata, wata guguwa ce ta tashi daga nan muryar bata kara magana ba.

Mama ce ta fashe da kuka tace "shi ke nan yanzu humaira haka zakiyi, allah ka dawo mana da humaira lafiyaah,ta ja maganar tana kuka, iyalle ce tace" ke karki damu kanki da allah, zata dawo nariga da nasan indo ciki da bai na fada miki zata dawo, kuma tinda na fadamiki zata dawo to ki tabbata zata dawo, ni na tabba akwai abinda ya rike indo da tini ta dawo, matsawa taui kusa da ita, sallamar da akayi ce yasa iyalle mikewa, tana mikar da salma.

FARHANA driving take amma sam hankalinta baya kan driving din, dik da cewar idanunta na kan titin amma sam hankalimta baya wajen road din, daidai inda danger ta nuna alamun tsayawa anan itama ta tsaya, sai a lokacin ta furzar da wata iska, sanann ta kalli gefenta, ba komai bane abinda ta gani, sai kabeer yanan mata wani shu'umin murmushi, a cikin firgici ta kalli danger anan taga ta bada hannu, da sauri ta figi motarta gudu take amma tana kallon motar kabeer ta mudubi, batayi aune ba taji ta bigi wata mota, kara ce ta karade wajen, a wannan dan takin motocin suka tashi yadda kasan a fikm din nan.

Abinda yayi matukar bani mamaki ba komai bane, illa hango farhana da nayi a gefen titi tana fitar da wani huci mai zafi, magana ta ji ance "ki kwantar da hankalinki aunty farhana, indo tana nan ba inda zataje, indai kabeer ne zan yi maganinsa nan da wani lokaci amma kuma ina so na dawo gida kafin nai maganinsa, daga haka bata kara jin magana ba.

Da sauri ta haye nafef ta hanyar gida, a lokacin ba wanda ya ganta, kallon jikinta tayi tana kalle kalle a can jikinta ta hango bag din ta data dakko da wayarta.

A can bangaren indo juyowa tayi ganin yadda jikin falmata yayi wani irin sawu na duka, tsugunnawa tayi ta kalleta sai kuma naga ta dunkule hannu, wata farar power ce ta bay yana, watsa mata tayi wata kara ta saki tana furxar da huci, indo ce tace "ki tabbata kin fadamin abinda kikayi wa ahmad ko kuma wallahi na kashe ki, cikin raunanniyar murya falmata tace" dan allah karki kasheni wallahi wallahi ni inada aure, sannan kuma yanzu haka ma mijina zai dawo, wata daroya tayi ta manya tace "auuh dama kina da aure amma kike wannan badakalar, har kika dauke min yaya ahmad di na,to wallahi bata karasa ba taji alamun za a turo dakin, gaba daya sanya dakin tayi yayi duhu, duhu mai tsanani.

Muhammad anas ne yana shigowa dakin yana kokarin kunna fitila,yaji ruwan duka a jikinsa, tin yana kururuwar kwatar kansa har yagaji ya saddakar ya fawwalawa ubangiji, a dai dai lokacin da dakin yayi haske, a wannan lokaci ne kuma dukan ya tsaya, wani huci ya furzar yana kallon indo, da tana zaune akan kujerar dakin, tana kallonsu, nuni tayi da hannunta, kafin kiftawa sai ga su a kulle, kallonsu tayi tare da mirmushin mugunta sai kuma ta bace battt, tana 'bacewa dakin ya zamana ya koma baki.


Da gudu ta shiga gida tana kwala kiran mama, a falo ta tarar da su, jamila ta gani yayar mahaifiyarsu hakan yasaka ta yin turus tana kallon ta, sai kuma ta tsugunna, kallo 1 zaka mata kasan a matukar tsorace take, mmama ce tace "farhana lafiya ina aiken da nai miki.

Karasawa tayi ta zube a jikinta tana kuka, cikin muryar kuka tace" mama wallahi da tini na mutu, mama kabeer ne, mama shi ne shi kabeer ne,iyalle ce ta dafa ta tace "to shi ne si yayi me, haba farhana kiyi magana mana, lumshe idanunta tayi, a wannan lokacin daddy ya shigo yana kwala kiram salma, ganinsu a zaune yasa shi kallon farhana yace" ke dama bake aka ce min kinyi accident ba, ba ke ce wacce aka turo min text din kin mutu ba.

Faehana ce ta fara girgiza kai, salma ce tace "dan allah kuyi min bayani kun barni a duhu, daddy ne yace" yanzun nan aka kirani cewa farhana tayi accident a kan babban titi, amma taya na ganki anan bayan ance min motar ta ko ne ko gawarki ba a ciro ba.

Jamila tin sadda ake wannan abin sai a lokacin ta saka baki tace "shi ke nan, ke yanzu taya akai kika dawo bayan an riga da ance cewa kin mutu, farhana ce ta fara basu labarin abinda ya faru da yadda akayi ta dawo,gaba dayansu tu'ajjibi suke.

Faehna ce ke sharce gumi tana kokarin mikewa, salma ce ta ce" allah gani gareka, allah ka sassauta min wannan jarabawar, allah ka bani ikon cinye wannan jarabawar, allah nagode maka, hawayen ta share, tare da daukar kullin maganin ta wuce.

Daddy ne yace "aunty yanzu na rasa ya zamuyi da wanan matsaltsalun da suke tahowa, ga farhana an fasa aurenta, shi wancan ba lafiya, dan mirmushi jamila tayi tace" karka damu abban ahmad, dama ai akwai Ramadan dan wajena dake kasar Poland 🇵🇱, ya nuna yana son farhana, amma ganin an saka mata rana da wani shi sa na bashi hakuri, amma yanzu idan da tana sonshi da sai kawai a hada auren, farhana ce ta kalli jamila, sai kuma ta sunkuyar da kanta.

Daddy ne yace "to farhana zaabi yana gareki, yadda kikace, farhna ce ta share hawayen face din ta tace" daddy ni bani da wani sauran magana dik abinda kuka yanke a kaina to zan karba, domin ku din iyayena ne nasan bazaku mini mummunan xabi ba.Wata kara suka jiyo, farhana ce ta zabura tace" wayyo yaya ahmad, gaba dayansu mikewa sukai suna kallon dakin nasa.
AISHATUL HUMAIRAH
       ..... Labarin Indo .....
❤️💚❤️💚❤️💚❤️💚❤️💚❤️
    =Na=
 AISHATU BINT MUHAMMAD
       (Matar Uncle)
          🤗 Zinariyar Nazari WRITERS association 🤗


🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀
The Story of life childhood,
Entertainment,
And Love.

NAZARI WRITERS ASSOCIATION


💮🌸SHAWARA KYAUTA🌸💮
Yar'uwa ki fahimci wannan, Akwai abokiyar Hira, akwai abokiyar SHAWARA, Akwai abokiyar sirri, kowace abokiyarki kisan matsayinta a gareki, Idan ba hakan ba, zakiyi Nadama, Ba kowace abokiyarki ce Mai nufinki da Alkhairi ba, sai kalilan daga cikin kawayenki, Amman Idan Zaki bi shawara tawa yar'uwa, ki rike Mahaifiyar ki wajen Faɗa Mata sirrinki da wadansu shawarwari na Rayuwar ki, Baga kawayenki ba Zaki tallata kanki ba, kin fahimci Karatun?

46, 🌿 47

A dakin suka tsaya sukai carko carko, farhana ce tai kokarin furta "mama lafiya na jiyo ihun yaya ahmad, mama ce da idanunta sukai jajur tace" eaa magani nake shafa masa farhana, bansan taya akai ma wannan sawun dukan ya bayyana a jikinsa, amma dai kinga da sauki, gaba daya kallon gadon bayan nasa sukai, wasu irin sawu ne karkace sawun dorina, aa har yafi na dorina, kallonsa suke, dagowa yayi yana kallonsu kamar wanda aka mintsina, sai kuma ya shige blanket, farhana ce ta karasa wajensa ta taba sa, wani irin bugu yayi mata da sai da ta furta"wayyo mama.


Indo ce tace kun kyauta, kunga kun zalince sa kuna tinanin shikenan kunci banza ko, a tinaninku ba wanda zai daukar masa fansa, wata daroya tayi tace "kai dai Muhammad anas anyi dan iska, dan iskanci ka rasa wanda zaka zalunta ka cuta sai abokinka, saboda son abin duniya ko, zaku je ku girbi abinda kuka shuka, amma ku sani ba a wannan nahiyar ba, haka zalika kuma ku tabbata sai kun dauki hukuncin abinda kukayi masa, wani kwakkwaran tafi tayi sai ga hijjah an daureta da wata sarka.

Da mamaki falmata tace "ke hijjah me ya sameki, me ya kawo ki nan, wata dariya ce again ta kara tashi, indo tace" ai bari ta ita ma bazaki mamaki ba sai na bayyanar miki da shugan iskancinki ba, wanda kukai kulla kulla wajen kun lalata rayuwar yayana, kuma wanda nakeso, wani tafin tayi again sai ga bokan falmata a kukkule, jikinsa dik sawun duka, kowa na falon zaro ido yayi yace "nashiga 3 dubun mu ta cika.

Indo ce tace" shiiit silent bad guys, kusani bazaku kara dawowa wannan duniyar ba, har sai na tabbatar da cewa kun girbi abinda kuka shuka, wani abu ta fara yi can kuma tace "wuntsil, tsanlin kuzo da tawagarku, ku debe min su ku kaisu inda ya kamata, sannan kuma ku tabbatar kun wahalar da su ku bace min da gani.

Mama ce take kallon ahmad din da akaro na farko yafara magana, cikin wata sarkakkiyar murya yace "aishatul humaira, da mamaki suke binsa da kallo, kowa na dakin iyalle tace" ahmad kana lafiya, bai kalleta ba yaci gaba da maganarsa,ba wanda ya kulasa, farhana ce ta mike ta fita zuwa kitchen, food flask ta bude tare da debo masa hadadadden dambun cou cous wanda yasha vegetables.

Fitowarta tayi dakin ahmad, matsawa tayi tana kokarin basa abaki amma ture kwanon yayi hade da daga idanunsa, ganin haka yasa mama karba amma ita ma din kin karba yayi, wayar mama ce ke kara, ganin an saka daddy yasata mikeww, domin tasan yana part din sa, iyalle dama ta riga data fita, farhana ce ta rage, ganin ba kowa yasata ajiye plate din ta fice.

Shigiwa sukai tin daga falon gidan daddy ke kiran salma, yayin da salma take daki ta rasa me ke damunta ta jiyo kiran mijinta, tin da taji wannan kiran ta fito da hanzari, turuss tayi ganinsa da indo, indo da gudu t akarasa ta rungume salma, da murmushi a face din su, farhana ce da iyalle suka fito suna murnar ganin indo, iyalle ce ta kasa jurewa tace "ke taya akai kika dawo kuma, kai yaron nan kodai su suka baka ita, alhaji ali ne ya zauna sannan yace" ku zauna.


Kowannensu raba ido yakeyi sakamakon ganin indo, indo ce ta karasa kusa da iyalle tace "dan allah iyalle menene ya faru da ni, meyasa nakejin kamar ba ni bace, dafa kanta iyalle tayi tace" aa aishatu ba komai me kikaji, daddy ne yace "aisha jeki ahmad yana jiranki, juyowa tayi tana murmushi tace" laaa yaya ahmad ya dawo kenan, mama yana ina, salma ce tai murmushi a takaice tace "yana daki maza kije,da gudu tai hanyar dakin.

Daddy ne yace "nasan ranku fall yake da tambayoyi, abinda nakeso kusani shi ne, nima na hangi humaira ne a gefen titi, wannan gefen titin na bayan mu anan na ganta a tsaye, nayi nayi ta fada min menene ya faru amma tace min aa ta manta komai, ba abinda zata iya tunawa, domin ita ta manta komai.

Iyalle xe tace "yoo ba dole ta manta komai ba, wallahi yarinyar nan aljanun kanta ne ke dawainiya da ita ya kamata a mata magani asan me za ayi.

Salma ce tace" baba iyalle ai koma menene humaira ta zame mana wani jigo a rayuwarmu, kuma a haka ta ceci tayuwar farhana, daga sharrun kabeer, sannan ina da san ran tabbas ahmad zai warke daga wannan mantawar da kwakwalwarsa tayi, gaba daya dakin jinjina kai sukai.

Daddy ne yace "farhana kina ganin zabin yamiki, idan kuma kina da wanda kikeso sai kiyi magana, girgixa kai tayi wayarta ce tai kara, ganin sunan kan screen yasata dagawa, banji me aka ce ba, sai ji nai tace" yanzu ok gani nan zuwa, kallon daddy tayi tace "daddy so nake na fita an kawo wani asibiti, yayi accident kuma dole sai naje.

Daddy ne yace" farhana aa kin manta me yafaru ne, hawaye ta share tace "daddy ka barni na fita dan allah, salma ce tace" to yanxu farhnaa idan aka barki kika fita, farhnaa ce ta katse ta tace "dan allah mama ku barni na fita, daddy ne yace" shikenan amma karki dau mintuna, wani key ya xaro daga aljihu yace "karbi wannan ki tafi da ita, kallon sa tayi tace" daddy wannan ita ce fa babbar motarka, kuma zaka bani, murmushi yayi yace "karki damu amma kuma ai tafi tsaro ko, karba tai tare da musu sallama ta huce.


Indo ce ta fito tace "mama yaya ahmad fa yunwa yakeji, kallonta dika sukayi ganin ahmad rike da hannunta yasa mama fadin," zaki iya zuwa ki debar masa ba yadda ban ba akan yaci amma ya ture abincin, indo ce ta yamutsa fuska tace "mama shikenan sai kuma ta kalli ahmad tace" wallahi yaya ahmad kana cin abinci kalleka fa, anya kanaso ka warke, abin mamaki murmushi yayi yaci gaba da binta, kitchen suka shiga.

A dining na kitchen din tai feeding nasa tanayi tana basa labari, dik da ba fahimta yake ba, amma yana jin dadin kallonta, janyo sa tayi suka dawo falo, tana kallon su mama suna hira bata ce musu kala ba ta wuce, sai da ta zaunar da ahmad sannan ita ma ta zauna, tashar mbc3 ta kai musu suka fara kalla, yayin da daddy da mama ke kallonsu cike da sha'awa, iyalle ce ta katse shirun da cewa "ke gidanku dan ubanki ki kai mana mutane kinzo kin kunna mana wadan nan masu suffar aljanun, iyalle ta kalla tace" wallahi iyalle idan kina zaginsu da daddare suke zuwa, suyi ta zane ka, kwalalo ido tayi tana raba ido kamar na shirwa, ita kuwa taci gaba da kallonta


. AISHATUL HUMAIRAH
       ..... Labarin Indo .....
❤️💚❤️💚❤️💚❤️💚❤️💚❤️
    =Na=
 AISHATU BINT MUHAMMAD
       (Matar Uncle)
          🤗 Zinariyar Nazari WRITERS association 🤗


🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀
The Story of life childhood,
Entertainment,
And Love.

NAZARI WRITERS ASSOCIATION


💮48🌸49

Farhana ce ta shiga room din, sanye da rigar ta ta lab Court sai face mask a face din ta, sai wata hand globe, shigarta ta fara kallon mara lafiyar, wata nurse ta kalla tace "tsawon mint nawa ya dauka anan, nurse din ce tace" doctor a kalla zai dau mint 50, girgiza kai tayi tace"wannan sai dai akaisa ga theater room, domin ciwukan jikinsa sun kazanta, kalla ko fuskarsa ba a iya tantancewa,umarni ta bada take aka wuce da shi.

Mama ce tace "dan allah indo ki samu ya shirya, xamuje gidan malam daganan kuma zamuje asibiti, domin a kara duba lafiyarsa, doctor yace mudawo yau, dan murmushi tayi tace" to mama zakuje dani, matsowa tayi ta dafa kanta tace "ba dole muje da ke ba shalele, maza kishirya sa, kema sai ki shirya ko.

Bayan wasu mintuna⏱️⏰

Tafiya suke, ahmad ne da indo a baya sai hajiya iyalle a kusa da su, daddy na driving ita kuma salma na gidan gaba, kowa yayi shiru idan banda surutun indo da takewa ahmad.

Waya ce take ruri, saurin dauka mama tayi, ganin sunan farhan ne yasata kin dagawa, katsewa tayi hakan yasata sakata a silent.

Dai dai kofar gidan malam suka tsaya, tin a bakin gidan suka ga dandazon mutane, sauka daddy yayi, iyalle ta kalli salma tace "to salma allah ubangiji yasa dai lafiya, mama ce ta amsa da" ameen baba.

Dawowar alhaji cikin mota yasa su suka fara zubo masa tambaya, bai kula kowa ba ya fara driving, direct hospital suka nufa,office din doctors ex anan suke waiting, shigowar dr ex yasaka su fara gaisawa, kama hannun ahmad yayi da niyyar su tafi, amma sam yaki mikewa, magana suka fara amma yaki kula kowa, hakan yasa mama tace "dan allah humaira ki masa magana yaje, tinda naga ba wanda yake jin maganarsa sai ke.

Kallon ahmad tayi tace" yaya ahmad tashi kaje kaji, idan muka koma gida zan siya maka katon teddy, na dinga goya maka shi kullun, dariya yayi sannnan ya mike, tafiya sukayi da dr ex.

Mama ce tace "wai daddy ahmad menene ya faru, daddy ne yace" a ina kenan, amsa ta basa a gidan malam, sosai kai yayi yace "dama allah yayi wa malam rasuwa ne, yau kusan kwana 2, shiyasa nayi ta kiran number sa bata shiga, gaba daya kowa na binsa da addua a dakin, kowa na jimamin mutuwar tasa.

Bayan awa 2 ne ta share gumin face din ta, sannan ta kalli fuskar mara lafiya, ba abinda ya subuce mata illa da tace "inalillahi wa inna ilaihi raji'un, gaba daya nurses din kallinta suke, farhana  ce tace" wannan ba kabeer bane dan gidan alhaji sani, gaba daya kowa sai a lokacin ya lura dashi, ba ta kara magana ba ta fito daga threater room din, kallon iyalinsa tayi sai kuma tai gaba bata tsaya ba.

Nurses din ne suka fito da shi domin kaisa dakin kulawa, tarar su sukai, hajiya dina ce tace "ya jikin nasa me yake damunsa, ba wanda ya kulata, ganin ta damesu yasa daya mai fada tace" ke dan allah karki dame mu meyasa baku bi bayan dr din ba, shi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login