Showing 21001 words to 24000 words out of 40600 words
tace "amma yaya kabeer bai kyauta min ba shi ne bai fadamin dazu ba, wata zuciyar kuma tace" kika sani ko shima bai sani ba.
Abu na 2 kuma ina mai sanar daku cewa, farhaan zai tafi kasar india karatu domin na riga dana gama komai sai tafiyarsa ta rage nan da sati mai zuwa, fuskar farrhan cike da farinciki yake cewa alhamdulillah allah nagode ma dakasa daddy ya yadda da tafiya ta.
Sai abu na 3 abinda ya taramu anan kenan, akan ahmad, kallon ahmad yayi yace "ahmad nasan ai kasan yayana nura, to humaira 'yar wajensa ce, tin bayan rasuwar mahaifiyarta muka yanke hukunci, cewa zamu hadaku aure, take zuciyar ahmad ta fara bugawa, yanaso yayi magana amma ya kasa, dan haka a ranar jumu' ar data huce anan ne muka je can wakaza, aka dauro aurenku da humaira, da sauri ya kalli daddy.
Ahmad ya kayi shiru, fadin mama kenan, bai ce komai ba sai yace to daddy allah yasa hakan shi ne alkhairy, daga haka daddy ya rufe taro da addu'a.
A bangaren ahmad tashi yayi amma aam zuciyar sa taki karbar wannan auren, kuma wai auren 'yar kauye yarinyar da ko hankali bai yadda tana da shi ba, kuma a haka ake tinanin ya zauna da ita, gata ma yarinya inaa gaskia bazan iya ba abinda ya furta kenan ya tashi ya fara hada kayansa, wayarsa ce tai kara saurin kallin kiran wayar nayi naga ansaka, my falmata da alamar heart kamar dai wannan ❤️, tsaki yaja har sai da ta katse sannan ta kara biyowa sai a lokaci yaji kawai kara ya daga.
A kunnensa ya kara yace "hello banji me aka ce ba, sai ji nayi yace kawai zanzo gobe zamuyi magana ne dake, ajiye wayar yayi ya nufi toilet, sai da ya cika jacuzzi da ruwa sannan ya shiga ya kwanata,tinani take yana surutai, why na dawo, meyasa a tsarina ni iya mace 1 nakeson na aura amma meyasa suka aura min humaira, yarinyar da ta taso a kauye, ni ba ita nakeso ba, gata yarinyar "yar karama bawata babba ba, da babba ce da nayi manage a haka da banasonta amma sun riga sun aura min ita.
Rasa mafita yayi dan haka yasashi fitowa.
WASHE GARI
Tin safe humaira bata fito, yayin da bangaren ahmad ya kwana bai bacci ba yana tinanin mafita, gaba daya idanunsa sun kada sunyi jawur kamar gauta,ganin bashi da mafita yasa ya kwanta ya runtsa idanunsa, yayin da zuciyar sa take yi masa zafi.
Kowa ya fito yana break banda ahmad"daddy ne yace ina yake, mama ce ta bashi amsa, daga haka suka ci gaba da cin abincinsu.
BAYAN SATI DAYA
Ahmad ne yafito yana sauri, farhana ce ta gaishe shi,kallonta yayi yace yawwa farhana dan allah ki fadawa mama na fita an kirani daga wajen aiki dan haka zan tafi zan iya dawowa zuwa nan da dare, daga haka ya fice bai jira amsarta ba.
Humaira ce ta fito daga daki da littafi a hannunta, kusa da farhana ta zauna tace "dan allah aunty farhana kinga wajen nan zaki gyara min, naga kamar nayi daidai amma kuma zuciya ta tace banyi daidai ba, farhana ce ta dara tace" ai kinyi daidai humaira, sai dai kawai ki jira uncle james yazo sai ya kara tabbatar miki,tashi tayi ta tafi daki sai kuma ta juyo tace aunty farhana wai ina yaya Ahmed, kallon ta ta kuma yi sai tace "yanzu ya fita amma kuma yace bazai dade ba.
Maimakon yayi hanyar office dinsu sai naga ya chanja akalar tafiyar, kofar wani gida ya tsaya dan karami ne mai gate milk, waya ya fito da ita ya kara a kunne, hello kifito gani nazo daga haka ya katse ya dora kansa a kan sitiyari, tinani iri2 ne ke ziyartar zuciyarsa amma ya rasa wanne zai dauka.
Fitowa tayi sanye da wasu arnan kaya, wasu riga da wando ne gasu sharara ga kuma sun wani uban kamata, dan kana ganin shatin pant dinta, daga sama kuwa ba abinda baka gani na daga dukiyar fulaninta, kanta ba dankwali sai wani gashin doki data baza, tana zuwa ta shiga motar, ba tare da wata fargaba ba ta fada kansa, tace "beb yau najika wani iri me ya faru, lumshe idanu yayi yace ina cikin matsala my falmata, narasa yadda zanyi, tashi tayi sai kuma tace me ya faru, bai boye mata komai ya fada mata.
Shafa face dinsa tayi tace "karka damu beb ka barmin komai a hannuna zan ji da lamarin nan, kasan yanzu dai muje ciki kasamu ko lemo ne kassha, bai mata magana ya fara kokarin fitowa, murmushin mugunta tayi tace" ai kazo hannu ahmad wallahi sai kayi dana sanin yi mani wulakanci.
Jan hannunsa tayi suka shiga cikin gidan, babban falo ta kaisa falon yaji komai na alfarma, ajiyesa tayi ita kuma ta shige kitchen, acan ne ta dakko lemo bayan ta balla kwayar magana a ciki, ajiye masa tayi a gabansa, batare da wani tinani ba ya fara sha, bayan mint 5 ne ya fara jin yanayinsa yana sauyawa, kimai ya fara bace masa, daga nan kuma bai kara tina komai ba.
Wayarta ta dauka, wata number na gani ansaka malam,kira tayi yaba daga wa tace "malam akwai matsala akwai matsala, an riga da an daura masa aure da wata, kuma ni har yanzu ban gama dashi ba, ban ji me aka ce ba, sai naga tayi murmushi tace to shikenan ba matsala.
Ajiye wayar tayi ta fara kokarin cire kayan jikinta, lokaci guda ta dawo daga ita sai pant da bra, nuni tayi da hannunta a lokacin ahmad dayake kwance ya tashi, nuni tayi masa da wani daki, sai da ya shiga sannan ta bisa a baya, tana shiga yadda itama take haka shi ma ya koma daga shi sai boxer, kofar ta bugo da karfi take ta bigemin fuska ban samu damar shiga ba.
Uncle james ne sai indo a gefe tana masa home work din daya bata, daga nan yace mata "humaira ina zuwa, falo ya shigo ya hango mama a zaune, gaisawa suka karayi.
Gyaran murya yayi yace" hajiya dama ya kamata a maidata makaranta domin na mata lesson kwana 5 kuma na tabbatar da cewa tana kokari, sannan kuma idan da dama hajiya a taimaka a sakata a makaranta ta, murmushi salma tayi tace "to james karka damu ka fara kokarin yi mata register zuwa nan da wani week din sai ta fara zuwa, james ne yayi murmushi yace" aa hajiya gobe tuesday kawai ta fara zuwa goben, mama ce tace "alalh ya kaimu james wato ka dage dai sai taje, sallama sukayi bai dade da fita humaira ta shigo, ajiye litattafan tayi tace" mama wai ya farhaan har yanzu bai kira ba.
Mama ce tace "aa humaira yanzu muka gama waya dashi har yace min ma na gaisheki, kuma yace idan ya dawo zai taho miki da gift din ki, dan murmushi tayi tace" to mama bara naje nai wanka, daga nan tai dakinta tana tinanin yaya ahmad.
AISHATUL___HUMAIRAH
..... Labarin Indo .....
❤️💚❤️💚❤️💚❤️💚❤️💚❤️
=Na=
AISHATU BINT MUHAMMAD
(Matar Uncle)
🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀
The Story of life childhood,
Entertainment,
And Love.
DASHEN ALLAH WRITERS ASSOCIATION
30🍂31
Sai wajen 9 ya dawo falon ba kowa dan haka ya shige room din mama, shiga yayi ya tarar tana sallah, tsayawa yayi ta idar sannan yace "mama dama gobe nakeson tafiya domin an min neman gaggawa a wajen aikina, kuma dama, mama ce ta katsesa tace" ehh inajinka sai me kuma, dama haka zance indo ta zauna anan idan na dawo sai mu tare saboda bazaiyiyu na tafi da ita ba, mama ce tai murmushi tace to allah ya kaimu, ka samu mahaifinka ka fada masa, cike da jin dadi ya mike yana fara'a, abinda ya fadawa mama haka ya fadawa daddy, dan haka tin a daren ranar ya tattara yanasa yanasa.
Indo kuwa yanzu an fara chanjawa dan kuwa cikin 'yan satittikan nan tayi kiba tagi fresh abinta, idan ka ganta ma in baka santa ba zakace ba indo bace, yau ma dai kamar kukkun kallo take a television din dakin nata, jin cikinta na kukan yunwa yasata fitowa, a falo ta tarar dashi yana waya, tsayawa tayi tana kallonsa, sakamakon gani tayi yana ta fara'a shisa ta tsaya kawai tana kallonsa, kamar haka aka ce juyo, juyowa yayi yaga tana kallonsa, katse wayar yayi yace "ke zo nan, karasawa tati tana fara'a.
Wayarsa yaci gaba dayi ga wata uwar yunwa datake ji, gashi yayi banza da ita, amma kuma tasan halinsa idan ya ta tashi zai iya cewa su kwana anan, a hankali ta fara rike masa kafa, cijin yan seconni ya sakar mata wani rankwashi, kara ta saki sai ga hawaye, yaya dan allah ka kyaleni wallahi yunwa nakeji, ganin tana hawaye yasa shi sakkowa, yace ki daina kuka ko kin manta mai na gaya miki a baya, gogewa tayi tace to na tashi natafi ko, aa ya bata amsa sai kin fadamin gaskia, wai so na kike, kasa magana tayi ganin haka yasa shi fadin "ko so na kike ki daina wannan mafarkin domin ni ba sanki nakeba, kuma dik da haka ma banga zan iya sonki ba ko nan gaba dan haka tashi ki huce karna kuskura kuma naji kin fadawa mama.
Kitchen ta nufa ymtaba shiga ta zube a kasa ta fashe da kuka, ba abinda taje tinawa sai kalaman yaya ahmad wai baya santa, kuma ko nan gaba kartai tinanin zai sota, inalillahi wa inna ilaihi raji'un ni indo ina zan ska akaina, na kawo kai na inda ba'a sona, tinda nake a duniya ba wanda yace baya so na sai shi,to ya zanyi kuma farhana tace shi aka auramin, tayaya zama zaiyu bayan yace baya sona, nikuma ga wani sonsa da kulkun ke karuwa a zuciyata.
Sai da tayi mai isarta sannan ta tashi ji tayi yunwar ta daina jinta, tashi tayi ta fara kokarin komawa dakin ta, a can din ma bata iya kallin ba sai kashe fitilan tayi da sauran kayan ta kwanta akan gado domin tayi bacci amma ya kasa zuwa, haka ta kwana sai dai bacci barawo ne ya saceta.
Washe gari tin karfe 6 mama ta shigo ta tasheta, amma ga mamakinta gani tayi ta har ta fito dafmga wanka, mama ce tai murmushi tace "auhh humairah har kin tashi kenan, eaa mama dama yanzu zanzo na gaishe ki, kuma da naga uncle james yace" na shirya yau zan fara zuwa makaranta shisa na tashi.
Mama ce tace yawwa to fito ma har kwayi sallama da mijin naki dan yace min da wuri zai huce, na tabbata da cewa yanzu zaki gansa, mama ce ta fita yayin da kirjin indo sai dukan 9² yake ta rasa me ke mata dadi, zama tayi ta shafa lotion, sai yar hoda dataga farhana na shafawa ita ma ita ta shafa, sai kuma lipstick, riga da siket ta saka snnan ta fara shirun fitowa bayan ta yafa dan kwanlin.
Hijjah dan allah kinaji na, ki kular min da gidan nan sannan kuma ki karbi wannan takardar ki tabbatar bayan tafiyar mu da awa 5 ki kaita gidan su ahmad, wadda aka kira da hijjah ce tace "falmata wai me ke damunki, ki. Kyale dan mutane mana naga dai kin tatsa ko, ke dallah rufemin baki ai wallahi sai na gama dashi sai na cinye dukiyarsa, sanan zan kyalesa, amma na kyalesa yanzu mai naci, dan haka ki abinda nace miki, dawowarmu sai nan da shekaru masu yawa, daga haka kuwa ta ajiye takarda, ta shiga dakinta ta janyo akwatinta.
Sallama yayi musu yayin da dik sai addua suke masa, harda indo data makale a gefen kofa, farhana ce taja hannunta tace ke dallah kije mana ki rakasa, ba yadda ta iya ta bisa a baya, jin kamar ana binsa ne yasa ya dakata ya juya, kallonta yayi yace to ke kuma menene, kike wani bina kamar jela zaki huce ki koma sai na tattakaki, bata iya magana ba, dik rashin kunyar indo da fitsararta dole ta kyalesa, juyawa tayi amma take taji hawaye na bin kuncinta,zama tayi a wajen ta fara rera kuka, yayin da shi gogan ko a jikinsa ya kada kansa ya kara gaba.
Gidan falmata ya biya daga nan ya dauketa suka tafi, tafiya suke daidai airport suka tsaya daga nan suka shiga bayan an tantacesu suka shiga sai kasar THAILAND 🇹🇭.
AISHATUL HUMAIRAH
..... Labarin Indo .....
❤️💚❤️💚❤️💚❤️💚❤️💚❤️
=Na=
AISHATU BINT MUHAMMAD
(Matar Uncle)
🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀
The Story of life childhood,
Entertainment,
And Love.
DASHEN ALLAH WRITERS ASSOCIATION
32💗💗33
BAYAN WATA 3
A wannan lokacin komai ya chanjaA bangaren farhana an kawo lefe na gani na fada na 'yayan manya masu ji da kudi, shirye shiryen biki ya kankama, ga kuma a bangare guda indo ke fama da karatun exam,dik da cewar ba katatun take ba, kullun suna tare da farhana.
Mama ce tace "daddy nifa lamarin ahmad ya fara bani tsoro, taya za a ce yau fa wata 3 amma ba ahmad ba alamunsa, ko an kira wayarsa baya dagawa, anya kuwa lafiya.
Daddy ya ya ce" karki damu dama ai yana irin haka idan aiki yayi musu yawa amma insha allah ai yana cikin aminci.
Yawwa kunyi waya da farhan, mama ce tace "eaa dazu nan ma muka gama, yake cemin bazai samu dawowa ba saboda karatu sun masa yawa, daddy ne yace" shikenan ai allah ya kyauta.
Humaira ce ta shigo sanye da kayan islamiyya tasa wani nikab, tsugunnawa tayi ta gaishe da mummy, sannan tace mama zan je makaranta dama shi ne nace bara nazo na fada miki, murmushi mama tayi tace "to humaira ki kula kinji banda kule kule saboda kinsan da aurenki ai, dan karamin murmushi ta kakalo dan ma baka ganin face din ta tace" to mama daddy atashi lafiya, mama natafi.
Har ta tafi ta dawo, mama yaushe iyalle zatazo, dariya mama tayi tace "ai zatazo yau ma daddy umya tura mota taje ta taho dasu, da murnan ta tafi tana fara'ah.
Tsakiyar falon gaba daya mutane ne kawayen farhana da 'yan uwansu, wata ce mai suna amira tace" humaira kar dai ace makarantar zaki tafi, murmushi tayi ta dage nikab din, masha allah allah mai halitta, ga hanci, ga ido gaskia allah yayi halitta a wajen nan, domin wani hatsabibin kyau indo tayi, abinka da fara sai ta kara zama gau kamar zabiya.
Aunty ameera dayake zan bada hadda ne shisa nake sauri, amma daga yau na miki alkawari bazan kara zuwa ba sai ansha biki, ameera murmushi tayi tace "yawwa yar kanwarmu kuma matar ahmad.
Saurin juyawa tayi tana kokarin boye hawayen idanunta, saurin sakin nikab din tayi ta fita zuwa farfajiya, musa driver ta gani yana hangota yayi wajen mota, bude mata zaiyi, kallonsa tayi tace" wai musa bana ce maka ka dai na bude min moto bane banaso wallahi ka barni na dinga budewa, musa ne yace "aa bakomai humaira girmanki ne, ki bari na dinga bude miki kinji.
Basu dade ba suka fita, tafiya suke ba wanda yace da wani komai, indo ce ta fada duniyar tinani, wata 3 baya, yayin da take wasa a garden, wata ash din mota ce ta Parker a bakin gate, kallon wani hannu tayi ya miko takarda sannan kuma yaja motar ya tsaya, ganin haka yasa indo tasha jinin jikinta, wajen idi mai gadi taje tace "wannan fa amsa ya bata cewa wajen hajiya za a kai, dan murmjshi tayi tace" kawo na kai mata, kai tsaye ya mika mata, maimakon ta kaiwa mama sai ta huce zuwa dakinta.
Maganar musa deiver ne yace "humaira mun iso sai da ya maimaita mata sau 3 sannan tai fiegigit ta ce, to musa nagode amma yau sai wajen 6 zaka zo saboda zan tsaya karatu, daga haka ta sauka ta shiga makarantar.
Sai wajen magariba musa driver ya dawo daukarta, a tsaye ya ganta cikin kawayenta na makarantar, hango musa ne yasa tayi musu sai anjima ta tafi.
Gidan ta shigo maimakon tabi ta kofar dazata sadata da falo sai tabi ta baya ta shige dakin ta tare da saka lock,ajiye jakar islamiyyar tayi ta kwanta tana sauke ajiyar zuciya, rintse idanunta tayi take ta fara tinanin mafarkin da take yi tin daga lokacin ds yays ahmad ya tafi, baya da 20 mint ta mike ta shiga toilet, sai da tai sallar magariba sannan ta fito daga dakin nata.
Falon ba kowa dik yawanci sun tafi sai gobe kuma domin gibe za'a fara gabatar da event din da aka shirya, zama tayi a daya a kujerun dake falon,rasa mai zatayi yasa ta tafi room din mama, knocking take amma shiru kakeji jin shirun yayi yawa yasa ta shiga amma bakowa.
Fitowa tayi ta shiga dakin farhana ita ta tarar da su ameera a zaune, gefen ved ta zauna tace "aunty farhana ina mama, murmushi farhana tayi mata tace" ai mama sun tafi gidan hajiya magajiya amma bansan dai me zasui ba a can din, amma ko ma mene yanzu zata dawo, ameera xe ta katse su tana dafa humaira tace "lafiya kike ko sis, dan murmushi ta kakalo iya saman fuska tace" is ok ba wani abin damuwa, bara naje naci abinci.
Tana fita wata kawar farhana tace "wai ita wannan bata zama a cikin mutane ne, ki duba fa ki gani, ameera ce tace" aa tana zama mana kuma da kike abin nan humaira badai hira ba.
Farhana ce tace "yawwa dama amira inaso mu tattauna kan lamarin hummy, da hummy tana da surutu gashi kuma yanzu ta daina, dik wani abu nada na halayyar humaira wallahi ta chanja, tamkar ba humairar dana sani ba, yanzu batason shiga mutane bata surutu, magana da kyar takeyi kamar an sakata. Ameera ce ta numfasa tace "farhana ai dama komai yana chanjawa, duba da yadda hummy take da, yanzu zakiga tayi hankali gaba daya girma ne yazo mata ke ki duba ki gani yadda ta nutsu mana dan haja ki bar wannan maganar.
Ko da ta fito kitchen tayi, abinci ta diba dik da ba wani na kirki taci ba ta rufe ta ajiye, dakinta ta shiga ta rufe, lokaci guda ta fara kuka, tin tanayi a hankali har ya fara fita yana damun su farhana, da sauri suka fito suna knocking door din, amma maimakon ihun ya ragu karuwa yayi, cikin wata kakkausar murya akace "ku bace daga nan idan ba haka ba