Showing 39001 words to 40600 words out of 40600 words
sakamakon grade na ya gaza, a haka mukaci gaba da rayuwa, na tsani naga ahmad yana dariya a duniya na tsane sa matukar tsana, hakan yasa na fara shirya abinda nake ganin zai fissheni domin na samu na lalata rayuwarsa.
Haka naci gaba da hada hanyoyi har dai na samu falmata, ita kuma ta samu hijjah, daga nan muka tsara komai ta yadda na samo musu gashin kan ahmad da rigarsa, kamar yadda malam ya buqata mu ka kai masa, da farko abin sai yaki aiki sakamakon ahmad ya kasance mai riko da addini amma daga baya sai nayi yadda nayi na dhiga jikinsa na rabasa da wannan abin, amma kuma sai nakasa, boka ne ya bamu shawarar cewa bazai taba aiki ba sai na je dashi gidan gala inda ake hada maza da mata suna rawa watto dai clubs.
Wata ranar sunday da daddare na samu na jasa zuwa clubs anan sai da nayi yadda nayi na dirka masa giya yana sha yana lumshe idanu, kafin wani dan lokaci ya fita daga hayyacinsa.
Nikam ganin haka yasa yda na daukes na kaisa wajen malam bansan abinda malam yayi masa savoda fitowa nayi sai wajen da nai awa 2 sannan ya kira ni na koma.
Cike da takaici ya zubar da hawaye yace"to ai sai ku fada min uban me kuka min, amma Muhammad anas allah ubangiji ya tsine maka allah ya isa tsakani na da kai.
Daddy ne yaxe "to kai kuma boka munajin ka sai me, bude baki yayi yace" wallahi nidai a sanda ya kawo mini shi din, na yi hade hade a inda nasamu na huda jikinsa na zuba masa wani ruwan magani, a lokacin ba abinda zaiji yana sha'awa kamar ace yana tare da vudurwarsa, amma gaskia karkai tinanin wani abu, iya dai hakan nai maka, daga nan kuma Muhammad anas ya dauke ka kuka fita.
Muhammad anas ne yace "a wannan lokacin direct gidan falmata na nufa, muna can nan muka kwana, a safiyar ranar bai tashi ba, saboda hadin da boka yayi masa, tashinsa ya ji sa a wajen falmata, daga nan yace ba inda zashi, da nace masa gida fa, sai yace mini zai ce musu yayi tafia.
Haka suka zauna falmata ce tace "ni kuma gaskia ina sha'awar ahmad a dik lokacin danagansa a wajena, amma da nayi kokarin rabarsa to tabbas za a samu matsala, domin boka zai ce aikin mu zai lalace.
Wata rana da nayi niyya aikata abinda nake tinani ne a wannan ranar boka yayi niyyar illata ni amma nasha da kyar saboda shigowar muhammad anas.
A wannan ranar ban kara kwana a Nigeria ba daga nan muka daga sai Thailand, a wanann lokacin ne na bawa hijjah wannan paper domin kar ai tinanin zai dawo, amma dayake allah yayi bazaku gani ba sai indota kwace.
A can kuwa hospital na kaisa a inda akai ta basa magungunan toshewar kwakwalwa, da farko baya masa aiki amma daga baya ya dawo yana aiki sosai, bayyanar humaira ita ce ta wargaza komai har yazo ga tonan asirin mu.
Hamma take jerawa, kallon mutanen falon tayi cikin muryarta mai dadin sauraro tace "mama wai menene ya faru, mama ce tai murmushi tace" taho nan humairah taho kinji, zama tayi tace"wai mama menene abunda ya faru kinji kaina mama kamar ya fita, su kuma wadan nan din suwaye.
Hijjah,boka,falmata da muhammad anas kowa a tsoraxe yake, kallon indo suke sai kuma suka sunkuyar da kai, daddy ne yace "humaira je ki shirya kizo yaya farhaan ya kaiki gidan auntynki, da murna tace dan allah daddy, saurin mikewa tayi tana murmushi.
Tafiyarta yasa daddy kallon ahmad da mama yace" to ahmad hujunci yana gareka, dan jinjina kai yayi yace "to nibdaddy me zan ce musu kawai su tashi su tafi idan ma sun cuceni sun sani idan basu cuceni ba ma sunfi kowa sani, amma daddy wallahi bazan taba yafe musu ba, dan haka ku tashi kubar gidan nan, tashi yayi ya dauki diaryn indo ya yi dakinsa.
Farhaan da kansa ya kad'a su suka tafi suna tafe suna bada hakuri amma kuma bai sauraresu ba
Mama ce ta daga hannu sama tana jera addu'o'i samun nasara, a fili ta furta "allah na gode maka da ka bani ikon cinye wannan jarabar alhamdulillah, tsugunnawa tayi ta dauki Paper sannan ta koma ta zauna, daddy ne yace" wai menene a takardar indo ce ta fito hakan yasa ta basar da zancen paper.
Indo ce tace "yawwa mama na shirya daga nan har gidan aunty farhana, to kije ki tambayi mijinki kinji, ba dan taso ba ta juya ta tafi, knock take, kamar kullun yau ma haka yace" shigo a kan kujera ta gansa yana gyara hular kansa, zatai magana yace "muje na kaiki gidan amma bazaki dade ba, da murna tace" to na yadda yaya ahmad.
Fitowa sukai sukayi musu sallama suka tafi, a mota tafiya suke indo sai zuba masa surutu take kamar radio, basu dade ba suka karaso gidan..
AISHATUL HUMAIRAH
..... Labarin Indo .....
❤️💚❤️💚❤️💚❤️💚❤️💚❤️
=Na=
AISHATU BINT MUHAMMAD
(Matar Uncle)
🤗 _Zinariyar Nazari WRITERS association_ 🤗
🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀
The Story of life childhood,
Entertainment,
And Love.
NAZARI WRITERS ASSOCIATION
63++++++64
Bayan kwana 3
Indo da ahmda suka koma gidansu wanda daddy ya basa, rayuwa suke mai cike da tsafta ba algus, humaira na bin mijinta sau da kafa yi nayi bari na bari, tabbas ahmad yana son humaira, sai dai muce allah ya kara dankon kauna.
Falmata ce ta fito sanye da kayan karuwancinta ita da hijjah, driving suke a mota sunayi suna ihu da tsalle domin yanzu komai yayi sauki, basu wani ankara ba sukaji motarsu ta hadu da wata ta tashi sama ta dawo da kasa, da kyar dai suka fito daga ciki da taimakon mutanen wajen.
Ahmad da aisha na leka gidan ganin yadda humaira ke kyalli fatar nan ta dau haske, farhana na gani a gidan inda take ta fito mata da magungunan mata ita kuma tana karba, farhana xe tace "ke yaushe zaki koma makaranta, dan murmushi tayi tace" sai mun koma abroad, murmushi farhana tayi tace "masha allah kanwata ta zama jinin abuja, murmushi tayi tace to aunty farhana gobe fa zamu tafi, addua tayi mata da nasiha hade da fatan alkhairy.
Washe gari suka daga sai London, anan suka ci gaba da rayuwarsu cikin tsafta, da kuma nuna kauna.
Kamar daga sama na jiyo ihu juyawa nayi nan naga gaba daya wajen ya kama da wuta gobara ce, kafin mutane su zo komai ya kare ya dawo saura toka, takaici wani mutum naga an sauke a nafef, kallon saurayin yayi yace "kai dai anyi lalatacce wai dik abinda ka saka hannu sai ya kone kai muhammad daga yau karna kara ganinka a wajen ma'aika tuna nafada maka.
_Bayan Shekara 2_
Wata kyakkyawar mata ce take sakkowa daga flight hannunta rike da baby 🤱, baya na kalla nan na hango ogan wato ahmad, nikam nace dama har ta aihu ne bansani ba, tafiya suke motace ta karaso kafin suzo, tana zuwa suka shiga bayan an saka musu kayan, daga nan sai gidansu.
Wani katafaren gida ne mai kyau da daukar hankali, tin kafin su shiga na tabbatar da murnar ganinsu ake, farhana ce na hango da yaro a hannu yana tafiya, hango motar yasa ta karasawa, yana fitowa ya fara hugging din ta, sannan ya dauki babyn hannunta.
Gaba daya gidan kowa na cikin farin ciki da kaunar ganin su baya da mama ganin jikokinta da tagani, farhaan ne ya leko yace "mama dan allah ki ajiye min farnaz idan nagirma na aureta, domin nafiso nima na samo kyakkyawa, dan wallahi mama bazan auri mummuna ba, duka ta kai masa yanayi yana dariya kusan kowa dariya yake.
.
Haka dai yaron aunty farhana ne yace "aa mommu ai dai farnaz ni kika bawa ita ko, zaro ido nayi jin yaro yana magana ba gwaranci a bakinsa, kowa na dakin dariya yayi.
Aisha ce a kusa da ahmad a kan bed shi yana gyaran document ita kuma tana bawa farnaz mama, dagowa yayi yana mata murmushi ita ta maida masa, sanan yace "ki shirya zamuje wakaza, zaro ido tayi cike da mamaki, ganin yadda tayi yasa shi yi mata kiss 😘 kusa da kumatu, yace" eaa mana ai bana magana 2 ko, duka takai masa karbar farnaz yayi yace "zo muje na kaiki farnaz na dawo kan ammiee daga haka nace to bye bye.
Haka rayuwarsu taci gana da wakana a wannan gidan cike da farin ciki da kaunar junansu,Faisal shi yake kusan kula da farnaz yarinyar humaira wato indo, nikam daga haka na tattaro biro na da littafi naja na tsaya domin jin inane ban leka ba.
Alhamdulillah dika anna na kawo karshen wannan littafi na Labarin Indo, kuskuren da yake ciki allah ya yafe mini, sakon da yake ciki allah ubangiji ya bamu ikon amfani da shi kuma mu gyara.
Alhamdulillah!!!*
_Nan na kawo ƙarshen wannan littafi Mai suna *_AISHATULHUMAIRAH (Labatin Indo)_*. Kuskuren da nayi cikin sa ina roƙon Ubangiji ya yafe min shi, abubuwa na magana da kuma alkhairi da ke ciki ina roƙon Ubangiji ya sa muyi tarayya cikin ladan._
_Sannan fans ɗina ina ƙara tunatar da ku cewa ƙofar gyara a buɗe take, don Allah duk wani abu da kuka nayi ko nake shirin yi da bai kyautu ba kada ku tsaya ku min magana, wannan shine soyayya ta gaskiya da kuma zaman tare._
_Ina matuƙar godiya gare ku fans ɗinah, masoya na har abada, ƙaunar ku gareni maras iyaka ina godiya, nima ina matuƙar ƙaunar ku har cikin raina, kuma ina jin ku tamkar ƴan uwa na ne._
_Masu Neman number waya na ga shi nan +2347033313681,na gode_
_Nan zan dakata, ku kasance da alƙalami na cikin littafai na masu zuwa...
Queen walie
Queen waleedah/Matar Uncle ❤️
🍀 🌷 🌸 🌷 🍀 🌷 🌸 🌷 🍀 🌷