Showing 12001 words to 15000 words out of 40600 words
bai dade ba ya dawo da kudi fall hannunsa.
Ajiye mata yayi, kallon kudin tayi tana kallon yammatan da dikkaninsu sun hada gumi sai makefa sukeyi,maimakon tayi magana sai wata mahaukaciyar dariya data saki tana yi tana karawa, sai kuma tace "wai ku tsaya wannan kudin nawane, saurayin ne ya tari numfashinta yace eaa naki ne wallahi na bar miki, ki dauka amma ki taimaka ki tafi, dariya take amma lokaci daya ta murtuke face tace" zan tafi amma ku tsaya na shiga cikin wannan talabijin din nagansu mu gaisa ko.
Da kyar ya daure uace "ba a shiga cikinta amma dan allah ki taimaka m, naji da allah ta basa amsa, daukar kudin tayi m, hade dayi musu waje sai kuma tace" to na tafi, gaba dayansu sauke ajiyar zuciya sukayi, jin maganarta ne yasa su juyowa, to ku juyomin sauran abincin har da naman, da saurinsu suka fara hada mata, sai da suka tabbatar ta tafi, sanan suka kalli juna.
Daya ce tace "wallahi aliya baki da hankali yanzu gashi nan kin daki aljana, yo aljana mana idan ba aljana ba wacece za a buga da wannan karfen amma ya lankwashe, wallahi ba ruwana idan ta dawo miki, kuma ke da kika kwada mata ke ce a ruwa.
Indo tinda ta fito take wakarta, hanyar komawa makaranta tayi, ta inda ta biyo ta nan ta koma, maimakon ta tafi hostel din su, dakin senior tabi daidai bed din aunty babba ne yasa ta tsaya ta bude wata leda, hura wani abu tayi, sai kuma ta fara bude lokanta, wasu kayan abinci ta gani dariya tayi tace yawwa ga inda nafison zuwa deba tayi sosai sannan ta boye, komawa tayi ta window ta bi ta shigar da kayanta, maimakon ta zagayo, sai kowa ya ganta ta fito ta kofa, ai ba wanda bai tsorata ba.
Aunty babba data kasa jurewa ne yasata kusan sakin fitsari, domin tabbas ta tsorata, indo ganin sun tsorata ne yasa ta fara magana "ya ku bil adama, ku tashi daga nan ko yanzu mu far muku, wajen zaman godiyar tamu yau kukazo kuka zauna, dik wanda bai tashi ba ina mai tabbatar masa sai dai uwarsa ta haifi wani, yara kamar jira suke haka suka fara gudu,masu aljanun cikinsu kuwa tini suka fara zubewa suna ihu.
Aunty babba tana komawa ta dane gadonta tana huci, ba abinda take fadi sai nidai allah yau yamin gam da katar, dama da ganin wannan wallahi kasan kanta da aljanu.
Kamar abin almara ta fara susa, lokaci guda ta virkice susa kawai take yi kamar wata kura,kuma dik inda ta sosai sai wajen ya dade ya kwaile ya zama kamar jini, a lokaci guda ta soshe jikinta, take ya fara radadi, ganin abinda yake faruwa ne yasa aka dauketa sai clinic.
Bayan Sati 5 abubuwa da yawa sun faru a ciki, tin daga dawowar aunty babba daga gida domin sai da taje gida aka mata magani, har zuwa yanzu dasu indo suke yin exam, ba laifi kullun indo tana zuwa makaranta, domin yin jarabawa, amma nidai kam waleeda bansan me take rubutawa ba.
A haka zangon karatu ya kare, dik da dik school din nan ba wanda baisan indo ba, a ranar kar bar sakamako kowa ya tafi yana dubawa, amma sun yanke ba wanda zasu bawa sai iyayensa sun zo daukarsa.
Yau tin sassafe garba ya fito da shiri, sai iyalle data ke yafa mayafi, gar mba ne yace "iyalle naga rana tanayi, kinsan halin makaranta ya kamata mutafi, da to ta amsa masa sannan suka fito, daidai inda mota take tsayawa suka tsaya, basu dade ba sai gata ta taho shiga sukayi sai makarantar su indo.
Tin a bakin gate suka fadawa mai gadi su suwane dan haka ya barsu suka shiga, indo dai tana zaune, fauzah ce da hussaina suka matso kusa da ita, sakamakon zasu tafi, hussaina ce tace "to aisha mu zamu tafi sai allah yasa kuma mun dawo amma zamuyi kewarki, murmushi tayi tana daga musu hannu har suka tafi, sai ji tayi kamar kar ta bar makarantar, amma idan ta tina da su salame da dije sai taji inaa dole yau ta diro jauyen wakaza.
Daga can nesa ta hango iyalle, kara murtsika idanunta tayi tana wasge baki, laa wallahi itace abinda ta furta kenan, da gudu ta karasa tana kama iyalle, ita din da murnan ta take kallon jikar ta ta.
Garba wajen shugaban makaranta ya tafi domin ya basu izinin tafiya, shigar sa ne yayi sallama, amsawa yayi yace "yawwa dama mal garba ina nemanka.
Jin haka yasa garba shan jinin jikinsa yace" to tayi halin kenan.
Pc ne yace" aa ko daya yarinya dai tayi kokari matuka, domin tabawa kowa mamaki a makarantar nan.
Wasu envelope ya janyo hade da gifts ya mika masa yace" to fatan zata dawo a karo na gaba.
Garba ne yace" amma yallabai bakamin bayani ba, daeiya yayi yace "koma menene zaka gani sai allah ya kaimu munga dawowarta.
Daga haka sukayi sallama, garba bai tsaya budewa ba, domin tsoron bude tajardar yakeyi, dan yasan indo itace zatazo ta karshe, wata zuciyar ce tace aa wannan kyautan fa na meye, da wannan tinanin suka hau mota sai kauyen wakaza.
SHIN MEYE A CIKIN WANNAN ENVELOPE
GA INDO ZATA KOMA KAUYEN WAKAZA
ME ZAI FARU
ALKALAMIN ✍️✍️✍️
QUEEN WALEEDAH Auntynmu🫧🫧💦
*HANYOYI HUƊU DA ZASU RAGE MAKA DAMUWA:*
-
♦️Kayi sallah / addu'a zuwa ga Allah!.
-
♦️Ka kyautata zaton anji addu'arka kuma an amsa maka.
-
♦️Kayi jira cikin haƙuri, kuma ka kyautatawa Allah zato.
-
♦️Ka gaskata cewa Allah shine yasan abinda yafi dacewa dakai.
-
"A duk sanda kaji damuwa a ranka, to ka samu kayi alwala kayi sallah koda raka'a biyu ce, sannan ka yawaita yin addu'a aciki, cikin ikon Allah za kaji damuwar ka ta kau"
-
"Kada kayi gajen haƙuri abisa jinkirin amsuwar addu'arka, sannan kuma kada ka gaza acikin lamarin ubangijinka, Allah shine kaɗai yasan abinda yafi dacewa dakai"
-
-
AISHATUL___HUMAIRAH
..... Labarin Indo .....
❤️💚❤️💚❤️💚❤️💚❤️💚❤️
=Na=
WALEEDAH MUHAMMAD
(Auntymu)
🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀
The Story of life childhood, Entertainment, And Love.
MARUBUCIYAR
A sanadin kishiyar uwa
Jannat
Kawancen mu.
And Now
AISHATULHUMAIRAH
16🖤17
Shigowarsu gari kuwa abi ka da kauye tini ko ina ya zaga ai indo ta dawo, anan kuma kowa ya fara tattare kayansa domin kuwa sun san halin abarsu basai an fada musu ba.
Daidai kofar gidan iyalle suka sauka, shigar da kaynta ta fara yi iyalki na mata sannu, garba kuwa shigowa yayi yaja tabarmar kaba, takardun ya janyo ya bude, ganin fuskar da fara'a yasa iyalle fadin "kai garba lafiya naga kana ta dariya, murmushin ya kuma yi yace" iyalle dole nai murna, ashe indo ta 1 tayi, zaro ido iyalle tayi tace "yanzu ace indon ce tai ta 1 garba.
Garba ne ya kalleta yace" wallahi nima iyalle abin ya bani mamaki ace kamar wannan indon ita da kwakwalwarta data kifi dik daya, taya akai ma har ta iya wannan abin arzikin, iyalle ce ta juya zatayi wa indo magana, gani tayi ta kwanta tana bacci, da fara'arta ita ma take kallonta..
Indo tin ranar data dawo daga makaranta yau kwananta 2 ba inda ta fita, domin ji tayi batasan garin ta fi so ta koma birni da zama.
Iyalle ce ta shigo dakin tace "yawwa indo dan allah tashi na aikeki saboda anjima zakiga kawunki Wannan yaro, da murnar ta tace" laaa abban ya ahmad ne zaizo, dan allah iyalle zan bisa mu koma tare domin ni kawai banason zaman kauyen nan, ko kallonta batayi ba tace to naji yanzu maza, jeki amso min daddawa da kuli kuli kuma kiyi sauri.
Indo fitowa tayi tana tafiya a hankali kamar ba indon dana sani ba ce, dije ce ta hangota ta karaso da gudu, har da haki tace "jiya muka je gidan ku nemanki iyalle tace ta aikeki, kinsam tin rannanr nake son ganin ki amma kin min nisa wallahi, dubeki yadda kika chanza, kika zama wata mai kyau indo.
Dariya indo tayi jin an yabeta, sai tayi dariya tace" hmm ai ke bazaki gane ba wallahi ina fada miki ruwan birni wani dadi ne dashi, domin ko zakiji har zaki yake, ke baki ga nayi fari ba, to ina fada miki sirrrin ruwan birni kenan, shisa idan kawu ali ya zo yau binsa zanyi kawai mu tafi domin so nake nan gaba nafi haka haske.
Haka suka tafi suna ta hirar su, rabi shirme da shiririta.
Ta kocar gidan mai gari sukazo zasu wuce, indo ce tace "zo muje mu gaida mai gari, tafiya sukayi bayan sun gaisa suka taho, mai gari ne yayi mamaki sai kuma yace" lalle makaranta tana sa mutum ya natsu ya zama mutum mai hankali yanzu dai kalli indo, waya zaci indo zatayi hankali a wannan rayuwar,daga haka ya jinjina kai yana tinanin haduwarsa da aljanunsa.
Bata dade ba ta dawo ita da dije suka zauna, tana bata hirar makaranta,dariya sukeyi iyalle tace kira indo ta daukar musu abinci, ci sukayi daga nan suka fice zuwa rafin dan marka.
Bayan tafiyarsu da awa 1 ne wata katuwar mota ce sai shining take tai parking a kofar gidan iyalle, zo kaga yara yadda suke bin motar, baya naga an bude nan naga wasu budurwa xe 1 sai kuma wani saurayi shima, kamarsu daya kamar an tsaga kara,basu dade da fitowa ba ne naga wata hajiya ta fito, itama, motar ce ta cigaba sai da tai parking mutum ya fito, wow masha allah, sanye yake da shadda blue color yayi matukar kyau, sai kuma matarsa data saka lace, ganin sun jeru me yasa shi fadin "to ku kuma su farhan me kuke jira. Let go mirmushi sukayi suka bisu a baya.
Da fara'arta iyalle take dubansu taba cewa"to fa kaga mutanen birni ai kuwa kunzo da wuri idan hakane, amma dai tin asuba kuke tafiya ko, gaba dayansu dariya suke farhan ne yace "aa kakarmu ba tin asuba muke gudu ba, inda tin asuba ne ai da tini mun iso.
Farhana ce ta kalli iyalle tace" wai nikam iyalle ina 'yarki ne naji gidan naki yayi tsitt kamar ba wata halitta, dariya dukansu suka sa, iyalle ce ta bata amsa da' ai ta fice domin ni tinda ta dawo daga makaranta tayi hankali abinta.
Salma ce ta murmusa tace "ai iyalle haka akeso a dinga hankali, amma dai ina fatan tayi abin arziki ko.
Alhaji ali ne ya katse hirar nan aka fara gaisuwa da hirar yaushe gamo.
Indo tana zaune a bakin rafin dan marka sai dije da ta haye sama tana ciro mangwaran bakin rafin, wata yarinya ce tazo dibar ruwa, sallama tayi musu amsawa indo ta amsa mata sai kuma tace "ke wai ba" yar gidan hajiya ba ce, yarinyar tasan halin indo, shisa ta tsugunna zata fara bata hakuri, ko kallonta indo batayi ba ta tashi ta bar wajen.
Sai da tayi nisa sosai sannan dije ta waiga taga ba indo, binta tayi amma kuma bata ganta ba, sai da kyar ta hangeta ta kusa kaiwa gidan mai gari, gudu ta kara ta matso, tana nishin gudun tace "wallahi indo kin bani wahala kinga uban gudun da nayi kuwa, wai anya indo kanki kalau kuwa, ohoo indo ta bata amsa, sai kuma tace" kutumelesi al kur'an su aunty farhana sun iso, ke dije tafi gida zamu hadu anjima, tana gama fadin haka ta sa gudu kamar wadda zata tashi sama.
Tana zuwa kofar gidan taga ana shiga da buhunan shinkafa, macaroni, talia da sauransu, maimakon ta shiga sai ta tsaya kusa da motar tana shafata, cike da fara'ah tace "wallahi bazan zauna ba kara naje can nai ta hawa mota inajin dadi.
Cikin gidan ta nufa zata shiga sai kuma naga ta tsaya sakamakon hango takardunta na makarantar boko da tagani suna dagawa, a hankali take tafiya yadda bataso kowa ya ganta, sai dak kashh farhan ya ganta, nan kuwa ya kwala mata kira, yar fara'ah ta kwakulo ta taho tana daria, farhana ce tace "wato da hucewa zakiyi ko, saurin jijjiga kai tayi, garba ne ya harareta yace" ka dubeta kamar wata mutuniyar arziki, ganin kowa na fadin albarkacin bakinsa a kanta ne yasa salma fadin taho nan humaira rabu da su dik kwayi kwa gama.
Dariya sukayi su ma, alhaji ali ne yace "amm humaira kinyi kokari sosai amma kuma abin ya bani mamaki, zan tambayeki ki fadamin gaskia saboda kawunki garba yace wai malpractice kikayi,kinaji na da gyada masa kai tayi.
Alhaji ali ne yace" me yasa banga rubutu a cikin littafinki ba ko guda daya, amma taya akayi kikazo first, bayan kuma nasan idan baki karanta ba ai bazaki rubuta ba, shiru tai kamar bazatayi magana ba, sai kuma tace "aa eaa dama, dama bana zuwa makarantar ne saboda sai kuma tayi shiru.
Alhaji ne yace" munajinki humaira, bana rubutu kuma bana zuwa, sai lokacin jarabawa na fara zuwa saboda kawu garba yace idan banyi abin arziki ba sai ya saida ni kowa ya huta, rananr da aka fara jarabawa, bayan an bani paper kawai kallon question din nayi bansan daga ina amsar taje zuwa ba kawai nidai na tsinci kaina da rubuta kowace tambaya ce tazo kaina.
Kowa na wajen shiru yayi, garba ne ya janyo takarda yace "to ai zan gani bara na gani idan da gaske kike, biro ya dakko da paper ya rubutu, mika mata yayi yace to amsa mini, karbar takardar tayi da biron, kallon rubutun tayi, take ta fara rubuta amsar, saida ta gama tsaff sannan ta miko masa, kalla yayi yana tu'ajjibi, bashi kadai ba, salma, ali, farhan da farhana, kallonta suke.
Alhaji ali ne ya kalleta yace "shikenan farhan ku tashi kuje kuga kauyen mana, dama kunce kun dade baku zaga ba, indo tashi ki bisu, tashi tayi suka fita, suna fita alhaji ali ya kalli garba yace" akwai abin mamaki game da indo wallahi amma ko ma menene komai zai bayyana very soon.
Gyara zama yayi yace "iyalle dama munzone game da auren da nace za ayi na indo da ahmad, iyalle ce tace" to shi ina amadun yake,
Amsa ya bata da cewa yana uk amma zuwa nan da sati 4 zai dawo, iyalle ce tace shikenan ai dik yadda kayi tinda yaranka ne.
AISHATUL___HUMAIRAH
..... Labarin Indo .....
❤️💚❤️💚❤️💚❤️💚❤️💚❤️
=Na=
AISHATU BINT MUHAMMAD
(Matar Uncle)
🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀
The Story of life childhood,
Entertainment,
And Love.
DASHEN ALLAH WRITERS ASSOCIATION
18💜19
Fitowarsu kallonsu farhan tayi tace "to yanzu mu tafi kasuwa ko kuma muje dandali, farhan ne yace" no humaira gaskia kar muje ko ina kawai ki kaimu inda yafi ko ina kyau a kaunyen nan, dariya indo tayi tace amma nima idan naje birni zaku kaini inda yafi ko ina kyau,farhana ce ta bata amsa da eaa mun yadda daga haka suka tafi.
Tafiya suke ta kasuwa sukabi, wasu kattin samari ne suka taso dai dai kan indo suka tsaya suna kallonta, kallon kya daku, farhan ne yace lafiya dai ko, daya ne ya kallesa yace kai ba ruwanka nace,farhan ne yace "ai kam da ruwana tinda yar uwata kuka tare zaku daka, dayan saurayin ne ya zaro ido yace" waya isa ya daki indo ya kwana lafiya, ai wallahi dik wanda ya daki indo to ka tabbata watan jinyarsa ya kama, dama ba wani abu bane,dan liti ne yake son indo, kuma shi ne, farhan ne yace "stop please kamar ya, indo wuce mu tafi farhana ce taja hannunta, har ya tafi ya dawo yace" sorry amma wannan tana da miji, sai dai kuyi hakuri, daganan suka wuce suka tafi.
Haka sukai ta tafiya, dik inda sukaje indo sai tace musu nan ne kaza kaza, sai wajen sallar magariba suja shigo gidan.
Zaman hira suka zauna yi gaba daya su, iyalle ce ta fara kokarin yashi tayi musu shimfida, garba ne da farhan suka shige bukkarsa, yayin da alhj da matarsa aka gyara musu dakin iyalle, sai iyalle da indo, farhana suka shige damin indo sarkin dauda, dik da sai da suka gyara, hakan bai hanasu zama da kura ba.
Washe gari tin da sanyin safiya suka tashi, iyalle ce fa fara fitowa, indo koda ta tashi zamanta fayi, farhana ce tace "ke indo ki tashi ki sallah, kamar bazata tashi ba sai kuma ta tashi, maimakon tai hanyar bayi sai tai hanyar waje, sai da tai wajen mintuna 20 sannan ta dawo, zaman karyawa sukayi, bayan an gaishe da juna, farhan ne yace to iyalle mufa nan da anjima zaki neme mu ki rasa saboda kinsan guduwa zamuyi, dan murmushi itama tayi tace "ai nasani hassan amma yaushe zakazo ai auren, farhana ce ta kyalkyale da dariya.
Sallamar alhaji ali ne yasa su yin shiru, tsugunnawa yayi yace wa iyalle" yace ba komai anjima idan an sakko daga masallacin jumu'a sai a daura, iyalke da farinciki ta mike tana tafe tana shi masa albarka, ita dai indo an sakata a duhu, idan ka cire farhan da farhana dik sun sani indo ce kadai take a duhu.
Muryarta sukaji tana fadin amma dai gaskia anty farhana zan biku birnin nan,kallon salma tayi tace "allah mama kalli wani sai yace ta girmeni, wai me kukeci ne kuke girma kamar burodi da yis, gaba dayansu dariya suka sanya, salma ce tace shikenan sai mu tafi kawai kinga da antashi kema sai na ringa baki abinda nake ba su farhana ko, dariya sukayi suma.
Daria tayi tace "aa tsaya a tambayi kawu, kawu zaku dani birni ko, da murmushi yace eaa mana humaira, indai zaki zauna me zai hana, bide dafaffun hakoranta tayi, tana cewa aradun allah sai na biku, nima naje naci abinda kukeci har kukeyin girma, dama na gaji da zaman kauyen nan ga kuma kawu garba tsauri.
Wai mama ina yaya ahmad ne m, kinsan allah na manta da shi sam ni hankali na baikai na tina da shi ba sai yanzu, wai yana ina, shi ba zaizo ya ganni ba, tinda ta fara maganar ba wanda yace mata kala, ganin anki amsa mata ne yasa ta yin shiru.
Farhana ce tace "amma humaira idan zamu tafi ba abinda zaki dauka a kayanki, kallon harara tayi mata tace" cabb aradun allah she na dauka, to in bandauka ba wanne zan saka, farhan daya kasa danne dariyarsa sakinta yayi. Can kuma yace "aa humaira ai tin kafin mukarasa gida ma zan siyo miki kala 20 kita sawa kina chajawa, dariya tayi tace allah yaya farhaan.
Hirarsu suke jefi jefi salma tana saka musu baki, don iyalle dama ta fita, bayan awa 2 gaba daya gidan ya cika da mutane nmga alummar