Showing 24001 words to 27000 words out of 40600 words

Chapter 9 - AISHATUL_HUMAIRAH (Labarin Indo) HAUSA NOVEL

08 Nov 2024

4914

sai na girgiza ku na yanka ku, na kuma bawa 'ya' yan aljanu jininku da namanku sun cinye.

Zo kaga 'yar tsere wajen su ameerah, farhana ce ta matsa, dakin mama tatafi nemo key domin wannan shi ne karo na 2 da humaira ta tada aljanu dik da tana jin tsoro amma ta dake, bata sha wahala ba ta nemo spare key, zuwa tayi zata bude, jin wata iska data doka ta da kasa yasata faduwa a wajen.

Farhana ganin ta tayi a wani waje mai matukar haske,wajen kuma ba daki bane katon fili ne, can nesa take hango wani abu, dan haka karasawa tayi tana gudu, tana zuwa dab dashi taga yaya ahmad kwance, yayin da aka daddauresa ta ko ina, ganin farhana yasa ya fara ihu yana kiran sunanta, matsowa tayi tana kokarin sunce sa amma ganin wata katuwar takobi data zo ta sassara namansa tai gutsi² da shi yasata ja da baya tana gudu, mutumin daya datsa ahmad ne ya kamota, a wannan lokacin ne allah yasa ta farka, tana haki ga wani uban gumi da yake tsiyaya a jikinta.

AISHATUL HUMAIRAH
       ..... Labarin Indo .....
❤️💚❤️💚❤️💚❤️💚❤️💚❤️
    =Na=
 AISHATU BINT MUHAMMAD
       (Matar Uncle)
🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀
The Story of life childhood,
Entertainment,
And Love.

DASHEN ALLAH WRITERS ASSOCIATION

34**35
Saurin mikewa tayi ta fada jikin mama tana kuka, gaba daya mutanen falon zagayeta suke,suna kallonta ita kuma tana jikim mama, mama tana jijjiga bayanta,da kyar aka jata aka zauna akan kujerun falon.

Mama ce tace "farhana ki nutsu mana, kallon mamar take tana hawaye, mama yaya ahm... Maganar ce ta makale yayin da humaira ta fito tana jada hanya, mama ras abinyi tayi domin ta kasa gane kan yaran nata,humaira ce ta matso ta zauna kusa da farhana, dik da farhana naja da baya amma hakna bai hana humaira shafar kafarta ba, dik wani abu da farhan atake a lokaci guda ta dai na ta dawo dai dai.

Juyawa tayi ta kalli mama, tana shirin magana amma take komai ya bace mata, ta rasa mai zata fada mata, komai ta manta daga sumar ta zuwa yanzu, humaira ma kallonta take domin ta rasa wannan wani irin abu ne yaje faruwa da ita, ganin ta kasa fada ne yasa humaira fashewa da kuka, a dai dai lokacin daddy ya shigo.

Banda shasshekar kukan indo ba abinda yake tashi a wajen, kuka take cin bakin kokarinta, iyalle ce ta karaso tana dafata tace "me yafaru indo menene, jin muryar iyalle yasa indo taji dadi a ranta, tashi tayi ta rungumeta tana kuka.

Iyalle tace" ki fada min me yake faruwa amma kin tsaya kina kuka, daddy yasan komai dan hakan ne ma ya taho da malam domin yazo ya duba indo.

Bayan wasu mintuna.
Malam ne a zaune a kan kujera yana kallon indo, sai da yayi a kalla mint10 sannan ya dago ya dubi mama yace kawo min ruwa a sabon kasko, bata bata lokaci ba sai gashi ta shigo da ruwan kamar yadda ya umarta,karba yayi ya fara tofi da alama karatu yake a zuciyarsa.

Yana gamawa ya watsawa indo ruwan tofin, wata razananniyar kara ta saki, take asalin fatarta ta fara chanjawa zuwa ja jawur, kowa na falon ya tsorata amma iyalle kokarin zuwa kusa da ita yake, malam ne ya dakatar da ita dan haka ta tsaya, tashi tsaye indo tayi ta karaso har gaban malam din, cikin wata irin murya mai amo da karsashi yasa ta fara magana "malam kayi hakuri mu bamuzo dan mu cutar da aisha ba, muna jikinta ne domin kawai mu taimaka mata, kuma muna taimakonta ta kowane bangare.

Malam ne yace "tayaya kuke taimaka mata bayan kuna barazanar zautata, muryar ce tace" malam ka taimaka zan gaya maka asalin labarin dalilin dayasa muke jikin indo,da kuma abinda yasa yau mukazo, sanann malam amma idan kaji tabbas zaka barmu baza ka mana komai ba,malam be yace "eaa nayi alkawari ina jinku kuma.

Muryarce tace" asalin labarin mun kasance mudin aljanu ne amma ba masu cutarwa ba, tin a wasu shekaru na bil adama, wani lokaci mahaifyar aisha, wato aminatu a jikinta muke, bayan mutuwarta ne muka dawo jikin diyarta, kasancewar munsan indo bata da kowa, sannan ada can ta kasance ana cutarta ne, amma tin a shekara ta 2 muka dawo jikinta domin muna taimaka mata mu bama su cutarwa bane, sannan kuma dikda kasancewar mu ba musulmai ba hakan bai sa munsa ta kyamaci addininta ba.

Sanann kuma an daura mata aure ne da mutum mutumi domin ahmad ba shi bane, ahmad ya dade da suma domin kuwa a kalla yau watan ahmad 7 a sume, kawai ana amfani da gangar jikinsa ne, amma ba shi bane, a yanzu haka ahmad yana wata duniyar ta daban amma idan kun bincika, zaku iya dawo dashi nan da sati 1,sannan kuma abinda baku sani ba gane da auren farhana da kabeer, sam kabeer ba mutumin arziki bane, idan kuma kuna tinanin karya muke fadi muku, to yanzu haka ku shirya ku tafi clubs anan zaku ganshi.

Suna zuwa nan take dakin yayi haske, wani irin haske ne, kowa na dakin hankalinsa ya tashi yayin da haskem ya daidaita anan suka ga indo a kwance a sume.

Malam ne yace "ku dauketa ku kaita daki sannan zan bawa mujahid ruwan rubutu yanzu ya kawo mata, daukarta sukayi suka wuce da ita dakin ya rage daga alhaji sai iyalle da garba.

Malam be yayi gyaran murya yace" tabbas aljanun aisha ba masu cutarwa bane, kuma a yadda suke magana na tabbatar da cewa ba karya suke ba, alhaji ali ne ya girgiza kai, mama ce ta shigo fuskar nan shabe shabe da ruwan hawaye,zama tayi malam yaci gaba da cewa, yanzu abinda ya kamata kuyi shi ne ku tabbatar da cewa kun samo ahmad domin tabbas yana cikin hadari, sannan zan kara dawowa domin tabbas nasan zasu dawo.

Malam ne ya mike ya yi musu sallama, musa driver akasa ya daukesa ya tafi dashi, kowa na dskin fuskarsa ba annuri, farhana ce ta dauki wayarta ta fara kokarin kiran number kabeer amma abin mamaki baya dagawa, daddy ne yace "farhana ya daga kuwa, hawayen face din ta take gogewa ta girgiza kai, daddy ne yace tabbas ya zama dole na san abin yi, ke farhana tashi ki tafi daki kinji, maimakon tai dakinta sai tai hanyar dakin humairah. AISHATUL HUMAIRAH
       ..... Labarin Indo .....
❤️💚❤️💚❤️💚❤️💚❤️💚❤️
    =Na=
 AISHATU BINT MUHAMMAD
       (Matar Uncle)
🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀
The Story of life childhood,
Entertainment,
And Love.

DASHEN ALLAH WRITERS ASSOCIATION

36-37

Zaman tattauna wa sukai, basu tashi faga falon ba sai wajen karfe 2 na dare, kowa dakin da aka saukesa ya nufa,iyalle ta nufi dakin indo, tana shiga a zaune ta hangi farhana na sallah tana kuka,sai da ta tabbatar ta idar da sallah sannan iyalle ta karasa kusa da ita ta dafa, kamar jira taje ta fashe da kuka.

Iyalle rungumeta tayi tana bubbuga bayanta, da kyar iyalle take bata baki amma kamar zugata take, wani juyi indo tayi ganin haske a dakin da kuma hayaniya yasa ta wartsake, kallon iyalle take da murmushi ta karasa tare da janyota tana dariya, iyalle ce ita ma tayi mata murmushin, ganin farhana tana kuka yasa saurin sakkowa tana fadin aunty farhana menene, me ya faru aunty farhana, ba wanda ya bata amsa sai kukan farhana ne yake tashi.

Ganin taki samun amsarta ne yasa ta fashe da kuka tana cigaba da tambayarsu, farhana ce ta ga tana kuka, saurin rungumota tayi tace "aa aisha ki shiru mana haba, kinsan menene ya hakuri zan fada miki, da kyar ta samu ta daina kukan, kallonta tayi tace" humaira ba wani abu bane dama, aurena aka fasa da kabeer, maimakon taci gaba da kukan sai ta mike tace "aikin banza da akan wannan dan iskan kike zubar da hawayenki a banza, gashi nima kinsa nayi asarar nawa, farhana da mamaki tace taya akai kikasan shi dan iska ne humaira, tabe baki tayi tace" nasani ne kawai, bandaki ta shiga ta doko kofar, iyalle da farhana kallon juna sukai.

Farhana ce tce "iyalle dama indo haka take ko kuwa sai da tazo nan ta chanja, iyalle ce ta bata amsa" aa nk kaina nan indo idan tayi wani abin tana bani mamaki saidai bana iya magana, suna cikin maganar ta fito.

Kallin farhana tayi tce "allah aunty farhana kuzo ku kwanta domjIdan ba haka ba wallahi yanzu zan hautsina komai, jin abinda ya fito daga bakinta ne yasa su saurin mikewa, domin yanzu farhana ta kara tabbatar wa da eaa lallae tana jin tsoron indo.

Washe gari kusan kowa na 'yan biki sun fara hallarta, saboda yau ne za a fara event, daddy ne da mama sai farhana, iyalle da garba, alhaji ali ne yace "to ni yanzu zan shirya naje na samu mahaifin wanann yaron kabeer domin muyi magana,mama ce tace" to allah ubangiji ya sawwake ya tsayar iya nan, fita yayi farhana ce tace "mama amma yanzu lamarin yaya ahmad fa, dammm gaban mama ya bada wannan sautin, iyalle data kula da yanayin salma, yasata fadin ke tashi kije kiga ni idan indo ta tashi.

Tana fita iyalle tace" salma kiyi hakuri kinji, dama haka rayuwa take, kowa da irin tasa kaddarar kuma kinsan da cewa ko wanne dan adam akwai irin jarrabawar da ake masa, idan har allah bai jarraveka ba, to lallai ka tambayi kanka.

Salma ce ta share hawayen fuskarta tace "to iyalle allah ubangiji ya bamu ikon cinye wanan jarrabawar, da ameen suka amsa, amma iyalle ya za ai da bakin da suka fara zuwa, ba wanda ya bada amsa sai kallon kallo da ake yi a cikinsu.

A falo farhana ta tarar da humaira cikin bakin da suka zo, karasawa tayi wajen ta tace "humaira kinci abinci kuwa, tabe baki tayi tace" me kika gani kika ce haka, ba komai naga kamar baki break ba, aa nayi zuwa nayi zan kallo kuma sun dameni da hayaniya.

Mikewa tayi tabar farhana a zaune a wajen, dakin farhana tayi sai kuma ta fasa ta shiga dakin farhan, tabe baki tayi ganin komai blue and white, a fili ta furta, shi kuma choice dinsa kenan, kullo dakin tayi ta taho saman upstairs.

Kallo wani daki tayi, a fili ta furta dakin yaya ahmad, yau kam sai na shiga dakin nan kodan naga meye a ciki, har ta bude kuma ta tabe baki ta rufo, hango iyalle datayi tayo hanyar.


Alhaji ali ne tsaaye a kofar gidan su kabeer, hango alhj ali ne yasa mahaifin kabeer cewa ya shigo, karamin falo suka shiga, tare dsa zamaa.

Bayan sun gaisa alhj aliyu ne yace "dama nazo ne akan maganar yaran nan, wato kabeer da farhana, nazo ne domin a fasa wannan auren,da mamaki mahaifinsa yake kallon alhj ali yace" me kake nufi ka mini bayani yadda zan gane.

Alhj aliyu ne yace "na samu hujjoji akan cewa kasan danka manemin mata ne kuma kasan da cewa yana shaye shaye amma me yasa baka fito ka fadamin ba sai a gari zanji, to wallahi kasani bazan iya aurawa yata dan ka ba, dan haka an fasa wannan bikin kuma yanzu haka anshigar da kaya da dik wani abu da kuka bayar, nagode.

Alhaji Sani ne yace "haba alhaji ali me yayi zafi haka to sai me dan dana yana shaye shaye yana neman mata ba, kuma kace aure babu shi ko, to kasani wallahi wallahi na rantse da allah sai na lalalta rayuwar farhana, tinda har kazo gida kanamin wadan nan kanan maganganun, sanan kuma ina mai tabbatar maka da cewa koda kabeer bai auri farhana ba, to wallahi thumma tallahi sai ya lalata rayuwarta, idan kuma kana ganin bazan iya ba to ka jira ka gani.

Alhj ali ne ya daga hannu ya wankesa da mari, yayin da idanunsa suka yi jawur, cikin zafin zuciya yace"sani idan baka aikata hakan ba to tabbas baka cika ba.Jin zafin marin yasa suka fara hayaniya, da kyar aka rabasu kowa na zage zage.

A can gida kuma anan aka fara debo kayan farhana ana fita dasu, domin a maida musu abinsu. Farhana na dski tana kuka indo ta shigo, ganin tana kuka yasa ta tabe baki tace "haka dai aunty farhana kina nan kina kukan naki, wallahi idan da ni ce ke da timi na ciresa a raina,amma kin wani damu da dan iska.

Farhana na jinta amma ta kasa mata magana, sai da tayi mai isarta sannan ta fita, ganin falon dik ywanci ba mutane yasata shiga dakin ahmad, wani sanyayyen kamshi ne ya doki hancinta.

Hawaye ne suka fara zuba a idanunta, kamar daga sama taji magana, kuka ba naki bane aisha, ki tsaya ki jajirce ki taimaki rayuwar mijinki, sannan kuma dik wanda yake da sa hannu wajen wanan aikin ki tabbatar kin hukunta shi, gefen kujera ta zauna, daga kanta tayi tana kallon wani katon hoto da yayi yana sanye da light blue din shadda, dinkin yayi matukar amsar jikinsa, a fili ta furta "masha allah allah mai halitta.

Sai da ta gama zagayenta a falon sannan ta mike tace" wai ka duba daki ko ina tsaff tsaff, kuma yau wata 3 mai shi baya nan, wata kofa ta hango direct kanta tsaye ta nufa, jin kiran da ake kwala mata ne yasa ta dakatawa, wata kakkausar murya ce tace "karki kuskura ki shiga dakin nan har sai kin nemo ahmad,jin haka yasa ta fara ja da baya,sai kuma ta fita da gudu. AISHATUL HUMAIRAH
       ..... Labarin Indo .....
❤️💚❤️💚❤️💚❤️💚❤️💚❤️
    =Na=
 AISHATU BINT MUHAMMAD
       (Matar Uncle)
🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀
The Story of life childhood,
Entertainment,
And Love.

DASHEN ALLAH WRITERS ASSOCIATION

38&39


Wayar mama ce take kara, kallon wayar tati ganin sunan yayarta yasa ta daga, daga can bangare aka ce "salma ki zo mu zamu tafi ne.

Sakkowa tayi ta hangi yayarta ta, da kallo ta bita ganin tana cikin damuwa yasa ta jata kitchen, atace" haba salma kiyi hakuri mana dan allah, dan an fasa wannan auren hakan ba shi ke nuni da cewa shikenan farhana bazata samu wani mijin ba, karki manta farhana nada masoya da yawa dan haka zata samu wani a hankali.

Sannan kuma ki cire wannan damuwar a ranki saboda kinsan me zata iya haifar miki, anyi ta barka da aliyu ma yagane halinsa tin kafin a daura auren, haka taci gaba da bata baki sannan ta fito hade dayi mata sallama ta tafi.

Shigowar daddy gidan kusan kowa ya gama watsewa, ganin mama a falo yasashi yayi hanyar part dinsa, mama a kage take hakan yasaka ta bisa itama domin jin yadda sukayi da sani, kasancewar tasan bashi da mutunci ko kadan.

A falo ta tarar da shi a zaune, gumi yake ganin yana gumi yasa salma karo masa Ac dakin, zama tayi kusa da shi hade da rike hannunsa, kallo daya tayi masa tasa a fusace yake, haka suka zauna kusan 10 mint ba wanda yayi magana, karar wayar salma yasa ta sakin ajiyar zuciya mai nauyin gaske, janyota tayi ganin farhaan ne yasata dagawa da hello.

A handfree ta saka ta, farhaan ne hace "mama ina kika shiga sai kiranki nake, bayan kuma nasan dai bakya nisa da wayarki, kodan ma ba wannan ba jna amarya farhaana, jin shiru yasa ya fara furta hello, da sauri tace" farhaan ina aiki ne idan na gama zan kiraka, bata ji amsarsa ba ta katse wayar.

Farhana ce ta fito daga wanka, ganin indo a yasata fadin humaira daddy ya dawo ne, da eaa ta bata amsa taci gaba da game a wayarta, jin karar kira yasa farhana juyowa tace "wanene yake kirana, a yayin data juyo ne idanunta sukai tozali da idanun indo da suka chanja kala, idanunta har kore kore yake, wayar ta daga ga ajiye ta tare da kure volume.

Muryar kabeer ce tace" farhana me yasa kikace kin fasa aure na, me nai miki, Farhana kasa magana tayi sai indo ce tace "saboda kasan ai halinka na neman mata da shaye shaye har ma da caca, jin muryar da bata farhana ba yasa fadin," ke kuma wacece, ke a suwa har zaki shiga magana ta da matata, wata dariya tayi tace "to baka isa ba aurene an fasa, ba za ai ba, dik abinda zakayi sai kayi mugani, kabeer ne yace" i swear sai na batar da ke humaira, sai na lalata rayuwarki sai nasa kinji kunya a idanun jama'a sannan sai na tabbatar da kin wahala, wahala mai tsanani, wahalar da zata saka ki gwammaci mutuwa ba rayuwaba,dariya ta kara yi tace "all the best idan bakai hakan ba to kai ba dan gidan sani bane, tsaki taja ta katse wayar, kallon farhana tayi tayi zuru zuru alamun tsoro a fuskarta, ko kallin ta bata kara yi ba ta huce ta bar dakin.


Har ta fita ta dawo tace "ke kuma aunty farhana indai har zaki ci gaba da wannan tsoron to tabbas ba abinda zaki iya tabukawa, idan makiyi yace zai yi maka abu, sai ka gani idan zai iya, koda gayi maka yana jin dadin to hakan acikin kaddararka take, ke ma ki dauki fasa auren nan a matsayin kaddara, sannan kuma ki cire tsoron wannan halitta aranki, jan kofar tayi ta fice, domin zuwa tayi wanka.

Tana shiga ta shirya shiga wanka, ta dan dauki minute sannan ta fito, wardrobe ta bude uniform din islamiyya naga ta fito da su a goge suke, har wani sheki sukeyi, shaf shaf ta shirya ta saka, jakarta da suke rataye ta dauka ta fito falon, jin falon shiru yasa ta nufar part din iyalle nan ma ba kowa a ciki, dan haka direct ta fita, wajen musa driver taje, mota ta shiga yajata ga bar gidan saboda ta ma makara ta sani.

Tana zuwa makarantar class ta shiga a lokacin malam ne a ajin nasu, kallonta yayi yace "aisha nuradden me ya saki makara, to humaira badai iya tsara zsnce ba, lokaci 1 ta tsarasa ta wuce ta barsa anan.

Acan gida kuwa farhana ce ta shiga dakin indo, amma bata ganta ba, nemanta take ta rasa ina ta tafi, har dakin iyalle taje bata nan, tsoro ne ya bayyana akan face dinta karara, zama tayi a kijerun falon tana kallon time, sallamar da akayi ce yasata saurin kallon kofar, ba kowa bane muhammad anas ne abokin yaya ahmad, rabonsa da gidan tin ahmad yana nan.

Zama yayi yana kallon farhana dake gyara

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login