Showing 18001 words to 21000 words out of 40600 words

Chapter 7 - AISHATUL_HUMAIRAH (Labarin Indo) HAUSA NOVEL

08 Nov 2024

4919

ce, kuma yar uwarki, dan haka banason haka, karbar girkin tayi tace fice min da gani, indo ce tace "aa mama ki kyaleta ai aradu gaskia ta fada ni kaina nasan ai yar kauye ce, dan haka ki kyaleta kuma tace ban iya cewa anti ba ko, rabu da ita zan iya ai wataran, saboda nafara koya a makaranta shi ne akai hutu amma nasan da an koma nima zan dage naje na koyo turanci.

Farhana ce ta kyalkyale da dariya tace "to mama kinji ko ai humaira batajin haushi ko mai kai mata, allah ya bata wankakkiyar zuciya wallahi, yanzu kinga ke kinji haushi amma ita ko a jikinta, salam jijjiga kai tayi tana mamakin hali irin na humaira, domin ita ba ruwanta, farhana ce ta katse mata tinanin da cewa "mama nakira broh amma yaki dagawa dama kuma so nake na tambayesa yaushe zai dawo, salma ce tace" ai kinsan hali ba dagawa zai ba, gobe zai dawo nasan kuma ba lalle ba ya dawo da safe nafi tinanin saukar dare ce, daga haka suka ci gaba da girkinsu.

Haka wunin ranar ya huce bayan da salma da farhana sai humaira suka je gyaran gashi da lalle, zo kuga indo yanda ta koma abinka da farar fata, gaba daya ta chanja tasha lalle ja da baki, ga wani gyaran gashi da akai mata, ohh ni matar uncle ashe dama indo tana da gashi, ban taba tinanin indo tana da gashi ba sai ranar, domin irin wannan gashin ne baki wuluk, gashi har gadon baya ya zubo. Fathana ce ta kalleta tace "humaira yanzu abinda ya rage miki ko shi ne kawai a samu a gyara wadannan dafaffun hakoran domin naga kamar kara dafewa suke,dariya tayi tace allah anti farhana kalle ni kamar ba ni ba, kamar wata 'yar india ashe dama ina da gashi haka yala yala, salma dai dariya take domin abin nata burge su yaje, sam ita indo bata jin haushin kowa, tana fatan ahmad ya sita fiye da yadda ita take sonsa.

Daga nan sai da suka biya ta mall ita da kanta salma ta zabomata kaya hade da atamfofi, kowanne saida ta dakko mata, masha allah mama tayi mata siyayya da bata taba zato ba, kusan komai da 5 ta tashi, daga nan suka dawo gida bayan sun biya ta siya musu kayan makulashe.

Tana yin Parking indo ta fito da dan gudunta ta shiga tin daga nesa take kwala kira "yaya farhan zo ka ganni, yana can yana danna waya yaji kira, jin muryar humaira hakan yasashi saurin fitow.

AISHATUL___HUMAIRAH
       ..... Labarin Indo .....
❤️💚❤️💚❤️💚❤️💚❤️💚❤️
    =Na=
 AISHATU BINT MUHAMMAD
       (Matar Uncle)
🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀
The Story of life childhood,
Entertainment,
And Love.

DASHEN ALLAH WRITERS ASSOCIATION

24▫️25

Kallonta yake yana murmushi, mama ce da farhana suka shigo suna murmushi suma, farhan ne yace "wayyo allah humaira ke ce wannan wai humaira dama haka kike, dariya tayi tace, nima ina nasan haka nake yaya farhan sai yau da mama ta kaini aka zamar dani haka, ai kaga na samu kudi nima sai nayi mama abinda yafi wannan dan makka dik sati sai taje, kai yaya farhan allah yaja da ran mama, kan upstairs ta haye tanayi tana fadin "bara naje na ga fuskata a mudubi.

Kamar kullun yauma haka indo ta tashi, kusa da mama take kwana, dan haka gau tana mikewa mama tace" je kiyi sallah kinji, bandaki ta shiga tinanin rannan tayi yadda farhana ta koya mata yadda ruwa zai zubo, kunna wa tayi ya fara zubowa, alwala tayo ta fito, ko second 20 ba ai ba, ta idar to mama ina kwana, salma amsawa tayi tace "lafiya lou humaira ya gajiya, dariya tayi tace mama ai bangaji ba, kece ma dai zance ya gajiya, tashi tayi ta fito, dakin farhana ta fara lekawa a zaune ta hangota tana karatun al'qur'ani, shiga tayi zama tayi ganin taki gama karatun ne yasa tace" gaskia aunty farhana nagaji kawai na dawo, ficewa tayi daga nan tai hanyar farfajiya.

Tana nan tana karewa komai na wajen kallo, jin horn yasata mikewa tana fadin 'to waye kuma wannan da zai shigo, wata black mota ce ta kutso kai, tsayawa tayi tana kallon parking din motar, mutum data gani ne ya fito ya sata sakin murmhshi, tace "laa na jikin hoto, sanye yake da kayan pilot, kallonsa take kayan sunyi matukar amsar jikinsa, ga suman nan a kwance tai luff, kamar yadda ta gansa a hoto haka ya kasance a zahiri.

Zuwa yayi zai gifta ta ya ganta sarai amma yi yayi kamar bai ganta ba, ganin haka yasa indo karasowa tana fadin yaya ahmad, wani kallo ya jefe mata, yace "dont touch me ganin bata gane me yake nufi ba, shiyasa yace karki kuskura ki taba ni, daga haka ya huce ko fishi batayi ba, ta bisa tin daga falo take kwala kira mama, aunty farhaan yay... bata karasa ba ta ji saukar rankashi, wani fitinannan rankwashi ya sakar mata yasa ta kwala ihu, sakkowar mama.


Ai fa kadawo yanzu zaka fara da 'yar marainiyar allah ko, da kallon tambaya yabi humaira data rike wajen rankwashin, mama ce tace zo nan humaira, bai damu ba dan haka yace mama katsesa tayi tace "dan allah jeka ka shirya sai kazo nasan nan da 10 mahaifinka zai karaso.

Tafiya yayi humaira ceta kalli mama tace" wallahi mama yaya ahmad ya chanja kamar bashi ne yake cewa nazo ba kuma nazo shi ne yake rankwashi na, amma kuma kinsan, katseta tayi tace ya isa to naji.

Wani dan karamin daki suka shiga, gaba daya dakin dakin yara ne komai black ne and white, ga wani dan karamin bed a gefe, da murmushi tace "laaa mama wannan shi ne dakina amma ko, kinga mama dungire mata kai tayi tace" wai humaira yaushe zaki rage surutu yau naga ikon allah, murmushi tayi tace ya hakuri, daga haka ta fito ta barta sai murna take ita kuma tai kitchen.

Sai wajen 11 mama ta fito da ledoji,zama mama tayi tana kwala mata kira, humaira ce ta fito ta tsaya tace "mama gani nazo ke kike kirana ko, eaa ta bata amsa, kiramin farhana, to tace ta wuce, a daki ta tarar da farhana tana shafa powder, tasan kashen farhana shisa tace" aunty farha ina wuni, da lafiya lou ta amsa, kizo inji mama daga haka ta fice.

Mama gatanna tace, tana zama ita kuma ta fito, salma ce tace "ki dauketa ku tafi wajen ali tailor ya gwadata sai ya dinka mata ya baki account number sai ki kawo na tura masa, daga haka suka fita suka huce.

Farhaan ya fito a gurguje yana kallon watch din hannunsa, yace 'mama wallahi na makara yau bakije kin tasheni ba, mama ce tace "ai kasan yanzu nayi yara dole na daina tashinka, matsowa yayi shafa masa kai tayi ya fita.

Kowa ya fita tashi tayi anan taga ahmad ya shigo, zama yayi a kasa yana cewa mama ko zauna mana, da murmushi tace" to ahmad ai da nadauka har yanzu baka gama hutawar ba, amma kuma gashi ka fito, mirmushin yake yayi yace "aa mama ai na fito ma, shafa masa kai tayi tace" yawwa son ya aikin ya tafiyar, alhamdulillah ya bata amsa, sai kuma yace "mama dama inaso muyi magana da ku ne, murmushi tayi tace to ahmad sai dai ka bari idan mahaifinka ya iso sai mu tattauna, dsn haka tashi kaje ka huta dan nasan zaman driving yana da wahala, daga haka ya tashi yana sosa kai.


Farhana da indo ko da sukaje wajen mai dinkin, gwadata yayi yana gamawa suka fito daga nan ta hice makaranta.

Parking tayi tace humaira zaki jirani anan mota saboda zan shiga lecture, idan kina da buwatar wani abu ki jirani kinji, gyada mata kai tayi ita kuma ta fita, tana fita ta bita da kallo tana kallon threater data nufa, shiru har yanzu bata fito ba, ga indo ta gaji ga kishirwa take ji.

Dubawa take amma ba ruwa ba alamunsa dan haka ta fito daga motar, tana sakkowa ta fara kokarin nemowa kanta ruwa, wasu gungun samari ne suka hangi imdo ta fito, daya ne ya kalli daya yace kai kalli wata halitta, wanda aka nunawa ne ya lashi baki yace "ai kuwa wannan kamar ba yar mutane ba, kaga baba musan yadda zamuyi da ita kawai tin kafin dare yayi mana.

Daya daga cikinsu ne ya ce shi zai je amma shi zai fara aiki, dikansu sun yadda, tafiya yayi daidai gabanta ya tsaya yace" yammata me kike nema, a takaice tace masa ruwa, zo na kaiki inda ruwan yake binsa tayi ganin yayi hanyar mota, anan take wani tunani ya fado mata, ai irin haka ce ta faru a film din data gani wancan satin.

A take launin idanunta suka fara chanjawa, gaba daya kana ganinta zakaga kamar aljanu, kafim ya ankara ta jawosa da karfi da hannu daya, kallon wani block tayi ta kwada sa da ita.

Sauran gayun kuwa kokarin gudu sukayi, inda a daidai nan indo ta zube tana ihu, farhana ce ta fito, ganin cincirindon mutane yasa bata bi ta kansu ba domin tasan ta bar indo tana jiranta, shiga tayi amma ganin wayam Yasata fadin, dama nasan za'ai hakan tana can gulma, shisa bata rabo da surutu, kutsawa tayi ta fara shiga, sai dai ganin indo a kwance ta sankare yasa hankalinta ya tashi, rasa mai taimakonta tayi sai da kyar aka samu aka kaita arabic department, sai bayan awa 1 sannan ta dawo dai dai, mikewa tayi tace anty farhana mutafi ko, daga haka bata kara magana ba.

Koda ta dawo gidan ma ba wanda ta kula, abinci ma da mama tace mata, amsa ta bata da nakoshi,dakinta ta huce, farhana ce ta fara bata labarin abinda ya faru, salma tayi mamaki kwarai domin tabbas humairah na wa i hali.

Sai bayan 30 mint ta shiga dakin nata, a kwance ta ganta sai murkususu take, ga in haka yasa ta matso gana dafata, sannu sannu humaira me yake damunki, da kyar ta iya furta marata mama, dan allah ki bani magani, tashi tayi da kyar ta samu magana ta bata, bata dade ba ciwon ya lafa, kallon mama tayi tace "mama dan allah ki bani wannan audigar da mata sukesawa idan suka jini a kasansu, doke bakin tayi tace aa ba haka ake cewa ba, haka ake cewa pad kar na kara jin kin fadi hakan, tasgi tayi cikin siyayyar data yi mata fa dakko ta bata, ta fito.

Mamaki taje dama indo tana yin period, dole dama da sake duba da yadda kirjinta ke fara fitowa, anan ta watsar da tinanin domin ta hado mata tea. AISHATUL___HUMAIRAH
       ..... Labarin Indo .....
❤️💚❤️💚❤️💚❤️💚❤️💚❤️
    =Na=
 AISHATU BINT MUHAMMAD
       (Matar Uncle)
🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀
The Story of life childhood,
Entertainment,
And Love.

DASHEN ALLAH WRITERS ASSOCIATION

26🌀27

Ko da ta dawo zama ganin bata kan bed yasatai tinanin tana tinanin tana toilet hakanne yasa ta ajiye tea din ta fito daga nan ta huce kitchen domin a yau zai dawk, dik da ma dai yace 10 na safe amma kuma gashi bai dawo ba batasan dalili ba, dan haka tasan tabbas yana hanya.

Girkinsu sukeyi sai can indo ta shigo, wajen zamanta ta nufa bakin sink ta zauna, kallon mama tayi tana wanke cup din datasha tea din.

Mama ce tace "humaira tin yaushe kika fara period, farhana a zuciyarta tace" to fa ashe yarinyar ta girma, maganar indo ce ta katseta tace "mama tin a makaranta kuma wata malama ce ta koya min yadda zan tsaftace jikina, da yadda zanyi wanka idan ya tsaya, dan murmushi tayi tace" to humaira yayi zo muje dakina ke farhana  karasa min akwai maganar da zamiyi da humaira.

Farhana bin su tayi tana dariya, lokaci guda ta tina abinds ya faru dazu take tsoro ya darsu a ranta, kamar ba ita bace me dariyar.

Zama mama tayi tace "humaira abinda nakeso dake shi ne, ki koyi sirri a rayuwarki kinji, kinga yanzu kin riga ds kin girma kin fara menstruation, a ka'idance dik Yarinyar data fara wannan abu to anasa ran hankali yazo mata, saboda haka yanzu ba komai ne zaki na fallasawa ba, kuma karna kuskura naji kinfadawa wani cewa period kike kinaji na ko, humaira da eaa ta bita kallo daya tai mata tace humaira ya ake wankan jinin haila.

Humaira shiru da bazatayi magana ba sai tace"YANDA AKE WANKAN HAILA

Wankan janaba iri biyu ne a taƙaice.
1. Wankan janaba na kamal
2. Wankan janaba na Ijza

Wankan janaba na sifatul kamal ana yinshi ne kamar haka:-👇👇

1. Niyya (A zuciya)sai kayi Bismillah,sannan sai ka wanke hannunka sau uku…!✋

2. Sai kayi tsarki ka wanke duk inda janaba koh Jinin haila ta ke sau uku, idan baka aski akai-akai wato kana barin gashi anso ka cuccuɗa gashin gabanka domin janaba zata iya ɓuya ko ta bushe ba tare da ka sani ba.

3. Sai kayi alwala irin yadda kake alwala idan zakayi sallah ,ana iyayin alwala so daya daya,ma’ana basai ka wanke koh ina sau uku ba,amma bazaka wanke kafa ba saika kammala wankan..!🦵

3. Sai ka diba ruwa a tafin hannunka guda biyu ka mummurza gashin kanka sosai sau uku saboda ana so duk ƙofofin gashinka da suka bude a yayin fitar shaawa  koh Jinin haila su koma daidai. Malamai sunce anfiso ka diba ruwan da tafukan hannayen ka maimakon ka kwara ruwan a kanka saboda kwara ruwa akai yayin wankan janaba koh Jinin haila yakan sa ciwon kai domin kofofin gashi suna budewa a lokacin fitar da najasar..

4. Sai ka raba jikin ka gida biyu, ka fara wanke bangaren dama tun daga kafadarka har zuwa kasa. Sannan shima ɗaya bangaren na hagu sai ka wanke ko ina tundaga kafadarka har zuwa kasa..

4. Daga karshe sai ka wanke ƙafafunka suma ka fara da dama sannan hagu.

Idan kai haka ka gama wankan janaba ta sifatul Kamal..Kuma  zaka iya yin sallah da wannan alwala da kayi a lokacin wankan tsarki ba sai ka sake wata alwalar ba.

Wannan wankan shi akeyi a wankan Janaba, Wankan Haila, Wankan Jinin Haihuwa wato Biƙi. Wankan Mamaci, Wankan Musuluntar Kafiri, Wankan Idi da kuma Wankan Jumu'a.

Banbancinsu kawai shine niyya, kowanne idan zakayi sai ka Kudirta a zuciyarka kayi niyyar yin "wankan abinda kakeso kayi kamar,Janaba,Biki,Idi, Juma'a, ko kuma Haila"

Kusani duk wanda ya mutu bai iya wankan tsarki ba akwai azaba inji manzon Allah SAW

Da mamaki take kallon indon, a ziciyarta ta furta alhamdulillah amma wannan malama allah ubangiji yayi mata albarka, inayi mata kallin sakarya ashe tana da kokarjn haka, mama ce ta kara kallonta a karo na biyu tace "a wace sura kike a makarantar, humaira ce tace" aa mama ai sai dai makarantar allao kuma  izuna 2,sallamar da akayi ce yasata yin shiru.

Kallon humaira yasa ya daure fuska, humaira tana ganinsa ta mike zata fita domin kuwa bata manta da rankwashin da yayi mata ba, har ga allah yanzu dama haushin sa take ji, gaoshe da mama yayi yace "dama mama zan fita shi ne nace bara na biyo na fada miki, da to ta ce masa, allah ya kiyaye daga haka ya tashi ya fito.

Nemanta yake amma bata falo, yana saka kafarsa a kofar farfajiya ya hangeta tsakiyar flowers din wajen, karasawa wajen yayi yace ke zo nan, humaira zuwa tayi ta fara zaro ido"ji tayi tace" i swear daga yanzu kika kara ganina baki gaishe ni ba sai na karya miki kafa, mai suffar aljanu kawaj, daga hak ya fice ya barta anan a tsaye.

A cikin wani irin salo yake driving motar tasa, yadda kasan baya san tafiya haka yake, yana cikin driving wayarsa ta fara ringing, kallon wayar nayi amma bansamu damar ganin me akasaka ba sakamakon saurin daukarta da yayi, cikin wata murya ya furta "hello sorry on my way daga haka ya katse wayar yaci gaba da kallon hanya.

Bai dade da fita daddy ya shigo, a falo ya tarar dasu su dika sai hira akeyi, muryar indo tafi ta kowa tashi, shigowa yayi dsuke da sallama a bakinsa, amasawa sukayi farhana ce ta tashi, tare da hugging dinsa tana fadin daddy sannu da zuwa, da yawwa ya amsa mata sannan ya kalli mamam, murmushi yayi mata ya huce part dinsa.

Mama ce ta tashi ta bisa, suna zaune sukaji karar wayar farhana, dagawa tayi tace to yaya Kabeer gani nan amma ka shigo palon mana, daga nan ta katse, juyawa tayi tana kallon indo tace mata "kije zakiga wani bako ki fada masa ya shigo.

Ita kuma ta shige, indo ce ta mike ta fito a jikin wata mota ta hangesa kirar benz a fili ta furta masha allah allah mai halitta, kaga wani mutum kamar balarabe, karasawa tayi tace" ina wuni aunty farhana tace ka shigo, daga haka ta juya shi kuma ya biyota a baya.

Tana shiga zata huce dakinta, sai ta tina ai tace ta kai masa lemo da ruwa kitchen ta shiga dayake farhana ta fara koya mata komai, a plate ta sako ruwa da lemo sai youghurt ta ajiye masa sannan ta juya ta koma dakinta.

Kowa yana kan dining yana cin abinci, indo kuwa bataso dan ba yadda zatayi, daddy ne yace "humaira yadai, dan tabe baki tayi tace" allah dady banason cin abinci a wannan teburin, farhaan ne ya kyalkyale da dariya yace "daddy tafi gane kasa fa, dik wannan maganar da ake ahmad bai sa baki ba sai ma tashi da yayi zai tafi, daddy ne yace" idan kayi sallah ka fito kasame ni a falo zamuyi magana da kai, juyowa yayi yana dan sakin fuska yace "toh daddy.

AISHATUL___HUMAIRAH
       ..... Labarin Indo .....
❤️💚❤️💚❤️💚❤️💚❤️💚❤️
    =Na=
 AISHATU BINT MUHAMMAD
       (Matar Uncle)
🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀🌷🌸🌷🍀
The Story of life childhood,
Entertainment,
And Love.

DASHEN ALLAH WRITERS ASSOCIATION

28✨29

Gaba daya falon kowa yana zaune idan ka cire indo da ita tin tini ta kwanta, saboda zazzabin daya rufeta, dik da dai farhana tayi mata allura.

Kowa yayi tsitt daddy ne ya bude taro da addua, sannna ya fara bayani kamar haka"assalamu alaikum warahmatullahi ta'ala wabaraka tuhu, dalilin taraku anan ba wani abu bane, illah saboda wasu abubiwa da sukazo mana, sannan kuma ina fatan kowa zai farinciki.

Abu na farko shi ne, na riga da munyi magana da mama da kuma mahaifin kabeer akan aurenku ke farhana, gashi yanzu ma har mun tsai da rana nan da wata 2 masu zuwa, farhana a fuskarta kuwa murmushi tayi a zuciyarta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login