Showing 24001 words to 27000 words out of 45625 words
ai bawani makara akayi ba tun da karfe 12:50pm muka isa makarantar kuma karfi 12 da rabi ake tashin su, kuma tun kan ɗalibai su watse mai gadi yace aka ɗauke su, to ashe dai ba'a makara zuwa ɗaukar su, ana zuwa ɗaukar su tun shabiyu ajira su har sai an tashe su a ɗauko su a dawo da su, babu wani ɓata lokaci a zuwa ɗaukar su, kai kuwuce mushiga ciki!."
nayi maganar cikin haɗa haushi biyu zuwa uku, akan me zaice ba'a zuwa ɗaukar su kan lokaci. sannan kuma wace dalilin ne yasashi zuwa ɗaukarsu ina ruwan shi dasu dakuma rayuwar su, yasa nayi kuka da tunanin ansace su ne. sannan ganin yan da yaran suka manne masa sai kiran sa da sunan dana hanasu suke.
tun da nafara maganar idanunsa akaina yayin da yake shafa sajen fuskar sa, kafaɗa yaɗaga kana yace
"Kinyi kokari, kiyi wayon sanin hakan tukun dan da kaɗan kikafi yaran wayo."
ido na waro amma lallai mutumin nan yana da rainin wayo karo na biyu kenan da yake cemin wai bani da wayo, yaran dana haifa yake cewa wai dakaɗan nafisu wayo. wani kallo na watsa masa tare da murguɗa baki nace "Allah yasa wayon suka fini, mece ce matsalar ka?."
nayi maganar tare da kuma murguɗe baki.
Bappa yace "Um to hakane kam amma ana zuwa ɗaukar su akan lokaci sai dai ɓacin rana, amma akiyayen shiyafi, mun gode sosai, in sha Allahu za'a kara azama wajen zuwa ɗaukar su."
hannunsu na fizgo ina faɗin
"Kuzo ku wuce ina magana kuna tsaye."
najanyo su fuuu muka nufi ciki anan na barsu shi da Bappa, cikin haushin jin Bappa yana saurarar sa, har shi zai gwada wa mutane yan da zasuyi da rayuwar su, ina ruwanshi, irin mutane masu shegen shishshigi kan abun da bai shafe su ba.
sai da muka shiga parlour kafin na sake hannun su, na zauna kan kujera, ina duban su sukam ma ko a jikin su sai wata tsafgar su suke.
kunnuwan ko wannen su na rike naɗan murɗa da karfi, suka haɗa baki wajen cewa "Wayyo Mommy."
nace "Sai na sinke kunnen har idan baku dai na abun da na hana kuba, wato duk hanaku da nake tayi bakuji ba ko shine yau abun naku yagirma har da binsa, kunsan shi ne? baku san mutum ba kukama binsa har da shiga motar sa, ina kuna so a yanka kanku ne?."
kai suka girgiza da sauri tare da faɗin
"A'a-a'a Mommy." nace "To ban hanaku ce masa Daddy ba bana ce muku ku bakuda Daddy nice Mommyn ku nice Daddyn ku ba?, ban ce kada wani ya sake baku abu ku karɓa kuci ba?, shine har yau zaku bishi kushiga motar sa, kunsan shine?,
to sai nayi muku duka yau sai na kaiku wa ɗawisu ta caccake ku bari ku gani."
namike tsaye tare da ruko hannun su ina cigaba da faɗin
"Ɗawisu kawai zan kai ku wasu sune zasu yin maganin ku."
kuka suka sake da karfi suna faɗin "Wayyo Mommy kai ki kai mu."
"Ai bazaku bari ba sai na kai ku gurin su su hana ku da kansu."
nayi maganar ina jansu.
ihu sosai suke suna faɗin
"Mommy mun bayi." komawa nayi na zauna kan kujera ganin sun tsorata sosai najasu jikina na rungume su, ina faɗin
"To kuyi shiru nafasa kai ku amma idan kuka kara sai na kaiku, zaku kara ko?".
kai suka girgiza da sauri nace "Kada ku sake zuwa gurin wan da baku sanshi ba bare har kushigs motar sa, kuma kada ku sake ce masa Daddy shi ba Daddyn ku bane nice nan Daddyn ku kunje jo?."
kai suka kuma gyaɗa wa suna jan shashsheka.
a hankali narika shafa kansu cikin tsananin tausayin su, wasu zazzafan kwalla ne suka ciko ido na, ban dakatar da su ba har sai da suka gangaro kan fuskata ta, nakai tafin hannuna na goge, yayin da nake daɗa mannna kan su a kirjina, ina jin tausayin su na daɗa shiga na.
maganar zuci nafara yi yayin da zazzafar hawaye mai cike da ɗin bin kuna ke cigaba da zuba a ido na.
"Kuyi hakuri bana so ku sanya wa ranku abun da babu shi a rayuwar ku, nafiso ku tashi da sanin cewa bakuda shi ni zan zame muku garkuwa uwa uba."
daɗa rungume su nayi ina jin kuna cikin raina lallai tabbas ba shakka anyi min tabo mai muni ni da ƴaƴana wan da bazan taɓa mancewa da shi a rayuwa ta ba.
kwallar idanuna na share tare da kokarin danne damuwa ta.
ɗago wa nayi jin sallamar Bappa na amsa ina mai cigaba da kokarin danne damuwar dake azalzala ta cikin zuciya, naɗan gyara zamata cikin dabara na share ragowar hawayen idona, ya karaso ya zauna. huf su Nasmah suka mike a jikina Naseem daya dubi Bappa yace "Bappa Daddy fa yana waje?." sai kuma ya juya da sauri yana faɗin
"Dan je guyin Daddy." ido na ware da mamaki kamar ba yanzu nagama masa barazana har da kukan sa ba amma gashi ya tashi yana faɗin zai je gurin mutumin.
Bappa yayi murmushi da faɗin
"Dawo nan mutumina, ai yatafi." yafaɗa yana ruko hannunsa kana ya cigaba da faɗin
"Yaro kenan shi kamar dabba yake duk mai kyautata masa to zakaga yana son kasan tuwa da shi,
wlh nayi mamakin ganin Ahmad Tijjani Sabil, nakuma yi mamakin ganin sa tare da yaran nan, koda yake hakan ba abun mamaki bane."
da ɗan mamaki na dubi Bappa jin sunan mutumin a bakin sa, Bappa ko daɗa faɗaɗa murnushin dake bayyane kan fuskar sa yayi kana yaci gaba da faɗin
"Yaron kirki ne sosai kinga ma bai ganeni ba sai da nayi masa tuni,
ai wannan yaro Allah dai ya masa albarka yakawo babban gudunmawa cikin rayuwar mu a Ruga, ya inganta mana rayuwa yakawo haske cikin rayuwar mu kwarai da gaske, lokacin da ɓarayin shanu suka addabe mu babu dare babu rana, sukashe mana makiyaya su kaɗa mana shanukai, kwasam sai Allah yajefo mana shi, wata rana yazo rugar mu a matsayin bako watan sa guda tare da mu, ranar da yazo ɓarayin shanu suka shigo rugar mu, suka saci shanukai suka raunata mana makiyaya Allah yatakai ta kwanan su na gaba, sai dai mun rasa makiyayin mu guda ɗaya kuma mun san su suka sace shi, ya kwashe su yakai su asibiti cikin gari, ranar hankali yatashi muka ɗau aniyar ɗaukar mataki da kanmu.
ranar da ya cika sati uku, har lokacin ɓarayi basu kara kawo mana hari rugar muba sai dai rugar da muke makota da su,
da yammacin ranar an je kai masa abinci kamar yadda aka saba sai aka iske shi da wani makiyayin mu cikin ɗakin da aka bashi yake kwana ciki, makiyayin da muke tunanin ɓarayin shanun nan sun tafi da shi, ya ɗaɗɗaure shi, yanata gana masa azaba da wani irin na'ura.
wan da yakai abincin yakurma ihu nan da nan jama'a suka taru munyi mamakin ganin makiyayin mu tare da shi yana bashi azaba,nan ƴan gari suka rika cewa a kashe shi ashe shima ɓarawon shanu ne muke tare da shi.
cikin tsawa yace duk mudakata yace kunzo nan kuna ta wani har gowar ku mara amfani kuje ku tare ƴan ta addan da suka dunfaro rugar ku domin kona ku su kuma tafi da dukiyar ku. cikin rashin fahimtar abun da yake nufi muka shiga kallon junar mu, shiko ci gaba da baiwa makiyayin mu azaba yacigaba da yi, dai-dai lokacin kuwa muka soma jin karar bindiga daga can nesa, nan fa hankali yatashi jama'a suka fara kokarin watsewa domin ɗaukar makamin kare kansu.
wani irin gigitaccen kara makiyayin nan ya saka lokacin da ya datse masa yasar hannun sa guda,
cikin tsawa yace masa, Ta wani kusurwa zasu shigo,? su nawa ne kuma?, wasu irin bindigogi ne a hannunsu?!!.
cikin tsananin jin azaba yasoma magana cikin matukar wahala yashiga bashi amsar tambayar dayayi masa.
munyi matukar mamakin jin abun da makiyayin nan yafaɗa to me haka yake nufi?, a lokacin bamu sami damar jin amsar tambayar muba,
sai muryar AHMAD Tijjani Sabil mukajiyo da karfi yana faɗin.
Kowa ya koma gidan sa kada wani yafito waje,duk abun da zakuji kada ku fito. kamar yadda yafaɗa kuwa haka mukayi batare da musu koni man jin ba'a si ba kowa yayi gidan sa, sai dai bamu zauna haka ba kowa da makami a hannusa domin kare kai.
ranar tashin hankalin da muka shiga ba zai faɗu ba, dan muna shiga gida ƴan tadaddan nan suka karaso cikin rugar mu, wasu suna kunce dabbobi wasu kuma suna ta harbi.
shigowar su dakamar minti ashirin, muka jiyo jiniyar sojoji ta ko ta ina suka sanya rugar mu a tsakiya.
nan suka shiga bata kashi ranar kamar rugar mu zata fashi dan harbin bindiga, an ɗauki tsawon mintina 30, kafin kikaji guri yayi tsit.
sai hayani ya da magana da turanci haɗe da hausa ake,
can aka fara magana da abun sauti irin wan da hukuma suke magana da shi domin sanar wa ko bada umurni wa al'umma,
aka ce kowa ya fito, nan muka fito cikin ɗar-ɗar duk da asanar wan nasu sun sanar mana da cewa hukuma ne ke magana,
amma a tsorace muke kuma bamu fito haka kawai ba sai da makaman mu, domin kare kai, duk da kuwa munsan su bindiga ne a hannusu mukuma akasin haka sai dai munsan Allah yana tare da mu.
koda muka fito ganin hukumar ne da gaske nan hankali yaɗan kwanta kaɗan, Allah yabasu nasarar cafke ƴan tadaddan nan wasu daga cikin su sojojin sun harbe su gasu kwance cikin jini, wasu kuma gasunan kwance a ɗaɗɗaure bindigogin su a zube a gefe.
Ahmad Tijjani Sabil yana tsakiyar hukuman nan yayin da wannan makiyayin namu ke kwance a gabansa shima a ɗaɗɗaure.
bayan jawabi da ban hakuri da hukumar nan sukayi mana, da alkawarin bamu kariya da tsaro, suka tattari ƴan ta'addan suka saka su cikin mota, Ahmad ya ɗaga wannan makiyayin namu yatura shi cikin mota,
nan wasu daga cikin sojojin suka tafi da ƴan ta'addan suka bar motan soja guda.
ranar acikin rugar mu suka kwana suna bamu tsaro kwanan su uku kafin suka tafi,
Ahmad kuwa bai bar rugar ba har sai da yagina mana makaranta da asibiti yazuba mana malaman asibiti dana makaranta, makarantar ne ma Fatu take ciki, tun daga lokacin muke samin tsaro sosai, munyi matukar farin ciki da zuwan Ahmad cikin mu dan kuwa ya tallafawa rayuwar mu kwarai da gaske, har rana mai kamar ta yau ba'a kuma shiga rugar mu da sunan sata ba."
Numfashi na sauke cike da alhinin labarin da Bappa ke bani nace
"Ikon Allah to shi wannan makiyayin naku yaya iyayen sa sukayi dajin shima ɗan fashin ne, yanzu ku duk zaman ku da shi bakusan shi ma ɗan fashi bane?".
yace "Sam bamusan ɗan fashi bane, to ai shi asalinsa ma ba bafulatani bane, zuwa yayi rugarmu tun yana yaro yace zai rika yi mana kiwo muna biyan sa, shekaru 16 muna tare da shi, muka bashi duk wani yar da ashe macuci ne bamu sani ba, yana ha'intar mu, har sai da Allah ya turo mana Ahmad Tijjani Sabil."
kai na jinjina cike da mamaki ina faɗin
"Tab lallai to shi ya akayi yasan ɗan fashi ne shi da yazo bai jima ba, ku da kukayi shekara da shekaru da shi baku sani ba?."
Bappa yace "Wlh duk kanin mu kowa abun da yayi ta faɗa kenan bayan komai ya lafa, sai dai bamu sami amsar tambayar ba, dan ko shi Ahmad ɗin da muka tambaye shi bamu sami wani kwakkwaran amsa ba, sai muma muka bar shi bamu tsanan ta masa tambayar ba, munji daɗi da farin cikin da Allah ya nufa shi zai zame mana karshen matsalar mu."
Bappa yana maganar ne cikin nuna tsantsar farin ciki da jin daɗi...
na ce "Lallai kam to Allah ya tsare na gaba."
ya am sa da amin amin kana yamike yana faɗin "Bari na shiga ciki."
yana tafiya naruko hannun su muka haura sama...
Yauma kamar kullum narako su Naseem ina tsaye har sai da naga fitar su,
kana na koma ciki, wanka nayi ina gama kimsawa nayi breakfast, wan da nasa Zulai takawo min shi cikin ɗaki,
ina gama breakfast ɗin nahaye gado dan bacci ne a idanuna
ban farka ba, sai wajen karfe shabiyu saura ƴan mintina dabasu fi 20 ba, wayata na janyo na kira Number Yakubu, kasan cewar yau juma'a da wuri ake tashin su, bugu ɗaya ana biyu ya ɗaga, nace
"Kayi maza kaje ka ɗauko su Nasmah." yace "To Hajiya da ma nima yanzu ina kan goge motar kenan yanzu zan tafi."
"Kabar wani goge mota katafi kaje ka ɗauko su." nayi maganar tare da kashe wayar, mikewa nayi nashige bathroom nayi wanka tare da dauro al'wala, ina fita na sauya kaya. ganin lokacin salla da saura sai na nufi kofa nafita kasa na sauka.
Talatu da Zulai duk suna parlour'n suna ganina sukayi min sannu da fitowa,na amsa ina yi musu yaya aiki, suka ce alhmdllh, an tsaftace gurin ko ina yayi tsaf sai kamshe ke tashi.
ina jin matukar daɗin zama da su sabo da suna baiwa aikin su kulawa sosai.
a ɗaya daga cikin kujerun parlour'n na zauna, tare da saka idanuna kan TV ganin shirin da ake.
zamata baifi da minti 10 ba najiyo muryar su Naseem daga kofa ta waje suna kwaɗa sallama, kallon kofar nayi da murmushi akan fuska ta, suka turo kofar da gudu suka shigo suna faɗin
"Mommy mun dawo Mommy mun dawo."
faɗaɗa murmushi na nayi tare da faɗin
"To sannun ku da dawowa."
in da nake suka taho da gudu na buɗe hannuna suka faɗo ciki na rungume su, ina dariya da faɗin
"An yi karatu sosai dai ko?."
kai Naseem ya gyaɗa. nace "To madallah." na dubi Nasmah nace "Likita na anyi karatu sosai ko?." itama kai ta gyaɗa tana washe baki, Naseem ko baki ya turo yace "Mommy ni baki ce min tojan ki ba."
cikin muryar dariya nace "Oh soja na."
shima dariyar yayi cike da jin daɗin sunan dana kira sa da shi.
Nasmah ko mikewa tayi a jikina tarike kugu tare da jujjuya idanun ta tace
"Ai nafi Naseem yin kayatu da yawa yana ta wasa da wani yayo, ni nayi kayatu da yawa dan yika yima mutane ayyuya kuma."
ido na waro yan da take yi da ido ya bani dariya nace
"A.a.a Naseem ɗin wato wasa kaje ka zauna kake yi ba karatu ba ko?".
nayi maganar tare da rike haɓa ina kallon sa, yace
"Hum kaiya ne take yi, nayi kayatu da yawa kuma Daddy yace nayi kayatu da yawa idan nayi da yawa da yawa, yace dai jo ya auke mu a gida."
Nasmah tace "Um ai Daddy yace ni ne dai jo ya auke ni nafika kayatu da yawa, ai nayi mishi kayatu da yawa ma yau kuma."
Naseem yayi kamar zai ture ta yana faɗin
"Ai nima nayi ma Daddy kayatu da yawa."
ido na waro da mamakin kin sunan da suke ambata sunan da nayi ta musu barazana kan kuma faɗar sa, nace
"Kai kurafa min baki, wani Daddy'n."
nayi maganar cikin tsawa dan ni a tunani na ma wani ne daban ba wancan mutumin da na kwaɓe su da shi ba.
Yakubu da yashigo rike da school bag ɗin su yakaraso ciki Talatu ta amshi jakar tayi cikin bedroom ɗin su da shi, ya washe baki da faɗin
"Ai Hajiya Ahmad Tijjani Sabil suke nufi, ai ina isa na iske su tare da shi abakin get din makarantar su tare da shi, naji yana tambayar su karatu suna ta zuba masa karatun da aka musu, nace kai ashe fa yaran nan za'ayi masu ilimi ne anan wlh kuwa."
yayi maganar yana mai cigaba da washe baki.
fuska na tsuke sosai tare da mai da dubana kan yaran kana na mike tsaye na ruko hannun su na janyo su muka haura sama,
muna shiga ɗaki na sake su ina faɗin "Ni ƴasu yazan yi da yaran nan wato ku bakwa ji, duk abun da zanyi ta faɗa muku bazaku jiba shi wannan Ahmad yake ko wane wlh dole na ɗau mataki a kansa, idan bana ɗau mataki akan lamarin ba zai rushe min ginin danake ta gina shi,
yana ta kokarin rushewa ya haka ne kam, ina ruwan shi da su meye haɗin shi da su da zai rika sanya musu wani ra'ayi a cikin zukatan su."
Duban yaran nayi nama rasa wani irin masifa zan musu, ko da na musu ma abanza gobe zasu kuma,
zubewa nayi bakin gado da tunanin yan da zanyi na ɓullo wa lamarin, yazama dole na ɗauki mataki kan lamarin idan ba hakaba, to kuwa tabbas ginin da nake ta kokarin gina shi domin yayi karko to kuwa zai iya rusa min shi, tabbas zan ɗauki mataki kansa, "Amma mene ne mafita?. nayi wa kai na tambayar ina gyara zama ta,
"Mafitar kenan kawai ki canza musu makaranta."
zuciya ta ta bani amsa, kai na jinjina da gaskata abun da zuciya ta ta faɗa min, hakanne kawai mafita ta yadda zasuyi nesa da shi, idan kuma ba haka ba to kuwa abun da nake ta kokarin cire masu kwaɗai tar sa a zukatan su shine zai faru, dan kuwa in har hakan yaci gaba da faruwa zasu tashi da sanin wani mahaifi a ransu wan da bana son su san haka, nice nan uwa kuma uba a rayuwar su, sam bana son su tashi da jin cewa zasu sa mi uba ni zasu cigaba da jina uwa kuma uba a rayuwar su.
bana so su sanyawa ransu abun da baza su samu ba a rayuwar su, to mene ne amfanin sanya wa ransu hakan,
gara kawai su san cewa ba su da uba, su ji a ransu ni ce uban nasu kuma ni ce uwan su.
wannan kaɗai shine mafita in sauya musu makaranta in nesan tar da su daga gare shi, in ma koyarwa yake a makarantar imma mene ne baya sake ganin su bare ya cigaba da cusa musu wani ra'ayin, ai dai sun rabu bashi basu, bazai sake ganin suba suma haka bare su sake kiran shi da wani Daddy,
"Ɗan rainin wayo har da cewa surika ce masa wani Daddy, sai kace wani uban su ko meye gamin sa da su oho."
naja dogon tsaki tare da yin kwafa kana na mike, nashiga tuɓe musu uniform ɗin su, ina faɗin
"Ku da shi ɗin duk zanyi maganin ku."
bathroom na jasu da kai na nayi musu wanka yau, muka fito na