Showing 9001 words to 12000 words out of 45625 words

Chapter 4 - HAMDAH part 3 Complete hausa novel

RASHEEDA   

04 Oct 2024

12669

farin ciki mara misaltuwa, wan da ita kanta batasan na mene ne ba.

Haka tarika binsu tana raba musu cike da shauki da jin daɗin da yagama baibaye zuciyar ta, har sai da ta tabbatar da kowa ya samu, kafin ta koma cikin mota tana jin su suna daɗa bin ta da addu'o'i mai kara mata nutsuwa da kwanciyar hankali.
daga masallacin kuwa titi-titi suka fara bi in da mabarata ke zama suma tarika mika musu sadaka. kana suka wuce asibiti, har sai da kuɗin da ta fito dashi yakare kafin tacewa direba su koma gida....



*(a can kasar Saudiyya cikin masarautar Saudi)*


Da sauri nafito daga cikin bathroom ina gyara gashin kaina dana wanke yazubo ya rufe min fuska har bana iya ganin hanya,
cikin hanzari na nufi gaban mirror karamar towel in dake rike a hannuna na naɗe shi a kaina ina tsane ruwan dake ɗiga daga gashina.
kana na ɗau na'urar dake busar da gashi nabusar da gashin, batare da ya bushi duka ba, nabaza shi ta baya domin iska yakarasa busar da shi.
zama ta na gyara na ɗau mai nasoma shafawa a jikina.
daga cikin mirror nake hango su Ukhtee ita da su Naseem sun sata a tsakiya sai surutu suke zuba mata, suyi da hausa su gwama da larabci abun ka da kwakwalwar yaro sukam tuni suka fini ji da iya mayarwa ma.
kai na jinjina a raina nake cewa
"Kai waɗan nan yara da surutu suke ko surutun wa suka ɗauko?."
ko ɗazu dasuke ta zuwaba Mammaa surutu sai cewa tayi wai ni suka gado, niko ina nake da surutu irin haka.
idan kaji maganar su kamar wan da sukayi shekaru huɗu wan da ko shekara uku basu cika ba saura wata huɗu nan gaba.
nayi murmushi kawai tare da girgiza kai, ganin Naseem yajuya fuskarta gareshi in zayi magana Nasmah ma haka.
wai su in zasuyi magana ala dole sai mutum na kallon bakin su in bai kallaba sun rika juyo da fuskar shi kenan.
wayan Ukhtee ne yashiga kara taɗago wayar tana dubawa kana ta maida duban ta gareni, daga cikin mirror'n muke kallon juna,
ganin ta mai da kallon ta kan wayar namike da sauri dan nasan ni ake kiran ganin yan da tayi zuruu tana kaloon wayar tawani langwaɓar da kai,
da sauri na isa bakin gadon, ina faɗin
"Bappa ko?". kai ta gyaɗa tare da mika min wayar, na amshi wayar na ɗaga kiran tare da kara wayar a kunne.
"Assalamualaikum Bappa." daga cikin wayar Bappa yace "Ke HAMDAH me kike yi ne har yanzu baki shirya ba."
da sauri nace "Ina kan shiri Bappa yanzu nafito daga wanka ina kan shirin, ina shafa mai ne yanzu." yace "Kada fa ki tsaya wani dogon shafe-shafe kisaka kaya kawai kada jirgi ya tashi ki rasa jirgi kada ki tsaya shiririta irin na rannan."
"To Bappa yanzu zan gama".
nakashe wayar ina mai jin wani farin ciki. wan nan karon bazan yi wasa ba kamar na wata guda da ya wuce, haka nayita lalawai har jirgi yatafi a bun sa, wannan karon kam ba Bappa kaɗai keson komawa ta ba ni kai na inason komawa kasata, hankali na gaba ɗaya yakoma kasata yanzu.
ina so najini a cikin ta, ba naganni cikin kasata kaɗai ba, ina so naganni cikin ahalina duk da nasan hakan ba abu mai sauki bane, har idan Abba bai sauka daga fushin da yake dani ba.

Mika mata wayar nayi ina kokarin juyawa, wani kiran yakuma shigowa.
murmushi nayi ganin Bappa ne yakuma kiran, da safiyar nan kiran sa na shida kenan kan nayi sauri kada jirgi yatafi.
"Hello Bappa". nafaɗa ina kai wayar kunne na, muryar sa na jiyo yana faɗin
"Kada ki ɓata lokaci dai kinji ko, kisaka kaya kawai kada ki rasa jirgi ki hanzarta."
nace "To Bappa."
na sauke wayar na mika mata da sauri na koma gaban mirror, a gaggauce nakarasa shafa mai sai pauda da man baki.
na mike da sauri na isa bakin gado in da dama nan nacire kayan da zansaka na aje na ɗauka na sa, dan sai da na shirya su Naseem da Nasmah kafin na shiga wanka, shiyasa shirin yayi min sauki.
tun da Bappa yakira waya nalura da yanayin Ukhtee gaba ki ɗaya yanayin ta ya sauya tayi wani ziruu da ita,
kai na kawar dan bana son muhaɗa ido da ita, dan yanayin nata zai iya sa jikina ya mutu.
cikin hanzari na kammala saka kayana,
ina cikin sa kayan ban kai ga gamawa ba Bappa yakuma kira.
Nan ma kuma faɗin nayi sauri yace, cikin hanzari na kammala saka kayan.

Na dubi Naseem da Nasmah ina faɗin
"Kutashi muje ko." ido
Naseem ya kura min yayin da hannayen sa biyu ke dafe da kuma tun sa kana ya ce "Mommy mataiyaci amuje?".
Nasmah ma tace "Tayan kaya amuje ko Mommy?." kai na girgiza musu nace
"Ba siyan kaya ko masallaci zamu je ba, kasar mu zamu koma can kasar mu in da aka haife mu."
ido yaran suka ware suna kallona kana Naseem yakuma cewa "Mommy kasar mu in da aka haife mu?."
yy maganar yana zura yatsarsa cikin baki alamun mamaki irin na yara.
kai na gyaɗa masa tare da ruko hannunsu ina faɗin "Kutashi muje." dan nasan idan nabi na surutun su sai mu makara anan har Bappa yakuma kira.
Ukhtee kuwa tuni idanunta suka kawo
ruwa kan kace me hawaye yafara sauka,
hannunta na rike cikin rauni tare da girgiza mata kai dan nima idanuna sun fara tara kwalla.
cikin harhaɗa larabci nace
"Dan Allah Ukhtee kar kisa jikina yayi san yi, baga waya ba zamurika magana ai tafiya ba mutuwa bace ai dai bamu rabu ba tun da akwai waya zamu rika gaisawa, bakin ce zaki zo kasar mu ba?."
kai ta gyaɗa min alamar Eh nace
"To dan Allah kada ki karya min guiwa da tafiyar kizo muje kin ga Bappa sai kira yake."
jiki a sanyaye ta mike.
koda muka fito parlour sai gani nayi babu akwatin kayan mu in da nafito da shi na ajiye ɗazu bayan nagama shirya mana kayan mu.
nan Ukhtee take sanar min direba ne yashigo ya ɗauka.
koda muka fita farfajiyar masarautar, a tsaye jikin mota muka tadda direba da alamu mu yake jira.
da sauri na juya na nufi side ɗin su Ukhtee dan yiwa Mammaa sallama,
narika bin part-part na masarautar ina yi musu sallama duk in da na shiga sai na fito da ƙwalla dan suma da kwallar suke rako ni,haka narika bin side mafi kusa da mu ina yi musu sallama dan idan nace zanbi na nesa da mu sai na kusan sai na ɓata lokaci mai tsawo ban gama ba.
daga karshe nashiga can cikin masarautar in da lokacin da mukazo aka canza diamonds ɗin nan aciki.
direct cikin katafaren parlour wan da aka kawata shi da adon zinari mai matukar ɗaukar ido muka shiga, adalin shugaba na zaune a mazaunin sa na alfarma, yayin da Alkur'ani ke gaban sa yana bita cikin nutsuwa. a gaban sa muka rusuna, cikin ladabi nayi masa barka da war haka,kafin nakuma cewa wani abu ya ɗaura hannunsa a kai na yana yimin fatan isa kasata lafiya, nayi mamakin yan da yasan abun da ya kawo ni dan ni a zato na bai san da tafiya ta ba. naji daɗin addu'o'in da yayi min kwarai da gaske, na mike cikin jin daɗi yayin da jikar sa wato Ukhtee ta rufamin baya, bayan itama ta gaishe shi, gaba ɗaya cikin parlour'n suka shiga yimin fatar isa gida lafiya ina amsawa da amin har muka fita.
a jikin mota na tadda su Mammaa cikin matukar bege kowa sai hawaye yake har sai da suka sa hawaye na ya karu.
direba na ganin mu yayi saurin buɗe motar yariko hannun su Naseem yasa su cikin motar, rungume juna mukayi da Ukhtee muka saki kuka a tare, gaba ki ɗaya gurin hawaye suke babu mai iya rarrashin wani,
zame jikina nayi cikin sauri nashige cikin mota, direba yatada motar.
motocin da suke jere a gaban mu guda uku sai wasu biyu a bayan mu,
motar farko mai tambarin masarautar haɗe da jiniya, shi ya fara fita, kafin biyu suka bi bayan sa sai kuma motar da muke ciki.
motoci biyu da suke bayan mu suma suka biyo mu, kamar dai ranar da muka shigo masarautar sai gashi yauma a haka muka fita.
muna isa airport batare da ɓata lokaci ba muka shige cikin jirgi, nan motocin suka juya.
bada jimawa ba jirgin ta ɗaga...

Bayan wasu ƴan awanni jirgin mu yasamu sauka cikin yar dar Allah da buwayar sa, cikin babban birnin tarayya Abuja da ke cikin kasata ★NIGERIA★.
bayan saukar jirgen da kamar minti 15 fasinjojin ciki suka fara sauka.
da sauri ganin Naseem da Nasmah sun mike kan kace me sun rufa da gudu sunyi bakin kofar fita in da mutane keta sauka,
cikin hanzari na rufa musu baya da sauri ina faɗin
"Kai kutsaya fa kar kuje ku faɗi."
ai ko da gudu suka fara sauka daga matattakalar jirgin suna dariya.
bayan su nabi ina dariya ganin inda suke sauka cap-cap-cap daga matattakalar kamar zasu kefe kasa ina cigaba da faɗin.
"Zaku faɗi fa kutsaya."
kan kace me sun sauka kasa, sauri na kara ina sauke kafata kan shinfiɗaɗɗiyar kasan kasata abun alfahari na ƙasata Nigeria, naja wani irin numfashi tare da shakar daddaɗan iskar dake kaɗawa acikin ƙasata.
ganin suna kokarin cigaba da gudun nayi hanzari na ruko su tare da faɗin
"Idan yaro ya faɗi yayi min kuka zan kara masa."
baki suka washe cikin kyakyata dariya Naseem yace
"Mommy baya mu faɗi ba." goshin sa na dungure nace "Zaku faɗi mana in zaku faɗin zaku sani ne wan nan gudun da kuke ai sai dai kuji ku a kasa kuzo nan ku tsaya."
na janyo su gefe guda.

Daga can gefe guda
da sauri aka buɗe wata motar da suke jere ɗan nesa da mu, wasu mutane biyu suka fito da sauri suka karaso in da muke, sannu da hanya sukayi min, na amsa ina kokarin janyo su Nasmah mu matsa gefe, daya daga cikin su ya mika min waya, kallon wayar da yake mika min ɗin nayi kana na mai da duba na kansa,
kai ya ɗaya tare da faɗin
"Ana maga na." ya fada yana kallon kan screen ɗin wayar, a hankali na sake Nasmah dake rike a hannun dama ta na amshi wayar, shikuma yayi saurin ruko hannun ta yaɗan matsa gefe kaɗan in da ɗayan mutu min ke tsaya ya harɗe hannu da bakin gilashi a aidon sa,
a sannu nakai wayar kunne na tare da yin sallama, daga cikin wayar akace
"Barka da isowa kasa Nigeria ki bisu su isa da ke masauki."
ɗan shiru nayi kamar naso nagane muryar mai maganar, sai kuma na sauke wayar batare da nace komai ba na mika masa wayar.
a hankali na soma tafiya suna biye da ni har gurin mota, da sauri ɗayan ya buɗe min murfin motar muka shiga in da tuni suka saka jakar mu cikin motar.
jere motocin suka fita kamar yan da aka kawo mu airport a can kasar Saudiyya.
muna fita daga cikin airport ɗin muka ɗau hanya, shiru nayi cikin motar ina raba ido cikin ƙasata yayin da zuciya ta ke kunshe da ɗin bin farin cikin gani na cikin ƙasata, ina jin wani farin ciki tabbas ƙasata abun alfahari na ne.
munyi tafiya mai nisa kafin muka isa wani katafaren hotel, hotel ne irin wan da manyan kusoshin kasa suke sauka a cikin ta...

Awani haɗeɗɗen ɗaki aka sauke mu sai da suka rako mu har bakin kofar room ɗin kafin suka juya, wan da ke rike da jakar mu kuma yashi ga ya ajiye, kana ya miko min waya yace "Ana magana." na amshi wayar a raina nake faɗin
"To yanzu kuma ina zai kuma cewa na bisu."
a sannu nakara wayar a kunne na sai jin muryar Bappa nayi yana faɗin
"HAMDAH sannun ku da hanya ya gajiyar hanya."
washe baki nayi dajin muryar Bappa da sauri nace
"Laaa Bappa mun iso lafiya kalau Bappa kana ina?."
nafaɗa ina washe baki cike da murna jin muryar Bappa da nayi yace
"Kuhuta ku kwanta ku huta sosai ina nan zuwa."
nace "To Bappa." na mika masa wayar ina cigaba da washe baki, mutumin ya fita tare da jamin kofa, numfashi na sauke tare da bin ɗakin da kallo, na isa bakin gado na zube bakin gado, in da tuni Naseem da Nasmah suka haye gadon sai salle suke.
kokarin tuɓe kayan jikina nake dan so nake naɗan watsa ruwa, naji ana knocking mayafi na naɗauka na mayar jikina, na mike na nufi kofar na buɗe ma'aikacin hotel ɗin nagani tsaye rike da babban tray, baya naja na bashi hanya yashigo ya dire try ɗin kan table kana yafita na mai da kofar narufe na murza key.
na dawo bakin gadon na tuɓe kayana nashige bayi,
wanka nayi sosai nafito na tuɓe su Naseem suma nayi musu wan kan.
bayan na shirya su nima na sauya kaya, kana na zuba mana abinci mukaci.
muna gama ci muka koma gado...

bayan haka da kamar awa 2 akayi knocking na mike naje na buɗe, ɗaya daga cikin mutanen da mukazo tare nagani tsaye yace
"Madam kun kammala zamu iya tafiya?".
kai na gyaɗa masa, juyawa nayi dan kiran su Naseem sai ganin su nayi a bayana suna kokarin fita daga ɗakin,
mutumin ya ruko hannunsu nikuma na koma na ɗau mayafi na nabi bayan sa muka fita..
tun daga bakin get ɗin da muka iso na fahimci banki muka zo dan gashi a rubuce (First bank) buɗe baki nayi a raina nake faɗin "To me mukazo yi a banki." bakin na rufe jin yana faɗin
"Bismillah fito muje ko." sai lokacin na lura ashe ma har sun fita har ya buɗe marfin ɓarin da nake ban sani ba, a hankali na zuro kafafuna waje na fito.
direct cikin bankin muka shige batare datsaida mu ko bincike ba, akasin jama'ar da nagani tsaye bakin bankin an tsaida su an hana su shiga.
tun da nashiga cikin bankin aka bani gurin zama ban motsa ba, duk wani cike-cike da kai kawo wasu suke tayi su da wan da mukazo da su, sai dai abun da yakamata ni nayi da kaina shine nake tashi naje nayi, awa 1 da zuwan mu aka kammala komai aka bani ATM,
muna fita daga bankin zato na masauki za'a maida mu sai ganin mu nayi a get ɗin wani banki, shima kusan mintunan da mukayi a bankin da muka baro mukayi a nan ɗin kafin muka kammala, nan ma da ATM ɗin bankin muka fita. ina mai jin mamakin kuma zuwan mu wannan bankin.
mamaki na bai karu ba sai da nakuma sin tar kaina cikin wata banki, wunin ranar muka kare ta a bin bankuna dan sai da muka je banki biyar kuma duk wan da mukaje da ATM ɗin sa muke fita..
sai yamma liss muka dawo masaukin mu, a gajiye na zube bakin gado in da ɗaya daga cikin mutanen da muka tafi da su yashigo da su Nasmah, wata laidar dake rike a hannunsa ya mika min yana faɗin
"Gashi ance na baki."
bin laidar nayi da kallo kana namika hannu na amsa shiku yafita,
zamata na gyara tare da zuba ATM ɗin da suke hannuna kan table ɗin gabana.
a sannu nashiga buɗe laidar dan ganin abun da ke ciki,
kwalayen wayoyi ne har guda biyu nagani ciki a sannu na ciro su ina jujjuyasu, rabon da narike waya haka a hannuna a matsayin nawa har na mance, sai kuma cikin hanzari nashiga buɗesu dan tun ban ciro su ba wayoyin suka tafi da ni, da sauri na ciro cazar wayoyin duka namike cikin hanzari naje na saka su a cj, ina saka wa kuwa suka nuna min acike suke, da sauri na dawo in da na tashi na kunna wayoyin, ai ko ina kunna wa sai ji kake ɗuɗut-ɗuɗut alamun shigowar message alert akai-akai.
ido na kurawa musu ganin alat ne na kuɗi suke ta shigowa, na bankunan da muka buɗe ɗazu, ido na zubawa sarautar Allah ganin kuɗaɗen da suke ta shigowa ni bama zan iya kiyaste adadin su ba.
sai da naji wayoyin sunbar kara kafin nashiga latsa su, contacts nashiga da sauri sai gani nayi babu number ko ɗaya, jiki a sanyaye nake kallon wayar, abu na farko da ya fara zuwar min shine lokacin da Abbu ya siya min waya yasaka min number family na aciki,haka narika bin lambobin ƴan'uwa na ina kiran su.
hawayen da yagangaro kan fuskata na share ina mai jin kewar ahalina, a sannu na mike na isa in da jakata yake na buɗe naciro number Ukhtee da ke rubuce a takarda, na saka cikin wayat kana na dannan mata kira,
tana ɗaga wa dajin nice mai kiran atare muka saki ihun murna.
hira mukayi tayi da ita har magriba kafin na mukayi sallama...

Kasan cewar ina fashin sallah gado na haye nayi kwanciya ta cike da kewar ahalina daya baibaye ni lokaci guda...
washe gari da rana Bappa ya iso Abuja, nayi murna matuka da ganin sa har nake jin wani ɓari na kewar ahalina dana kwana dashi ya yaye da ganin sa.
isowar sa ba da jimawa ba muka bar cikin hotel ɗin har da kayan mu.
wani katafaren gida mai matukar kyau da tsaruwa gida ne babba wan da girmansa yakai ya kawo tsarin sa gwanin burgewa, a bakin ramɓasheshen get ɗin gidan motar gaban mu ya tsaya, wan da mutanen da suka ɗauko mu a airport da wan da muka haɗu dasu a banki jiya dakuma wasu karin mutun biyu da yau nafara ganin su, sune acikin motar, motar da muke ciki ke biye da su, sukayi hon, abakin get ɗin ramɓasheshiyar gidan........★








Mommyn Twins ce
























HMD
WASA FARIN GIRKI!!!✍🏻

_(Book 3)_





🅿️4









Asannu a ka wangale tamfatsetsen get ɗin gidan, motar gaban mu yakusa ciki, a hankali direban dake jan mu ya danna hancin motar cikin gidan, a tsakiyar farfajiyar gidan duk suka faka motocin, a sannu na zuro kafafuna waje, "Ya ilahi ya littahi".
abun da na furta kenan lokacin da na dai-dai ta tsayuwa ta a cikin gidan, bin gidan nashiga yi da ido har ina wai ga gefe da gefe na.
gaba ɗaya gidan da tsaruwar sa yatafi da ni, tsaruwan gidan yawuci misali komai an tsarashi a inda ya kamata yana ajiye a in da ya dace,gida ne babba mai ɗauke da part har huɗu, daga gefe can gabar da gidan side ne guda ɗaya sai kuma gefe ta hannun dama shima side ne guda sai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login