Showing 3001 words to 6000 words out of 45625 words
wani ɗawai niyar da za'ayi ni zan biya, zan kuma tsaya wajen ganin ba'a sami wata matsala ba, aje a kaita labour room."
kai Dr Mukhtar ya jinjina kana yace
"Okay." yadubi nurse ɗin yace
"Akai ta labour room.
tace "Okay sir." tajuya da sauri tana faɗin "Kubiyo ni."
suka fita dukan su mai labour'n da kawar tata.
suna fita da sauri Raliya ta dubi Na'ima zatayi magana Na'ima tayi saurin soma yiwa Dr mukhtar magana.
"Dr irin su ne idan suka haihu suke kashe ɗan, har idan akabar ta ta tafi bazataje wani asibitin ba wani gun zataje ta haihu ta kashe ɗan, ko kuma ta jefar da shi to ni ina son abun da zata hai fa har idan na miji ne."
Dr mukhtar yayi wani dariya tare da faɗin
"Ai tun ɗazu na fahimci hakan ai tun da naga kuna wannan kallon-kallon Na'ima Raliya bakuda kyau sai an haɗa da wanka, ai na san hali tun a makaranta har idan kukayi wannan kallon-kallon to wata tsiyar za'a kulla."
dariya suka sheke da shi suka tafa kana shima ya miko hannu suka tafa da shi dukan su.
zaman sa zagyar da kyau sannan yace
"To meye kaso na a ciki?."
Na'ima tace "Kana da kaso mai tsoka yanzu dai kaje ka bata kulawa ta haihu kuma kayi fatan namiji zata haifa, yau nima zan haihu."
yace "kwarai kuwa har an shiga dake labour room".
dariya suka saka dukan su.
Nan sukayi ta wasu magan ganun su sakanin su batare da ni naji ko fahimtar me suke nufi ba..
Bayan awa uku, kukan jariri ne ya soma tashi daga cikin labour room, Na'ima da Raliya da har yanzu suna zaune a office ɗin Dr Mukhtar suka wani saki murmushi, lokacin da sakon Dr Mukhtar yashigo wayar Raliya wato tex message yana sanar musu da abun da aka haifa,
ciki murmushin mai kunshe da ma'anoni da dama Raliya tace
"Kai sannu Na'ima kin sauka lafiya kai gaskiya haihuwa akwai wuya kinsha fama yau."
itama wani dariya ta sake cikin kware wa a zunzurutun makirci da hatsabiban ci tace
"Na haihu yau ni Na'ima gaskiya haihuwa a kwai wuya".
darika suka kuma shekewa sukatafa.
Dr Mukhtar da yanzu shigowar sa office ɗin bayan ya amshi haihuwar, zama yayi kan kujerar sa yana faɗin
"Gaskiya yau ba sauki oga SALEEM ya haihu um wayaga oga SALEEM da ɗa abun ba sauki hhhhh".
"Shima yazama baba ni kuma mama".
Na'ima ta faɗa tana wani faɗi.
nurse ce tayi knocking tashigo taɗan dukar da kai tana faɗin
"Sir an gama kimsa komai sai dai har yanzu tana bledin, munyi iya kokarin mu bai tsaya ba ko zaka zo ka duba ta."
kai ya girgiza kana nurse ɗin ta fita da sauri,
a tare Na'ima da Raliya suka mike ganin Dr shima ya mike sukabi bayan sa.
dukan su suka shiga ɗakin da aka tanada domin haihuwa.
nan da nan yasoma baiwa yarin yar taimakon gaggawa ganin yan da jini ke fita a jikin ta,
batare da ɓata lokaci ba tadawo cikin hayyacin ta ,jinin kuma ya tsaya.
jaririn da nurse's suka gyara shi suka kunshi cikin ɗankwalin mahaifiyar sa sai musu-musu da kuka yake ga dukkan alama niman abinci yake,
nurse ta ɗago shi ta maso gaban gadon da mamarsa take, wan da a ƴan min tunan da ta sami kanta bayan Dr yabata taimakon da ya kamata har ta iya mikewa tazaune.
tamika mata shi tana faɗin
"Ga abun da kika haifa nan kuma da alama niman abinci yake gashi bakuzo da flas ba, bare a bashi ruwan zafi ya sha."
kin karbar sa tayi sai kukan da ta fashe da shi.
kawar ta da suka zo tare ita ta karɓi ɗan tashiga jijjiga shi, wayar ta dake cikin aljuhun wandon makarantar jikin ta yasoma kara alamar shigowar kira,da sauri takai hannunta guda ta cusa cikin aljuhun wan donta,
ɗaya hannun kuma ta gyara rukon jaririn da kyau ta zaro wayar.
ido ta waro kan screen ɗin wayar murya cike da tsoro tace
"Mama." sai kuma da sauri taɗaga kiran takai wayar kunnen ta tare da yin sallama.
ɗan shiru tayi sai kuma tace
"Mama gani nan dawowa an tashi ne bansami abun hawa ba shine yasa na tsaya".
tana sauke wayar da sauri tadubi kawar tata tace
"Mama ce takira ni taga lokacin tashi yayi har yanzu ban koma gidaba, bayan ko makarantar ma banje ba,ni sai yanzu ma na ga agogo tun ɗazu lokacin tashi yayi, tofa zantafi gida yanzu yaya zamuyi ina tsoro kada Baba yadawo yasamu ban dawo ba,
kema zaki tafi gida ba kawai tun da yanzu kin haihu? muje na rakaki gidan ku nima sai na wuce gida,
karfa Mama tasa yayu na su biyo ni kin san fa in nakai wannan lokacin sawa take aje a nimo ni".
tana maganar ne cikin tsaro sosai.
itako mai jego kuka kawai take takasa cewa komai.
Dr yace "A'a taya za'ayi ta tafi yanzu bayan yanzu ta dawo hayyacin ta,sai mun daɗa ganin yanayin jikin nata kafin mu sallame ta, yanzu kam ma allurar da akai mata zai fara ai ki in tayi bacci ta farka mukaga yanayin karfin jikin ta sai mu sallame ta, yanzu dai ke kije tun da ke a na kiran ki."
to tace da sauri ta mika mata ɗan,
yanzu ma kin karɓar ɗan tayi.
Raliya ce ta karɓi ɗan a hannunta tace
"To kije kawai."
ai ko tafita da sauri.
bayan fitar ta Dr Mukhtar ya dubi yarinyar yace
ta kwanta ta sami bacci, a hankali ta gyara kwanciyar ta,su kuma suka fita suka koma, office ɗin sa.
suna zama Na'ima tace
"Bani ɗan na ganshi."
Raliya ta mika mata kyakkyawa fari kuwa da shi, sai dai yaron bashida girma ɗan kankani ne hakan kuwa bazai rasa nasaba da rashin samun kulawa da ya kamata tun aciki ba.
takafe shi da ido tana wani irin murmushi tana ɗan jijjiga yaron.
after 4 hr.
hakan kuwa yayi dai-dai da farkawar yarinyar da ta haihun a bacci, alhmdllh taji karfin jikin ta kwarai.
nan tanimi tafiya gida nurse tazo ta sanar wa Dr yace taje ta kira ta.
tare nurse ɗin suka shigo da yarin yar,ya nuna mata kujera ta zauna kana yacewa nurse ɗin taɗan basu guri, nan ta fita tajawo musu kofa.
duban yarinyar yayi kana ya ce
"Inane gidan ku".
cikin kame-kame tashiga faɗin
"Um..um..gidan mu gidan mu."
sai kuma tayi shiru.
da kyau yakuma duban ta sannan ya ce
"Bana son wani ɓoye-ɓoye nasan wannan ɗan bashi da uba cikin shege ne dan haka kawai tan bayar ki nake ki bani amsa inane gidan ku?."
kwalla ta matse tare da mutsutstsike yatsun ta kana ta soma magana,
"Gidan mu yana..yana Unguwar Bakaro".
kai ya jinjina yace
"A Bakaro kike?."
ta gyaɗa kai, Raliya ta jinjina kai kana ta ce
"Ah to shikuma uban ɗan a ina yake shima a Bakaron yake?".
tace Eh.
"To yan zun ina zakije keda ɗan idan kika fita daga nan?".
Raliya tayi mata tambayar tana dubam ta, shiru tayi tare da musutssuke yatsun hannunta.
Dr Mukhtar yaɗan tsura mata ido kana yace
"Yanzu ina zaki kai ɗan idan aka baki shi?."
kuka tafashe da shi tana faɗin
"Wlh idan na tafi da shi gida yan kani za'ayi wlh iyayena sun ce sai sun yanka ni yanzu ma in na koma gida nasan suka na za'ayi idan na tafi da shi zasu yanka ni".
kuka take sosai tana faɗin zasu yanka ta,
Na'ima kuwa carap tayi tace "To ni zan rike miki ɗan ni ina son shi nasan idan kika fita yaddashi zakiyi ko ba haka ba?".
tafaɗa tana duban ta.
da sauri yarin yar ta gyaɗa kai tace
"Wlh in natafi da shi gida ne za'a yanka ni in naje dashi gida ne."
Na'ima ta ce "To ya isa, in kika je da shi gida ne za'a yanka ki idan kika fita da shi daga nan kuma yaddashi zakiyi to ni ina son shi zan rike shi".
hannu ta saka ta buɗe jaka ta ciro kuɗi masu yawa gudan dubu-duba ne a ɗaɗɗaure ɗauri uku,wacce a kalla ko wani ɗauri guda yakai 100k ta mika wa yarin yar tana faɗin
"Karɓa in kinje kya nima abun da zaki rika ci wan da yakamata masu jego suci, ba sai kin jira iyayen ki sun yi miki ba tun da nasan cewa bayimiki zasuyi ba, da ma ace ɗan da uba ne tun da bashi da shi kuwa ba mai saurarar ki, gashi sai kije kiyi jego shikuma ɗan ina son shi zan rike shi, dan bazan iya zuba ido ina gani azalinci ɗan da baiji ba baigani ba ku mutane kurika jin tsoron Allah, ɗan da bai san komai ba aje a jefar da shi ko a kashe shi."
da sauri yarin yar ta mika hannu ta karɓi kuɗin har hanunta na rawa ganin yawan kuɗin, kana ta yimusu godiya ta mike da sauri ta fita,
har takai bakin kofa Na'ima tace
"Idan kikaje gida aka tanbaye ki ina abun da kika haifa sai kice yana ina?."
"Ya mutu tun a ciki!."
tayi maganar cike da karfafawa tana daɗa dunkule makudan kuɗin da ta bata.
murmushi Na'ima tayi tare da faɗin "Da kyau." da sauri yarin yar tayi waje ta haye abun hawa ta wuce gidan su cikin zillumi da tsoro..
bayan fitar yarinyar Raliya da Dr Mukhtar suka tuntsire da dariya, cikin muryar dariya Dr Mukhtar yace
"Kin ji Na'ima har da ɗan guntun wa'azin ta wai ku mutane kurika jin tsoron Allah tun da kin samu a sama ai dole kijefo wa'azi ciki hhhhh."
"In da kuɗi meye bazan samu ba kai bakaji takashe ɗan nata tun a ciki ba, wannan kuma ni na haifa."
tayi maganar tana leko fuskar yaron da yake baccin sa.
Dr mukhtar ya gyara zama tare da sauke numfashi sannan ya ce
"To yan zu ya za'ayi ne?."
tace "Dr ni da na haihu kuma me yazaunar da ni a nan a kaini labour room mana."
dariya ya sheke dashi Raliya ma dariyar tayi tana faɗin
"Ai kuwa mai jego a gado yakamata a same ta a kwance ba'a zaune a office ɗin likita ba."
nan suka mike suka nufi labour room bayan sun gama shirya duk yan da abun zai tafi.
suna shiga ta haura gado ta kwanta, tayi shame-shame kamar wacce ta haihu da gaske.
Waya Na'ima ta mikawa Raliya tace
"Kirashi a waya".
Raliya ta amsa ta danna number SALEEM......!
Mommyn Twins ce
🌺 *HAMDAH* 🌺
*WASA FARIN GIRKI!!*✍🏻
*NA*
*RASHEEDA S DIRECTOR*
_(Book 3)_
Littafin na siyar wa ne ki biya ki karan ta.
domin biyan kuɗin littafin sai ka-ki tuntuɓi wannan number 08034690723
🅿️2
Wayar tayi ta ringing har ya yanke bai ɗaga ba, ta dubi Na'ima tace
"Bai ɗaga bafa. "
ta ce "Sake kiran shi kin san shi ai murɗaɗɗen mutum ne idan baiyi ra'ayi ba bazai ɗaga ba yanzu haka wayar tana kusa da shi ɗagawar ne dai baiga dama ba."
kuma kiran nasa tayi namma har ya yanke bai ɗaga ba, sai da ta kirashi har sau uku a na huɗu ne ya ɗaga.
ganin ya ɗaga kiran takai wayar kunnen ta tare da faɗin
"Asslamu'alaikum SALEEMA Raliya ce muna asibiti da Na'ima tahaihu."
SALEEM dake zaune a office yana ta tarkasa ƴan kayakin sa dan locin tashin sa yayi har ya wuce ma, ƴan wasu aiyuka ne suka tsaida shi. yamike zumbur yana faɗin.
"Haihuwa kuma? yaushe cikin nata yakai na haihuwa cikin ya fita kenan?."
yajero tanbayar da alamun hankalin sa a ɗan tashe yake.
ta ce "Eh haihuwa ce ba fita cikin yayi ba sai dai bakwaini ta haifa ɗa na miji."
numfashi yasauke jin akasin abun da yake zato,shi gaba ɗaya jin lamarin na bazata ya mantar da shi zata iya haifar cikin tun da yakai wata bakwai, ya ce
"Ina jaririn yake yanzu yana cikin wani hali yana dai lafiya ko?."
"Eh gashi can a cikin kwalba."
katse wayar yayi batare da yace komai ba, Na'ima da take jin duk abun da yake faɗa kasan cewar tasa wayar a amsa kuwa ne ta ce
"Lallai ma wannan wato shi ta jaririn yake bazai fa taɓa sauyawa duka ba."
dariya Raliya tayi tare da faɗin
"SALEEMA kenan miskili kafi mahaukaci ban haushi bafa zai sauya ba dan kuwa a jinin sa yake."
SALEEM na kashe wayar, wayar Mamie ya kira, zaune Mamie take da su Aunty Rafee'at Aunty Jaleela da su Ummi kiran sa ya shigo.
bayan sun gaisa yake faɗa mata Na'ima ta haihu.
"Haihuwa." Mamie tafada da karfi
kana ta ce "Wani irin haihuwa ciki wata bakwai." ya fuskanci yanayin da yashi ga lokacin da Raliya ta sanar masa da haihuwar shi Mamie ta shiga yanzu.
yace "Eh ta haihu bakwaini ta haifa tana asibiti ma yanzu."
"To Allah ya raya." Mamie ta faɗa a takaice tare da kashe wayarta.
gaba daya hankalin ƴan cikin parlour'n yakoma kan Mamie, Ummi ce da sauri tace
"Wa ta haihu Na'ima ce?".
Mamie tace
"Wai haka, wai ta haihu". Mamie ta faɗa tana taɓe baki.
Ummi ko baki ta washe tana fadin
"Ikon Allah, kaji ikon Allah ko to Allah dai yasa abun da aka haifa nacikin koshin lafiya".
baki Mamie takuma taɓewa tare da faɗin
"Ina kuwa zai zama cikin koshin lafiya ciki wata bakwai sai dai yabada wahala dai".
a ɓangaren Aunty Jaleela ma fuska ta yamutsa tana faɗin
"Gayyan wahala dai ciki wata bakwai ai ba arziki."
"Ina kuwa arziki duk uban iyayi da cikin ashe dai rabin halitta za'a haifo ba arziki."
Aunty Rafee'at ta faɗa, tana tura ɗankwali gaban goshi.
duk kanin su in ka gansu babu wani mai farin ciki da jin daɗin haihuwar, akasin Ummi da fuskarta ke ɗauke da annuri bakin ta ya kasa rufuwa sai faɗi take
"Kai masha Allah Allah dai ya raya mana."
mikewa Ummi tayi tana cigaba da faɗin
"Kai masha Allah zamu wuce asibitin ba yakamata mu tafi asibitin yanzu".
Mamie ta kawar da kai gefe tare da faɗin
"Ummi'n Fauzan ni gaskiya ba yanzu zanje asibitin nan ba gaskiya inaga kamar ina da abun yi, ai dare yayi yanzu ga magriba yakawo kai."
Ummi ta girgiza kai tana faɗin
"Kai Mamie'n Nusaiba yakama ta dai muje yanzu ace babu wani nashi a can gaskiya baiyi ba."
fuska Aunty Rafee'at takuma yamutsawa tana faɗin "Um ni kamma kucire ni a tafiyar dan yanzu Abba'n Adeel zaizo ya ɗauke mu."
dakuwa Ummi tayi mata tare da faɗin
"Maza tashi kushirya ke Jaleela tashi maza muje".
Aunty Jaleela da tazo har wuya ta kwaɓe fuska kana tace
"Ni wlh ina ji ma kamar kar inje dan nima Daddy'n Fadeel nasan zai zo yanzu."
haɓa Ummi ta rike tana sallallami da kyar dai ta tirsasa musu ta samu suka fita, suka nufi asibitin bayan sun sanar wa su Abbu.
A asibitin suka tadda SALEEM shima isowarsa kenan a tare suka shiga cikin asibitin.
direct ɗakin hutu suka nufa in da nurse tayi musu jagora zuwa ciki,take sanar musu da cewa an mai da Na'ima can domin ta huta.
nan suka tadda Na'ima kwance tana ta sauke numfarfashi Raliya na tsaye a kanta tana ta yi mata sannu.
da sauri Ummi ta matso in da take tana faɗin
"Sannu sannu kinji Na'ima, kin sami kanki kalau?".
dakyar ta buɗe baki cikin yanayin mutum yasha wuya murya can kasan makoshi tace
"Lafiya lau."
Mamie ko kallo ɗaya tayi mata kana tace mata Sannu.
namma da kai ta amsa.
Aunty Rafee'at kam ko kallo bata ishe taba, Aunty Jaleela ce ma a sama tace mata sannu ita ma.
Ya SALEEM da ya naɗe hannu a baya yana tsaye tagurin kafafun ta yadan dubeta kana yace
"Ina yaron yake?". Raliya tace "Yana can ansashi a kwalba.
kai ya jinjina cikin yanayin nan nasa, ya maida duban sa kan nurse ɗin da ta yimisu jagora yace
"Muje a nuna mana in da yake, ina Dr yake?".
ta ce "Yana office".
fita sukayi duka har da Raliya,
Raliya tayi saurin shigan office ɗin Dr tare suka fito da shi, ya mikawa Ya SALEEM hannu suka gaisa ba yabo ba fallasa Ya SALEEM ya amsa masa gaisuwar, kana ya gaida su Mamie sannan ya wuce dasu ɗakin da aka ajiye jaririn wan da yake karkashin kulawar na'urori..
Can suka hango jaririn cikin kwalba
wan da ake saka jariran dabasu kai watannin haihuwa ba, yanata wutsul-wutsul da kafafunsa.
murmushi Raliya tayi a kasan ranta dan ganin shirin su yana tafiya yan da ya kamata.
da sauri Ya SALEEM ya karasa jikin kwalbar yana leka cikin kwalbar.
su Ummi ma gaba ɗayan su suka karaso jikin kwalbar,
Ido Mamie ta kurawa jarijin da ake kiran sa da bakwaini gashi dai ba wani girma yake da shi ba ɗan kankani ne, sai dai yanayin sa da wayon faskarsa ya girmi na bakwaini.
kai ta girgiza tare da juyawa ta kalli likitar tace
"Wannan shine bakwaini an ya ma kuwa anyi lissafin cikin nan dai dai ko dai tara ne an ɓata lissafin kaga yaron da wayon sa."
da sauri Raliya tace
"Bai cika tara ba bakwai ne ai ko jiya ma sai da mukayi lissafin watannin da ita, yau kuma sai ga haihuwa kingan shi ai ɗan misilili da shi".
Ummi tace "Ai kuwa gashi ɗan kankani irin su idan suka tashi girma sai an gansu dan sai anci tuwo an koshi kafin a iya ɗaukar su".
Ya SALEEM kam duk baya jin su dan ya gama shagalta da kallon yaron wai shine yau da ɗa, wannan ɗan nasa ne, wani murmushi yayi a kasan ransa wan da har sai da yabayyano kan fuskarsa.
Aunty Rafee'at data kafe yaron da ido tarr sai lokacin tayi magana.
"Wai wannan yaron shine bakwaini gaskiya wannan baiyi kamada bakwaini ba sai dai in ku kuka ɓata da lissafin".
tayi maganar cikin gatsali.
wani kallon sama da kasa Raliya ta bita da shi. Aunty Rafee'at ma irin kallon ta wasa mata tare da girgiza kai tana cigaba da yi mata wani kallon shekeke, sannan ta juya ta fita a cikin ɗakin bayan ta gama ai kawa Raliya kallo masu cike da ma'anoni da yawa..
ko minti 30 basuyi a asibitin ba Mamie tace sutafi, haka dai suka fita suka koma gida.
Haushi da bakin ciki kamar Na'ima tayi yaya, wai ace kalar gaisuwar da surukar ta zata yi mata kenan, babu wani gaisuwa mai nuna tausaya wa babu wani nuna farin cikin samo mata jika da tayi.
Raliya tace "Ni da ɗina da ke gajen hakuri dan Allah kibar wannan maganar kiyi shiru, ke kam dai ba kin haihu ba ina ruwan ki da su, wan da kika haifa masa ne idan ya miki zakiji zafi,ina ruwan ki da su ba wa ɗan su kika haifa ba, can ta matse musu ke meye damuwar ki, kinga wannan shegiyar yarinyar
zan nuna mata ni ƴar bariki ce cikakkiya ma kuwa ciki da waje na,
wai shegiyar Rafee'at ɗinnan kinga wani kallon da take min,
kinga wani kallon da take min kuwa, zan nuna mata