Showing 45001 words to 45625 words out of 45625 words
amsa, tare da gyara wa Nasmah zama kan kafarsa ya saka mata cup ɗin a baki yana faɗin
"Sha maza muje ki hau lilon doki daga gun kisha Chocolate ko."
ai ko tabuɗe baki ya kafa mata cup ɗin, sai da tasha fin rabi kafin ta ɗaga kanta.
Dr dake tsaye a gefen su yayi dariya tare da faɗin
"Nasmah Daddy ne kaɗai mai yin rarrashi a yarda ko?."
Inna Wuro ta ce
"Ai kam mu duk rarrashin da zamuyi sai dai ta sa mana ihu."
duk sukayi dariya ban da ni da kuma shi da ya murmusa.
"Ɗan shishshigi." nayi maganar a kasan raina tare da jan guntun tsaki a fili. duk suka juyo suka kalle ni.
Inna Wuro taciga da faɗin
"Har uwar tata ma taki yar da rarrashin nata."
mike wa yayi tare da sakata a kafaɗar sa yasoma tafiya tare da faɗin
"Tasan itama bata wuce rarrashin bane."
yana kaiwa nan yayi waje Dr ya rufa masa baya, ido na waro tare da yin kwafa wannan mutumin sainayi maganin sa.
Inna Wuro da Faty kuwa dariya sukayi.
Faty ta ɗauki sallayar da mukayi sallah muka nufi waje.
a can farfajiyar asibitin muka iske su suna tsaye suna magana da Bappa.
kafin mu karaso ya shige motar sa in da ya saka Nasmah a gefen sa yaja motar mai gadin asibitin ya buɗe masa get ya fita.
cikin takaici haɗe da mamakin karfin hali irin nasa nabi bayan motar da kallo.
bansan dalilin sa na son yimin shishshigi cikin rayuwa ta ba, akan wani dalilin zai tafi da ita, to ma ina zai kaita tun.
maganar Bappa naji yana faɗin
"HAMDAH muje ko." juyowa nayi sai gani nayi har kowa ya shige mota.
"Bappa akan wani dalili zai tafi da ita?."
ya ce "Gida zai kai ta dan taki yar da na karɓe ta kuma aciki ma yace min taki yarda da ku,idan ya barta zatayi ta kuka ne kuma likita ya ce ba'a so tarika kuka, sabo da ciwon kannan nata sai ya iya motsa mata, muje zamu same su a gida ma yan zu,
yaron arziki mai son taimakon al'umma."
da sauri na ce
"Waya ce masa bukatar taimako muke." nayi maganar ina waigin hanyar da suka fita tare da murguɗa baki kamar yana gani na.
murmushi Bappa yayi kana ya ce
"Babu wan da ya ce masa ana bukatar taimako halinsa ne hakan."
juyawa nayi na shige cikin mota ba tare da na kuma cewa komai.
Koda muka isa gida ganin babu motar sa yasa nayi tunanin ko har ya ajiye ta ya wuce ne, da sauri nashiga ciki.
Naseem da ke tare da su Zulai ya rungume ni yana yi min oyoyo.
su Talatu sunayi min sannu da dawowa ya mai jiki, ban iya basu amsa ba sai tambayar su nayi "Ina Nasmah?."
"Hajiya ba tana asibiti ba."
cewar Zulai. kaina girgiza tare da faɗin
"An dawo da ita gida." Talatu tace "A'a Hajiya ba'a dawo da ita ba."
da sauri na juya nafita waje a sakar gida na tadda su Bappa suna kokarin wucewa part ɗin su na ce
"Bappa bai fa dawo da ita ba."
murmushi yayi tare da faɗin
"Zai dawo da ita je ki huta."
juyawa kawai nayi badun naso ba sai dun bana so nayi masa musu.
Nakai tsawon awa guda zaune cikin parlour zaman jiran dawowar ta,
ganin guri ya fara rufawa magriba ta kusa sai na mike na haura sama, sai da nayi wanka na gabatar da sallar magriba kafin na sauko.
nasa Zulai ta kawo min tea sai a lokacin na sa wani abu a ciki na.
zuwa yanzu kam ina ji bazan iya cigaba da hakuri da sa sammanin dawo da ita ba, yunkurin mike wa nayi dan zuwa gurin Bappa, ya faɗa min gidan sa naje na ɗauko ƴata.
da sauri na waigo kofa jin an turo kofar parlour'n........!
Mommyn Twins ce