Showing 6001 words to 9000 words out of 45625 words

Chapter 3 - HAMDAH part 3 Complete hausa novel

RASHEEDA   

04 Oct 2024

12664

halina bata sanni bane."
Na'ima tace "Him in dai wannan Rafee'at ɗin ce ta wuce sammanin ki, wannan yarin yar da kike gani nima inada cikin ta kuma zanyi maganin ta, zan je musamman gurin boka domin yamin maganin ta,
zatagane da ni take rabu da ita mance da ita dan wlh sai ta gane kuskuren ta."

Jin an murɗa handle yasasu yin shiru da zancen nasu,
Na'ima ta gyara kwanciyar ta kamar ɗazu, ta daɗa marairace fuska da shagwaɓe fuska.
ya karaso bakin gadon yadube ta kana yace
"Ya jikin?". cikin makirci da salon iya kirsa tace
"My SALEEM kaga ɗan mu ko,ya bani wahala yaron nan,
ɗan ka yabani wahala My SALEEM da kyar na iya haifo shi."
gefen fuskarsa ya shafo tare da naɗe hannun sa ɗaya a bayan sa,
"Ɗa na."
yafaɗa a kasan zuciyar sa yayin da yake jin wani abu yana tsarga masa mai kama da farin ciki, can karkashin kasan zuciyar sa kuwa, jin wani abu mai nauyi yake yana kokarin tasowa sai kuma yanayi biyun suka shiga kokawa da junan su, yayin da farin cikin ya danne wancan nauyin da yake jin nauyin sa na yau yafi na kullum. har sai da yakai hannu ya dafe kahon zuciyar sa.
daga Na'ima har Raliya ido suka zuba masa ganin yan da ya dafe kirjin sa da karfi tare da rumtse idanunsa,
wani abu ne ya gilma masa cikin duhuwar kwayar idanunsa da suke a rufe, wani irin bugawa kirjin sa yayi kamar an fizgi zuciyar sa, sai yarika ganin wasu abubuwa guda uku masu haske suna yi masa yawo cikin ido yayin da bugun zuciyarsa ya tsanan ta, dai-dai lokacin da yaga abun suna daɗa tunkaro sa tamkar suna tahowa gare sa,
a zahiri kuma idanunsa a buɗe. sai kuma a sannu suka rika yin nesa dashi sai da sukayi nesa dashi sosai kana duhu takuma gilmawa sakanin su.
cikin tsananin karfi ya ware idanun sa, jin muryar Na'ima tana faɗin
"Ya dai My SALEEM?".
hannayen sa biyu ya cusa cikin sumar kansa kana ya burzar da wani huci mai zafi daga bakin sa
"I'm sorry."
ya faɗa tare da juyawa yabar ɗakin da sauri, yayin da yake jin zuciyar sa naciga da yi masa nauyi, acikin ƴan kwanakin nan hakan yana yawan faruwa da shi akai-akai, musamman in ya kwanta bacci yarika irin wannan mafarkan kenan, sai yari ganin haske guda uku suna dumfaro shi sai sunzo daf da shi sai su bashi baya yayin da duhu kuma zatazo ta mamaye hasken. abun da yake gani cikin mafarkin sa shi ke kokarin zuwa masa a zahiri, to ko bacci yafara a tsayen har ya fara mafarkin?.
yarika jefowa kansa tambayoyin da bashida amsar su..

Bayan sa Na'ima tabi da kallo cikin takai ci, a tunanin ta ɓarin jiki zaiyi idan yaji ta haihu, idan yaga ɗan kuma murna zai yi ba adadi, sai kuma gashi sai wani shashshan kamshi yake,batare da ya nuna farin ciki da hakan ba.

A can kuwa bayan komawar su Mamie suna tare a parlour kowa na faɗan albarkacin bakin sa.
Mamie kam sam taji wannan ɗa bai kwanta mata a rai ba,
kwata-kwata taji ɗan baya cikin ranta, tana yi masa wani irin kallon da ita kaɗai tasan ma'anar sa.
Aunty Rafee'at fuska ta yamusa ganin su Fauzan da Nusaiba na ta murna wai matar Ya SALEEM ta haihu zasu sha suna tace
"Dalla kurufa mana baki, ni wallahi wannan ɗan ma kwata-kwata bai min ba wlh ya ɗauko jinin uwar sa, ni bai min kama da bakwai niba haka bakwaini yake,sau nawa nake ganin ƴaƴan da ake haifarsu wata bakwai sai ace wai wannan ɗan wata bakwai ne, to can ta matse mata sai taje ta ta fama taje can tayi ta haifar bakwaini ita ta sani".
kai Mamie ta girgiza.
Aunty Jaleela tace
"Ai wlh nima Aunty Rafee'at ɗan baimin kama da ɗan bakwai ba, sai dai idan ko sun ɓata lissafi ko kuma wani munafurcin ta ke kullawa ciki yafi wata bakwai tace bakwai to meye amfanin hakan, meye na cewa ciki wata bakwai bayan tasan cikin yafi bakwai ɗin".
Ummi ko cemusu tayi
"To ku in ban da abun ku ta yiwu ta ɓata da lissafin ne in mutum ya ɓata da lissafi kam shi zai rika lissafi kuma alhalin ba haka bane, ai ba wani abu bane kakan iya ɓata da lissafi, kuma ai ana iya haifar wata bakwai yayi rai me lafiya ma yatashi har yafi ɗan wata taran kwari da kuzari, kar ku mance fa a asibiti ta haihu in ba bakwai ba taya za'ayi a sashi a kwalba likitan ai yafiku sanin me yake, Allah dai ya rayashi da imani".
"To amin".
cewar su dakaji amin ɗin kasan baikai can kasar zuci ba...

Bayan kwana uku
tun da sukaje sau ɗaya basu kara zuwa ba sai ranar da ta cika kwana uku shima da kyar Ummi tasa Mamie suka koma asibitin, anan suka tadda ƴan gidan su Na'ima, nan ma basu wani jima ba suka baro asibitin.
satin su Na'ima biyu a asibitin, zaune suke da kawar ta Raliya Na'ima ta dubeta tana faɗin
"Kai Raliya wlh nagaji da zaman asibitin nan haka,
wai shin dole ne sai mun yi wata biyu a asibitin nan, dole wai saimunyi wata biyu wlh nagaji da zaman asibitin nan, wai dole ne har sai ɗan yacika wata tara kafin mu koma gida, gaskiya asan yan da za'ayi kije ki sami Dr asan yan da za'ayi gaskiya, wlh nagaji da zaman asibitin sati fiyu fa ina nan,gaskiya kije ki same shi asan yan da za'ayi nakoma gida."
Raliya tace
"Gaskiya nimafa nagaji da sintirin yau asibiti gobe asibitin nan,kullum kenan mutum na hanyar zuwa asibiti alhalin duk kanin ku lafiyar ku lau, jariri yana nan yana shan madarar sa ke kina nan kina narkar abincin ki,
nikam mafa inada wasu a hannu wlh ina da wan da na karɓi kuɗin su, akwai wan da na karɓi kuɗin sa na kwana uku gashi nan ko wuni ɗaya bamuyi da shi ba, sakanina da shi da daddare mu kwana shi da yaso muje Abuja muɗan shana,
gaskiya bari naje na samu Mukhtar asan yanda za'ayi ki koma gida, nasamu naje su fanshi kuɗin su".
ta karashe maganar tana mikewa tsaye ta fita ta nufu office ɗin Dr.


Bayan Raliya sun gama tattaunawa da Dr Mukhtar yace
"To gaskiya akwai yadda za'ayi zata iya komawa gida abisa ita ta tirsasa tagaji da zaman Asibitin, nikuma sai na bada wasu shawarwarin da zata ɗauru akai bayan ta koma gidan".
nan suka tsara yan da abun zai tafi.
a ranar da yamma suka sami sallama suka koma gida, bayan shariɗoɗi da shawarwarin da Dr ya bata a gaban ƴan uwan ta da kuma gogan wato SALEEM.

Tun da suka koma gida yaron kullum a kwance yake idan akazo barka ma sai tace ba'a ɗau kar sa sabo da likita yace, kada a rika yawan sa masa hannu, sai dai azo a ganshi a kwancen kawai acikin bargon da kullum yake dukunkune a ciki.
haka tayi ta rainon ɗan da masu da ita da ɗan ma'aikatan ta da kuma ƴan uwan ta, koda waɗan da suke kanta sukaga nonon ta ba ruwa basu kawo komai ba sai cewa sukayi ai dama gaka wasu matan suke sai an nimi magani.
tuni aka nemo maganin wanke nono da ku ma ruwan nono, kan kace me ruwan nono yakawo tashiga shayar da ɗa.
lokacin da suka cika wata biyu,wato ɗan yacika wata tara kenan washegari tahaɗa wani gagarumin taro.
biki irin na masu ji da naira, biki akayi na gani na faɗa naira tayi kuka, ranar SALEEM katuwar saniya ya yanka da katon rago,
yaron yaci sunan baban Na'ima.
ko da taji sunan da ya raɗa masa sam bata so ba dan taso yayi wa babansa ne takwara.
yace mata shi halacci yayi mata yasa wa ɗan sunan mahaifin ta.
ranar kuwa kaɗan ya rage Raliya suyi faɗa da Aunty Rafee'at kan cewa da Aunty Rafee'at tayi yaron ma ko kama da su baiyi ba duk da kuwa girman da yake ta karawa,amma ko alamar kama da su bayayi sai dai in ya ɗauko zuriyar uwar sa dan ko kama da uwar tasa ma baiyi ba.
shike nan kawai suka kama zasuyi faɗa, wai akan me yasa Aunty Rafee'at zatace haka ai duk wan da yaga ɗan yaga SALEEM, dan kuwa farin SALEEM ɗin ma ya ɗauko tun da kuwa yayi kama da uban sa ai ba sai yayi kama da dangin uban sa ba. cikin masifa da bala'i da tsagwaran bariki Raliya take maganar.
Aunty Rafee'at ma kuwa bata yi mata da sauki ba tayi mata wankin babban bargo.
Allah ma ya taimaka Ummi tazo sunan ita ta raba faɗar. ta kora Aunty Rafee'at da Aunty Jaleela tace duk su tafi an yafe musu sunan, dan ganin abun na daɗa girma dan har Aunty Jaleela tashiga faɗar....



After 1 year


Acan kasar Saudi

Da sauri na fito daga cikin bedroom cikin hanzari jin kiran da Ukhtee take kwaɗa min, abakin kofa mukayi kiciɓus da ita, fuska na kwaɓe ganin tana yi min dariya
"Ni gaba ɗaya kin firgita ni na ɗauka wani abun ne".
nayi maganar cikin harshen larabcin da nake ɗan tsinta a gurin ta.
murmushi tayi tare da ruko hannuna
tace "Zo ki gani ga ɗan'uwan ki yazo shi yace nayi mishi magana da ke".
tayi maganar ne cikin yaren ta da kuma yanayin da zan fahimta, dan yanzu ba laifi nakan fahimci abun da ake faɗa da larafci har nakan iya ɗan gwamusa wa wajen yin magana da bashi da tsawo mafi sauki.
ta janyo ni muka nufi parlour.
turus nayi ganin wan da yake zaune a parlour'n su Naseem da Nasmah sun zagaye shi sai zuba masa surutu suke.
sai kuma nayi murmushi tare da karasowa cikin parlou'n ina faɗin
"La Uncle Mahmoud kai ne yaushe ka zo?".
dan yanzu kunyar kirashi da sunan sa nake.
shima murmushin yayi yana faɗin
"Ban jima da isowa ba,Naseem yace min kina bacci da zaije ya taso kine nace a'a yabar hajiya ta huta".
baki nawashe ina zama kan kujera jin abun da ya faɗa
nace "Uncle Mahmoud kenan wai hajiya, hajiya kuma".
yace "Eh mana hajiya kai, taya za'a taso hajiya a bacci lokacin tashin ta baiyi ba ai dai gara abar hajiya tayi bacci da kyau da kyau".
dariya kawai nayi kana nace
"Sannu da zuwa ya hanya? yasu Bappa da Inna wuro da Fatu".
yace "Hanya lafiya lau, sai dai badaga gida nake ba, amma dai Duk suna Lafiya".
Naseem da Nasmah suka mike a jikin sa sukabi bayan Ukhtee aguje sukayi side ɗin Mammaa.
janyo table ɗin da ya ɗaura system ɗin sa a kai yayi, yajuyo shi ta gabana yana faɗin
"To hajiya komai fa ya kammala, shiya sa ma na dako musamman tun daga Nigeria zuwa nan na sarnar miki ki kuma ganewa idonki, ba sai an kira ki a waya an sanar miki ba."

Ido na kurawa system ɗin, ganin bidiyoyi sunata bayyana cikin system ɗin, masu ɗauke da tamfasa-tamfasan gidaje wane a turai motoci gidajen mai masallatai makarantu haɗe da kamfanoni da dai sauran su.
cikin tsananin mamaki na dubeshi nace
"Wannan fa Uncle Mahmoud?".
nayi tambayar ina nuna cikin system ɗi. yace "Ah ai kin ki ya kammala wakilci a ka naɗa ni domin a kawo miki kiganewa idon ki musamman nataso domin shi".
da ɗin bin mamaki nakuma kallon hotunan dake bayyana kan system ɗin kana na maida dubana gareshi nace
"Waɗan nan ɗin?."
yace "Kwarai kuwa sune,nakine sun kammala yanzu ke kawai muke jira ki koma abubbuɗe su, sannan kuma ba a gari ɗaya akayi su ba a state da dama ne nacikin kasar mu Nigeria, ga jerin sunayin garirruwan da akayi gine ginen a cikin sa".
ya daddanna system ɗin,sai ga sunayen garuruwan sun bayyana da kuma abubuwan da akayi a kowa ni garin.
yace "Kin ga yanzu zaki koma Nigeria a dai-dai dan kullum sai Bappa yayi maga, yanzu ma yace mu dawo tare sai dai ni bagida zan koma ba zan wuce Uganda tare da abokan aiki na, akwai wani abun da zamuje muyi a can".
kai na jinjina dan nifa har yau ganin abun nake kamar wasa nace
"Him..Him.."
kasa magana ma kawai nayi sai Him. nake ta faɗa ina kallon ikon Allah,yayin da nakeyi wa Ubangiji buwayi gagara misali tasbihi a can kasar zuciya ta.
rufe system ɗin yayi kana yace
"Kin ga abubuwa yan da suka kammala ko, ko mai masha Allah, yanzu wani suna kike ganin za a sakawa kamfanoni da gidajen mai dai duk sauran kaddarori, wani suna kike ganin ya dace a saka musu, domin idan akaje yin katin gayyata da sanarwa ayi amfani da wannan sunan, da zai zamo shine sunan duka kaddarorin".
Shiru nayi yayin da na saka yatsa na guda kan kuma tuna nayi sama da ido na alamun tafiya duniyar tunani, tare da ɗan kyafkyafta idon.
kana nayi kasa da idon cikin washe baki nace
"Yauwa na tuno sunan da nake so a saka masa *HAM'NAS*".
nayi kaganar cikin zakuwa ina cigaba da washe baki.
yanayin yadda nake maganar sai da ya bashi dariya ya ce
"To meye ma'anar *HAM'NAS* ɗin kuma".
fuskata narufe da tafin hannuna cikin muryar dariya haɗe da zakuwar jin yadda na haɗa kalmomin suka tafi normal nace
"Kaga ma anar sa, HAM sunana ma'ana HAMDAH, NAS kuma Naseem and Nasmah".
dariya sosai ya sake yana faɗin
"Kaga yarin ya mai basira, tabbas wannan suna yayi kuwa ba shakka *HAM'NAS* Co Fitroleum Nigeria Limited *HAM'NAS* Intranational School Of Science And Technology *HAM'NAS* Store Complex *HAM'NAS* Clinics *HAM'NAS* International Hospital, Eh ba shakka lallai sunan yayi *HAM'NAS* Allah ya taimaka yayi jagora".
tsabar zakuwa kasa kuma cewa komai nayi sai baki na da yakasa rufuwa..★
A ranar da yamma Mahmoud ya wuce Uganda........★







Mommyn Twins ce










HMD




🅿️3







Yau juma'a babban rana, ranar da duk kanin al'ummar musulmi suke farin cikin zuwan sa, al'ummar Annabi suna ta kai komo hada-hada da shirye-shiryen tafiya masallaci domin sallar juma'a.
da sauri Ummi tafito daga cikin bedroom ɗinta sanye da mayafi akanta, fuskarta ɗauke da yelwataccen annuri, da ka ganta kasan tana cikin matsanancin farin ciki. da sauri ta nufo bakin kofa,
lokacin Fauzan yasako kansa da gudu kaɗan yarage yayi karo da Ummi,
Ummi ta ce "Kai Fauzan bazaka rika yin abu cikin nutsuwa ba ko."
baki ya washe yana waigen bayan sa da faɗin
"Yau wa Ummi direba yadawo daga masallacin nace masa yafito da mota zai kai ki unguwa."
yana maganar yana waigen bayan sa yana wurga hannu alamun zakuwa, sarai Ummi tagane shi so yake ya bita dan tun kan afita a sallah yake fita dubo direba ko yadawo, dan ko masallacin shi baije ba dan ko da tace masa yaje masallaci cewa yayi wai shi a gida yau zaiyi sallah.
fita Ummi tayi tana faɗin
"To naji."
bayan ta yabi da sauri yana faɗin
"Ummi nima zan biki Ummi dan Allah kije dani kin ga wancan Juma'ar da ɗayan wancan juma'ar bakije da ni ba, akwai bashin tafiya unguwa biyu da bake je da ni ba."
"Tafican da alla kai ko ina za'aje sai an je da kai kai mata ne, da Nusaiba zamuje kai sai ka jira idan Abba ko Abbu'n ku suka dawo sai kayi musu rakiyar."
kafa yashi bubbugawa yana biye da ita a baya tare da faɗin
"Ummi nikam dai kije dani ina ranar da Nusaiba kuka je."
suna isowa tsakar gidan Mamie da Nusaiba suna fitowa,
dagudu Fauzan yaje in da suke yaruko hannun Nusaiba da take gyara mayafin ta da ta fito dashi rike a hannu tsabar sauri, jan ta yayi kusa da Mamie yana faɗin
"Allah yau bazaki je ba dani za aje Mamie rike min ita kar ki sake ta sai nashi mota mun tafi."
Mamie tace To cikin muryar dariya ganin yan da ya janyota tana torjewa kamar masu kokawa,
Ai ko Mamie na rike ta yajuya a guje yayi gun mota yana dariya da faɗin
"Yarinya yau badake za aje ba agida zaki zauna."
kukan shagwaɓa tasake tana jan hannunta dake rike a hannun Mamie tana faɗin
"Ai wlh dani Ummi zata tafi da kai namace ce sai ka rika bin mata unguwa, Mamie sake ni kuma sai na maka duka."
yana isa jikin motar ta zille a hannun Mamie tarufa a guje suka kama rige-rigen shiga mota.
tana faɗin
"Da kai mace ce kuma ai Ummi tace dani zata rika zuwa unguwa."
"Allah baki isa ba yaukam dani za a tafi ai sau uku ana tafiya dake unguwa ni ba a tafiya da ni sai naje."
yayi maganar yana shigewa cikin motar a guje, itama shigewa tayi ta ɗaya barin tana cewa
"Bazan taɓa zama a gida ba sai dai kai ka zauna."
Ummi kam baki ta rike tace
"Oh yaran nan sai shegen son yawo duk in da mutum zai je sai kun bishi kamar jakka."
dariya Mamie tabisu da shi.
da sauri direba yafito yabuɗe wa Ummi kofa tashiga, da sauri Nusaiba ta dawo gefen ta yazamo sun sata a tsakiya.
sunata yiwa junan su gwalo direba yaja motar suka fita bayan Mamie tayi musu a dawo lafy.

koda suka haura titi direba ya juyo ya dubi Ummi yace
"Hajiya ina zamu fara zuwa?."
yayi tambayar ne dan yasan rana irin ta yau wato ranar ko wata juma'a Ummi tana fita zuwa asibitoci kan titi in da mabarata suke zama dakuma masallaci in da mabarata suke zama, domin basu sadaka a kowace ranar juma'a, dan haka yake da tabbacin wannan fitar ma zuwa guraren zasuyi dan iwar haka suke fita.
Ummi tace "Babban masallaci zamu fara zuwa."
yace "To Hajiya." nan yajuya akalar tafiyar izuwa babban masallaci.
suna isa direba yagyara parking a gefe, Ummi tafito rike da jakarta, yayin da Fauzan da Nusaiba suka rufa mata baya,
ta isa in da mabarata suke jere a bakin masallacin, ta buɗe jakarta tarika ciro kuɗi tana raba musu, tana bin kowa layi-layi tana mika musu sadaka.
duk wanda ta mika masa sai ya kwararo mata addu'a da fatan samun biyan bukatun ta na alkhairi ga mahaliccin ta.
duk wan da ta bawa idan yayi mata wannan addu'ar sai kaga ta saki wani murmushi tare da fatan tabbatu war hakan acikin zuciyar ta.
akasin da da idan sunyi mata addu'ar saboda raunin dake zaune cikin ruciyar ta har sai ya kai ga tayi kukan zuci, tana ji ina ma Ubangiji yakarɓi addu'o'in nasu da wanda take hana idanun ta bacci acikin kowani dare, ya kare mata ɗiyar ta a duk in da take.
gaba ɗaya yau ɗin nan ta tashi ne cikin farin ciki da jin daɗi tana jin kanta cikin wani irin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login