Showing 12001 words to 15000 words out of 45625 words
kuma gefen hagu shima side ɗaya, sai dai ƴan madaidaita ne ba wasu manya ba.
daga tsakiyar gidan kuwa wani side ne na musamman wan da yazamo sauran side ɗin sun sashi a tsakiya shi kam gini ne mai hawa ɗaya babbane ya tsaru iya tsaruwa, daga saman side ɗin har kasan sa yaji ado da gilasai masu ban mamaki an kawata shi tamkar a turai,daga kasa kuma an zagaye shi da wasu flaw's masu matukar kyau da ɗaukar ido,
gaban side ɗin wani shinfiɗaɗɗiyar swimming pool ne wan da aka kawatashi da rubber grass malaye har bakin kofar shiga side ɗin.
gefe can kuma parking space ne ɗauke da lafiyayyun motoci da suka kai guda uhu a cikin sa,
daga farin shiga gidan kuma gefe da ɗakin mai gadi masallaci ne shin fiɗaɗe agun,
sai kuma ɗakuna guda ɗai-ɗai a jere guda uku a gefe da masallacin ta can.
Maganar Bappa naji yana faɗin
"Muje ciki ko HAMDAH." da sauri nadawo daga duniyar kallon gidan dana tafi, da murmushi kan fuskarsa dan ganin yan da na tafi gaba ɗaya na shagalta da kallon gidan.
na ce "To Bappa". a hankali nabi bayan su side ɗin da ke gefe ta hannun dama muka nufa a hankali nake taka kafata ina cigaba da baza ido cikin gidan har muka isa cikin side ɗin.
masha Allah ɗan madaidaicin side ɗin ya tsaru matuka.
side ne mai ɗauke da 3 bedroom ko wanne da banɗaki a cikin sa, ɗan madaidaicin parlour haɗe da dinning
da kitchen da komai da komai, an tsara komai yan da yakamata duk wani abun bukata an tanadar babu abun da babu.
ɗakunan cikin parlour'n muka rika shiga wan da komai akwai hatta gadon ɗakunan duk da shinfiɗar su, sunsha lafiyayyun bedsheets.
bayan mungama zagaye cikin side ɗin gaba ɗaya, muka fita ɗayan side ɗin dake gefen hagu muka shiga, shima kamar wancan side ɗin yaji komai. kowa sai faɗin masha Allah yake, nidai kasa magana nayi sai binsu nake inata baiwa idona abinci sabo da gaba ɗaya yanayin tsarin gidan yatafi dani.
daga nan ɗaya side ɗin dake can gabar da gidan muka nufa, shima tsaruwan sa da tsarin sa kamar sauran part biyun nan,
koda muka fito daga cikin part ɗin baki na washe nadubi Bappa dake ta faɗin
"Kai komai yayi masha Allah komai fa yayi yadda yakamata". baki nakuma washewa ina faɗin "Kai wlh Bappa gidan nan Allah yayi kyau kaga fa nan irin wancan can ma irin wancan kai tsarin gidan yayi kyau komai iri ɗaya, sai dai kawai kalolin kayan cikin sune daban-daban".
dariya Bappa yayi kana yace "Da gaske gidan yayi kyau ko?."
"Wlh kuwa Bappa." nafaɗa da sauri ina cigaba da washe baki, shima dariyar ya kuma yana girgiza kai kana muka rufawa mutanen baya in da suka nufi wannan kayatacce rantsatstsen babban side ɗin nan dake a tsakiyar gidan wan da yazamana da sauran side ɗin sun sashi a tsakiya.
a hankali muka isa bakin kofar da sauri ɗaya daga cikin mutanen ya isa bakin kofar side ɗin wan da yake na glass ya ɗaura hannunsa gefe kan wasu madannai ya daddanna sai ga glass ɗin yafara bada sauti ɗan baya yaja kana ya dubeni yace
"Bismillah Madam ɗan zo ki tsaya a nan."
ya nuna min kan step ɗin da yasauka akai wan da saika haura kansu kafin ka isa bakin kofar,step ne guda uku, nuna kai na nayi alamar ni?. yace "Eh." a hankali na matso na haura kan step ɗin, daga in da yake yamika hannunsa yakuma danna wasu lambobin kana yace na ɗaura hannuna kan nan yanuna min wani ɗan zagaye da hoton yatsu, a sannu nakai hannuna na dai-dai ta yatsuna kan zanen yastun, nan yafara bada sauri ɗit-ɗit sai kuma yakuma danna wata lambar data fito mai alamar Okay. nan take kofar tazuge gefe ai ko da sauri na ɗaga hannuna.
ya juyo yana duba na kana yace
"Madam wannan kofar special ne mai amfani da zanen yatsune mutum ɗaya ke amfani da shi, sai kuma wancan". yanuna wata kofar dake gefe ya isa gurin muma mukabi bayan sa,ni dai cikin rashin fahimta nake jin sa, yace
"Shi wannan common door ne kamar yanda aka sani kowa zai iya amfani da shi."
ya murɗa handle ɗin kofar yabuɗe muka shiga ciki.
sai gamu mun bayyana cikin wata katafaren parlour ya ilahi ya lilahi, har bansan san da na furta "Kai! amma wannan duk yafisu kyau!".
nayi maganar cikin hakikance gaskiyar abun da ke cikin zuciya ta wan da maganar fitowa kawai tayi,
Bappa ko karamar dariya yayi tare da jijjiga kai.
suma sauran dariya suka bini da shi, nan muka fara kusawa cikin katafaren parlour'n, baki da hanci gaba ɗaya na buɗe wajen kallon katafare kayataccen parlour'n, faɗan tsaruwar sa da misalta tsarin parlour'n ma ba zai misaltuba, yaji kayan alatu da more rayuwar duniya tsaruwan sa ya zarce sauran side ɗin da muka shiga babu haɗi ko kaɗan.
bedroom ɗin dake cikin parlour'n muka rika shiga ɗaya bayan ɗaya, bedroom ne zafafa har guda huɗu masu ɗauke da tsalatsalan bathroom,
daga gefe da parlour'n kuwa katon dinning area ne sai kitchen babba a gefe.
sama muka hauwa wan da shi kanshi step ɗin haurawan sama abun kallo ne domin kuwa shima an kawatashi na musamman.
wow masha Allah shima tsarin saman kamar kasan sai dai banbancin kalolin kayan dake cikin su, kalar kujeru da labulayen bedroom and parlour kasan white and ash da ɗan ratsin lemon-green. saman shima 4 bedroom ne a cikin sa kalan kayan bedroom and parlour'n kuma white and sky-blu.
Antsara komai yadda yakamata sai tashi da sassanyan kamshi mai haɗe da kamshin sababbin kaya yake.
kai gidan ya haɗu fa nidai bakina yakasa rufuwa wajen kallon tsaruwan gidan, bayan mun gama zaga lungu da sako na saman muka gangaro kasa anan muka yada zangon mu cikin parlour'n kasa.
Kowa sai yaba kyau da tsaruwar gidan yake, ɗaya daga cikin mutanen yadube ni kana yayi gyaran murya sannan ya ce
"Madam komai yayi ko? komai ya miki wannan gidan yayi miki? kokuma mu isa wani gidan?."
kallon sa nayi cikin rashin faminta sai kuma na maida dubana ga Bappa danaji yana faɗin
"Duk da dai bataga sauran ba amma ga yanda take ta washe bakin nan ai ba a magana."
da sauri nace "Bappa gidan..". bai bari na karasa ba yace "Gidan ki wannan gidan duk girman ta nakine akwai kuma ire-iren su suna nan".
ido na waro kamar a mafarki nakejin zancen, "Wannan ya miki?". mutumin yakuma jefo min tambayar, kai nashiga gyaɗawa da sauri sai kuma naruko hannun Bappa ina faɗin
"Eh wlh yayi-yayi Allah Bappa gidan yamin kyau sosaiiiii".
Dariya Bappa yayi yace "To sake min hannu kada ki ɓala".
ai ko sauran mutanen ma suka rika dariyar ganin yan da nake washe baki ina jijjiga hannun Bappa, Naseem da Nasmah dariya suka rikayi suna tsalle jikin Bappa kamar wan da sun san abun da ake.
Mutumin yacigaba da faɗin
"To masha Allah wannan side ɗin shine naki a yanda aka tsara ginin gidan, sauran kuma ke kikasan yan da zakiyi da su, yanzu mu zamu koma mubarki ki huta zamu dawo zuwa gobe, domin sauran baya nai."
Sukayi mana sallama suka fita, suna fita, na dubi Bappa ina waro ido nace
"Bappa wai da gaske wannan gidana?". Bappa yayi murmushi tare da faɗin "Daɗina da ke akwai shirme." hannu nashiga tafawa ina faɗin "Kai wlh gidan nan yayi min mugun kyau." ya ce "To sai ki goyashi kuta yawo tun da dai naki ne." ido na waro tare da sa dariya nace
"Bappa gidan zan goya?." kanshi ya jinjina yana murmushi.
rungume Naseem da Nasmah nayi cikin tsananin farin ciki, sai kuma na sake su.
da sauri nace "Bappa ina su Inna wuro da Fatu?."
yace "Suna can ruga". nace "Bappa shine bakazo da su ba kace su dawo nan suzo mu zauna da su a nan, kaji Bappa."
nafaɗa ina jijjiga hannun sa, "Kaji Bappa kace su zo". nakuma faɗa ganin yayi shiru bai ce komai ba,
yace "A'a HAMDAH su zauna acan zan koma ai nima".
ido nakuma warowa da karfi nace "Bappa ni kaɗai za'a barni a wannan gari gudan, da ni kaɗai zan zauna a gidannan ai dani daku zamu zauna."
nayi maganar ina nuna cikin parlour'n "Tap Allah bazan iya zama ba dan Allah Bappa kace su dawo nan, wannan gidan ai tsoro zai rika bani ni kaɗai a cikin sa, kaji Bappa?."
nafaɗa ina bubbuga kafafuna a kasa. "To babu damuwa zasu zo amma ba yanzu ba."
na ce "Bappa sai yaushe." ya ce "Bari dai mana a gama Hajiya HAMDAH."
dariya yake bani in naji ance Hajiya HAMDAH, ai ko na washe baki,
yace "To meyasa bakisa hakorin hajji ba acan?."
"Kai Bappa,hhhh to zan sa in na kuma komawa."
"Allah ya kai mu ai kamar yanzu ne shekara zata kuma zagowa Allah ya nuna mana cikin masu rai da lafiya."
yayi maganar yana mikewa tare da cigaba da faɗin
"To ni bazanje masallaci gashi ana ta kan kiran sallah, mutumin zo muje muyi sallah".
da sauri Naseem ya mike ya roko hannunsa suka fita.
Da sauri na mike inata daɗa waigen cikin parlour'n inshiga wan ɗakin in fita inshiga wancan haka narikayi, daga nan kuma naja hannun Nasmah muka haura sama ina faɗin
"Bari naje na zaɓi bedroom ɗin da yafi min."
koda muka haura ɗakunan duka na shiga kana nazaɓi ɗaki ɗaya, nan cikin bedroom ɗin nabuɗe bathroom ɗin sa na shiga mai girma da tsaruwa kamar ɗakin kwana.
kayan jikina na tuɓe duk da ban jima da yin wanka ba nacika ruwa cikin basin nashige ciki, lumshe idanuna nayi ina jin daɗin ruwan na ratsani, najima sosai a ciki kana na wanke jikina da sabulu mai sanyin kamshi da nagani cikin bathroom ɗin, sannan nafito.
Na sami Nasmah gaban mirror ta ɗauki janbaki sai murkawa take a bakin ta.
dariya nayi ina faɗin
"Oh wannan yarin ya ke kam akwai ki da son janbaki".
itama baki ta washe tana cigaba da kwaɓula janbakin a bakin ta.
da sauri na sauka kasa akwatin kayan mu na janyo nadawo ɗakin, a sannu na isa gaban wardrobe dan na shirya kayan ciki, ina buɗe wa ido na ware cikin wardrobe ɗin ganin kaya ashake a ciki, kama daga kan leshi atamfa material shadda dogayen riguna iri-iri, sai dai ba a ɗinke suke ba,a hankali na zaro ɗaya daga cikin dogayen riguna wan da suke jere gefe guda masu kyan gaske, na dawo gefen Nasmah na zauna, kana na sauya kayana da dogon rigar nan...
Tsabar farincikin da nake jin kaina ciki yau bazai misaltuba, muna zaune har su Bappa suka dawo muka sauko parlour'n kasa muna ɗan taɓa hira dakuma kallon tv.
duban Bappa nayi sai kuma kamar an zabure ni na mike ina faɗin
"Bappa ina zuwa."
sama na haura in da na aje karamar jakata ta hannu na ɗauko na buɗe jakar naciro wayoyin da jiya aka bani wan da tun da na kunna su nakuma kashewa najefa cikin jakar, dakuma ATM ɗin da jiya aka bani su a banki, nadawo in da Bappa suke da sauri nace
"Kagani Bappa jiya mutanen nan suka ɗauke ni sukayi ta kaini bankuna sukayi ta buɗe min account, muna dawowa kuma suka bani waɗan nan wayoyin ina kunna su kawai Bappa kaga kuɗin da sukayi ta shigowa kawai kuɗi sunata shigowa cikin accounts ɗin".
nayi maganar ina wawwaro idanuna alamun tsantsar mamaki.
Murmushi Bappa yayi irin nasu na manya kana yace "HAMDAH kenan ai kuɗin kine yake shiga cikin asusun bankin ki, duk wani abun da kikaga yake faruwa duka, duk waɗannan mutane dasuke ta zirga-zirga da ɗawainiya da ke, duk umurnine daga sama, duk kanin su an ɗaurasu ne jagora akan lamarin, shiyasa kikaga duk waɗan nan abubuwa suke faruwa duk abun da kikaga sunyi umurnine, sunce min ma gobe idan Allah yakai mu za'a fara kai ki guraren da akayi ayyuka wato guraren kaddarorin ki, kije ki gaggansu gobe za'a fara tafiya shiyasa sukace kihuta yanzu."
kai na jinjina alamun gamsuwa, ikon Allah abun kamar a mafarki yake zuwar min.
knocking ɗin da ake ne yasani mike wa nanufi kofar da nafi zaton tanan ake knocking ɗin, na isa jikin kofar na buɗe,
wani nagani tsaye rike da basket har guda biyu a hannunsa, ɗan risinar da kai yayi alamun girmamawa kana ya ɗago yayi min barka da warhaka, na amsa kana yace min order ne daga hotel ɗin su akace yakawo nan gidan, kai kawai na girgiza kana nabashi hanya yawuce ciki.
dinnig table ya isa ya aje kayan abincin kana yayi mana sallama yafita.
muna nan zaune a parlour sai wajen la'asar mukaje mukaci abincin, daga nan Bappa yakuma fita domin zuwa Masallaci shida Naseem.
Washegari da safe kamar yan da mutanennan suka ce zasu zo suka iso,
suna zaune a parlour nikuma ina ciki domin kimsa su Naseem, ina gama kimsasu muka sauko nan muka ɗunguma.
yau munsha yawo kaman kaman domin kuwa tundaga unguwar muka fara, wani gida mukaje sakanin sa daɗan rata da gidan da muke ciki, sannan muka wuce wasu unguwanni biyu duk kanin su da gidaje ɗai-ɗai, wan da an gama musu komai suna kulle,suka nunnuna min dakuma tabbacin nawa ne, nasha mamaki kwarai daganin manyan gidajen wai kuma a matsayin nawa.
daga nan wani tsalelen gidan mai muka je tun daga can nahango ( *HAM'NAS Co Petroleum Nigeria LIMITED* ) wan da aka rubuta da manyan harufa a saman gidan man, tunga nesa zaka iya hango shi ɓaro-ɓaro.
idanuna na lumshe tare dayiwa Ubangiji buwayi gagara misali tasbigi a kasan raina kana na buɗe,
Mun zaga gidan man na yaba da tsarin sa kwarai yana rufe ne ba'a fara aiki da shi ba,
daganan kuma wasu gidajen man mukaje har guda uku duk masu ɗauke da ( *HAM'NAS Co Petroleum Nigeria LIMITED* ) daga nan muka kuma zuwa asibitoci suma masu ɗauke da sunan ( *HAM'NAS International HOSPITAL* )
suma asibitotin guda uku a gurare daban da ban manyan gaske, sai dai duk a kulle suke anzuba kayan aiki komai da komai acikin su sai dai ba'a fara ai ki da suba.
daganan kuma makarantu da kamfanoni muka nufa duk kanin su da tambarin *HAM'NAS* International School Of Science's And Technology, *HAM'NAS Store Complex's su ma duk ba'a fara ai ki da suba. sai kuna masallatai manya guda uku anzuba komai a ciki suma ba'a fara amfani da su ba.
Zuwa yanzu kam nidai komai ganin sa nake kamar almara nafara yarda kan cewa komai da gaske ne, sai yamma muka dawo gida, mun dawo a gajiye suke faɗa min cewa muhuta nan da kwana uku sai mu fara tafiya guraren kaddarorin dasuke garurruwa nesa da nan, nace to Allah ya kaimu..
Damin Bappa narikayi nace nidai yasa su Inna wuro da Fatu suzo kafin mutafi nan da kwanan ukun,
yace a'a abarsu tukun ba yanzu ba,
haka dai dole yasa direba yaje ya taho da su dan na tubure a la dole sai an kawo su, ko da direba zaije ɗauko su nace yace musu kada suzo da komai, dan cikin side ɗin dana matsawa Bappa sai ya zabi ɗaya daga cikin side ɗin gidan wan da zasu zauna ciki, akwai kaya komai na bukata sai suzo suyi amfani dashi abun da babu sai a karo musu kamar kayan sawa shi da babu a sauran side ɗin.
hakan kuwa a kayi ranar da su Inna wuro sukazo murna kamar nayi yaya, suma agefen su ba'a magana, na rungume Fatu inata murna, tarika ɗaukar su Naseem cikin tsananin farincikin kuma ganin su.
a ranar ma Uncle Mahmoud yazo har da matarsa da yaran su, dan su anan Abuja suke gun ai kin sa.
nan muka wuni da su wunin ranar yayi min daɗi matuka, sai narika jin su tamkar wani ɓari ga ahalina,
ganin su yaɗan rage min kewa da begen family na.
Yau asabar hakan yayi dai-dai da kwanaki ukun da zamuyi tafiyar, da sassafe muka ɗauki hanyar suwa Kano, motoci biyu muka tafi dasu motar mu ni da Naseem da Nasmah dakuma Bappa,sai ɗaya daga cikin jagororin ke zaune a gefen direba, ɗaya motar kuma mutane huɗu ne a cikin ta suna gaba muna biye da su.
mun isa cikin garin Kano da misalin ƙarfe 12:30pm sai da muka tsaya mukayi sallah kafin muka nufi inda zamu,
gidajen mai muka fara ziyarta kafin asibitoti dakuma kamfanoni.
bamufi awa biyu a cikin Kano ba muka ɗau hanyar Kaduna a kaduna muka kwana, washegari muka nausa Katsina.
Sati biyu muka ɗauka muna yawon zuwa garuruwa ganin in da aka zuba ayyuka, masha Allah duk garin da mukaje daga gwamnatin su muke samun tarba da karɓa mai muhimmanci, daga karshe muka biyo garin Bauchi,
lokacin da motar mu tashiga cikin Bauchi state, tashin hankalin da nashiga bazai misaltuba, wani irin tashin tsikar jiki da sanyi mai matukar shiga jiki su suka ziyarce ni, wani irin ɓari da kakkarwa nasomayi lokaci guda har hakorana suna garuwa da juna, sai kuma wani masifaffen zufa yashiga keto min, hankalin Bappa yayi musifar tashi ganin halin dana shiga lokaci guda,
cikin tsananin tashin hankali jin bakon yanayin daya ziyarce ni lokaci guda tamkar ƙwaƙwalwa ta zata fashe jin wani irin abu mai matukar nauyi da kara ya dankare min a kai, kunnuwa na tamkar ana busa wani irin busa mai matukar kara da firgitar wa, da karfi nakai hannuna na toshe kunnuwana cikin matukar jin azabar dake kokarin tarwasa min rayuwa nashiga faɗin
"Bappa mu tafi Bappa kace musu kada mu tsaya Bappa mutafi wayyo Allah na".
kaina nashiga juyawa da karfi jin yan da zabar da nakeji na karuwa nan take nanimi tunani na na rasa.
cikin ɗaga murya ganin numfashi nakokarin barin jikina Bappa yace
"Direba yi hanzari mufita a cikin garin nan yi maza da sauri!".
gudu direba ya kara bai tsaya ba sai da muka fita a garin, gabaki ɗaya, hankalin kowa yayi masifar tashi ganin halin da nake ciki,
Bappa ko karatun Kur'ani yasoma yanayi yana tofa min, hankali na bai dawo jikina ba har sai da mukabar eriya'n Bauchi gaba ɗaya.
A hankali narikajin abun da nake jin na sassauta har ya washe.
numfashi Bappa ya sauke tare da saida karatun da yake, kai ya girgiza tare da faɗin
"Kai mutum abin tsoro ne Allah kashiga sakanin nagari da mugu akwai hisabi ranan gobe kiyama".
yadubeni da kula yace
"Sannu ko HAMDAH".
kai na girgiza yace "Me kike ji yanzu?". nuna masa kaina nayi da hannu dan shi ke yimin ciwo sosai.
"Zai bari insha