Showing 18001 words to 21000 words out of 45625 words

Chapter 7 - HAMDAH part 3 Complete hausa novel

RASHEEDA   

04 Oct 2024

12662

ya jajirce yatsaya kan lamari na yazamo silar isata matakin danake yanzu, matar sa ta zame min uwa ƴaƴan sa suka zame min yan'uwa.
Rungume su Naseem nayi a jikina ina jin wani irin kuna, rumtse idanuna nayi da karfi jin kaina yana wani irin tsara min, lokacin da tunanin abun da yayi silan rabani da ahalina yashiga yimin yawo a kwakwalwa da zuciya ta. zunbur na mike nashige bedroom ɗina, sam bana son narika tunawa da hakan duk ranar da na tuna nakan kwana cikin kunci da bakin ciki da matsanancin ciwon kai, dan ranar zan kwana ina kuka.

Zubewa nayi kan kado nakife fukata jikin pillow, kai na rika juyawa ina ta fafutukar son na mance da tunanin, amma ina sai daɗe tahomin yake, da karfi cikin karaji narika faɗin
"Wlh Allah Abba ban taɓa ai kata zina ba, Ya SALEEM ba wani ɗa na mijin daya taɓa sani na mace bayan kai, duk da karancin shekaru na Inna ta ta tsoratar dani haɗe da kyamatar dani illan dake cikin zina, Ya SALEEM kai ka sanar dani mene ne aure, a lokacin da kuma nasan mene ne auren akayi min kagen zina aka kuma sheganta min ƴaƴa, bazan taɓa aikata zina ko da ace bani da aure bare ina da shi ɗin."
wani irin kuka ne ya tsuɓuce min, na kankame jikin pillow'n ina cigaba da kuka mai tsanini.
nakai tsawon awa guda ina kukan kana da kyar na sai-saita zuciya ta na baiwa kai na da kai na hakuri, kana nagyara kwanciya ta wan da ba bacci nayi ba, sai tulin tunani daban-daban.
har yamma ina nan kwance, ganin tunani yana kokarin kassara ni sai na mike nanufi side ɗin su Bappa,
a can na iske su Naseem, har dare muna can sai wajen bayan sallar isha kafin muka koma side din mu.
zuwa lokacin kam naji saukin damuwa ta kwarai dan su Inna wuro sun yaye min shi da hirarsu mai ɗebe kewa.

Washegari Lahadi ma ban yarda na zauna a side ɗi na ba da sassafe na wuce part ɗin su Inna wuro acan mukayi breakfast, a nan nawuni muna hirar mu cikin jin daɗi.

Yau Monday da misalin karfe 7 narako su Nasmah har sai da naga tashin su kafin na koma ciki, ina gama abun da zanyi nawuce side ɗin su Bappa, ina shiga bayan mun gaisa Bappa yake cemin
"Dama yanzu nake da shirin niman ki, kan ai kin masallacin nan ne harfa an rigada an gama shi, wan da aka bashi kwangilar jiya yake sanar min da cewa an gama."
da murmushi sosai kan fuskata nace
"Kai masha Allah kai amma dai ai kin yamin sauri wlh."
Bappa yayi murmushi tare da faɗin
"In dai da kuɗi a kasa komai cikin sauki yake zuwa, in dai da kuɗi ai komai mai sauki ne Allah dai yaba da ikon cin jarabawar da yayi dan shi kanshi arziki babban jarabawa ne, yakan kai mutum wuta yakan kaishi aljanna, kuɗi kamar takwabi yake idan kayi jahadi da shi shigar aljanna mai sauki ne idan ka ai kata ɓarna da shi shiga wuta mai sauki ne, Allah yasa mudace."
Amin Amin. duk muka amsa da shi
cikin washe baki nace
"Bappa masallacin nan fa nagina ne saboda Inna duk ladar arika kai mata kabarin ta, shima asibitin da yanzu ake gina shi idan a ka gama komai kyauta za'a rika yi duk ladar arika kai mata cikin kabarin ta".
"Masha Allah masha Allah".
abun da Bappa da Inna wuro suka rika faɗa kena.
Bappa yace "Ubangiji Allah ya tabbatar mana da hakan Allah yajikanta da rahama ya kai mata dukkanin ladan kabarin ta ya kyautata namu bayan nasu, kai sannu HAMDAH kinyi tunani kwarai da gaske Allah ya saka miki da mafificin rahama."
Amin. nace ina mai jin sanyi da daɗin addu'ar da yake min.

Muna nan zaune a parlour ban ankara ba sai gani nayi karfe 12 har da ɗori,
wayata na ɗaga da sauri ina faɗin
"Ikon Allah lallai guri babu wuya dubi 12 har ta gota an yama Yakubu yadawo kuwa bari dai na kirashi naji."
nayi maganar ina laluɓo lambar sa, wayar tayi ta ring bai ɗaga ba, nakira yakai sau biyar bai ɗaga ba, na sauke wayar ina faɗin
"Oh to ya ajiye wayar a ina ne shi ga lokacin ɗauko su Nasmah daga School yayi, gashi nayi ta kiransa bai ɗaga wayar ba."
Bappa yace "Ko ina ya aje wayar to shi, ina yaje haka ayi ta kirashin baya ɗaga wa".
nace "Wlh ɗazu ne na ai keshi gidan Hajiya Firdausi matar ministar Bukar, akwai wasu kayan da tayi min tallar su wan da tayi odar su daga jamani, to sun yi min na tura da kuɗin to ɗazu take faɗa min direban ta baya nan ko zan turo nawa direban ya amso min, shine na tura shi to gashi har yanzu bai dawo ba nayi ta kiran shi ma bai ɗauka ba".
nayi maganar ina kuma ɗaga wayar nakuma niman lambar sa.
Hajiya Firdausi matar ministan Abuja ne,
na yar da idan Allah yayi maka rufin asiri babu irin mutanen da bazaka gani ba ka kuma yi tarayya da suba,
ire-iren irin waɗan nan matan manya muna hulɗa da su sosai wasu sun girme min nesa ba kusa ba, wasu ma sun haife ni sun juya amma haka muke cuɗan ya da su.

Mikewa nayi da sauri ganin na kuma kiran sa har sau biyu nan ma bai ɗaga ba, nace "Bappa bari naje kawai na ɗauko su har yanzu bai ɗaga wayar ba, kar suyi ta jira kasan mutumin ka yanzu haka yana kan musu rigimar zai dawo gida".
Bappa yace "Maza hanzarta kam ga guri nata kan tafiya".
da sauri nafita ina shiga side ɗina mayafi kawai na yafa dan dama a kimtse nake na ɗau ɗaya daga cikin makullen mota da suke cikin drower, da sauri na sauka na nufi parking space.
kana nashiga motar nayi wa motar key, tun kafin na karaso bakin get maigadi ya wangale min get yana fadin "Adawo lafiya".

Saboda yanayin gosulo na bata lokaci sosai a hanya dan har karfe ɗaya ta cika har ta ɗan gota, kafin nan na isa makarantar su.
tun kafin nakaraso get ɗin makarantar, na zubawa kofar makarantar ido sosai dan ganin wasu yara rike a hannun wani mutum "Kamar su".
nafaɗa a file, nayi saurin isowa gurin, da mamaki nazuba musu ido ganin suɗen ne, yana rike da su suko sai washe baki suke,
shikuma mutumin yana ta tafiya da su yana nufar wata mota dake fake taɗan can gefe da get ɗin makarantar, yayin da yake ta girgiza kai alamun yana jin surutun da suke ta zuba masa.
cikin hanzari na isa gefe nafaka cike da mamakin ganin nufar motar yake gadan-gadan na ɓalle marfin mota na fita da sauri, cikin hanzari nasoma bin bayansu ina faɗin
"Kai Naseem Nasmah!, malam ina zaka kaisu kuzo nan ku wuce mutafi".
mutumin bai juya ba sai su yaran ne suka juyo sai kuma suka kawar da kansu suka juya suka cigaba da tafiya suna cigaba da zuba masa surutu.
da sauri nasha gaban su gani yan da suka batsar kamar basu sanni ba nace
"Kai ina muku magana kuna jina ina zakuje kuwuce mutafi malam ina zaka kaisu?".
sai sannan mutumin yaɗan dukar da kansa dai-dai tsawon su kana yasoma magana
"Kunsan ta ne?." batare da yaɗago ko ya dube ni ba ya ce "Ke a ina kika sannu bamu hanya mu wuce."
ido na waro cike da mamaki jin abun da yafaɗa tare da mamaita kalmar nasa
"Nasan su? nasan su fa kace, da alla malam ka sake su ina magana kana cigaba da tafiya da su."
gefe na ya gota batare da yace komai ba ya karasa jikin motar nima da sauri na rufa musu baya ina cigaba da faɗin
"Kai malam ina tambayar ka ina zaka kai su wai kana tambaya ta nasan su ne, ni zaka tambaye ni nasan sune, tambaya ta kake nasan su? dalla kasake min yara muwuce,ina ne zaka dasu kake nufar cikin mota da su?,
idan baka sake suba yanzu-yanzu zan kira maka hukuma anan."
baiyi magana ba sai mika hannun sa yayi yabuɗe marfin motar, yaɗau ko kwalin chocolate yaciro chocolate guda huɗu yabawa Nasmah biyu ya baiwa Naseem biyu kana yace
"To ga tsarabar ku kuci wannan yanzu, wannan kuma sai kusa a aljuhu."
yafaɗa yana cusa musu wani chocolate ɗin cikin aljuhun wandon su.
da mamaki nake kallon su ganin yan da sukayi tamkar basu sanni ba, sai murna da tsalle suke suna faɗin
"Ye am bamu da yawa ye am bamu da yawa."
cikin takaici nakai hannu zan fisge chocolate ɗin, da sauri mutumin ya janye su gefe kana yaɗago kansa tare da zuba idanun sa cikin nawa,
wani irin dirrr naji a cikin jikina tamkar jan wutan lantar ki.......!







Mommyn Twins ce













6



Yan da idanun sa yasarkafu cikin nawa haka babu zato ko sammani shi yasani shiga yanayin,
sai kuma na gyara tsayuwa ta da kyau, wani kallo yake bina da shi daga sama har kasa kana yace
"Na ɗauka kafin kiran hukuma ihu zaki yi ta yi kitara jama'a kice ga ɓarawo yazo satar yara, ke ba'a yi miki ihu ba har ke zaki wa wani ihu? karfe nawa ne yanzu wai wannan lokacin ne lokacin zuwa ɗaukar yara a makaranta,abar yara can kowa ya watse sai su kaɗai a cikin makaranta, sabo da baki san abun da kike yi ba an turaki ɗaukar su kin tsaya kin ɓata lokaci a hanya kina damuwar ki wata kila ma kinbi gidan kawayen ki kin gama sharholiyar ki,
kafin nan kika zo wai ke a hakan kinzo ɗaukar su a makaranta, karfe nawa yanzu?. karfe nawa ne yanzu?!".
yakuma nanata tambayar, yana maganar ne ida nunsa a kaina da kuma alamun jaddada tambayon da yake jefa min,
gashi dai maganar cikin faɗa yake yin sa amma lamɓansa a hankali suke motsawa.
dogone yana da faffaɗar kirji da zubin kakkarfan maza, fuskarsa na ɗauke da ɗan siririn saje wan da ya zagaye fuskar nasa har zuwa ɗan gemun sa da bai wuce rabin kamu ba, irin gemun da gayu suke bare.
baza a kirasa da fari soll ba sanna kuma ba baki bane, hasken sa dai-dai.
kwantaccen gashin kansa baki sitif yasha gyara mai tsamtsi da tsulɓi sai wani yal-yal yake, sabo da iskar dake kaɗawa.

Kaina nakawar gefe tare da murguɗa baki nashi a wanne zai zauna yana wani masifa to ina ruwan shi ne ma.
ɗan rutsunawa yayi yarage tsawon sa dai-dai tsawon yaran kana ya dubi ko wannen su yace
"Idan kunje gida kuce wa Mommyn ku kada a sake turo Aunty ku ta ɗauko a School a rika ai ko me wayo yarika ɗauko ku, wan da bazai barku kuyi ta shan wahala a nan ba, kunji ko?."
kai suka gyaɗa suna ta faman shan chocolate "Yauwa to kuje gida sai gobe zan kawo muku wani chocolate ɗin, kada ku man ta in kunje gida kufaɗa wa Mommy kada a kuma turo wannan Aunty'n naku ɗaukar ku a School a aiko mai wayo."
yayi maganar yana yi musu alama da suje in da nake yana binsu da murmushi,
ido na waro cikin masifa nabuɗi baki zanyi magana, dai-dai lokacin mota ta faka gefen mu, da mugun gudu, Yakubu direba yafito da sauri ya iso in da muka yana faɗin
"Ranki shi daɗe Hajiya wlh gosulo ne yatsare ni tun ɗazu babu ta yan da zanbi na koma da baya na canza wata hanyar, gaba da baya motoci suka sani a tsakiya,jibi kumatu na har mari nasha dana nimi in juya dan na canza hanya, Hajiya a gafarce ni, wlh gosulo ne, ita kuma wayar sam na mance jiya da zankwanta bacci nacire ta a kara yau har gari yawaye kuma ban mai da kararta ba, Hajiya ayi hakuri da Allah."
maganar yake tamkar zai zuba guiwowin sa a kasa yana tafa bayan hannun sa a cikin ɗaya tafin hannunsa alamun roko,
banyi magana sai juya wa nayi nanufi gun motar dana zo da ita, dan wannan mutumin yakure ɓata min rai.

Muryar Yakubu naji yana faɗin
"A'a ranka shidaɗe ina wuni barka da warhaka."
bude motar nayi nashige ciki batare da naji amsa gaisuwar da yake yi masa ba.
sai juyawar sa nagani yamatsa jikin motar sa yana kokarin bude marfin gidan baya, da sauri a ka buɗe gidan gaba wani ya fito cikin hanzari yarigasa kai hannu jikin kofar yabuɗe, kana yaɗan ja dabaya ya bashi hanya yashige motar ya mai da murfin ya rufe, kana shi kuma yakoma mazaunin direba yaja motar sukayi gaba.
Yakubu yakamo hannun su Naseem ya kawo su motar da nake yabuɗe gidan baya yasaka su, yace
"Hajiya bari na rufe wancan motar sai na kaiku gida a wannan na hau abun hawa na dawo na ɗauki wanca ɗin."
yajuya da sauri ya nufi in da motar da yazo da ita yake, fita nayi nakoma baya in da su Nasmah suke, yana kulle motar yadawo yashiga mazaunin direba yaja motar.

Munbar harabar makarantar da ɗan nisa kana na juyo na dubi su Nasmah dasuka gama kwaɓe jikin su da chocolate, ganin ina kallon su sai Nasmah ta miko min na hannuta tace
"Mommy akici". cikin masifa nace "Ai sai kun sha duka ba kun iya kwaɗayi ba bakusan mutum ba kuka ma binsa, waya sani ma ko mai satar mutane ne yayi gaba da ku wata kila ma badun na iso da wuri ba da yanzu yayi gaba da ku, yaje yayi kuɗi da kanku,
idan kuka kara ganin mutum baku sanshi ba kuka bishi sai na zane ku, bare har ya baku abu ku karɓa sai na yanke hannun ku, yajaku mota zaiyi gaba da ku Allah ya so ku ai da kuna can Allah kaɗai yasan halin da kuke ciki, badun na iso da wuri ba, ɗan rainin hankali wai arika ai ko mai wayo yarika ɗaukar ku to ina ruwan sa ma daku tukun, mttsss." nayi maganar tare da jan tsaki.
baki Naseem yawashe cikin ɗan sallen murna daga zaunen da yake yace
"Ai Daddy yace dai caya mana mota."
wani irin faɗuwar gaba naji da ya ambaci sunan Daddy da sauri nace "Kai Naseem waye kuma Daddy?." Nasmah ce ta caɓe zancen da faɗin
"Daddy daya bamu chocolate yace dai cayamin jigi haida mota da chocolate da yawa."
da karfi jin yan da zuciyata ke tafarfasa kai na ke sara min nace
"Kai ya isa! idan na kara jin kalmar wani Daddy a bakin ku sai na fasashi, ku bani chocolate ɗin nan."
nafaɗa ina karɓe chocolate ɗin hannun su na zuge glaas ɗin motar nayi wurgi dashi.
maganar Yakubu najiyo wan da tashin hankalin da nashiga ciki yanzu sama-sama nake jiyo shi yana faɗi
"Hajiya ai shi wannan mutumin bamai satar yara bane mutumin kirki ne, shine Ahmad Tijjani Sabil mai kamfanonin nan wan da ake nuna shi agidajen talabijin, ai ko ɗazu dana kawo su makaranta na tarar da motar kamfanin shi tana sauke kujeru dawasu kayan amfani na makaranta,ai kin sa kenan yana da yawan taimako kuma taimakon sa yafi yawa a inda yara suke."
"Ahmad Tijjani Sabil."
na mai-mai ta sunan a raina ina ta son tuna in da nasan sunan, sai a lokacin na tuna ɗazu da safe ake labarai a kansa a gidan tv anan nataɓa jin sunan.
Naseem yace "Ai nima Daddy yace dai taya min mota in tuka akaina."
cikin tsawa nace "Ban ce kada naji wani ya kara min maganar wani Daddy anan ba?, rufamin baki idan ka kara sai na fasa ma baki bari ka gani."
Yakubu kuwa ci gaba da zuba yake wan da ma gaba ɗaya hankali na baya cikin motar da jikina gaba ɗaya.

Muna komawa gida nakira *HAM'NAS* Store Complex nace a kawo min motar wasan yara guda biyu da wasu kayan wasa, batare da ɓata lokaci ba motar ShopRite ɗin ya iso, a ɗakin kayan wasan su aka jibge musu,
ihun murna suka sake ganin motocin cikin tsallen murna Naseem yace
"La iyin motan da Daddy yace dai taya mana babba."
da sauri na mike daga kan kujerar da nake zaune cikin ɗakin kayan wasan su, hannayen su duka na riko nadawo na zauna, inajin zuciya ta na min mugun ɗaci da kuna a duk san da naji sun furta kalmar Daddy a bakin su,
duban su nayi dukan su nace
"Kuna ji ko Naseem Nasmah?, shi wancan mutumin ba Daddy'n ku bane baku sanshi ba kuma ku bakuda Daddy, nice Mommy'n ku kuma nice Daddu'n ku bakuga na siya muku mota ba, idan kuka sake faɗar Daddy bazan sake siya muku mota ba, kuma zan sa akwashi waɗan nan ma a tafi dasu, baku da Daddy nice Daddyn ku kunji ko?."
kai suka gyaɗa nace "To maza kuje kushiga motar ku." ai ko da sauri suka ruga in da motar suke suka shiga,
ina tare da su a ɗakin sai zaga ɗakin suke a cikin motar, suna dariya.
numfashi nasauke ganin suna cikin farinci sosai, Nasmah ta danna motar ta motar tatafi tsuu zata garu da jikin garu-bango da sauri na mike na tafi da gudu na taro ta, na ciro ta ciki ina faɗin
"To ya isa haka muje kuyi wanka kuci abinci sai kuma anjima zan sa afito muku da shi can tsakar gida kuyi wasan acan."
nayi waje da su.

Yau Juma'a da wuri Talatu tagama yi musu shirin makaranta, narako su har sai da motar kaisu makaranta yafita kafin na juya a hankali, gaba ɗaya yau jikina baya min daɗe a hankali na isa bakin swimming pool na cire takalmata gefe na zauna bakin swimming pool ɗin na zura kafafu na ciki, a hankali nake motsa ruwan da kafata ina ɗan lilashi ciki, wasu hawaye ne masu ɗumi suka zubo kan fuskata banyi kokarin sai da su ko danne zuciya ta daga abun da take jiba, tun jiya nake jin kai na cikin yanayin ina so nayi kuka ko zanji sassaucin abun da nake ji cikin zuciya ta, sai dai ban sami damar yin kukan ba saboda su Naseem, sam bana so nasaka musu rauni cikin zuciyar su, dan aduk san da irin wannan damuwar ta taso cikin zuciya ta zama nake a ɗaki nayita kuka, aduk san da sukaga ina kuka sun rika tambaya ta me ya same ni idan nayi shiru ban basu amsa ba ko nace musu babu komai suma sai su fashe da kukan su rungume ni muyita kukan.
tabbas ina ganin rauni da damuwa aduk san da hakan tafaru agare su, duk da kuwa kasan cewar su yara wan da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login