Showing 36001 words to 39000 words out of 45625 words

Chapter 13 - HAMDAH part 3 Complete hausa novel

RASHEEDA   

04 Oct 2024

12670

makarantar bana Gwamnati bane, makaranta ne ma irin na ƴaƴan masu kuɗi,
lokacin da na shiga makarantar nayi arba da wasu yara guda biyu, sunata wasanni da kayakin wasan da aka kai musu, duk da yara dayawa agurin amma nafi ganin farin cikin waɗan nan yara guda biyun sosai cikin matukar farin ciki da kuma jin daɗi suke ta wasa da kayan da motar Company na ta sauke,
naji daɗi matuka ganin farin ciki a fuska da zukatan ɗaliban, amma sai dai hankali na yafi karkata kan farin cikin da ke baiyana ga waɗan nan yara guda biyu,
kasan cewar lokacin tashi yayi nan ɗalibai suka fara watsewa, wasu diraibobin su suka zo suka kwashe su wasu kuma motar makaranta ta kaisu, haka yara sukayi ta watsewa.
ina nan a cikin makarantar muna magana da shugaban makarantar bayan mun gama maganar na fito, lokacin tuni students sun watse, a bakin get na tadda waɗan nan yara guda biyun, da lokacin da na shigo makarantar su na fara ganin su da ɗin bin farin ciki kan fuskokinsu, tare da mai gadin makarantar suna zaune a bakin get.
ko da na iso gurin su kan su na shafa tare da duban mai ganin na ce,
yaya su ba'a zo ɗaukar su bane kokuma motar makaranta zasu bi kuma naga ɗalibai duk sun watse.
mai gadin ya ce
Ba motar makaranta zasubi ba direban su ne zai zo ya ɗauke su ko mai akayi dai yanzu yana hanya, yau an ɗan makara ne wajen zuwa ɗau kar su.
kan su na daɗa shafawa sai nayi waje cike da jin sha'awar yaran, ina fita kuwa sai suka biyo ni a baya, sai na tsaya naruko hannun su ina tanbayar su yaya sunan su,
kai yaya sunan ka nafara tambayar na mijin sai yace min sunan sa Naseem, ita kuma macen tace min sunan ta Nasmah,
nafahimci wayo sosai tattare da yaran duk da kuwa ƙarancin shekarun su, dan bazasu wuce shekaru uku zuwa uku da rabi ba,
bayan nayi musu tambayar sai suma suka mai da min tambayar.
to kai ma yaya sunan ka, wayon yaran ya burge ni sosai jin yan da suma suka iya mai da min tambayar,
Sai nace musu sunana Daddy, kin san wani irin yanayi nagani a tare da su lokacin da nace musu suna na Daddy?."

Dan sakai ta maganar yayi tare da daɗa matse hannun ta cikin nasa kana yaci gaba da faɗin
"Ihun murna suka sake haɗe da tsalle suka rungume ni suna faɗin laa kai Daddy ne irin Daddy'n su Aeeman,ɗin class ɗin mu, to kai Daddy'n su waye ne?, maganar yaran yasa Ni shiga wani yanayi, sai dai farin cikin danake hango wa tare da su da kuma fahimtar da nayi kalmar sunan Daddy dana furta musu yazo mu su a sabon abu ko makamancin haka,
Sai na ce musu Daddy'n ku.
kin san me yaran sukayi?."
nan ma hannun ta yakuma damke wa cikin nashi kana yaci gaba da faɗin.
"Da ɗa rungume ni sukayi suna ta tsallen murna da nanata kalmar sunan Daddy,
wani irin abu naji acikin jiki na da zuciya ta, a duk san da suka furta kalmar Daddy a gare ni, sai naji wani irin farin ciki da jin daɗi mara misaltuwa a gare ni, cikin kan kanin lokaci naji yaran sun shige cikin zuciya ta,
har nake ji tamkar ƴaƴan da na haifa ne a gaba na suke kira na da wannan suna,
abun da na daɗa lura da yaran a lokacin sosai na ke hango jin daɗi irin na samun sabon abu a tare da mutum, sai suka ce min
Daddy kai ma zaka bamu chocolate irin wan da Daddy'n Aeeman yake bashi. na ce musu kwarai kuwa, to lokacin akwai ragowar Chocolate a mota wan da nake baiwa yara a gidan marayu idan naje,
sai na ruko hannun su nace muje na basu chocolate yana mota ma kuwa.
lokacin da muka nufi gun mota, a dai-dai lokacin wata yarin ya ta iso gurin a cikin mota."

Sai kuma yayi shiru batare da yaci gaba da Maganar ba.
ita ko zaman ta tagyara sosai wannan karon ita ta mai da tafin hannun sa cikin nata tasar kafe yatsun su guri guda, kana ta sanya idanun ta cikin nashi, cikin daɗa karfafa shi da bashi kwarin guiwar gama fidda damuwar da take ganin tamkar ta yaye masa, tagyaɗa masa kai cike da bashi kwarin guiwar yaci gaba da da fidda damuwar da take yi masa kallon cuta ce barin sa a ransa.
A hankali kuwa yaci gaba da maganar yayin da ya daɗa sarkafe hannun nasu sosai,
ya ce "Kawa kin san me naji?, wani abun mamaki naji wan da ban san mene ne shi ba,
bayan da yarin yar ta ɗauke su ta tafi da su,
sai na tsinci kai na cikin wani irin yanayi mai ka ma da da muwa,
mai kama da son in sake ganin su, amma nafi alakanta son in sake ganin yaran ne,
bayan kwana biyu sai naji tunanin nawa yanata rikiɗa, madadin tunanin yaran su biyu sai ya dawo uku, zuwa lokacin na gama fihimtar har da ita yarin yar nake son sake gani.
nayi mamakin kai na matuka,
wata rana dana fita muka kuma haɗuwa da su a kan hanya ta ta zuwa mittin,
a tunani na ganin da nayi musu wannan rana shike nan zuciya ta zata huta da tunanin abun da bai shafe ta ba, amma ina bayan rabuwar mu da su sai naji tamkar kara min ake.
Bayan wasu kwana biyun sai nasa ayi min bincike a kan su wato ita da yaran dana ke yi musu kallon kannen ta ne,
nayi mamaki matuka lokacin da labarin su ya iso min, dajin waɗan nan yara nata ne ma ana ita ta haife su.
mamaki na shi ne ganin ta kara ma sosai, nasamu cikakken labarin su, da duk kanin bayanan tarihin rayuwar su..."
shiru yayi tare da jan numfashi ya sauke, sannan ya ce
"Labarin su mai cike da ban tausayi na girgiza da jin lamarin, sai dai a yanzu su ba abin tausayi bane, dan Ubangiji ya zartar da ikon sa gare su..."

A hankali yashiga bata labarin su kamar yan da aka kawo mishi cikakken tarihin su, bai ɓoye ko rage mata komai ba kamar yadda baiyi da farko ba, bayan gama shaida masa abin da aka sanar masa a kan su sai ya cigaba da faɗin
"Kin san wace ce wannan yarin yar?."
kai ta girgiza jiki a sanyaye yayin da idanun ta suka cika da ƙwalla tap suna shirin zubowa.
taji bala in tausayin su da jin labarin su jikin ta yayi matukar sanyi.
ya ce "I ta ce mai Company *HAM'NAS*."
ido ta waro ta ce "Mai Company *HAM'NAS* mai *HAM'NAS* Nigeria Limited?."
"Kwarai kuwa ita ce."
kai ta jinjina tare da faɗin
"Allah mai iko wan nan shine sakayyar da mafificin rahama yayi mata sakamakon cin jarabawar da ya ɗaura mata tabbas labarin rayuwar ta abun a tausaya ne, a da yanzu kam Allah yayi mata sauyi da mafificin rahamar sa."
sai gata tana hawaye cikin matsanancin tausayin labarin rayuwar HAMDAH da taji, har da jan sheshshe ka.
ta kai hannun ta share hawayen ta tare da faɗin
"Allah kayi mana mai kyau kasa mu dace duniya da kiyama."
ya ce "Amin." sai ya saki hannun ta yakoma ya kwamta tare da lumshe idanun sa.
a sannu ta gyara ita ma sai ta kwanta gefen sa tare da yin pillow da damtsen hannun sa, a hankali takai hannun ta kan fuskar sa, a sannu tashiga shafa gefen fuskar sa, in da kayataccen saje ke kwance a gurin lub-lub gwanin ban sha'awa.
duban sa tayi da kyau cikin kulawa a hankali ta ce
"Aboki." idanun sa da suke lumshe yaɗan buɗe su a kanta sannan ya amsa da
"Na'am." in da ya am sa can cikin kasan mako shin sa, laɓɓan sa ne suka motsa tanan ta fahinci ya amsa kiran nata.
idanun ta cikin nashi, sannan tace
"Aboki bayan sanin labarin ta kuma sai me baka karasa bani labarin ba."
idanun sa ya lumshi cikin son kawar da zancen ya ce
"Wani labarin kuma ai na gama baki labarin."
murmushi tayi tare da faɗin
"Baka kara sa ba da saura dan acikin duk kanin labarin da ka bani baka bani asalin gundarin labarin ba, kawai dai ka ce min kana
jin wani abu a kanta mene ne shi?."
"Ba ko mai fa." yafaɗa a takaice yana gyara kwanciyar sa, tare da juya wa ya fuskanci jikin garu, yana faɗin
"Zanyi bacci ki tai maka min kisa yayi daɗi."
hannun ta ta cusa karkashin gashin kansa ta bayan keyar sa, yana jin haka da sauri ya juyo dan yasan jan masa sumar zatayi da karfi bawai tayi masa yan da zaiyi baccin ba.
dariya tayi tana faɗin
"Ai da baka juyo ba Aboki yau aski zan maka."
ido yaɗan waro ya ce "Aski da hannu."
farr tayi da ido ta ce "Zan nimo abin yin askin ai taɓawa nake naji ta in da zan fara."
ya ce "Faɗi gaskiya dai ƴar guntun muguntar ce ta motsa."
dariya takuma in da shi kuma ya murmusa yana kokarin mai da idanun sa ya lumshi tayi saurin dakatar da shi ta hanyar faɗin
"Me zaka ɓoye min ne iye sai fa ka karasa bani labarin nan dan baka gama bani ba."
shiru yayi bai ce komai ba,
Murmushi tayi tare da faɗin
"To ni bazan karasa baka labarin, tun da yau ka aro hijabi ka sakata sakanin mu, zan yaye ta yanzu dan babu ita sakanin mu har gaba da abadan."
ɗan numfashi ta ja tare da cigaba da faɗin
"Tun da ka sanya ido kanta Ubangiji yayi ikon sa,ya datsa maka sonta, a lokacin da baka taɓa sammanin a kwai ranar da hakan zata kasan ce da kai ba, dan kai a tunanin ka ni kaɗai ce Ubangiji ya dasa maka sona cikin zuciyar ka, babu wata macen da zata kuma samin gurbi cikin zuciyar ka,
ka mance da cewa Allah shi ne sarkin mulki mai yin yadda yaso da bayin sa, nasan ka da son yara amma son da kake yiwa waɗan nan yaran na daban ne, kana yi musu irin son da uba yake yi wa ƴaƴan sa, haka ne ko?."
tayi magaran tana duban sa da murmushi sosai kan fuskar ta.
numfashi ya sauke kana ya janyo ta jikin sa sannan ya ce
"Haka ne." ya faɗa dan babu ɓoye-ɓoye ko karya sakanin su, ko yan zu ma dayayi kokarin yin hakan sabo da wani dalilin yasha wuya sosai da fama da abun cikin zuciyar sa.
wani yelwataccen murmushi ne ya baiyana kan fuskar ta, kana ta ce
"Kana son ta?." kai ya gyaɗa alamar Eh sannan ya ce
"Amma abar maganar domin bana jin zan iya haɗa ki da wata."
gyemun sa taja, sai kuma ta ɓata fuska sannan tace "Haka Allah ya ce, bana son ka canza daga halin dana sanka baya yi maka kyau,
dama kan haka kake masaltawa zuciyar ka aje damuwar da bata saba ba, shine har kake son ka koyi karya ko?,
kana son ta, tun daga farkon labarin ta naji nima ina son ta ina son ƴaƴan ta, ita ta musamman ce yarin ya karama mai halin man ya ba kasafai ake samun irin su a duniya ba, ni ma ina son ta, zan ku ci gaba da son duk wani abun da kake so har idan bai saɓawa Shari'a ba har karshen rayuwa ta zan cigaba da son sa."
mike wa zaune yayi ya lankwashe kafafun sa kana ya dubi ta da ɗin bin farin ciki da jin daɗin kasan cewar ta cikin rayuwar sa ya ce
"Haki ka babu wan da yakai ni dace da samun mace ta gari, da ace kowani na miji irin ki ya samo a matsayin mata shi da damuwa ko tashin hankali bazai gansa ba har karshen rayuwa, Allah yayi miki albarka matar aljanna, faran tamin da kike Allah kema ya faran ta miki fara ƴar duma-duma ta."
"Ameen Ameen ameeeeeen."
tafaɗa tana jan ɗan gyemun sa irin na gayun nan.
sai kuma da sauri ta saki gyemun ta ce
"Ka faɗa mata kana son ta kuwa?."
kai ya girgiza ya ce "Ban faɗa mata ba."
ta ce "To me ya sa?." ya ce "Sabo da baza ta amince ba."
"Kamar ya, zakace bazata amin ce ba, baka tin kare ta da batun ba ka bata laifi." tayi maganar tana rike haɓa.
kuma tun ta yaja kana ya ce
"Um to tana da masifa tsiwar tsiya ce da ita."
dariya tayi sosai tare da tafa hannu ta ce
"Masifa haɗe da tsiwa kuma, a'a kada kayi wa kanwa ta fin tsayi." shiko murmushi yayi yana faɗin
"Allah idan ta fara tsiwa sai kin sha mamaki."
dariyar ta kuma ta ce
"Zata amin ce kai dai je ka latsa ta kuma ka gani in sha Allahu zata amin ce, wata mace ce zataki tayin ka duk haɗuwar ta da dukiyar ta kuwa,
ai mijin nawa da farin jinin sa aka halitto sa, shiyasa ma har gida ake kawo masa hari, wannan bazawarar taka ma jiya ta zo."
dariya duk kanin su suka fashe da shi, zillo tayi gefe ganin yami ko hannu yana kokarin ruko ta, tasan sarai baya so tari yi masa maganar ire-iren waɗan nan matan da suke kawo masa hari.
janyo ta yayi jikin sa ya rungume yana faɗin
"Zakiyi baya ni." dariyar take tana daɗa shige wa cikin jikin sa.
Kissing yashiga ai ka mata yana faɗin.
"Hakika nayi dace da mace ta gari ƴar uwa ta jini kawa kuma abokiyar shawara,
tabbas duk wan da yasa mi mata kamar ki yagama more yaruwar sa har gaba da abadan,
ke matar aljanna ce insha Allahu da yar dar Allah zamu shiga aljanna ni da ke da kafafun mu."
Baki ta turo gaba ta ce
"To HAMDAH fa?."
ya ce "To har da ita." mumushi tayi tare da daɗa rungume shi ta ce
"In sha Allahu kuwa Allah ya tabbatar mana."
ya am sa da amee. nan suka shiga nuna wa junan su tsantsar kauna da soyayya in da zancen ya sauya suka lula duniyar ma'aurata...


Wane ne AHMAD?......!






Mommyn Twins ce




11



Ahmad Tijjani Sabil shine cikakkoen sunan sa, mahaifinsa Alhaji Tijjani Sabil shahararren ɗan kasuwa ne wan da ya jone da siyasa,yayi suna ya shahara a kaf faɗin Nigeria har ma da kasashen ketare,
mutum ne adali mai gasjiya da rukon amana da son jama'a, yana da taimako matuka musamman ga nakasa dashi.
matan sa biyu Hajiya Karima da Hajiya Harira. Hajiya Karima itace uwar gida shekarun su biyar da ita Allah bai sabu haihuwa ba,
bayan shekaru biyar ɗin yakaro aure in da ya auro Hajiya Hariri, cikin yar da da buwayar Allah tana shiga Allah yabata ciki.
hankalin Hajiya Karima yayi masifar tashi, sai dai bata nuna wa a fili ƴar kasa take yi dan ta iya makirci, a fili kam nunawa take tana son cikin sosai.
bayan wata tara Hajiya Harira ta haifo ɗan ta namiji yaci suka Ahmad.
Ahmad yatashi cikin gata da soyayya, tun daga kan sa Allah bai sake basu haihuwa ba.
Ahmad ɗa ɗaya tilo ga Alhaji Tijjani Sabil, yayi karatun sa na primary da secondary a nan kasa Nigeria in da daga nan Alhaji Tijjani Sabil yaɗaga sa daga nan ya millashi kasashen ketare acan ya kammala karatun sa in da ya dawo Nigeria da sakamako mai kyau.
dawowar Ahmad Nigeria da wata ɗaya aka ɗaura musu aure da ƴar uwar sa, wato yarin yar kanin mahaifinsa, Rasheedat,
wan da dama can suna soyayya tun kafin ya bar Nigeria, a gidan su ta tashi shakuwa ce mai karfi sakanin su wacce har takai ga haifar da sosayya, yabar ƙasa Nigeria da alkawarin aure sakanin su, dan haka yana dawowa batare da ɓata lokaci ba aka ɗaura musu aure tare da gaggaru min biki, irin namasu akwai.
Ahmad da amaryasa Rasheedat zama suke na amana da sansar kauna da soyayya da tarairayar junan su, basa kaunar abun da zasuyi ya ɓatawa ɗayan su rai, babu wan da yake ɓoyewa wanin sa sirrin sa,
yar da da amin ta da suke yi wa junan su, har ya kai ga suka lankayawa junan su suna, in da Ahmad yake kiran ta da kawa dan acewar sa bashi da kawa kuma aminiyar da ya wuce ita.
ita ce murfin rufe sirrin sa itace sirrin sa ma gaba ɗaya.
Ita kuma take kiran sa da aboki dan kuwa bata da wan da ya fishi, shine kawa kuma aminin ta. yan da suke gudanar da
rayuwar su gwanin ban sha'awa.
bayan wasu shekaru da auren su mahaifinsa sa wato Alhaji Tijjani Sabil yayi hasarin mota a hanyar sa na zuwa airport in da zai tafi kasar waje domin gudanar da wasu kasuwancin sa, nan take Allah ya karɓi rayuwar sa.
Bayan rasuwar sa da shekaru biyu Hajiya Hariri wato mahaifiyar Ahmad ita ma ta rasu, sakamakon ciwon zuciyar da ya kamata bayan rasuwar mijin ta da yayi faraɗɗaya batare da ciwo ba.
Ahmad yashiga tashin hankali rashin uwa da uba daga karshe ya fawwalawa Allah komai.

Bayan rasuwar mahaifansa duk kanin ragamar dukiyar mahaifinsa da kaddarorin sa yadawo karkashin kulawar sa, shiyake kula da komai sakanin dukiyar sa da kuma dukiyar mahaifinsa.
Shekaran su 8 kenan da aure Allah bai basu haihuwa ba,
ko dai-dai da rana ɗaya Ahmad bai taɓa sawa kan sa damuwa kan rashin haihuwar su ba, ya san cewa Allah ne bai kawo lokaci ba,
shi yake rarrashin Rasheedat a duk san ta nuna damuwar ta kan rashin haihuwar nasu.
yakan yi mata tuni kan cewa Allah ne mai badawa kuma bai mance da su ba lokaci ne dai baiyi ba.
Ahmad mutum ne mai son yara duk da kasan cewar sa mutum mai son yara, bai taɓa tunanin kara aure wai ko dun zai sami ƴaƴa ba.
a duk in da yara suke zakaga ya na yawan ziyar tar gurin, kamar makarantun yara da gidan marayu, ko tafiya yake idan yaga yara sai ya tsaya ya nimi yayi musu wasa da kuma kyauta, shi yasa yawan cin taimakon sa tafi yawa kan yara da gajiyayyu, sai dai masu karfin ma bai barsu ba.
Ahmad yayi suna a duk faɗin Nigeria tai makon sa yazaga ko ina.

(Wannan kenan kaɗan daga cikin labarin Ahmad)★




A can cikin garin Bauchi
Ummi Aunty Rafee'at da Aunty Jaleela Nusaiba ne zaune cikin parlour'n Ummi, suna ta hira, kamar yadda suka saba a kowani makon karshen wata suna kawo wa iyayen su ziyara.
suna tare cikin parlour suna ta hira,
Fauzan ne yafito daga cikin bedroom ɗin Ummi hannun sa na bayan sa da alama wani abun yake ɓoye wa. Aunty

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login