Showing 1 words to 3000 words out of 45625 words

Chapter 1 - HAMDAH part 3 Complete hausa novel

RASHEEDA   

04 Oct 2024

12672

🌺 *HAMDAH* 🌺
*WASA FARIN GIRKI!!*✍🏻


*NA*
*RASHEEDA S DIRECTOR*


_(Book 3)_


_(Bismillahirrahmanurrahim.) Alhamdulillah ina yiwa Ubangiji buwayi gagara misali godiya da ya kuma bani iko a karo na uku nakuma dawowa domin kawo muku cigaban labarin HAMDAH ina rokon Allah ya bani ikon kammala shi lafiya👏🏻_

(Afwan a karshen book 2 nasaka (After 1 year)
I'm so sorry typing ero ne👌🏻)




Littafin na siyar wa ne ki biya ki karan ta.
domin biyan kuɗin littafin sai ka-ki tuntuɓi wannan number 08034690723




🅿️1





Bayan wani lokaci.
Tuni ai kin hajji ya karato gamasu niyya tuni aka fara shirye-shiryen tafiya ai kin hajji. kan kace me kasar Saudiyya tacika tayi makil da al'ummar Musulmi.
yanzu bama samun wani zama kullum muna hanyar zuwa bautar Ubangiji, ba dare ba rana kullum Bappa na tasani gaba wani sa'in tare muke tafiya da su Naseem da Nasmah,wani sa'in kuma na barsu wa Mammaa mahaifiyar Ukhtee kawata da nayi anan cikin masarautar Saudi jika ga Masarautar Saudi. dan tare muke tafiya da Ukhtee ita kuma Mammaa ciwon kafa ke damun ta bana bazata samu daman fita afara aikin hajji da itaba.
acewar ta sai an zurfafa ibada sosai kan lokacin Abdul Malik yayan Ukhtee da yake karatu can jami'ar Madina yashigo zai fita da ita guraren ibada a kan keken zama irin na masu ciwon kafa. kasan cewar na yaye su Nasmah kuma suna cin komai gashi sun saba da matar sosai, shi yasa wahalar su ta ɗanyi min sauki ko zamu fita ban cika tafiya da suba....
cikin yarda da buwayar Ubangiji aka kamla ai kin hajji na wannan shekaran lafiya.★
tuni mahajjata suka fara komawa kasashen su,nan muma muka fara shiri damin ko mawa kasar mu.
ana gobe jirgin mu zata ɗaga. tun safiyar ranar jama'ar dake cikin masarautar sukayi ta zuwa sallamar mu. duk wan da yazo sai ya nuna baison tafiyar mu wasu ga fuskokin su wasu kuwa sai sun kai ga furtawa. Ukhtee da Mammaa da tun safiyar ranar muke tare da su a side ɗin mu,
suka tirje wai sam sai dai Bappa ya barni a nan, ai ko nan kowa yace ya barni shi ya tafi bayan wani lokaci sai na koma.
ni dai dariya kawai nake binsu da shi, sai dai zuwa yanzu jikina yayi sanyi ganin yan da Ukhtee take kuka.
bilhakki ta rungume Nasmah tana faɗin bazan tafi ba.
Bappa ko ido yake binsu da shi cike da mamakin ganin zunzurutun kauna gun waɗan nan larabawan.
ana cikin haka kiran Mahmoud ya shigo wayar Bapp.
nan yake sanar wa Bappa yasami masaniya daga shugaban kasar mu anfara duk ayyukan dana lissafa kuma bazai ɗau wani lokaci ba insha Allah za'a gama,
Bappa yayi fatan alheri kana yakashe wayar.
koda naji labarin daga bakin Bappa nayi matukar mamaki dan ni har yau ganin abun nake kamar wasa bazai yiwu ba.
Bappa ya mai da hankalin sa kan mutanen da suke cikin parlour'n, abun da ya lura shine suna matukar son ba'i musamman wata kabilar, bugu da kari wan da Allah ya ɗaukaka a cikin su, babu garin da zai waye wasu daga wasu unguwanni daban-daban wasu kuma daga ɗan garuruwan dake gefen gari basu shigo ganina ba, na zamo abun kallo da hira a gurin su, haka zasuyi ta hotuna da ni da su Naseem.
numfashi Bappa ya sauke ganin gabaki ɗayan su kalma guda suke nanatawa..
dun dole Bappa ya amsa musu badun yaso ba da sharaɗin zasu sako ni a jirgi nan da ɗan kwanaki kaɗan.
ai kuwa ihun murna Ukhtee ta sake ta rungume ni tana sunbata. gaba ki ɗaya parlour'n yakaceme da murna...
washegari da misalin karfe 4 na asuba jirgin su Bappa ya ɗaga suwa kasar mu ta gado wato Nigeria★.
kafin ya tafi sai da yayi ta min nasihohi da jan hankali mai ratsa jiki..
tun da Bappa ya koma kusan kullum sai munyi waya ta wayar Ukhtee har da su Inna wuro.
Alhmdllh bazan ce komai ba game da zamata anan cikin masarautar Saudi batun samin kula da tarairaya ni da ƴaƴana kuwa ba'a magana...




A can kasar Nigeria cikin garin Bauchi state.

Na'ima ce da kawar ta Raliya,tafe cikin mota suka ɗau hanyar wani asibiti dake nan cikin G.R.A wan da shine Na'imar ke zuwa awo.
Raliya ke jan motar Na'ima na zaune a gefen mai zaman banza.
Raliya ta ɗan muskuta ta dubi kawar tata kana ta mai da idanun ta kan titi tare da faɗin
"Aminiya yanzu yanda kika tsaran nan kina ganin hakan zai yuwu kuwa baza'a sami wata matsala ba dai ko?".
Na'ima tasauke numfashi tare da gyara zaman ta cikin karfafawa da gaskata muradin ta tace "Kada ki damu aminiya Nice fa Na'ima baza'a sami wata matsala ba tabbas zai yiwu zai yiwu, yau ɗin nan kuwa zan haihu, Raliya ina cikin haɗari dole ne kawai na ai watar da hakan, kinsan kuwa jiya da daddare muna kwance da SALEEM yaɗaga rigata yana duban cikin yace shi har yanzu baya ganin garman cikin ciki wata 7 amma har yanzu bai taso ba,
kin san me yafi firgitani kuwa?".
tayi tambayar tana duban Raliya.
Raliya ta girgiza kai cikin takai ci taci gaba da faɗin
"Aminiya sunan wancan ɓatacciyar yarin yar, ya kira min har da min misali da ita, wai lokacin da take da ciki bai cika wata huɗu bama amma yaɗan taso".
ido Raliya ta waro tace
"What! ya akayi har ya iya tunota? to gaskiya kawata kada kiyi wasa".
Na'ima cikin damuwa da bakin cikin tuno da HAMDAH da SALEEM yayi tace
"Shiyasa nake son bin duk wata kofar da zaibi ya tuno da wancan banzar ɓatacciyar da ko a muce ko a raye oho, duk wata kofar zanbi na toshe duk da nasan bayida wani kataɓus, ko da ya tuno tan ma, amma ni kwata-kwata bana son na rikajin kwatankwacin irin sunan ta a bakin sa,
bakiji abun da boka yace min ba, yana son yara sosai hakan zai iya yin tasiri wajen rika tuno ta da ita da abun da ke cikin ta duk da hakan ba wani abun damuwa bane amma ni dai sam bana son jin kalmar sunan ta kan laɓɓan sa,
to ko yau da safen nan ma muna kwance dashi yaɗaga rigata yana shafa cikin yace wai anya abun da ke cikin nan yana da lafiya kuwa shi baya ganin yana girma,
nace masa ai jikina yabi Allah ya taimaka ma ina da tumbi,ke nifa kullum a narka abinci nake aciki na in kika ga abincin da nake ci yanzu wai dun kawai tumbi na ya kara girma,
yanzu Raliya cikin nan wata 7 ne yana daf da shiga wata 8 yazama dole na ɗau mataki in ba hakaba komai zai iya ɓaci,
kin ga wancan hatsabibiyar kanwar tasa Rafee'at ranar da muka haɗu a gidan su har habai ci take min wai mai cikin tuwo, ni har na fara zargin ko ta gane ne".
Raliya ta saki dariya har tana dukan sitiyarin motar tana faɗin
"Ai wannan Rafee'at ɗin shegiyar gaske ce sai ana taka mata burki".

dai-dai nan suka isa get ɗin asibitin, hon Raliya tayi mai tsoron bakin get ɗin yawan gale musu get.

a gefe in da aka tanada dan ajiye motoci suka faka suka fito suka nufi cikin sibitin.
kofar wani office direct suka nufa tare da yin knocking,
daga cikin office ɗin aka basu izinin shigo wa.
wanda ke cikin office ɗin yana zaune cikin shigar likitoci yana ganin su ya washe baki tare da faɗin.
"A'a manyan kasa kune tafe?".
cikin fari da ido Raliya taja kujerar da ke fuskantar sa ta zauna tana faɗin.
"Kanana dai ai kune manyan kuna zaune AC na ratsa ku kuɗi na shiga yadda yakamata me yamuku saura?".
Na'ima ma kujerar taja tazauna kana suka shiga gaisawa,
suna ɗan taɓa hira da dariya sakanin su da kagan su kasan tabbas sunyiwa juna farin sani.
Dr Mukhtar Lawan abokin su Na'ima ne sosai abota ne na tun a makaranta duk kanin su gar tasan garne, duk wani iskanci da sheke ayar da sukayi lokacin suna makaran ta tare sukeyi, har kuma yanzu wani kullin tare suke tufke shi. acikin su shine kaɗai yaɗan maida hankali kan karatu har yake cin moriyar karatun da yanzu yake a matakin Dr, asibitin mallakin sa ne wan da mahaifinsa yagina masa bayan zamowar sa Dr.
duk hirar da suke Dr Mukhtar idanunsa a kan Raliya,yakafe kirjin ta da ido wan da ɗinkin rigar jikin ta ya bayyanar da nonuwan ta kusan rabi a waje.
fiki-fiki yayi da ido cikin yanayin shiga tarkon Raliya yadubi Na'ima kana yace
"Na'ima kawarki Raliya takini fa taki na ganta kwata-kwata yanzu ko waya na kirata muɗan haɗu taki ta bani da ma mu haɗu, sabo da tasami manya wan da suka fimu bata hurɗa da mu".
yakarashe maganar da mai da idanunsa kan Raliya wacce tadaɗa bankaro kirji tana wani fari da ido.
dariya Na'ima tayi tace
"Kai haba aminiya ai ko ba komai dai zakizo wannan haɗaɗɗen office ɗin kiɗan rika ɗebe maba kewa."
fuska Raliya ta yamutsa cikin salon kwarewa a harkar bariki takuma bankaro kirji yayin da yatsarta guda ke saman wuyan ta tana ɗan yawo da shi har zuwa kirjin ta, ta saman nonuwan ta,ido ta kanne a kansa kana tace.
"Dr kenan ku abun naku ai sai a hankali in ka shirya yanzu Na'ima ta wuce ta bamu guri amma yanzu zaka ajiye min rabin miliyan anan shima ɗin dai-dai azo sallama ne".
tanuna saman table ɗin gaban sa.
ido ya waro da karfi ya furta
"500k ai ko ai kina na wata guda bai kai rabin miliyon ba".
dariya duka suka saka.
Dr Mukhtar yace
"Ina kinji ko Na'ima kawar ki tafi karfi na sai dai mugani kawai mu latse baki, ko za'a ɗan taimaka min naɗan lallasa ne basai ciki ba iya waje kawai". yakarasher maganar da dariya haɗe da tsigar zolaya.
baki Raliya ta taɓe tana faɗin
"Yanzu dai muyi abun da yakawo mu, Dr muna da damuwa fa".
Na'ima ta karɓi zancen da faɗin
"Kwarai kuwa Dr akwai matsala".
yace "Wani damuwa kuma ai ni a tunani na yanzu bakuda wata sauran ragowar damuwa ke Na'ima da kike da SALEEM a hannun ki".
"A'a Dr gaskiya da saura nasame shi kam amma da saura munaso mukuma samin shi sosai yazamo nawan da gasken gaske".
zaman ta ta gyara da kyau ta daɗa fuskantar shi kana tace
"Dr yau nazo haihuwa".
ido yawaro yace
"Haihuwa kuma antaɓa haihuwar da ba ciki?". yafa da dariya
sai kuma yakuma sakin dariyar shakiyyanci
yace "To ai cikin naki baikai na haihuwa ba tukun".
wani goron numfashi ta sauke kana ta daɗa gyara zaman ta da kyau tace "Dr tunani na kenan ranar da cikin nan zaikai na haihuwa, ace ciki yayi wata tara yaya zanyi narasa yanda zanyi,
rabon da naji wani abu yasani shiga damuwa irin haka na mance, Dr taya zanyi nasami ɗa kune manya aikin kune kunfimu sanin yadda za'ayi".
jakar hannunta ta aje gefe kana taɗaura hannayenta biyu kan teburin gaban su sannan tacigaba da faɗin.
"Ko nawa ne zan biya har idan nima bukatata zata biya".

Ɗan shiru yayi yayin da yake ɗan juyawa kan kujerar da yake kai, sannan yasauke numfashi kana yace
"Gaskiya wannan buka taki babbace a gaskiya yanzu samin ɗa a cikin asibitin nan da kamar wuya, yanzu an saka matakan tsaro iri-iri, kinsan kwanaki fa munyi ta shari'a da wasu mutane wan da mukayi musu canjen ɗa,munyi ta samin matsala dan ma allah ya rufa asiri,
amma mezai hana tun da kince kinason ɗan cikin gaggawa kije gidan marayu, gidan marayu yakamata kije, akwai wan da suka haifi ƴaƴa zaki iya samin wan da yau ma ta haifa ta yar aka samu aka kai shi gidan marayun,
to inaga kije ki ɗauka a can ɗin zaifi".
kai Raliya ta jinjina alamun gamsuwa da shawarin nasa tace
"Eh gaskiya hakan ma kawai za'ayi gidan marayun zamuje mu samo ɗan acan kagama babu wanda ya isa ya zarge mu, sukuma hukumar gidan marayun zamusan yadda zamuyi da su tun da akwai ƴaƴan banki".
Shiru Na'ima tayi yayin da ta zurma cikin tunani naɗan wani lokaci kana ta ce
"To shike nan amma kuna ganin baza'a sami wata matsala ba ko?, dan nifa bana so maganar tafita naso ace munyi shi anan sakanin mu basai ansako wasu ciki ba".
Dr Mukhtar yace "Ai samun ɗa a gidan marayu shine kawai mafita kuma rufin asiri, tun da jakar ku na cike da makullin kulle bakin wasu ai an gama,
idan mukace a nan ne zamu samu to za'a iya samin matsala dan har yanzu asibitin nan idon hukuma yana kansa sun saka ido sosai suna jiran suji wani abun yakuma fita su sami mafakar hujjojin da suka tara, wan da naki bada damar hujjar tasu tayi aiki idan da kuɗi meye bazamuyi ba".
ido Raliya ta kanne tace "Wai wan da kayiwa ai kin nan nawa ne yabaka haka?".
wani munafukar dariya yayi kana yace
"Miliyan 10 tabani kuma ko wani wata ina ɗaukar albashi daga gurin ta".
"Bayan 10 million tana kan baka wani kuɗin kuma?".
Na'ima tayi maganar da fuskar mamaki.
yace "To ai kin wasa nayi mata kaɗan fa yarage yataɓa nawa aikin dan ma Dad yatsaya da gaske kan lamarin, canjin ɗa ai bakaramin kasada bane, jigo na canza mata da shi ɗa na miji na musan ya mata da mace, to kuɗin wasa suke samu a kasar nan 10 million wani kuɗi ne agurin su,
duk wata 300k nake ɗau ka a gurin ta tukuicin godiya."
dariya suka sheke da shi cikin muryar dariya Na'ima tace
"Kai Mukhtar wlh bakada dama shine ko ɗan salalan nan babu."
"Haba wani salala ke me zakiyi da kuɗi yanzu kinada jakar kuɗi a gefen ki, kinada ABDALLAH IDRIS ABDALLAH me kuma zakiyi da kuɗi, ai nine abun a taimaka dan ko Raliya kuɗin da take samu bani samun irin sa".
mikewa Na'ima tayi tana faɗin
"Kace dai bazaka bamu ba kawai musan in da muka ajiye ka, aminiya tashi mutafi gidan marayun nan yanzu ba'a bori da sanyin jiki".

zai yi magana sai kuma yayi shiru sakamakon hayaniyar da yaji ke ɗan tashi daga can waje da alama a cikin parlou'n asibitin ne in da mutane ke zama dan jiran ganin likita.
wata nurse ce ta shigo bayan tayi knocking an bata izinin shigowa,
ɗan rusunawa tayi tace "Sir gawasu sun zo da alama haihuwa ce sai dai basuzo da kayan haihuwa ba, nace sukawo kuɗin kayan haihuwar sunce basuda kuɗi,nace to su koma suzo da kuɗi sunki tafiya, kuma yara ne dukan su nayi ta tuhumar su ina iyayen su sunyi shiru na ce suje su kira babba san nan su taho da kayan karɓar haihuwa ko kuɗin kayan tunda akwai anan sunki tafiya,kuma da alamu labour take sosai zata iya haihuwa cikin mintuna kalilan gasu can zaune a parlour sunki tafiya."
Dr yace "Yara kuma? akira su su shigo."
tace "Okay sir."
tajuya da sauri ta fita, jim kaɗan suka shigo,
tana gaba ƴammata biyu na biye da ita ɗaya da ciki rukuku ɗayar kuma tana tallafe da ita, sanye da uniform ajikin ta. da kaga mai cikin da alama nakuda take sosai dan sai tauna baki da yarfe hannu take tana ta faman zubda kwalla da faɗin "Wayyo nashiga uku."
Dr yadubi wacce suke tare da mai cikin yace
"Me yake faruwa wace matsalar ke tafe da ku?."
tace
"Haihuwa tazo shine na rako ta."
Na'ima da Raliya kuwa ido suka zubawa yaran wan da akalla shekarun su bazai wuce 16 ba.
Dr Mukhtar yace
"Ke kaɗai kika rakota haihuwar ina iyayen ku?".
shiru yarinyar tayi tana duban mai cikin da sai daɗa shiga yanayin nakuda gadan-gadan take.
sai kuma ta dubi likitan cikin rauni tace
"Iyayen ta suna gida nima kawai tazone tace narako ta asibiti."
ɗan shiru Dr mukhtar yayi idanunsa a kansu kana yace
"To ina mijin ki?." yayi maganar idanunsa akan mai cikin.
duk kanin su shiru sukayi sai raba ido suke, ido ya kure su da kyau yakuma faɗin "Nace ina mijin ta? ita kaɗai zata taho haihuwa babu wani babba ko shi mijin baisan haihuwar yataso bane kirashi a waya yanzu yazo dan bana karɓar haihuwa sai an ajiye kuɗi an kuma sa hannu tukun".


Cikin kame kame ƴarrakiyar tashiga faɗin
"Um..um mijin..ta..mijin ta."
sai kuma tayi shiru. duban mai labour ɗin yayi da kyau yace
"Kirawo mijin ki yanzu yazo kice masa bazamu karɓe kiba har sai yazo."
kasa tayi da kanta batare da tace komai ba sai hawayen da ke cigaba da sauka a idon ta,
girgiza kai yayi kana yace
"Ba miji kenan wannan ciki ba uba baya da uba ko?".
da sauri ƴar rakiyar ta gyaɗa kai tana tsilli-tsilli da ido kamar an tare ɓera kana cikin in-ina tace
"Wlhy likita tsautsayi aka samu bata da miji, kuma yanzu iyayen ta sun kore ta da sukaga tana labour sun ce tafita musu a gida taje can ta haihu ba a gidan suba,
shine tazo gidan mu nikuma naga kamar zata mutu shine na rakota asibiti, dan Allah likita ka taimaka mata."
gaba ɗaya suka zuba musu ido. wani murmushi Raliya ta sake.
ido Na'ima ta bita da shi dan tasan ma'nar murmushin nan nata tace
"Aminiya sabon shiga harka ko?". baki Raliya ta taɓe tare da faɗin
"Oh yaro man kaza har yaushe zakayi sake irin haka ta kasance, ka ɗaukar wa kanka wahala shi ba mai uba ba wahalarka a banza, uban titi da bazai kalleka cikin halin labour yace ma sannu ba, tuni ban wanke shi na zubar ba in ma yasami shiga kenan mttss".
taja wani dogon tsaki tare da faɗin
"Kara mar ƴar iska bata san yan da zatayi iskancin bama."
Dr Mukhtar da Na'ima kasan cewar suna kusa ne suna juyo duk abun da take fata akasin su da suke tsaye a sakiyar office ɗin.
Dr Mukhtar yayi murmushi tare da faɗin
"Ko zaki sata a hanya ne idan ta sauke kayan dake jikin ta".
harara ta dalla masa tare da kuma jan wani gajeren tsaki.
Dr Mukhtar ya mai da duban sa kan yaran sannan yace
"To a gaskiya bazamu karɓi haihuwar ba, na ɗaya babu kuɗin karɓar haihuwa sannan babu wani babba a tare da ku, bazamu karmi haihuwar ba saboda gudun matsala, bugu da kari kuma ɗan bashi da uba,
muzo mu karɓi haihuwa wani abu ya faru azo a dakatar min da asibiti gaskiya yanzu na daina irin wannan kasadar gaskiya kuje kawai kuje wani asibitin."

Da sauri Na'ima da Raliya suka juyo a tare tare da yiwa junan su
kallon-kallo, sai kuma da sauri Na'ima ta juyo gun Dr tace
"Dr a taima musu a karɓi haihuwar ni zan biya kuɗin duk

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login