Showing 42001 words to 45000 words out of 45625 words

Chapter 15 - HAMDAH part 3 Complete hausa novel

RASHEEDA   

04 Oct 2024

12675

ni da shi aka sanar min da tana asibitin na kuma kira wayar tayi ta ring ba'a ɗaga ba,
kuka ne naji ya zo min nayi saurin toshe baki na a raina nake faɗin
"Shike nan ta mutu."
kokarin mai da kiran nake dai-dai nan najiyo muryar Yakubu yana faɗin
"Hajiya mun iso."
da sauri na ɗago dan ban san har mun iso ba.
da sauri na buɗe motar na fito batare da na jira faɗin da yake bari ya zo ya buɗe min motar ba.
da sauri haɗe da sassarfa nayi cikin asibitin, a kofar shiga cikin parlour'n asibitin na haɗu da Aunty'n su Nasmah tana kokarin fitowa cikin sauri take tafiya da ka ganta gaba ɗaya hankalin ta a tashe yake.
tana gani na ta juya da sauri tana faɗin
"Madam ta farfaɗo amma tana ta kuka."
da sauri nabi bayan ta ina faɗin "Ina take."
tun da ga cikin parlour'n nake jiyo kukan ta, da gudu nanufi kofar room ɗin da nake jiyo kukan ta ciki,
wasu daga cikin ma'aikata asibitin sukayi yunkurin dakatar da ni, ban ko saurare su ba
na tura kofar na sa kai ciki.
ina ji Yakubu daya biyo ni yana sanar musu da ko ni waye.

Likitoci har guda uku a tsaye a kan ta suna rirrike da ita sai ihu take tana bige-bige, da gudu na isa in da take na kusa sakanin su na rungume ta,sai kawai nima na fashe da kuka ina faɗin
"Nasmah me ya same ki, me ya same ki Nasmah?!!."
kuka sosai na ke ina rungume da ita, itama kukan take tana ta fisge-fisgen nan kamar wacce bata cikin gayyacin ta.

Turo kofar aka yi da karfi yana gaba wani na biye da shi.
in da muke suka karaso da sauri, wan da ke biye da shi ɗin ya dubi likitocin da ke cikin ɗakin yana faɗin
"Wai har yanzu bakuyi wani abu a kai ba?."
cike da girmamawa sukace "Sir muna kai kenan yanzu ta farfaɗo so taki tsayuwa Muna kan kokari ke nan mu shawo kan matsalar, ruwa za'a saka mata sai dai taki tsayuwa sau uku ana samun jijiya sai ta gauce ya ɓata, zamu nima ta kafan ta ko kai ne a saka mata, na hannayen ta kam duka mun rasa su."
cikin faɗa Dr da suka shigo tare da Ahmad da alama shine babban su ya ce "Shirmen banza sai kace ba ai kin ku ba."
sai kuma ya dubi Ahmad ya ce
"Sorry Sir ko mai zai dai-dai ta insha Allah."
kai kawai Ahmad ya jinjina ya ɗan maso in da nake rungume da ita ya ce
"To meye amfanin kukan, kin rungume ta kina kuka ita tanayi, to da wanne zata ji da ciwon da ke damin ta ko da wannan kukan naki?."
hannu ya mika ya ɓamɓare ta a jikina, sake masa ita nayi dan na rasa abun yi guda ɗaya ganin yanayin nata yakuma jefani cikin kiɗi ma, da firgici da tashin hankali, ya ɗago ta ya saka ta a kafaɗar sa ya na faɗin
"Kun ɓula ta da yawa dubi yan da hannayen ta suka fara kumbura."
"Sorry Sir ta ki tsayuwa ne."
ɗaya daga cikin likitocin yafa ɗa. tsaki yaja kana ya ce
"Me yasa tun kan ta farfaɗo baku ni mi jijiyar ba, sai da ta farka zakuyi ta ɓula ta."
"Sorri Sir hakan bazai yiwu ba do le sai ta farfaɗo."
tsaki yakuma ya, yana jijjiga ta da bubbuga bayan ta, yana faɗin
"Shiiit ya isa sorry baby yi hakuri kin ji sorry sorry."
maganar yake daf kunnen ta yana ci gaba da jijjiga ta da bubbuga bayan ta.
baya nayi, najin gida na da jikin garu-bango, ina mai cigaba da kukan cikin yin kasa da sauti.
Dr da suka shigo da shi ya ya nufi kofa yana faɗin
"I'm coming Sir." sai yayi waje sauran likitocin suka bi bayan sa.
bai yi magana ba sai ci gaba da jijjiga ta da hura mata iskar bakin sa cikin kunne yake, a hankali kukan nata yarika raguwa, sai ajiyar zuciyar da take sauke wa a kai a kai, har tayi shiru tana mai cigaba da sauke ajiyar zuciya.
jim kaɗan likitan ya dawo wannan karon su biyu suka shigo, yana gaba ɗaya daga cikin waɗan da ɗazu suke kan ta na biye da shi rike da wasu kayakin amfani irin na ma'aikatan lafiya.
Dr ya dubi Ahmad da murmushi yana faɗin
"Ikon Allah abun da mu likitoci muka kasa yi gashi uba yayi wa ɗiyar sa, baby da ma so kike sai Daddy'n ki yazo kafin ki bamu damar yin ai kin mu ko."
yayi maganar yana leko fuskar Nasmah da ke lumshe da alama bacci ke son ɗaukar ta.
murmushi Ahmad yayi yana shafa kanta, kana ya ce
"Yan zu zaku iya yi mata abun da ya kamata."
Dr ya ce "Okay." ya mika hannu ya karɓe ta yana kokarin kwantar da ita kan gado.
ai ko ta buɗe ido tare da sakin kuka.
da sauri Ahmad ya ɗauke ta yashiga jijjiga yana faɗin
"Shiiit Nasmah ya isa yi shiru jinki." ai ko tayi tsitt,har kuma lokacin ida nunta suna lumshe.
zama yayi bakin gadon kana a hankali ya kwantar da ita yana ɗan jijjiga ta da faɗin
"Sorry kwanta a saka miki magani kiji sauki ko,babu zafi yanzu a gama miki mu tafi hawa doki."
alama yayi wa Dr da ya soma ai kin sa, yakuma ce masa yabita a hankali, kana shi kuma yarika shafa kanta yana yi mata magana a hankali daf da kunnen ta.
a hankali likitan ya soma gudanar da ai kin sa irin na kwararren likita.
bugun fari ya samo jijiya a hannun ta na dama,
batare da ɓata lokaci ba ya ɗaura mata ruwa mai ɗauke magunguna masu karfi da inganci.
nan da nan cikin sakanni kalilan bacci yayi gaba da ita.
bayan likitan yagama duk abun da ya
kamata ya dubi Ahmad yana faɗin
"Allah ya sawaka in sha Allah ko mai zaiyi normal idan ta farka."
ya an sa da amin kana likitocin suka fita.

Numfashi na sauke mai sauti san da ido na ya sauka kan Nasmah da ke bacci tana sauke numfashi a hankali, idanuna na rumtse tare da jan sheshsheka cikin kukan da nake har lokacin, sai dai zuwa yanzu kukan nawa a hankali yake fita.
cikin zuciya ta nake yiwa Ubangiji godiya ganin ta sami bacci.
har lokacin yana sunkuye a kanta yana shafa kanta yayin da ɗaya hannun sa ke rike da hannun ta da akayi mata karin ruwa.
maganar sa najiyo yasani buɗe idona a kan sa.
"Ke kin ishe mu da wannan koke-koken na ki, kifita waje kije kiyi sa a can kin dame mu, ko so kike ki tashe ta da Wannan kukan naki mara amfani,
tun tuni yarin ya tana tare da ciwo kin barta da shi a jikin ta har sai da yayi (C), ke baki da wayon sanin yaro bashi da lafiya ne,
a hakan ne kike cewa ke zaki iyar musu yaushe kikayi wayon kula da kanki bare ki kula da su."
baki na murguɗa cikin zubda ƙwalla na buɗi baki zanyi magana, sai wayata ta fara ring, dago wayar nayi ina mai share hawaye ganin Bappa ke kiran, sai nayi picking call ɗin na kara wayar a kunne,
daga cikin wayar Bappa ke faɗin
"HAMDAH wani asibiti ne?."
ina faɗa masa sunan asibitin ya kashe wayar.

Zama nayi kan kujerar da ke gefe na jin kafata ta gaji sosai,
ina mai ai ka masa da harara ina ci gaba da murguɗa masa baki.
magana ya soma yi yayin da idanun sa ke kan Nasmah da take ta baccin.
"Wayon ki a iya nan kaɗai ya tsaya,
sabo da ke baki da wayon magan ce naki shine ita ma zaki barta da shi ko, dubi idon ki ke kan ki ma baki da lafiya amma baki da wayon da zaki iya magan ce ciwon naki."
a fusace cike da tsiwa nace
"Idan kai ke raba wayon bana so karike shi, har abada kada nayi wayo."
nayi maganar ne cike da jin haushi, ban san meye damuwar sa na jifana da kalmar rashin wayo a koda yaushe a duk san da muka haɗu da shi ba.
yabi ya ishe ni da wasu maganganu ya barni naji da damuwar ciwon ƴata.
fuskar Nasmah ya shafa tare da sakin murmushi har sai da dimple ɗin fuskar sa ya bayyana.
baki na taɓe tare da kawar da kaina gefe, dan zuwa yanzu hankali na yafara kwanciya, bai kuma magana ba sai zaman sa daya gyara ya daɗa gyara rukon hannun Nasmah da ke hannunsa sakama kon ɗan zaburan da tayi cikin bacci.
ni ma ido na na mai da kan waya ina ɗan lallatsawa.

Tun daga can waje nake jiyo muryar su Bappa ina kokarin mike wa suka turo kofar, Bappa na gaba Inna Wuro Faty Yakubu da Sule direban su Bappa, suka shigo.
hankali tashe Bappa yake faɗin
"Subhanalillahi garin yaya me ya same ta haka?."
dai-dai nan suka karaso bakin gadon da Nasmah take kwance.
Bappa ya leko fuskar ta yana cigaba da faɗin
"Amma ta farfaɗo ko."
Ahmad ya ce "Eh ta farfaɗo yan zu dai bacci take."
"Masha Allah, kaji ikon Allah ko yarin ya tabar gida lafiya sai kuma ga ciwo, kai sannu Nasmah."
Inna Wuro ta faɗa tana shafa kanta. Bappa ya dubi Ahmad yana faɗin
"Sannu Ahmad sannu fa da kokari Allah ya saka da alheri."
murmushi yayi kana suka
shiga gaisawa, bayan gaisuwa da jajen abun da yafaru Bappa ke faɗin
"Wai haka kawai ta suma kuma me likita ya ce ke da mun ta?."
Ahmad da idanun sa ke kan Nasmah dake ta baccin ta har yanzu kana ya ce
"Typhoid ne har yayi mata (C) da mamaki ace wai ciwo irin haka har yayi yawa a jikin yaro irin haka ba'a sani ba, har yakai matakin da zai iya sumar da ita wai duk ba'a sani ba."
Bappa ya ce "Ikon Allah amma kuwa abun da mamaki, wai da ma bata da lafiya ne HAMDAH? ko irin zazzaɓi a tsatstsayen nan ne take?."
ya karasa maganar yana duba na. da sauri ganin yan da wannan Ahmad ɗin yake taso ya mai da alhakin ciwon ta kaina.
na ce "Lafiyar ta lau bata kuma zazzaɓi a tsatstsaye."
"Kuma bata taɓa ce miki wani gurin ta na ciwo ba, yaro ke nan Allah sarki kuma kema baki taɓa lura da yanayin ta ya sauya ba."
cewar Inna Wuro, tayi maganar cikin jimami da alhinin ciwon nata.
"Babu wani alamar da na taɓa gani na ciwo tattare da ita, kuma bata taɓa cemin wani gurin ta na ciwo ba, in ban da shekaran jiya da nake
kwance kai na na ciwo ita ma tazo ta ce min kanta na mata zafi, kuma nasan a lokacin ɗin dan nima na ce kai na nayi min ciwo ne shi yasa ita ma ta faɗa."
nakarasa maganar ina ɗaga hanci sama dan ganin yan da ɗan shishshigin nan keta wani girgiza kai. da sauri na mai da idanuna kan sa jin yana faɗin
"Ashe dai ta ma faɗa miki bata da lafiya amma bakiyi serious a kai ba, dan ta faɗi kan ta na zafi lokacin da naki yake ciwo sai ya zama nata karya ne?,
taya za'ayi ki fahimci hakan tun da baki da wayon sanin haka."
ido na waro baki buɗe jin yakuma jifata da kalmar rashin wayo,wai shin wannan mutumin me yake jin kansa ne,shi ji yake yafi kowa wayo kowa yi masa kallon rashin wayo yake?.
a kufule na buɗi baki zanyi magana, Bappa ya katse ni da faɗin
"Ai shi yaro idan ba lura kayi da yananin saba wani ɗan bashi da azancin faɗar abun da ke damin sa, ko da yana jin wani gurin sa na ciwo, sai dai in kai ka gane hakan daga yanayin sa na yau da kullum, kirika lura da yanayin su tanan zaki rika fahimtar ciwon su,
Allah sarki da gaske kan nata nayi mata ciwon ne sai tace yana yi mata zafi, Allah yabaki lafiya Nasmah."
Amin duk aka amsa da shi, baki na tura gaba muna gaɗa ido dashi na murguɗa masa baki, wani murmushi ya sake sai da dimple ɗin sa suka bayyana,ya mai da idanunsa kan Nasmah yayin da fuskarsa ke nan ɗauke da murmushin nan.
ido na ɗan kurawa fuskar sa wan da dimple ya daɗa kawata shi. baki na taɓe ina mai ɗauke idanuna a kansa...

Muna nan cikin ɗakin kiran sallar azahar ne yasa su Bappa fita dan zuwa masallaci, har da shi, yarage daga ni sai Inna Wuro da Faty.
Inna Wuro ta shiga toilet ɗin cikin ɗakin ta yi al'wala tafito tace da ni naje nima nayi muje masallacin cikin asibitin muyi sallah, tun da ga Faty in muka dawo sai itama taje tayi... muna isa masallacin ana idar da sallah, su mazan suka koma ciki mukuma muka shige cikin masallacin.
ko da muka idar muka koma ciki, abakin gadon na kusa da Nasmah in da ɗazu yake nan yanzu ma yake zaune.
zaman mu baifi da minti 20 ba akayi knocking ɗin kofa, Yakubu dake tsaye ta kusa da kofar yabuɗe.
wasu maza guda biyu suka shigo niki-niki da kayan abinci duk kanin su sanye da rigonan irin na ma'aikatar hotel.
cikin girmamawa suka shiga gaida Ahmad kana suka gaida ƴan cikin ɗakin, suka dire manyan basket ɗin dasuka shigo dashi, nan suka shiga zuba abinci suna mikawa kowa, da mamaki nake kallon su dan nidai a sani na ban bada umurnin kawo abinci daga wani hotel ba.
maganar ɗaya daga cikin mutanen naji ya na faɗin
"Gashi hajiya." ɗago idanuna nayi daga kan wayar da nake natsawa na dube shi, plt ɗin abinci yake miko min, kai na girgiza tare da faɗin
"Nakoshi."
"A'a me kikaci HAMDAH nasan tun fitar ki ba abin da kika ci."
cewar Bappa yana duba na.
"Bana jin yunwa." nafaɗa ina mai da idanuna kan wayar. "Zama da yunwa bashi da amfani wan da gashi komai yazo da sauki kici abinci itama bakiga tana baccin ta ba, sauki ce ke samuwa cikin bacci insha Allah."
Inna Wuro ta ce "Insha Allahu kuwa lafiya nata kan samuwa."
ni dai ban kuma cewa komai ba,
plt ɗin abincin suka mikawa Faty dake kusa da ni.
wani ɗan ma dai-dai cin basket daga cikin waɗan da suka shigo da su, abincin cikin sa na musamman shi suka zuba masa suka mika masa hannu ya daga tare da faɗin
"Akarawa kowa yaci."
Bappa da yakai loman abinci yahaɗi ye ya ce "A'a Ahmad ai wannan ma ya ishe mu maza karɓi ka ci wannan ya ishe mu haka ga abibci nan idan bamu koshi ba duk zamu kara, Allah ya saka da alkhairi an gode sosai Allah yakara buɗi."

Jin yan da Bappa yake ta zuba masa godiya yasa nasan cewa shi yayi odar abincin, baki na taɓe a raina nake faɗin
"Sai kace ance masa bamu ci abinci bane ko yunwa ke damin mu."
wayar sa ce tayi kara yamike yafita batare da ya karɓi abincin ba,
Bayan sa nabi da kallo
"Gulma shi da yasa a kawo dan tsabar gulma shi ne yaki ci to da waya mai da mayunwata."
Faty dake daf da ni ta juyo tare da faɗin
"Adda HAMDAH me kika ce?."
"A'a bada ke nake ba da wancan ɗan gulmar nake."
"Wafa?." ta faɗa tana kallon waɗan da suke cikin ɗakin.
"Ba kowa." na faɗa ina mai da idanuna kan waya.
tun da ya fita bai dawo ba ganin ya jima sosai bai dawon ba yasa nayi tunanin ya tafi ne, gara ma ya tafin ɗan shishshigi.
har wajen la'asar muna nan zaune Nasmah bata farka ba zuwa lokacin kam bakin gadon na dawo na zauna. akai-akai likitoci ke zuwa duba ta, tun bayan fitar sa.
ana kiran sallar la'asar su Bappa suka fita bayi Inna Wuro ta shiga ta ɗauro al'wala tafito ta shinfiɗa sallayar da nasa Yakubu ya ɗauko a mota, ina nan zaune kusa da Nasmah da har lokacin take ta kan bacci, ido na tsura mata gaba ɗaya yanzu na kagu ta farka. na ɗau alwashin duk likitan da yakuma zuwa zai saka wani allura cikin drip ɗin dake shigan ta zan hana, dan na lura kamar shi ke da ɗa sata cigaba da baccin. ban tashi ba har sai da Faty ta idar da nata sallar, kana nashiga toilet ɗin room ɗin bayan nayi al'wala nazo na gabatar da salla.
ko da na idar ina nan zaune kan sallayar ina lazumi,da sauri na ɗago kaina jin Inna Wuro tana faɗin
"Nasmah kin farka ne?."
da sauri na mike ganin tana ɗan motsa hannun ta, da sauri Inna Wuro dake gefen ta ta roko hannun nata da aka mata karin ruwa da shi take ta kokarin ɗaga shi,
cikin hanzarin na iso bakin gadon ina faɗin
"Nasmah Nasmah tashi kada ki sake komawa baccin nan."
a hankali ta buɗe idanun ta na bin cikin ɗakin da kallo.
sannu Inna Wuro da Faty suka shiga jera mata.
ɗaya hannun ta na roko da murmushi ganin idanun ta wasai naci gaba da faɗin
"Sannu Nasmah kan naki ya dai na yi miki zafin?."
fuska ta kwaɓe sai kuma ta fashe da kuka.
"Subhanallahi yi hakuri kinji Nasmah yi shiru kinji idan kikayi kuka kan zai ci gaba da yi miki zafin fa yi shiru abin ki."
Inna Wuro ta faɗa da alamun rarrashi.
kai na gyaɗa tare da faɗin
"Eh kin ji yi shiru abin ki Nasmah." sautin kukan nata takuma karawa tana ta kokarin fizge kannulan da ke hannun.
da sauri ya turo kofar ya shigo , cikin hanzari ya iso bakin gadon. ta gefen da nake ya tsaya tare da ruko hannun ta da hannuna ke kai, da sauri na ɗauke hannuna dan yan da ya sauke hannu nasa kan nata sai da ya taɓa nawa hannun.
ɗan matsawa nayi ganin yan da mukayi daf da juna.
"Shiiit ya isa haka bar kukan nan."
ya faɗa yana shafa kanta kana ya ɗago wayar sa ya daddanna ya kai kunnen sa "Na shigo." yayi maganar yana sauke wayar.
kan ta yaci gaba da shafawa yana kuma cigaba da faɗin
"Yi shiru bari azo a cire miki wannan abun ki huta."

Cikin mintinan da basufi 3 zuwa 5 ba Dr ya shigo ya cire mata ruwan dan dama saura kaɗan ne ya rage, a na cire mata Ahmad ya ɗago ta ya saka ta kafaɗar sa yashiga jijjiga ta har tayi shiru.
bakin gadon ya zauna kana ya ɗaura ta kan cinyar sa, ya dubi Faty ya ce
"Fatimah haɗa mata tea ta sha." yayi maganar yana kallon basket ɗin da ma'aikatan hotel ɗin nan suka zo da shi suka tafi suka barshi a nan cikin room ɗin.
Faty ta ce tom. ta haɗo tea ɗin da sauri ta mika masa, ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login