Showing 30001 words to 33000 words out of 45625 words

Chapter 11 - HAMDAH part 3 Complete hausa novel

RASHEEDA   

04 Oct 2024

12668

faɗin "Yanzu kam an bar kuka idan za'a tafi."
"Dama ai rashin sabo ne yanzu kam an saba."
cewar Inna wuro. Bappa yace "Hakane kam wai me yasa ne aka sauya musu makarantar ko yayi musu nisa ne? ko da yake *HAM'NAS* International School yafi shi nisa, me ya sane?."
"Babu tsaro yan da yakama ta a makarantar shi yasa."
nafaɗa a takaice.
Inna wuro tace "Hakkum gaskiya sabo da Allah kam ya kamata su kara sa ido kan ɗaliban su, susan duk wani wan da zai kawo ɗalibai yakuma zo ɗaukar su, duk da dai ranar Malam yace min mutumin kirkin nan ne Ahmad Tijjani Sabil yaje ya ɗauko su ake tunanin ko masu garkuwa da mutane ne, amma dai ya dace sosai su sa ido kan ɗaliban su."
kai kawai na jinjina batare da nace komai ba,akasan raina kuwa faɗi nake
"To waya sani ma ko mai satar mutanen ne dole zan sa jami'an tsaro cikin gidan nan tun da har ya fara shiga cikin gidan nan yana leken asiri."
maganar Bappa dana ji shi ya kashe min zancen zucin danake
"HAMDAH har yanzu banji kin ce komai ba kan maganar mu ta rannan,
Yakamata yanzu kam kiyi aure ki fidda miji na gari kiyi aure, domin darajar ki yadaɗa ninkuwa, kwanakin can munyi maganar nan bakice komai ba,
daraja da kimar hace baya ɓata cika cif har sai tana tare da abokin rayuwa wato mijin aure."
tea ɗin da na kurɓa ne nahaɗiye shi da kyar, sam bana son jin wannan kalmar gaba ɗaya naji nakoshi da abincin a hankali na mai da cup ɗin na aje kana a hankali nasoma magana.
Bappa aure kuma, ai ni bazan yi aure ba rayuwa ta a haka tafi min."
yace "A kul ɗin ki kada na sake jin wannan maganar, a wannan shekarun naki zaki ce baza kiyi aure ba, nutsuwa bata taɓa cika sai da abokin rayuwa, kiyi na zari sosai ga abokan kasuwancin ki da suke zuwa gidan nan, ko wannan Alhj Muttari nan ai mutumin kirki ne ko ranar yaso yimin zan cen sai dai bai fito muraran yayi maganar ba,
in yaso sai ku dai-dai ta kiyi auren ki kamalar ki ta daɗa cika."
Inna Wuro tace
"In ban da HAMDAH ma ai mutane basu taru sun zama ɗaya ba, dan wani abu yafaru da rayuwar auren ki na fari bashi zai sa nan gaba yakuma faruwa ba,ai Allah baya taɓa jarabtar bawan sa da abun da bazai iya ba, duk kuma musulmi an sanshi da karɓar kaddara me kyau ko mara kyau,
ki gode masa ta hanyar kuma kara yin wa ni auren."
"Hmm." kawai nace dan bana jin kamar abun da suke faɗan zai kasan ce, har can kasan kololuwar raina bana jin zan kuma aure, babu abun da natsana a yanzu kamar aure.
meye acikin auren ban da tashin hankali da musifa, in dai har aure nutsuwa ce kamar yan da suka faɗa to gara na tabbata ni bani da wannan nutsuwar.

Duk wani nasiha da jan hankalin da su Bappa suke jin su kawai nake,dan a yanzu babu abun da nafi tsana ma kamar aure!.
sai da na bari suka gama yi min nasihar kafin na mike nace dasu zanje na ɗan kwanta kafin su Naseem su dawo, abin cin da ban karasa ci ba kenan nafito.
ina fita daga side ɗin wata mota na shigo wa cikin gidan, a hankali na ke tafiya har na iso in da motar tayi parking kasan cewar dole sai nabi ta hanyar kafin na wuce side ɗina,
ina isa dai-dai in da motar take sai ji nayi an.......!








Mommyn Twins ce





9




An buɗe murfin motar, baya na ɗan yi da sauri dan kaɗan ya rage marfin ya bige ni, kasan cewar nazo daf da motar sosai. da sauri na ɗago dan ganin wan da ke cikin motar, ido na waro da ɗinbin mamaki ganin mutumin da su Nasmah suke cewa Daddy ne, tsayuwa ta na gyara ganin yazuro kafar sa waje yafito daga cikin motar,baki na buɗe cikin masifa ganin yan da yayi kusan bige ni da murfin motar sa, "Malam ya haka baka ganine?."
nayi maganar ina yi masa kallon sama da kasa.
tsayuwar sa ya dai-dai tare da mai da murfin motar ya rufe, kana yashiga nuna min yatsa tare da kaɗa yatsar yasoma magana.
"A kan wani dalili zaki rika birkita wa yara ƙwaƙwalwar su, kinyi yunkurin sauya musu School abaya, ba'a baki dama ba shine kika ajiye su a gida tsawon sati guda, sannan kika sauya musu Makarantar, ilimi kike so su samu ko kuwa birkita musu ƙwaƙwalwa kike son yi, kada ki kuma yunkuri da tunanin sauya musu makaranta kan wani dalilin ki mara amfani, idan kuma ba haka ba."
sai yayi kwafa tare da kaɗa yatsar sa.
kamar daga sama nake jin maganar nasa mamakin sa da furucin sa suka sani gyara tsayuwa ta ina yi masa kallon kacika mai karfin hali.
"Dakata malam."
nafaɗa ina ɗaga masa hannu, kana nacigaba da faɗin.
"A kan dalilan su ƴaƴana ina da ikon yin komai da su, dalilina mai amfani, kada ka kuma cewa dalilina bashi da amfani tun da baka sanshi ba,
ƴaƴa nawa ne nike da ikon yin komai kansu, malam kafita daga rayuwar ƴaƴana kana ta yau darar su da danganta su da kai, da suna mai kama da uba, ƴaƴana basu da uba kuma basa bukatar uba domin bazai yi musu amfanin komai ba, rayuwar su a haka tafiye musu rayuwa da uba sau dubu dan bashi da wani amfani a gare su."
sassauta maganar da nake nayi tare da haɗe hannaye na biyu kana nacigaba da faɗin
"Dan Allah kafita daga rayuwar ƴaƴana kada ka yaudare su da wannan kalma ta uba, dan basu da uba kuma basa bukatar uban, kuma ba shegu bane ƴaƴane tsaftatattu mafiya daraja."

Afusace yashiga matso ni, ganin yan da yanayin sa ya sauya gaba ɗaya, sai na shiga ja da baya, shiko maso ni ya cigaba da yi tare da nuna ni da yatsa, yana huci kana yasoma magana cikin ɗaga murya
"Idan kika sake cewa basu da uba sai ranki yayi mummunar ɓaci, idan kika kuma sako kallamr yaudara sakani na dasu!..."
sai yayi kwafa tare da kaɗa yatsar sa alamun gargaɗi,
mamakin ganin karfin halinsa muraran nake, wai ni da ƴaƴana ake nuna min iyakata a kansu,
bil hakki da gaskiya yake maganar dan kuwa fuskarsa ta nuna, niko
baya na kuma ja ganin yan da ya matso ni sosai yana maganar kamar zai kai min hannu,
wani irin kallon shekeke nabisa da shi sannan na ce
"Idan ba yaudara bace mene ne, kana cusawa yara abun da babu shi, cikin rayuwar su,
ina sanar maka da hakan ne sabo da matsaltawan ka kansu, na dai faɗa maka kafita daga tsafgar ƴaƴana idan kuma ba haka ba zan sa ayi maka gargaɗin da zaka fi fahimta."
ina kai wa nan najuya.

Shan gaba na yayi a fusace cikin muryar da yake nuni da tsantsar gargaɗi ya ce
"Yazamo na karshe fitar kalmar nan daga bakin ki, idan kika sake kika sake furta kalmar durkuso cikin rayuwar su, bazan sa ayi miki hukunci ba ni zan yi miki hukunci da kai na! ki sake nanata kalmar basu da uba kigani!."
yayi maganar cikin
fusataccen amon sauti, a zaburi namatsa gefe dan maganar nashi ta shige ni rabon da ayi min ihu da tsawa irin haka har na mance, shiyasa abun yazo min a sabo.
ba zato naji kafata ta ta dama ta wuce cikin abu kamar rami, da sauri na juyo sai kawai na tafi luuu gaba ɗaya, idanuna na rumse da karfi ina jiran najini a kasa, sai jina nayi zundum cikin ruwa,
kara na ƙwalla wan na hakan yayi sana diyyar wucewan ruwa cikin bakina,
fafutukan niman numfashi nashiga yi, da niman ceton kaina, duk buɗe bakin da zanyi sai ruwa ya wuce ciki, nayi-nayi na iya mike wa tsaye na kasa, duk da kuwa zurfin ruwan idan zan shiga da kafata iya kirji na yake zuwa min.
Shiko Ahmad da sauri ya faɗa cikin swimming pool ɗin ganin yan da ta ke bubbuga hannu da yin sama da shi
da alamun niman ceto.
hannu na ya ruko da karfi ya ɗago ni yamikar da ni tsaye.
ruwan da ke kunshe cikin bakina dana ki haɗiye shi dan cikar da ciki na yayi, na furzar da shi tare da sauke tagwayen numfashi, ina damke cikina da ruwa yacika shi, a wahalce na na ɗago hannuna ɗaya na share fuskata tare da tattaro gashi na daya rufe min fuska, na mai da shi baya,
ida nuna na sauke kansa, dai-dai lokacin daya kai
hannu ya share ruwan dake fuskar sa, sai a lokacin na lura ruwan dana furzar daga baki na a fuskar sa na fesa.
shima idanun sa a kai na tun daga gashin kaina yake bina da kallo har kasa, kasan cewar rana ya taso ya haske cikin ruwan ana iya kallon abun da ke kasan ruwan.
dogon tsaki na ja dan nakasa magana tsabar haushi, bugu da kari yan da cikina ya cike tam da ruwa.
a hankali na soma tafiya cikin ruwan har na isa bakin gaɓar gun matattakalar shiga da kuma fita daga cikin swimming pool ɗin,
a sannu na soma hawa maganar sa na jiyo,
"Ki tsaya a taimaka miki kirage ruwan da kika sha."
cigaba da haurawa ta nayi batare da
waige ko tsayu ba,
ina karasa fita da sauri nayi hanyar part ɗina jin zuciya ta na tashi, cikin sauri na shige cikin side ɗin direct sama na haura,
ina shiga bedroom ɗina da sauri nashige bathroom, ai tun kan na karasa bakin toilet nafara sheka amai tsakiyar bayin, zallar ruwa narika aman sa.
da kan sa aman ya tsaya kamar yadda yazo bazato ba sammani, numfashi narika sauke wa ina tallafe da cikina da yanzu nake jin sa wayam, sai dai ɗan murɗar da yake min.
a daddafe na tsaftace bayin na tuɓe kayan jikina da suka jike gaba ɗaya na wurgasu cikin wishing machine, nafito doguwar riga mara nauyi na zura, kana na isa bakin gado na zauna ina mai cigaba da sauke numfashi,
tsaki narika ja a-kai-a-kai tsabar haushin da nake jin kaina ciki, har lokacin kasa iya furta komai nayi.
idan na tuna ruwan da na hambuɗa a cikina sai naji kamar nayi ihu, sauki na ma ɗaya jiya-jiyan nan nasa aka fidda ruwan dake cikin swimming pool ɗin, aka wanke cikin sa a ka kuma zuba wani, ban kuma yi amfani da shi ba.
wani dogon tsakin naja yayin da na kai bayana na kwanta kan gado.
mamakin karfin hali da takaicin mutumin nan suka rika zuwar min,
wai ni yake yiwa gargaɗi kan ƴaƴana,
ya kuma yi sanadiyyar faɗuwa ta cikin ruwa, badun kwanana na gaba ba wata kila da yanzu ana kan shirin kai ni makwanci.
Dole nasa jami'an tsaro cikin lamarin dan ban amin ta da mutumin nan ba, awani dalili zai rika shiga min cikin gida kai tsaye har yarika yimin barazana kan ƴaƴana.

Mikewa zaune nayi tare da ɗaukar waya ta, number Mr Aliyu nakira wato P.A na, ko da ya ɗaga bayan mun gaisa na ɗaura da faɗin
"Mr Aliyu ina so a saka min jami'an tsaro a gidan nan."
da sauri ya ce "Madam meke faruwa akwai matsala ne?."
yayi maganar cikin nuna damuwa sosai kana yaci gaba da faɗin
"Ai Madam tun farko shiyasa nace azuba jami'an tsaro gida kamar wannan dole sai da manyan Security masu rike da bindiga, kikace abar mai gadi kaɗai ma ya isa, ina kuwa zai isar wa gida kamar wannan, yanzu kuwa zan fita in sha Allahu anjima zamu zo da su."
na ce "To Allah ya kaimu."
nakashe wayar, ina katse kiran kiran Bappa na shigowa, na daga da sallama daga cikin wayar Bappa ya ce
"HAMDAH ko kina bacci ne?." na ce
"A'a ba bacci nake ba Bappa." ya ce
"To kizo yanzu maza." da sauri na mike jin yana faɗin haka ya kashe wayar.
cikin hanzari na nufi side ɗin su Bappa da sauri na dan Bappa bai taɓa min irin wannan kiran ba nasan komai akayi akwai wata masalar, da ire-iren waɗan nan tunanin nashige cikin side ɗin.
turus naja na tsaya yayin da jikina ya kama ɓari ganin Yakubu durkushe yana kuma rungume da uniform ɗin su Nasmah,
cikin tsanani tashin hankali na karaso cikin parlour'n gaban Yakubu natsaya cikin rawar murya da kuka keson kwace min na ce
"Ina yara na?!."
nayi maganar cikin rawar murya sosai tuni hawaye yacike ido na.
Bappa da ke zaune kan kujera ya dube ni tare da faɗin
"Zo zauna nan HAMDAH." yanu na min kujerar da ke kusa da shi, ban iya bin umurnin Bappa ba dan kuwa hankali na yakai kololuwa wajen tashi, duba da yan da Yakubu yake ɓari yakuma rungume uniform ɗin gam-gam.
Inna Wuro ce ta mike tazo taruko faɗata ta jamyo ni ta zaunar da ni kan kujerar, tuni hawayen da suka cuko idona suka fara zuba. Bappa ya girgiza kai yana faɗin
"Muma mun shiga irin yanayin nan da kika shiga a yan da yashigo mana kamar an rakoshi a guje,
tam bayar da na fara mishi shine ina yaran suke ganin uniform ɗin su a hannun shi, da kyar ya iya ba mu amsar suna nan kuma suna makaranta, yaji tsoron ya tinkare ki kai tsaye shiyasa yazo nan."
kai Yakubu yashiga gyaɗa wa yana ɗan rarrafowa da guiwar sa yana kuma faɗin
"Dan Allah dan Annabi Bappa Malam ka rokar min afuwar ta wlh duk yan da naso na hana faruwan haka bai yuwu ba, wlh fin karfi aka nuna min muraran."
Bappa ya katse shi ta hanyar ɗaga masa hannu ya ce
"Ya isa." kana Bappa ya juyo da kallon sa gare ni ya ce
"Lokacin da suka fita zai kai su makaranta a hanya suka haɗu da Ahmad Tijjani Sabil ya sai da su, yake tambayar su ina zasuje ganin ba hanyar makarantar su suka nufa ba, sannan kuma ga wata uniform ɗin daban a jikin su, to shine shi Yakubun ya shai da masa in da zasu, shikuma Ahmad yace kada ya kuskura ya kaisu wannan makarantar yawuce ya kaisu wan can makarantar su, to dai a takaice tare suka tafi da shi wancan makarantar da aka cire su yasa aka basu wani uniform, yakuma tuɓe musu najikin su shine yabashi wan da yacire musun yace ya mai do shi gida,
to shine ya dawo hankali tashe yakuma ji tsoron yaje ya tinkare ki da batun shine ya zo nan,
kafin na kira ki sai da na kira shi Ahmad ɗin sabo da ina da lambar sa dan ranar da yazo nan na karɓi lambar sa, ashe dai zatayi amfani gaba akuma irin wannan ranar,shine na kira sa dan ji dalilin sa na yin hakan,
ya bani tabbacin dalilin sa na yin haka, kuma na gamsu, yace yawai ta canza musu makaranta a karancin shekarun zai iya birkita musu ƙwaƙwalwa gara abar su idan suka gama can ɗin kan lokacin sun daɗa wayo sai suyi gaba, kuma nima nayi nazari naga hakan yafi abarsu a can ɗin, nayi masa maganar dalilin ki na canza musu makarantar yace za'a kara tsaro sosai babu wata matsala."


Yakubu da tun da Bappa ya soma maganar yake ai kin gyaɗa kai da buga bayan hannun sa cikin ɗaya tafin hannun sa, yayi kalar tausayi, Bappa na gama maganar shima ya ɗaura da faɗin "Wlh tallahi Hajiya na rantse miki da Allah, ba laifi na bane, na dage wajan ganin ba'a kuma samin wata matsala ba kamar yadda nayi miki alkawari, wlh Hajiya dana buɗe baki zanyi masa musu dawani yafito daga cikin motar sa, ya shake ni sai da naji kamshin kabari, shi ya hana mutumin da yanzu na sheka,
ki gafar ceni Hajiya ki tai maka kibar ni a bakin aiki na."

Numfashi na sauke jin akasin abun da nake tunani yafaru a kansu, dan Ni nagama tunanin hatsari sukayi sun mutu shine yakawo kayan su gida.
duban Bappa nayi ina shere hawayen fuska ta nace
"Yan zu Bappa ka amin ce da abun da yafaɗa kenan?, to shi ina ruwan shi da su me ya shafe shi da lamarin su da har zai rika shiga, har fa Daddy yake cewa surika ce mishi meye gamin sa da su."
murmushi Bappa yayi irin tasu na manya kana ya ce
"To in ban da abin ki HAMDAH ai wan da ya nuna yana son naka yagama yi maka komai a rayuwa, kuma da kike cewa yana shiga lamarin su basu kaɗai ba lamarin koma waye yana shiga, idan baki mance ba na taɓa baki labarin sa nazu wa rugar mu da yayi, muma ba lamarin mu yashiga ba yakuma jiɓanci lamuran mu, yayi silar magance mana wutar fitinar da take ta kunno mana,
ko jiyan nan da daddare munkalli labarai gidan TV wasu iyaye sun fito suna mika masa godiya kan gudumawar da ya bada kan ƴaƴan su, su iyayen ma basu ma sani ba ƴaƴan ne suka dawo gida suke faɗa musu alkhairin da yayi musu,
a makarantar gwamnati suke karatu ya cire su ya mai dasu na kuɗi,
sannan kin ce meye gamin sa da su,
ke da kike taimakon bayin Allah meye gamin ki da su?,
ai shi tai mako basai wan da kasani kake taimaka masa ba, duk wan da Allah ya sa da rabon sa yafaɗo ta kansa sai ka taimaka masa ladan ka na gurin Allah,
shiya sa Allah ya halittomu kala biyu mai kuɗi da kuma talaka hakan kuma jarabta ce, idan kai me kuɗi ne kayi kokarin cin jarabawar da yayi maka, wato kajikan na kasa da kai, ka kuma tsare dokokin Allah, to da yardar Allah babu shakka zaka shiga aljanna ta sanadiyyar jaraftar ka da yayi da arziki,
idan kuma kai talaka ne, karike talaucin ka kabi dokoki Allah, kai ma zaka wuce aljanna da yar dar sa.
shi tai mako ba sai wan da kasani kake yi masa ba.
kiran sa da sunan uba kuma da suke yi, ai duk ɗa nagari shike daraja nagaba da shi yakira sa Yaya wan da ya haifesa kuma yakira sa da sunan uba, wan da yayi jika da shi yakirasa da Kaka, abun alfahari ne ɗanka yazamo daga cikin irin waɗan nan ƴaƴan, ba ai bu bane dan sun kirasa da suna Daddy tun da yakai ya haife su, zaki so ace ƴaƴan ki suna da rashin kunya ko basu da tarbiyya?."

Shiru nayi batare da nace komai ba.
murmushi Inna Wuro tayi,dan ta fahimci

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login