Showing 39001 words to 42000 words out of 45625 words
Rafee'at ta dube shi tana faɗin
"Autar Ummi me kake yi ne cikin ɗakin ka ɓata shiru kamar baka nan?."
"La wayar ki Aunty Rafee'at ya ɗauka yaje ya ɓoye yake yin Game da shi." Nusaiba ta faɗa tana rike haɓa da yin sama da wuya tana leka abun da yake ɓoyewa bayan shi.
harara ya dalla mata tare da faɗin
"To haɗel ina ga wayar Aunty Rafee'at ɗin can kan hannun kuje ra."
huf Nusaiba ta mike dan son ganin abun da yake ɓoye wan, ta bayan sa tazo ta fizge abun da ke hannun san
tana faɗin
"Ai sai naga abun da kake ɓoye wan in ma abu na ne sai ka bani."
rikewa yayi da karfi bata sami damar kwace wa ba ya ce
"Dalla masa can idan kika yaga fa."
"La Fauzan mu gani a ina ka samu."
Nusaiba ta faɗa tana mika hannu ya bata abun da ke hannun sa,
kusa da Aunty Rafee'at ya zauna in da dama nan yake zaune ɗazu kafin ya tashi ya shige wani ɗakin dake gefe a nan cikin parlour'n.
gaba ki ɗayan su suka maida kallon su gare shi kana kamar haɗin baki Ummi Aunty Rafee'at Aunty Jaleela Suka ce
"A ina ka sami hotunan nan?."
da sauri Aunty Rafee'at ta karɓi wasu daga cikin hotunan in da Aunty Jaleela ita ma ta karɓi sauran,
nan take annurin fuskokin su ya ɗauke, damuwa hade da ɗin bin kewar wacce ke cikin hoton yadirar musu lokaci guda.
a ɓangaren Ummi kuwa kasa iya furta komai tayi gaba ɗaya jikin ta yayi sanyi, ɗan kuzarin da ke tattare da ita ya kauce.
Fauzan ya ce
"A ɗakin da aka zuba kayan Aunty HAMDAH na samu cikin akwatin ta."
"Allah sarki HAMDAH dube ta kamar a kirata ta amsa."
cewar Aunty Rafee'at tana nuno wa Aunty Jaleela ɗaya daga cikin hoton HAMDAH da suke hannun ta.
karɓar hoton tayi tana duba yayin da idanun ta suka kawo ƙwalla.
wani hoton ta Aunty Rafee'at ta zubawa ido nan take sai ga hawaye shar a idon ta, murmushi tayi yayin da ƙwalla ke cigaba da zuba a idon ta, kana ta ɗago hoton ta na faɗin
"Kaga ƴar gidan Inna an sha gayu, Jaleela kin tuna hoton nan?."
Amsar hoton tayi ta ce "Wannan hoton kamar shine wan da ranar da mukaje Dass muka samu taje takar ɓo shi nan ko?."
dariya
Aunty Rafee'at tayi yayin da ƙwalla ke cigaba da zuba a idon ta tace "Ƙwarai shi ne taci ƙwalliyar ta Inna'r ta ta bata kuɗi taje ta ɗauki hoto, ta kawo kikayi ta kushe wa har Inna ta ce mu tattara mu koma in da muka fito, tun da tsiya zamu kawo mata gida, kin san Inna da HAMDAH, Allah sarki Inna Allah yayi miki rahama."
Aunty Jaleela tayi murmushi tare da share wasu zafafan hayen da suka zubo mata ta ce
"Ai ita ta fara taɓo ni wai naga hancin ta ashe dama haka yake ko Ya SALEEM ɗin da ake cewa hancin su iri ɗaya nata yafi nashi ƙyau,
in duba na gani ta fini ƙyau."
"Ke dai baki da hakuri HAMDAH kuma zolaya."
cewar Aunty Rafee'at tana murmushi.
ta ce "Allah babu waninnan Aunty Rafee'at kin san kakar ta ai bata ganin laifin ta yarin yar nan ta raina ni kamar ni wata sa'ar ta bacin na bata shekaru da yawa, ko Ummi?."
ta karasa maganar tana duban Ummi dake zaune shiru.
Ummi ko kai ta jinjina tare da mai da hawayen da suka ciko idon ta kana ta ce
"Ganin ta ma har tayi miki rashin kunyar ai abun daɗi ne."
kaf parlour'n yayi tsit yayin da zuciyoyin su ke kuna tunani da kewar HAMDAH yadawo musu sabo fil a zukatan su
hannu Ummi ta kai ta share wasu zafafan hawaye tana faɗin
"Ko wani hali take ciki ko a muce ko a raye Allah kaɗai ya barwa kan sa sani."
Sallama Abba da yanzu shigowar sa yayi, duk babu wan da ya amsa masa, har ya karaso cikin parlour'n ya zauna babu wan da ya lura da shigo war sa,
ya fahimci duk kanin su hankalin su baya tare da su,
yana zama kuwa dai-dai lokacin Ummi take faɗin, kalmar ta na karshe.
shiru yaɗan yi yayin da yanayin sa yasau ya.
gyaran murya Abba yayi, sai a lokacin duk kanin su suka juyo in da yake, nan suka shiga yi masa sannu da dawowa,kana ya mike jiki ba ƙwari yayi cikin bedroom ɗin sa...
A can cikin unguwar
G.R.A kuwa
Na'ima na hango da kawar ta Raliya zaune cikin bedroom ɗin Na'aima, daya daga cikin ma'aikatan gidan ne tayi sallama bakin kofar ɗakin,suka ce ta shigo.
ta shigo rike da yaro a hannun ta wan da akalla zai iya kai wa wata 11 zuwa shekara ɗaya,
baki Raliya ta washe tana faɗin
"Kawo min shi nan kaga magajin gida ɗa ga Abdallah Idris Abdallah in kiya SALEEM, kaga Irfan ɗan gidan SALEEM sai girma yake."
mika mata shi ta yi ita kuma tayi waje.
dariya Na'ima tayi ta ce
"Kai aminiya wannan kirari haka har kinsa naji wani karin da ɗi."
zama Raliya ta gyara kana ta dubi aminiyar nata ta ce
"Sha kurumin ki kiji daɗin ki wata rana kece ke rike da ragamar dukiyar SALEEM."
tafawa sukayi tare da shekewa da dariya Na'ima tace
"Kamar yan zu kuwa, ko yanzu ma na fara jin kamshin su."
wani dariyar suka kuma shekewa da shi.
kana Raliya ta dubi ɗan tana faɗin
"Wai har yanzu bai fara tafiya bane duk uban kayan in ganta lafiyar da ake tafka mishin nan?."
"Sati biyu daya wuce yafara ɗan takawa, ai kam yana yana ci da shan abubuwan guna jiki dan duk fitan da SALEEM zai ya idan zai dawo sai ya shigo da wani abun."
Raliya ta ɗago yaron tana dudduba jikin sa tare da faɗin
"Ai kuwa dubi jikin sa kamar ɗan turawa luwai-luwai da shi sai sheki yake."
shiru sukayi da maganar nasu jin an turo kofar,
Ya SALEEM ne ya shigo da sallama ai kuwa yaron najin muryar sa ya fara tsalle yana mika hannu,
daga bakin kofar ya tsaya lai dar dake rike a hannunsa ya aje nan bakin kofar,
Raliya ta gaishe sa kai a kasa kamar mutumi yar kwarai, a takai ce ya amsa mata gaisuwar nata batare da ya dube ta ba,
Na'ima ta mike tare da karɓar Irfan tana faɗin
"Oh ji yaro daga ganin uban sa yaka ma murna wai fa gurin ka yake son zuwa."
tayi maganar tana nufo shi,
kafin ta iso in da yake yajuya yayi waje.
bin bayan sa tayi tana faɗin
"My SALEEM barka da dawowa."
"Yau wa." yafaɗa a takai ce tare da nufar side ɗin sa tabi bayan sa.
yana shiga bedroom ɗin sa, wayoyin sa ya zuba su kan beside kana yashiga tuɓe kayan jikin sa.
in da yake ta karaso cike da muryar kirsa ta ce
"My SALEEM tun ɗazu Irfan yake ta murnar ganin ka baka ganshi bane?."
bai yi magana ba sai da ya karasa tuɓe rigar jikin sa kana ya mika hannu ya karɓi yaron, shiko sai washe baki yake, murmushi yayi masa tare da lakace kumatun sa kana ya ce
"Hy ykk." baki yaron yakuma washewa.
sai ya mika mata shi kana ya cigaba da tuɓe kayan jikin sa, yarage daga shi sai boxes kana ya wuce bathroom.
baki ta taɓe ta gyara rukon yaron tayi waje,
tana shiga ɗakin ta Raliya ta dube ta ta ce
"Ya naga kin dawo da shi bazaki bar sa gun uban sa suzau na ba."
baki ta taɓe tana zama bakin gado,
ta ce "Ai wannan uban nasa murɗaɗɗen uba ne ke bakiga shigo war sa da nake masa magana juya wa yayi ya fita batare da yace ko mai ba, da ace agaban wasu yayi min ai da ya dizgani dan ma Allah ya taimaka a gaban ki ne."
"Wai kina so ki ce min baya karɓar sa ne ko me?."
"A'a yana karɓar sa har ma yayi masa wasa ko kwanakin can ma dayayi ciwo yake hanani bacci ɗaukar sa nake da daddare na kai masa shi su kwana, yana yi masa wasa amma yan da yake masan bai min ba,
baya nuna rawan jiki irin wan da uba yake nuna wa kan ɗan sa musamman idan yaro yana karami kamar shi ɗin nan,
wani lokaci har nayi tunanin na nime ki muje gurin boka sai kuma na shashantar da abun, dan nasan miskilanci a jinin sa yake, in baki mance ba boka ma haka yace mana, shi yasa ma kawai na dai na damuwa."
Numfashi Raliya ta sauke ta ce
"Har naji sanyi in dai wannan ne kawai ai bawata matsala bace, adai juri zuwa rafi, ina labarin kuɗin da Dr Mukhtar ya nima lokacin jinyar Irfan ɗi, kai Dr Mukhtar bashi da mutunci in dai a kan kuɗi ne to komai ma zai iya."
matso wa kusa da ita Na'ima tayi, kana ta waiga gefe da gefen ta sannan cikin kasa da murya ta ce
"Ai baki sani ba shekaran jiya ya tura masa da 500k kan wancan 500k ɗin nan yanzu jibi zamo koma asibitin na basa kason sa na am so nawa, daga nan kuma yakuma tsara yan da wani kuɗin zai kuma zuwa."
dariya Raliya tayi suka tafa tace
"Kai aminiya daga haifan yaron nan zuwa yanzu da ko shekara bai cika ba an tatse sa abun da ya fi 5 Miliyan."
fuska Na'ima ta yamusa tare da faɗin
"Um ai ma dai wani wahalar banza nake, kuɗin nan namune ni da magajin sa, da na karɓi wannan bazan kuma karɓar wani ba, zan karɓe su ne a dunkule da zaran lokaci yayi."
Raliya zatayi magana wayar ta ta fara ring, tsaki taja ganin mai kiran nata tare da tura wayan gife.
Na'ima ta dube ta ta ce "Ya dai aminiya ba tsohon kamu kenan."
ta ce "Rabu da jarabebbe sai azabar jarabar tsiya baya bada kuɗin arziki, ranar kusan kwana yayi a kaina yaɗau naira dubu 50k yabani, shine yau ma yake son muje mu kwana, ina zan iya wannan tsiyar sabon Alhajin dana yi yanzu haka mun shirya tafiya kwana da shi, account ɗi na yayi nauyi yaushe zan tsaya kula irin su kananun ƴan iska,
tsabar jarabar sa wai baya gane yin harka da roba wai zai cire nace wlh kana cire wa zan fita na tafi,
na isa ai na san waɗan da nake harka da su ba condom."
dariya Na'ima tayi tana faɗin
"Ai da kun je shima an gwada lafiyar sa sai kuce gaba da fafata wa."
"Allah ya sawake min ai bana harka da talaka irin sa dubu 50k fa, ka kwana a kai na kaɗau naira dubu 50k ka bani kamar na zama shegiya."
wani kiran da ya kuma shigo wa wayar ta ce ya katse musu hirar ɗaga wayar tayi rai ɓace dan a tunanin ta wannan wan da taki ɗaukar kiran sa shi yakuma kiran ta yanzu.
murmushi ta sake ganin ba shi bane wan da take sumayen jin kiran sa ne,
ta ɗaga kiran cikin kwarewa da iya bari ki ta kara wayar a kunne.
mike wa tayi tana faɗin
"Okay I'm coming."
sai ta sauke wayar a kunne, ta dubi Na'ima ta ɗauki jakar ta tana faɗin
"To alhaji na ya zo bari na tafi sai mun yi waya."
tayi mata sallama ta tafi.
Abuja★
Yau tun tashi na nake jin jikina ba daɗi da alama zazzaɓi ne ke son rufe ni, a daddafe nayi al'walan sallar a zahar nazo na gabatar da Sallah.
ina idar wa na haye gado naja bargo na rufe jikina, kasan cewar yau Lahadi babu school su Naseem suna gida,
so nake na samu na ɗan rumtsa kafin su shigo, ko zan samu baccin ya saukar min da zazzabin, dan bazan iya shan masa magani ba kwata-kwata bazan iya ba dan zan iya yin amai. kwanciya ta na gyara ina jan hanci na daya toshe, nasan zazzaɓin mura ne na ruwan sanyin dana yi ta shiga, kwana biyu ana sanyi ruwan cikin swimming pool yana yin sanyi sosai kuma haka nake shiga ciki.
idanuna na lumshe a hankali ina jin kaina na tsara min, so nake nayi bacci ko zan samu zazzaɓin yaɗan sauka, batare da nasha magani ba.
Nasmah ce ta turo kofa da gudu ta haye gadon ta faɗa jikina, ta yaye blanket ɗin dana rufe jiki na har zuwa kai na, ta leko fuska ta tana faɗin
"Mommy kina da lafiya ne?." murmushi nayi tare da gyaɗa mata kai, da jin kalar hausan nata,
idan zata ce mutum bashi da lafiya sai tace wai yana da lafiya ne.
fuska ta ƙwaɓe tare da mara baki ta ce
"Nima ina da lafiya." tayi maganar tana shige wa cikin blanket ɗin.
kwanciyar ta na gyara nayi mata pillow da hannu na, na dube ta da murmushi ganin yan da take ta wani mammatse ido tana cuno ɗan karamin bakin ta gaba wai ita a dole bata da lafiya.
na ce "Me ke yi miki cewo?." kyakkyafta ido tayi takuma cuno ɗan karamin bakin nata gaba kana ta nuna kan ta da yatsar ta. na ce "Kan ki ke yi miki ciwon?."
ta ce "Eh cine yake min jafi."
shafa kan nata nayi tare da faɗin
"Sannu bari nasa Dr yazo ya baki magani ko zai bari." kai ta gyaɗa,
mumrmushi na kuma ganin ta mai da idanun ta ta lumshi nasan bacci take ji sai na ja blanket ɗin na gyara rufe mata jikin ta, ina mai cigaba da kallon fuskar ta da murmushi wato adole tun da nima bani da lafiya ita ma bata da shi, oh Nasmah kenan iyayen manyan ce.
a hankali nima na mai da idanuna na lumshe babu jimawa kuwa bacci yayi awon gaba da ni.
Da misalin karfe 4:30Pm na farka na ɗan ji daɗin jiki na sabo da baccin da nayi amma dai hanci na na nan a toshe ciwon kan ma haƙa.
ahankali nayi ƙoƙarin ɗaga kan Nasmah a hannun na na maida shi kan pillow sai ta farka, sai na ɗago ta nayi da ita bayi wanka nayi mata kana nafito da ita, ni ma na koma nayi.
bayan na idar da sallar la'asar na saka kaya itama na saka mata, kana na ruko hannun ta muka fito, kasa muka sauka muna shiga cikin parlour'n Naseem da Faty suka shigo, zama nayi ina faɗin
"Gara da bakuzo tun ɗazu ba sai da muka gama baccin mu."
dariya Faty tayi tare da faɗin
"Kai Adda HAMDAH ai har munfito ɗazu zamu zo, sai kuma muka wuce gun lilo, da mun hana ku bacci."
murmushi nayi na ce "Gara da kuka tsaya can gun lelon ai da yanzu kun hana mu yin bacci ku bakuyi ba mu ku hana mu yi."
Talatu data dire tray'n abinci saman kan table ɗin gaban mu, ta ce
"Barkan ku da hutawa, uban ɗaki na muje kayi wanka naga gimbiya kam da wankan ta ta sauko, kai ne ka tsaya gun lilo ko ka ɗebo rana."
tayi maganar tana ruko hannun Naseem.
sukayi cikin bedroom...
Washegari ya kasance ranar Monday bayan su Naseem sun tafi makaranta bacci na koma,
cikin bacci naji wayata tana ring, idanuna a rufe na mika hannu na janyo wayar, na ɗago shi tare da buɗe idanu na kan shi, ganin sunan daya bayyana kan screen ɗin wayar.
yasani ware idanuna sosai, sunan shugaban makarantar su Naseem ne.
nayi saurin ɗaga kiran tare da kai wayar kunne, muryar sa na jiyo hankali tashe yana faɗin
"Madam gamu a asibiti Nasmah ta."
ɗip wayar ta yanke cikin tsananin firgici na mike zaune nan da nan na nimi baccin da nake ji ɗin na rasa,
hannunna na ɓari na dan na number sa na mai da masa kiran, yayin da nake jin kirji na na dukan uku-uku.
"Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un." na furta a fili, wayar tayi ta ring har ta kusa yanke wa kafin aka ɗaga da sauri cikin matukar firgici da tashin hankali na ce
"Ina Nasmah take me ya same ta?!." ya ce
"Gata nan kwance ta......!
Mommyn Twins ce
12
Da sauri cikin matukar tashin hankali tun kan ya karasa abun da zai faɗa na ce "Tamutu tamutu ko?!!."
nayi maganar hankali a mugun tashe dan nagama tsinkewa da yan da naji yake maganar.
ya ce "A'a Madam ba mutuwa tayi ba, dama bata da lafiya ne?,
tun zuwan su School ɗin Aunty'n su tace taga yanayin ta kamar batajin daɗi, shine ta tambaye ta sai tace mata wai kan ta keyi mata zafi, to tafita taje ta ɗauko magani a office kenan ta dawo ta samu tana rike da kanta tana kuka tana faɗin kanta zafi, kan tayi aune ma ta faɗi kasa a sume, tun ɗazu muna asibiti ban so kira na sanar ba sai ta farfaɗo amma har yanzu likitoci sun kasa shawo kan ta."
"Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un wlh lafiyar ta lau ta bar gida."
na furta da karfi yayin da jikina ke cirawa cikin azama na duro a gadon wayar na kare a kunnena ina tambayar sa wani asibiti ne, yana faɗa min nakashe wayar batare da na tsaya sauraran abun da yake cigaba da faɗa ba.
wardrobe na buɗe na janyo mayafi na takalmi mara tudu na saka da sauri nafita na nufi ƙasa, bibbiyu nake haɗa steps,ina sauka na nufi kofa har ina haɗawa da sassarfa.
su Talatu suna zaune cukin parlour'n da sauri suka mike ganin yanda na sauko a firgice, tambaya ta me ke faruwa suka shiga yi suna biyo ni a baya,
tuni nayi waje ban tsaya basu amsa ba, har parking lot suka bini, suna tambayar abun da ya faru. sai a lokacin na ce da su "Nasmah ce ke asibiti asume."
salati suka shiga yi suna tambayar garin yaya.
wan nan karon ban tsaya basu amsa ba dan ji nake tsayuwa basu amsa ma ɓata lokaci ne.
kan kace me sabbin Security ɗin da aka zuba cikin gidan sun iso in da muke, ganin yan da su Talatu suketa rafka salati, suma duk tambayar da suke ban tsaya basu amsa ba, su Talatu ne suka sanar musu abun da ke faruwa.
Yakubu nashiga kwaɗawa kira,
da sauri haɗe da gudu yafito daga cikin ɗakin su, da sauri na shige cikin mota, yana ganin haka ya koma ɗakin da sauri ya fito rike da makullin motar cikin hanzarin yashige motar.
cikin matukar da muwa da rawar murya nace
"Yakubu kayi sauri ko ka bani key ɗin motar ni naja."
key yayi wa motar tare da figar ta aguje, da gudu mai gadi ya buɗe get muka fita a gidan, sai da muka haura titi kafin yake tambaya ta in da zamu nafaɗa masa sunan asibitin.
duk gudun da Yakubu yake gani nake kamar bayayi asibitin tayi min nisa.
Number da aka kira