Showing 96001 words to 99000 words out of 122551 words

Chapter 33 - MATAR MAKAHO COMPLETE HAUSA NOVEL

07 Sep 2024

16752

ta maida su kayan sawan ta, ko mai bata shafawa saboda wari yake mata, haka turare ma koh wani iri bata Amfani dasu.



Zaune take a taburma ita kad'ai ta mimike kafa, don khadija ta tafi kasuwa, babu school yanzun suna hutun first time, kosai ne a gaban ta da kunun kyad'a tanaci, sosai sumayya tayi jiki tayi kiba, wuyanta har guru guru yayi, hips natan nan sun kara buduwa haka ma breast nata, daman akwaisu bare yanzun da dalili.



Sallama akayi a tsakar gidan, na muryoyin mutane abin ya bata mamaki jin kamar muryar sani, bata gama shan mamaki ba saida taji suna gaisawa da y'an gidan Adara dake tsakar gida, suna tambayar su kofar sumayya.



Mikewa tayi tsaye koh d'an kwali babu tsaban mamaki daga ita sai zani a kwankwaso da have vest, jin sun nufo kofar ta, kamar a mafarki Amma dai bara ta tsaya taga ikon Allah, bude kofar shashin ta akayi, da sallama





Suman wucen gadi tayi, wallahi ita harta manta da wasu shugaba family, sai sa'i da lokaci take tunasu, cigaba tayi da tsayuwa tanabin wa'inda suka shigo da kallo.





Dada ce a gaba sai matan uncles nata da yaransu harta surkunayen su momy ce kawai babu, ko wance cikin shiga ta Alfarma kana ganin su kaga inda naira ta samu matsunguni, murmushin yakene koh wance a fuskar ta, da kunya suma tsayen suke suna bin sumayya da kallo, kamar yanda itama ke binsu da kallo.



Mamakine ya kamasu ganin yanda sumayya ta koma, sam bazaka taba cewa auren talaka take ba, sumayyar suce ta zama buhu haka?



Takwarata bazaki bawa tsohowa wajen zama bane?gidan ki guda fa nazo, dada tace tana kara bin sumayya da kallon mamaki yar jikanta gabaki d'aya ta canja.





"Ga taburma bismillan ku"tace tana shiga d'aki hijab ta saka ta d'auko babban dardumar ta, ta kara shimfid'awa a gefe, ganin taburmar bazai d'auke suba, dardumar ma bai gama d'aukar suba wasu a bakin dakali suka zazzauna.



Zama sumayya tayi akan kujera tsugunu bayan ta d'auko sa a kitchen" ina kwanan ku"?



Lafiya sumayya, ya maigidan naki?



"Lafiya" kawai sumayya ta amsa kamar irin bata ganesu innan ba.



Yar nan kice kika dawo haka gaskiya aure ya karbeki sosai wallahi, Hajjo matar babuji tace



"Umm ikon Allah kenan ai hajiya, sai ya baka abinda wasu basu so ba"amsar da sumayya ta bata kenan tana cigaba dacin kosanta kamar irin taga sabbin fuskar nan.



Jikin dada yayi sanyi, ganin halin koh in kula da sumayya ta nuna musu, da ace dane koh makaranta sumayya ta dawo inta ganta saita mata oyoyo ta rungume ta, suna wasa da tsokanar juna irin na jika da kaka, amma yau kallon banza sumayya ta mata, kawalli yaufa wuni muka zo miki, gabaki d'ayan mun nan munyi kewar ki yar mu.



"eh dole kuzo mini jaje ai, tunda kunsace mijin hankalin ku ya kwanta, abinda ake so a gani dai insha Allah baza'a gansa ba, koh xaku mutu haka zaku ganni ku barni, don Mu Allah muka rike" tana magana tana shan kunun ta kamar ba ita ke magana va







Miemie ce ta mike, habba sumayya wannan wani irin banzar magana ne, ya zaki bude baki kina fad'awa hajjo da dada irin wannan magana?





"Keee mimi, ban kasa dake ba karki kuskura ki kwasa, dasu nake babu ruwan ki a maganar nan, kona karta miki layin rashin mutunci"



Eyeeee lallai sumayya, yaushe kika koma mara kunya haka?



"Kubra kenan rashin kunya ai dole na koya, koh kin manta gidan da nake ciki ne"?sumayya ta bata Amsa



Habba sumayya wannan ba halinki bane, don Allah kiyi hakuri mu da kika gan munnan bamuzo don kara bata miki rai bane, munzo gyara abinda muka bata ne, aunty husna surkuwar uncle Abubukar tace.



"Keee Husna karki kuskura kisa baki a maganar nan, ina ganin mutuncin ki, sannan kina maganar ku gyara abinda kuka bata, wani abin kuka bata da har xaku gyara?aini koh sanin ku banyi ba"



Mamakine ya cikasu sumayya ta zama yar tasha, sun shiga uku, yarinyar da koh zagin yara bata iyya ba yau harda zagen manya haka.



Sumayya dafa iyayen ki maza muka zo gidan nan suna waje.



Kallon mammu sumayya tayi, jin abinda tace"meya kawo ku gida na kuma gayya guda haka"?



Munzo ne akan auren ki da yaron nan MAKAHO, tundadaman baso kike ba mumuka miki dole, sam yanzun bamu lamunce ba takardan ki xai baki baziki zauna da misk.................







*************

Muhammad dai yau shida indo , zasu cikin camaroon tallan nono, ta uzzura masa yau saiya rakata, dayake shima yana son zuwa cikin birni yasa sa binta, yau gidado ne kawai yaje kiwo, bappa da matar gidado wance cikin ta ya tsofa haihuwa yau koh gobe.



Cikin Cameroon suka shiga, indo na tallan nono shikam sai kallon gari yake abinsa, basu dawo da wuri ba sai yamma lilis suka dawo.



Bappa ne xaune a bakin masallaci yayi tagumi, su Al'ameen suka same sa, gaidashi sukayi suka wuce cikin gida.



Da dare bayan isha'i Bappane da iyalansa zaune a tsakar gida harda Muhammad, hira ake sosai, tunda muhammad yazo gidan baitaba ganin sun zauna haka ana hira ba, harda inna da matar gidado lantana,



Bappa bakajin dadi ne?



Gidado lafiya ta klau, bansan meke faruwa ba tunda na tashi yau nakejin babu dadi a jikina.



Toh Allah ya kyauta bappa, inna tace tana kallon sa don tun safe itama ta lura akwai abinda ke damun sa.



Ameen Talatu.





Amma bappa wani irin abune yake damunka haka?





Gidado mubar zancen nan kawai bashi da Amfani.



Kamo wani tadin akayi, sai hira ake muhammad nad'an saka baki kad'an kad'an in aka sakosa a zancen.





Sosai yau gidan bappa aka sha hira sai chan dare, muhammad ya musu sallama, kwanciya yayi bayan yayi Alwala yayi addu'ar bacci, haka kawai yake jin kirjinsa na bugawa, kwanciya yayi, yayi likimo a gado,har bacci ya d'auke sa.



Ta bangaren su bappa, sallama sukayi da juna bayan wucewar muhammad don shiya fara tashi, kowa yaje ya kwanta, Amma dai jikin su a sanyaye, yau dai indo taki kwana ita kadai a dakin ta, tace da innar ta zata kwana, dole tasa inna komawa d'akin indo tabar bappa a dakin sa.





Da misalin karfe 1:14am agogon cameroon, Al'ameeen ya farka da salati jin ihu tako ta ina da salati, gari ya kaceme da hayaniya, karan yara da matane kota ina, ga ruwan bindigogi dake tashi, da sauri ya dirka daga kan gadon jin inna na salati da karfi tana wuta wuta jama'a cikin yaren fulatanci

.................<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß





Fan's<ØKß>ØQÝ naga messenge inku ta PC nagode Allah yabar kauna wa'inda bamma reply ba sumin Afuwa abinne da yawa=ØLÜ



<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß

>ØÑÝ
>Ø¯Ý *MATAR MAKAHO* =ØhÜ
>دÝ

~ Na ~



<ØCß *Rukayya Ibrahim* <ØCß





Page7ã 2ã &7ã 3ã

Fita yayi a d'akin da gudu yayi waje, jikinsa rawa ya soma ganin An cinnawa gidan bappa wuta, ga sauran gidaje duk wuta ke tashi da karan mutane da guje guje.



Gidado ne ya fitoh d'aki rike da matar sa, da tashin hankali yasa ta nakuda, ya kalli bappa dake xaune shuru, babu alamun tashin hankali a fuskar sa hakama babu alamun kwanciyar hankali.



Inna ce ta mike da sauri ta isa garesa, hannun lantana ta kama wance ke kokarin faduwa,gaskiya haihuwace gadan gadan fa bappan gidado musan abinyi.





Hanyar wajen gidado ya nufa hannunsa d'auke da wuka sharbebiya.



Kai gidado ina zaka?koh bakajin abinda ke gudana a waje ne?muhammad yace cikin tsananin tashin hankali.



Kaga ku zauna a ciki bara na fita, mu munfi karfin ana kashemu, muna buya sai dai a fito a gwabza, yana magana yana kokarin barin gidan.



Kaiiii gidado, fitar da zakayi ba shine mafita ba, kanada tabbacin inka fita zaka dawo ka samemu a raye?wuta fa aka kunna wa gidan nan, mafita zamu nemawa kan mu, na fita a garin gabaki d'aya.



Allah ya sauwaka, mugudu mubar mahaifan mu, da Arzikin mu.





Gidado kabi abinda yaron nan ya fad'a, don yafika gaskiya nakuda matar ka take, kamata yayi ka fitar da ita, ga indo can sumar ta biyu,inna tace tana nuna indo dake zaune a gefe kamar ruwa ya cita.





Shuru gidado yayi ya tsaya sosai jikinsa ke rawa , kowa yasan yanda ran fulani yake baci in an tabo musu dukiya ba sauki, gaskiya inna saidai kuzo kutafi da ita kaima muhammad ka bisu, mukam zamu kare shanukan mu, yayi maganar yana tsinka zanar bayan gidansu wanda wuta bai iso gunba.



Soyayyar da ka iyya jure shadi akanta, da soyayyar tsakanin uwa da d'a, bazaka iyya sadaukar da arzkinka ba, gidado ku rayu tare?



Mikewa inne tayi, gidado ya ciccibi matarsa da tiyo ya fashe ruwa yana zuba, da gudu indo ta rike hannun inna, muhammad ma binsu yayi a baya, har sun shiga bandaki kafun suka tuna da bappa yana bayansu, juyawa dukansu sukayi suna kallon sa har lokacin bai motsa ba.



Inna ce ta dubesa, Bappan gidado yakana zaune kazo mu tafi baka ga halin da yarinyar nan take ciki bane?





Kuje kawai Allah ya tsare hanya, ni bazan iyya gudu a rugan mu ba.



Habba bappa yanzun kafison ka zauna azo a kashe ka, hakan bai dace ba koh a addinan ce, kana da damar kare kanka, ka bari a kashika, muhammad ya karasa maganar yana karasowa kusa da bappa.



Don Allah bappa y'an dillo, indo tace tana kuka.



Girgiza kai bappa yayi, kuyi hakuri bazan iyya zuwa ba.



Muhammad ne ya dube gidado, kaga gidado ku tafi da inna, lantana da indo , ka fara fitar dasu, muna zuwa da bappa.





Sanin taurin kai da kafiya irin na bappa, yasa gidado da inna suka fita ta zanan bayan gida, harda lantana data gama galabaita da indo.



Zama muhammad yayi kusa da bappa sosai zuciyar sa ta tsinke, ganin yanda wuta yaci rabin gidan yanzun ma wani irin turiri da rad'adi yakeji a jikinsa ga hayaki, bappa don Allah badon niba kazo mu tafi a rugan nan, rayuwar ka tana da matukar Amfani wa Ahlinka, kasan wani irin hali zasu shiga in aka waye gari baka?akan iyya rasa dukiya, wata rana su dawo, Amma ba'a taba rasa uba wani ya maye gurbinsa har Abada, kama iyalinka adalci ka rayu dasu koh ba kome zasu walwala koh ba shanukai, akansu rayu bakai ba dukiya.



Kuka bappa ya fashe dashi, babana bazaka gane bane yanda abin yake, akwai zafi azo a same ka har gidan ka a kwace maka dukiya, a kwace maka muhammali, asaka gudu kamar barawo ina sukeso muje, irin wa'innan mutane, sune sukayi sanadin iyaye na, shekara talatin baya, mu kullun cikin zulumi muke bamuda sakat?



Kayi hakuri bappa, rayuwa tafi kome muhimmanci ita d'ayace, kayi hakuri mu fita anan, yana maganar yana kama hannun bappa ganin jikinsa yayi sanyi, kamasa yayi suka nufi bayan gidan, suka fita ta zanan gidan.



Da ido bappa yake bin rugansu dashi, ganin gawawwakin fulani cikin jini manya da yara, kota ina hayaki ne.



Tafiya suke kamar wasu barayi a hankali a hankali, suna bin ciyaye kamar a mafarki muhammad yaga yan ta'adan nan sanye da kakin sojoji ga bindigogi manya manya a hannunsu, kafun ma su buya tuni sun gansu, ai da gudu muhammad ya kama hannun bappa suka nausa daji, da gudun tsiya, suma suka rufa musu baya.



Gudu muhammad yake da bappa suma suna binsu a baya, bappa ne yayi tuntube ya fadi tim, da sauri muhammad ya dakata kokarin tayar da bappa yake, Amma bappa ya kasa saboda ya buga kafarsa mai ciwo a dutse, ka tafi kawai yaron nan ni inaji lokacina yayi, Allah yamaka Albarka ya sadaka da ahlinka lafiya, sai wata rana.bappa yace.



A karon farko muhammad ya sake kuka mai karfi, harga Allah a d'an zamansu da bappa jinsa yake kamar mahaifinsa, don Allah bappa karkace haka, bara na d'agaka, ciccibar bappa yayi, yana gudu kamar kiftawar walkiya yajisa a kasa dagashi har bappa, mummunan buguwa sukayi muhammad saida tsakiyar giransa ya tsage, saiga jini bappa ma gwuwarsa ta kwarzane sosai.





Kafun ma ya mike tuni yan ta'adan nan sun kewaye su, d'aya daga cikin sune ya taka kafar muhammad saida yaci ta baki, jini ya balle masa, bindiga d'ayan yasa ya buga a kan bappa, kara bappa ya sake yana dukawa hade da rike kansa da karfi yana salati, jin wani irin azaba mai tarin yawa na bazata.



Don Allah kuyi hakuri, karku cutar dashi don Allah, muhammad yana magana yana kuka.





Kai ragon maza kaika san Allah ne?wani a cikinsu yace.



Kuyi hakuri...



Bamuda imani bare hakuri.



Bappa dake duke har lokacin jikinsa sai rawa yake tsabar azaba, kamasa d'ayan yayi ya kwantar kaman rago yasa masa wuka a wuya.





Ai muhammad na ganin haka yayi wani irin mikewa da karfi, ya bangaje mutumin da ya takasa, duk wani tsoro ya fitar masa a rai ganin tabbas abu biyune zai faru rayuwa koh mutuwa, rugawa yayi da gudu ya nufi bappa, kafun ma ya iso garesa tuni mutumin ya dirza wukar jini ya fantsama.



Zuciyar muhammad ta riga ta kikashe yanzun, yaga mutuwar mahaifiyarsa, kaninsa, amma bai taba ganin mutuwar da ta mugu-mugun ratsasa ba irin wannan, sharbeben Adda dake rataye a jikin d'aya daga cikin yan Ta'adan ya zare da karfe, kafun giftawa da bismillah tuni muhammad ya shiga fad'a da mutanen nan, cikin bazata da rashin tsammani,Allah kad'ai yake kira, yakini kawai yasa a ransa koh yakashe koh a kashesa, suna da bindiga shikam wukane kawai, sosai suke..zuba alburusai yana kaucewa, cikin rashin sa'a wani yasake bullet, ya kuskure sa a hannun hagunsa, ihu yasa da karfi yayi kan mutumin, wukar hannunsa yasa ya fille masa kai,sosai jikin muhammad yake bari ganin yau da kansa ya kashe mutum shi muhammad, mutum hudu ya kwantar, daman su hudun suka bisu.



Mikewa yayi ya sabe gawan bappa, sai kuma ya rasa ina zai nufa dashi, tunda fa ya fitoh baiga su inna ba, wani shawara ne ya fado masa, aje bappa yayi ya sabi bindiga da wuka ya koma cikin rugan su gidado.



Tun daga nesa ya hango fulani da aka tara waje d'aya, cikinsu harda su gidado da wasu kattai suka danne sa, sai lantana dake kwance bata motse, sai jinjira a gefe tana cillara kara cikin jini koh cibi ba'a yanke mata ba, Alamu dai daga haihuwarta ta riski wannan masifa.





Bin jikin ciyayi muhammad yayi ya saita mutanen da suka danne gidado, su biyar gabaki d'aya ya sakar musu bullet one by one, ai take yan ta'adan nan suka fusata suna sake ruwan harsashi ta saitin muhammad, da sauri ya kwanta a kasa.



Wanna daman gidado ya samu da wasu matasan fulani suka d'auke wukake da adda aka fara aran gama.



Inna dake gefe da sauri ta rarrafa zuwa wajen jaririyar, wuka ta karba a hannun wani ta yanke mata cibi, nadeta tayi a d'an kwallinta ta kama hannun indo, tare da wasu matan suka ruga a guje, sukayi daji kowa yayi takai takai, aka bar gawan lantana a wajen, don ta rai ake.



Muhammad yau an zama zaratan maza sosai ake gomxa fad'a, duk wani tsoro nasa yau ya kau, yakini d'aya a ransa zaiyi rai koh ah ah, ganin yanda wasu dakarun barayin nan suka fara shigowa rugan, suna karuwa har sun fara ninkesu, gashi mata da yara da suka rage a raye sun dade da gudu, yasa muhammad d'aga murya da karfi, kowa yayi ta kansa karuwa suke aje-aje zasufi karfin mu.



Ai yana maganar nan da gudu ya kama hannun gidado da wani saurayi zaiyi sa'an sa suka nausa daji da gudu, haka ma sauran mazan ana harbinsu suna gudu wasu na faduwa matantu, barayin suka mara musu baya, yayinda su kuma suka raba kawunan su, kashi-kashi.



Muhammad gudu suke a daji koh gabansu basa gani, gudune irin na bakin Rai bakin fama, nausawa daji suke yan ta'andan nan na binsu, a hakan suka ringa gudu, (wani abu sai tashin Hankali kayi abinda koh da kudi aka had'aka bazaka iyya ba, sai kaga masifa)sosai sukayi nisan kiwo, gudu suke mutanen na binsu suna sake bullet, Allah ya tsare su, har suka isa wani baban ruwa fad'awa sukayi ciki, yaufa muhammad da kansa ya tsallake ruwa, suna tsallaka kogin har lokacin mutanen na binsu, sosai suka kara azama basu jima da gudu bayan tsallake kogi na biyu, suka hango wani kauyen, ganin Hakan ne yasa mutanen juyawa suka barsu.



Faduwa muhammad yayi dasu gidado a kasa, ganin sun shigo cikin mutane, A raye basu mutu ba, karasawa sukayi cikin gari.



Sun ma rasa ta ina zasu fara, fahimtar da sukayi garin kamar babu alamun musulunci, ganin yanda mutanen garin suke, buya Al'ameen sukayi basu bari hankalin yan kauyen ya dawo kansu ba, a hankali suke bin cikin gonaki har suka tsallake kauyen lokacin dare yayi sosai, don akiyasce zaikai 10:00 na dare, gindin wata bishiya suka samu suka zauna, kowa na maida numfashi koh bacci basuji yau, muhammad kam jingina yayi da jikin bishiyar ya lumshe idanunsa yana tunanin rayuwa, tunda ya tashi yake ganin jarabawa iri iri, Amma baitaba zata zaiga irin nayau ba, ace tun 2 na dare yana cikin tashin hankali har dare war haka, ada yayi tunanin zuwan sumayya da farin cikin da ya samu, baitaba tunanin akwai sauran wani damuwa ba, ya zauna da sumayya da zuciya d'aya, duk da an sanar dashi ita ba mutuniyar arziki bace, auren jingina za'a basa, hakan yaji A Ransa zai iyya zama da ita cikin aminci, baitaba sawa ransa, don sumayya tayi ciki zai gujeta ba.



A Ranar daya samu tabbacin farin cikin sa, sumayyar sa budurwa ce, yaji dukkan wani damuwa kunci ya yaye, a lokacin rayuwa yake tuna musu mai dadi nan gaba,don ya tabbatar auren sa da sumayya akwai dalili, bai d'auka zaiga irin masifar yau ba, shine yayi kisa?kisan ma mutum d'aya ba, ba biyu ba, atake yaji aransa tabbas yanason zama SOJA don ya bawa kasarsa gudumawa, da maganin ire iren mutanen nan, indai da rai da lafiya koh kurtune inya koma gida zai nema, tunda ba ilimi mai zurfine dashi ba, insha Allah sumayyar sa sai tabar Amsa sunan MATAR MAKAHO zuwa MATAR SOJA........









*******************

Bazaki cigaba da zama da miskini ba yanzun sumayya, mahaifin kima yace gobe in Allah ya kaimu zaku wuce garin su mahaifiyar ki.



"Kin gama, koh baki gama ba"?



Na gama sumayya.



"Toh bara kiji, ni a haka naga mijina kuma nake son zama dashi a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login