Showing 75001 words to 78000 words out of 122551 words

Chapter 26 - MATAR MAKAHO COMPLETE HAUSA NOVEL

07 Sep 2024

16760

zata saloon gyaran gashi sai tayi lalle tama khadija



Gidan goggo taje tayiwa khadija lalle ja da baki itama tayiwa kanta sai dai bata ma hannun dama ba manna masa gam tayi khadija tasa mata lalle akai



Lallen su na kamawa ita da khadija saloon suka wuce aka gyara ma khadija gashi don ita kam bata wanke kanta a sefe, kitso khadija ta watsa mata a saloon sai kusan la'asar sumayya suka dawo, kai taga ikon Allah jama'a ne tirem a kofar ta Al'ameen ya rufe kofar d'aki ya fita sukam suna zazzaune a baranda



haka ba yanda ta iyya ta hau musu lalle



Dayake ana da tabbacin gobe sallah ne yasa khadija had'a musu miyan sallah ta d'aura zobo tana gama had'awa ta juye a robobi tasa a firij



muhammad ma ya turo kayan marmari da sumayya tace zata markad'a a blander tayi juice dashi



Sai dare sosai mutane suka watse ita da khadija suka kai nikan shinkafa bayan sun dawo suka kwaba, yaukam khadija a gidan ta kwana da sumayya a waje yayanta na d'aki



*RANAN SALLAH*

yau take sallah ranar farin ciki ga dukan wani musulmi kowa ka gani fuskar sa d'auke da farin ciki hakan take a wajen su sumayya tun asuba khadija ta fara tuyan masa



sumayya ma wuta ta hura ta d'aura shinkafa don yau dai ba'a gas koh hot plate za'ayi girki ba



Vegetables inta ta kama yayan kawa su green beans green pepper yellow pepper piece cabbage carrot harda k'wai ta d'aura a wuta ga babban kwalban BAMA a zaune agefe



karfe 7:30 sumayya sun gama girkin sallah,

manyan kulolin ta masu shegen kyau, bata taba bude suba sai a ranan mai guda biyar ne ta zuba shinkafa masa coslow miyan ganye da miyan stew sai manyan manyan kofunan zamani ta juye zobo a ciki d'aya kuma mango juice duk sunyi sanyi har suna raba ta sake maidasu firij, wannan na gidansu Ammar kenan, sauran juyewa tayi a babban kula haka ma miyar duk d'aki ta shigar dasu sanin halin mutanen gidan



Wanka tayi ita da khadija suka saka kayansu mai kyau da hijab Al'ameen ma gezena insa sabo ya saka koh sanda sumayya ta hanasa rikewa ita ta kama hannunsa khadija ta rike musu sallaya rufe kofa sukayi lokacin karfe 8:30 sauri suke karsu rasa sallah



Suna fita a gidan sun tsaya a bakin titi amma ba keke koh wani keke suka tare a ciki haka suka fara takawa, kamar hadin baki saiga Ammar ya shawo kwana da motar sa packing yayi a gabasu hade da budewa ya fitoh sanye yake da wani d'anyen yadin shaddane mai kyau sai hula da takalmi agogonsa sai d'aukar ido yake.



Ashe gwara danayi sauri tun d'azun ina ta tunanin bazan same kuba taima ?



Laii Ammar kaine sannu ina kwana?



Lafiya muahmmad barka da sallah.



Ai ba'ayi sallar ba tukum, muhammad ya basa amsa



"Ina kwana"?sumayya tace tana had'a fuska ganin yauma kamar kullum idonsa akanta



Lafiya sumayya muntashi lafiya?



"Lafiya mungode Allah"



Khadija kam kuri tayi tana kallon sa toh a ina tasan bawan allah nan ne kam ta kasa tunawa, a hankali ta ma sumayya magana, aunty nikam a ina kukasan wannan ne?



"Habba khadija kin manta mutumin da yazo asibiti lokacin da za'a mini tiyata ya baki kudi ki ban"



Oh na tuna na tuna Aunty , ina kwana?tana gaida Ammar



kin amsawa yayi hannun muhammad ya kama muje koh ku shiga mota muyi sauri karmu rasa sallah



Ba musu dukansu motar suka shiga yaja suka kama hanyan masallaci



Allahu Akbar anyi sallah lafiya jama'a kamar kasa suna ta fitoh wa a edi kowa ka gani fuskar sa a washe sai gaisawa ake da juna abin gwanin sha'awa kowa na sanye da sabin kaya sai dai na wani yafi na wani tsada



Bayan su Ammar sun fitoh a cikin cunkoson jama'ar dake masallacin, yaso kaisu muhammad gidan su amma sukace ya maidasu gida zasu d'auko abincin da zasu kai gidan nasu



Ba musu ya mai dasu gida abincin muhammad ya d'auko musu a kula ya fitoh waje dasu juice taburma ya shinfid'a musu ba kyama Ammar ya zauna sukaci abincin da muhammad sai santi hake don gaskiya abinci ne na kece raini



Ta bangaren sumayya abinci ta sassaka a kwanuka ta baiwa khadija ta rabawa mutanen gidan ADARA kowa da plate nasa ta zubawa goggo ma ta kai mata tana dawowa sukaci abinci tukum kafun suka sake wanka lokacin azahar yayi sallah sukayi sumayya ta watsawa khadija make-up sosai khadija tayi kyau tana sanye da dogon riga na zani holland mai shegen kyau sai gyele da jaka tare da takalmi hada agogo da su sarka masu azaban tsada sosai sumayya ta kashewa khadija kudi a sallan nan



Ita kam les tasaka sai mayafin ta babba powder kawai ta shafa sai kwalli da man baki don A matsayin ta na matar aure hakan baidace ba tayi kwalliya ta fita tana d'aukar hankalin maza



Al'ameen ne ya shigo duba su sumayya sun gama shiryawa ne Ammar ya dawo yana jiransu



"Don Allah yayan khadija ka sake wanka mana ka chanja kayan jikin kan nan"?



Meya samu na jikin nawa?



"Ba kome amma dai ya kamata ka chanja tunda gidan masu kudi zamu gwara mu kece raini"



Kai sumayya kin cika shirme amma dai bara na watsa ruwan shap shap yayi wanka ya fitoh sabon gezena da sumayya ta d'inka masa shiya saka mai tsadane sosai sai takalmi da agogo yau harda glass sumayya ta d'auko tasa masa lias na hannu riga duk ta makala masa, hannunsa ta kama suka fitoh bayan khadija ta rufe kofar



Kulolin suka d'auko guda biyar sai jup na juice da zobo duk suka jera a boot na motan Ammar



Tunda sumayya ta fitoh idon Ammar ya sauka akanta gabaki d'aya ya tatara hankalin sa

Gareta sai kallon ta yake kamar idanunsa zasu zazzago



Sumayya kam tun fitowar ta ta lura da kallon da Ammar ke mata kamar maye duk d'aga ido da zatayi sai sun had'a ido ganin yanda duk yabi ya zuba mata na mujiya yasata juyawa da sauri cikin haushi tayi cikin gida



Khadija dake kokarin shiga motar ganin sumayya tayi cikin gida yasa ta kwala mata kira, aunty sumayya kin manta wani abune?



Sumayya koh juyowa batayi ba tayi shegewar ta ciki



da sauri Al'ameen ya fita a motar jin khadija tace masa sumayya ta koma cikin gida yabi bayanta..........











<@<@<@<@<@<@<@<@<@

08146017245 *hohoho wani Kaya Sai amale shin kunsan kayatattun magungunan Mata na maman haidar*

*Kayan maman haidar basuda matsala domin traditional medicine ne Kuma anahadasu da ingantattun itatuwa masu karfi da Basu da illah*



<@<@<@<@<@<@<@



*1 Gumbar kankana da ayu* <@<@

2 *Gumbar ayu zallah* <@<@

3 *Gumbar Madara da kwakwa*<@<@

4 *Kaza mekwai* <@<@

5 *Zabo me zuma*<@<@

6 *Kaza me allurai<@<@ sahihiyar mallaka ba boka ba malam*<@<@

7 *Kwallin idonka inadona*<@<@<@

8 *Tauwadar mata*<@<@<@

9 *ketar larabawa magani me kankarowa mace kima da daraja*

10 *Maganin sanyi me fatattakarsa duk kuwa nacinsa Koda bakya haihuwa indai matsalar sanyice gwada wnnn*

11 *Maganin nono. Sahihi*

12 *Maganin hips and bobbs*

13 *hodar. Ni I'ma koramar mata*

14 *nakasan Mara babban sirri*

15 *kafi jijjibi*

16 *daga Sha Sai wanka kasaitacce magani*

17 *Dan kwankwalati namata da mazajensu Kevin Mata*

18 *matsin kinfi budurwa dubu ko haihuwa nawa kikai Babu magana*





<@<@<@<@<@<@<@<@<@

*Maman haidar Bata tsaya anan ba*

*takawomuku hadaddan sabulun gyaran jiki da hadin dilka Mesa sheki da laushin fata gaman kitso Wanda laraba ke amfani dashi inkin gwada saikin dawo kudai kunemeta awannan number* 08146017245

<@<@<@<@<@<@<@<@<@<@<@



<@<@<@<@<@<@<@<@<@<@<@

>
>د *MATAR MAKAHO* =h


~ Na ~






('Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za'a ga mistake Koh typing error Amin afuwa=L

free book >'



*Wannan page nakune Queen fauzee da ogan ki naga comment naki jiya*=



Page5 8 &5 9

Cikin gida yabi sumayya, yana kiranta amma koh juyawa batayi ba, har suka shiga kofar su



Ke sumayya bake jinane, koh me? sai magana nake kin mini banza.



"Na fasa zuwa kaban key na bude d'aki"?



Akan me kika fasa zuwa, koh ince me akai miki, nadai san lafiya muka fitoh?



Ba kome kawai dai na fasa ne, tace tana tunanin ta fad'a masa abinda Ammar ke mata, wani zuciyar kuma ya gargade ta, kartayi ta jawo wata rigimar kuma abanza.



Ke sumayya koh ba magana nake miki bane, nace menene dalilinki na fasa zuwa ?



"Nikam nafasa nace maka kuje kawai"?



Akan wani dalilin?



"Kaina ciwo yaka kuje kawai"



Ai shikenan nima na fasa zuwa, bara nakira, khadijan ta dawo,yakarasa maganar da kokarin juyawa



"Da sauri ta rike masa hannu"nifa ba ina nufin ku fasa zuwa bane,bafa"



Ni kuma in bakije ba bazanje ba



"Shikenan muje"



Haka sumayya tanaji tana gani tabi muhammad suka fitoh waje, ido ta d'aga ta kalli Ammar



Sunkuyar dakai Ammar yayi, tunda yaga fitowar su bai sake d'aga ido ya kalleta ba



Shiga motar sumayya tayi, muhammad ma gaba ta bude masa ya shiga, ita da khadija a baya.



Ammar motan yaja suka cillah titi,sai millionaire sweet khadija kam sai bin gidajen unguwan take da ido, kamar wata wawuya, tana d'aga ido, suka had'a da Ammar ta mirrow hararanta yayi ya kauda fuska



A kofar wani makeken gida sukayi packing Ammar ya danna hon, da gudu maigadi yazo ya bude musu get, kusa hancin motarsa yayi zuwa ciki.



Suna packing Ammar ne ya fara budewa ya fita da,sauri ya zagaya ya bude ma muhammad bangaren sa hannunsa ya kama, yatai maka masa ya sauko



Sumayya ma budewa tayi ta fitoh ta tsaya, tana kallon khadija dake ta kalekale koh fita takasa "khadija menene haka bazaki fitoh bane"?



Da sauri ta fitoh tare da d'an sosa kumatun ta najin kunya.



Cikin gidan suka shiga, sumayya kam, koh d'aga ido batayi ta kalli waje sau biyu ba , gaban ta kawai take kallo, don ita wannan gida baikai ta masa kallon hauka ba



Suna isa kofar falon Ammar yasa hannu ya bude,shiga sukayi bakin su d'auke da sallama



Wa'alaikumu salam oyoyo laleemon bee warugo, wata bakar mata hajiya kyakkyawar gaske, kallo d'aya zaka mata kasan ita ta haifi Ammar,sai wasu yan mata guda biyu, da saurayi zaiyi sa'an khadija, duk suka mike ganin su sumayya sun shigo cikin falon.



Murmushi d'auke a fuskar muhammad ganin yanda mutanen gidan suka taresu da mutunci,yauwa hajiya jam bandu, noi shumre yan julijam?



Jam sai jam,muhammad?tace tana kallon sumayya dake tsaye, bismillah sumayya on jod'a mana?



Ba musu sumayya tazauna akan d'aya daga cikin kujerun falon Ammar ma waje yanunawa muhammad ya zauna sai khadija da tuni ta dade da zama abinta.



Gaisawa sukayi da hajiya, kannen Ammar suka gaidasu,Kayan ciye ciye aka jera musu a gabansu, dangin nama da kayan ci.



Ammar ne ya aike kannen sa suka d'auko abincin da suka kawo a motar,sosai mamarsa taji d'adin ziyaran nan, abincin ma atake suka zuzzuba suna ci, sosai hakan yama sumayya dadi ganin basuda wulakanci koh jijidakai sam.



Har yamma suna gidan sosai khadija ta sake sai hira take da yan matan, muhammad ma hira yake da Ammar da Abbas sabanin sumayya da hajiya keta janta da hira, itakam daga eh sai ah ah .



Kai Aunty sumayya tsaya maimuna ta d'auke mu hoton sallah, khadija tace tana matsowa kusa da sumayya don tun d'azun hotona suke d'auka, ba musu sumayya ta mika wayarta iPhone wa maimuna ta dauketa da wayan.



Da mamaki maimuna kanwar Ammar ke kallon wayan, da sumayya ta mika mata, koh su basu rike waya mai tsadan wannan ba, sai wannan da yayansu yace rayuwansu abin tausayi, Amma ita bata ga tausayi anan ba mata kamar balarabiya, ga aji, dajiji dakai, ga sutura mai tsada irin wanda mom in su ke sawa, Karba tayi



khadija da sumayya suka gyara ta fara d'aukarsu hoto



Ganin maman Ammar tabar falon, yasa sumayya tashi ta kamo hannun Al'ameen ta jashe zuwa d'aya kujeran suka zauna, dafa kafad'arsa tayi "maimuna d'auke mu pls hoton yayi kyau



Ai da gudu khadija ta dawo bayan kujeran ta tsaya, daman 1siter ne Al'ameen azaune akai, sumayya a hannun kujera, ita kuma ta tsaya a bayan kujeran, d'aukarsu hoto maimuna take duk da muhammad ba kallo yake ba, Amma dai hoton yayi kyau, saidai ba camera yake kallo ba



TikTok maimuna ta shiga ta kunna waka, tana musu vedio sosai yayi kyau, fa'i ma shiga tayi da Abbas kannen Ammar, duk sun shiga vedio abu da iphone ga background, ba karamin kyau sukayi ba, Ammar ne kawai bai shiga ba.



Sai dare maman Ammar ta barsu suka tafi bayan sunci abincin dare, da suka tashi tafiya turare da zani ta baiwa khadija, sumayya kam sarka mai kyau ta bata fari, sosai sukayi godiya.



Tunda suka kama hanyan dawowa, sumayya ta lura akwai abinda ke damun mijinta, ganin yanayin sa ya sauya sosai.



Bayan sun dawo gida, har gida Suka raka khadija,ruwa ta iba takai band'aki ganin yanayin Muhammad, kamar ba lafiya, gabaki d'aya yayi laushi kamar bashi ba"yayan khadija nakai maka ruwa, koh zakayi wanka"?



Toh,kawai yace yana mikewa,wankan ya shiga koh towel bai d'auka ba, saida sumayya ta kai masa



Bayan ya fitoh wanka d'aure yake da towel, daga kagan sa, kasan ba lafiya,a hankali yake tafiya yana dafe da kirjin sa, yashigo d'akin.



da sauri sumayya ta bisa da kallo,dayake yanzun basa shakkan juna, sosai bakaman daba,yasaka ta tube kaya a dakin, towel nata ta d'aura ta fita, ban d'aki ta shiga tayi wanka, fitowa tayi ta shiga dakin da mamaki take kallon Al'ameen, ganinsa har lokacin zaune koh kaya baisa ba yayi tagumi.



Al'ameen dake zaune ji kawai yayi sumayya ta kamo hannunsa,A hankali tayi magana "yayan khadija lafiya"?



Janyota kawai yayi gabaki d'ayanta ta fado kansa, a hankali ya sa hannu ya dad'a mannata a jikinsa.



" yayan khadija bansa kaya ba"?



Na sani sumayya ai naji jikin ki d'aure da towel.



"Meke damunka"?



Zuciya ta ke dokawa da karfi, sumayya inaji a jikina akwai wani babban Al'amari dake tinkaro ni.



" kamar ya"?



Sumayya zuciyar kowa na bugawa, sannan wani sa'in mutun najin zuciyar sa na luguje, Kamar yaji tsoro,koh baida gaskiya,koh yayi laifi.



"Hakane"



Amma ni wannan bugun zuciyar bana tsoro koh fargaba bane.



"Name kenan, bangane ba"?



Lumshe ido yayi yana kara manna sumayya a jikinsa,irin wannan lugujen na ringaji lokacin da mami na zata bar duniya, Aranan haka na wuni da lugujen zuciya.



Haka ranan da zan makance, ma irin bugun nan na ringa ji, haka ranan da salim zai bar duniya,sumayya inaji a jikina akwai abinda zai faru dani duk da bansan gaibu ba.



"Subahanallah insha Allah ba abinda zai tinkare ka sai Alkhari"



Insha Allah....Sumayya!



"Na'am yayan khadija"



Don Allah sumayya, yau ki bani hakkina, sosai nakejin wani irin matsanacin bukata, tun da yamma.............





Ta bangaren hajiya kami, kamar yanda boka yace, haka ta d'auke mujiya har cikin gidansu, bayan ta saka kejin a buhu, a d'akin ta ta ajesa a karkashin gado, kamar d'a haka take masa jinya, A washe garin ranan da sumayya zata fara period, a daren ranan, Alarm kamila tasaka a wayan ta, da misalin karfe 2 na dare ya tashe ta, mikewa tayi a hankali ta bude kejin zata d'auki mujiya.



Da wani irin mugun sauri taja baya tare da zaro ido.....mujiya ne tayi mushe, bakinta har rawa yake ta d'auki waya, lalubo number Harira tayi, ta kara wayan a kunne



Ta bangaren Harira kam,tana tsaka da baccin ta,don a silent ta saka wayar sam bata san ma, wata kamila na kiranta ba



Jifa kamila tayi da wayan,jin Harira bata d'auka ba



Washe gari da sassafe koh karyawa,kamila batayi ba ta ciccibi mushen mujiyan nan, tayi gidan Harira,don wallahi ta kudurta A ranta bazai yuba, bazata kashe kudi abanza ba, sai an biyata kudin ta, haka kawai ita ba muhammad ba, ita kudin ta ya tafi



Koh sallama babu ta shigo falon Harira, tana kwala mata kira.



Da sauri mijin harira ya d'ago, yana kallon kamila, lafiya baiwar Allah?



Lafiyar kenan, ina Harira?



Kafun ma yayi magana, harira ta fitoh daga d'aki cikin mamaki jin muryan kamila da sassafen nan, kamila lafiya?



Lafiyar kenan, kika gannin nan,wallahi kinji na rantse bazanyi asaran kudina ba, kin sanni bani da mutunci tam.



Da sauri Harira ta kamo hannun kamila, sukayi wani d'aki dake cikin falon, ganin mijinta a zaune a falo, kamila ke kokarin tona mata tsilili



Ke kamila bana son iskanci kinji koh, zaki zo mini gida da sassafe,agaban mijina kina kokarin zubar mini da mutunci.



Au mijin da kikace kin shanye ne, har zakiji tsoron yasan wani abu a game dake?



Ji hauka toh don ka asirce, mutum sai akace ka fad'a masa ka masa asiri ?ji mahaukaciya



Ke duk ni ba wannan ba,mujiya ta mutu, tana boot na mota na,ki wuce mu koma inda muka karbo she, yaban kudina in yasan bai iyya aiki ba, mena karbamin kudi(daman wannan halin kamila ne indai akan kudin tane bata da mutunci)



Ke da sassafe, koh karyawa banyi bane, zan kama hanyar mutum biyu,toh baki isa ba, don uwarki ni, xaki tsaya kina bawa umurni.



Ganin Harira tad'au zafi, daman ita bata iyya fushi ba sam, yi hakuri Harira raina ne ya baci, don Allah ki taimaka,mu koma wajen mutumin nan.



Ki jirani nayi wanka, na karya saimu tafi?



Ok kawai tace tana zama,abakin gadon d'akin ta zabga tagumi.



Sai kusan 9 suka d'auki hanya, gabaki d'aya kamila sai masifa take, akan malamin bai iyya aiki ba



Bayan sun isa,aje masa kejin mujiyan, kamila tayi a gabansa



D'aukar mujiyan yayi ya kakkala, yanka cikinta yayi ya fitar da layan,warwarewa yayi atake, yaga rubutun sunan sumayya ya kone murus, kamar wanda aka saka kalanzir da petur aka banga masa, d'aga ido yayi ya kalli kamila.



A gaskiya raba Wa'innan ma'aurata baban matsalane, don asirin da aka musu mundin aka rabasu, xa'a iyya samun matsala aikin wasu warware wa zaiyi,gashi sun rike ibada sosai,koh wajen kofa da Aljan zai kusance su sun tushe sa,makiyansu na tare dasu, tabbas suka gane akwai mai kokarin bata musu shiri,zasu iyya ganin bayanki don su mutuwa koh Rayuwa,agunsu don cika buri ba kome bane.

Ina mai baki shawara,kamila ki hakura da kokarin rabasu,kidai nemi wani hanya da zaki malleke sa, Amma banda asiri tunda kika ga nayi iyya kokari na ba'a dace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login