Showing 48001 words to 51000 words out of 122551 words

Chapter 17 - MATAR MAKAHO COMPLETE HAUSA NOVEL

07 Sep 2024

16764

samu ba



Toh shikenan bara na d'auko hijabina, Sumayya tace tana shiga d'akin



"Yayan khadija zanje lallen saina dawo ga abincin ka karasa ci"tace tana d'aukar hijab nata da jakan lalle purse ta bude 50k ta d'auka,zata fita a d'akin



Toh baki karasa cin abincin ba?



"Ah Ah Alhamdulillah kaci kaikam nikam sai nadawo"



Sumayya muje na rakaki kinji?yace Yana mikewa



"Ah ah ga yaro zamu tafi tare,sai dai kazo ka d'auke ni anjima"



Kamar karfe nawa?



"Kana da agogone"?



Oho,nikam ki fad'amin.



"Yanzun 8:12 zuwa 10:00 sai kazo ka d'auke ni"



Toh shikenan yace Yana zama,d'aukar abincin yayi ya cigaba da ci



Sumayya Kam fita tayi da yaron,sai da sukazo kusa da titin first bank taga shagunan a bude kamar Rana ga wuta ako ina,"tsaya Kai mu Shiga shagon nan" tace ma yaron tana Kama hannunsa suka tsallaka titi,shagon ta shiga"excuse me"tace ganin Mai shagon inyamurine



Yes ma barka da zuwa shigo ciki customer ki duba Kaya



Da mamaki sumayya ke kallonsa Ashe ya iyya hausa,yauwa "sannunka,Kaya nake so"



Ok wani iri?



"Jallabiyoyi"



Ok ki shigo gasunan kizo ki zaba Wanda ya miki,yace Yana zazzaro Mata jallabiyoyi sunfi kala goma



Guda uku sumayyaa ta zaba masu masifan kyau fari da baki Mai maiko sosai da hula sai Kuma Mai aiki ruwan sararen samaniya,takalmi ta sai Masa Mai kyau na tambarin Adidas silifas ne,sai t-shirt da 3quiter sai Jean's,sosai Sumayya Tama Al'ameen sayayya harda Turare na maza ta sai Masa da abin haske Kai da gemu,sai kusan 9:26 suka je gidan Matan da zatama lalle



Lalle Sumayya ta Mata baki da ja, Al'ameen tun 10 yazo Amma Basu Gama ba,ya zauna Yana jiranta a kofar gidan



Suna Gama lallen Sumayya ta karbi kudinta laidan da ta aje a kulle a gefe na kayan da ta saima Al'ameen ta saba,waje ta nufa



Tana fita taga yayan khadija a zaune



"Yayan khadija mu tafi Koh"tace Masa



Kun gama?



"Eh mun Gama"



Ok yace Yana mikewa tafiya suke shuru,can dai Al'ameen ya kasa hakuri Jin yanda yakejin motsen laida a hannun Sumayya



Sumayya nikam laidan menene a hannunki Kato haka don nasan dai laida kananu basa Kara haka?



"Abu na saya"ta basa amsa



Kala baice ba suka cigaba da tafiya har suka Isa gida,Dayake sunyi wanka dazun yasa Kaya kawai suka chanja



Yauma kwanciya sukayi tare bayan Al'ameen ya Gama kwsan rabonsa



Washe gari da safe bayan Al'ameen ya tafi masallaci, Ghana must go nasa ta bude Daman jiya ta kirga kayan jallabiya ukune sai wando da riga D'aya sai 3quiter D'aya sai armless D'aya sai gajeren wando biyu vest D'aya, kwasosu tayi ta juye a basket na dattin kayanta,sabbin kayanda ta suyo jiya ta mayar cikin bakkon ta shirye Kamar yanda kayan suke a kirge sauran Kuma ta aje sai Randa ya wanke kayansa biyu masu dattin saita musanya Masa,



Vaseline insa da ya kusa karewa ta juye a laida daukar manda ta siyo Masa tayi ta diga a cikin gongomin kamar yanda baseline insa yake, Haka ma tamasa da sabulu



Sai 6:30 Al'ameen ya shigo gidan



Sumayya Kam ganin ya shigo d'akin da sauri ta d'auki takalmin sa ciny'ayyen ta saka Masa sabo,ta dawo d'akin,kudi ta basa 2k yasai musu dankalin turawa boket D'aya sai k'wai guda biyar,



Fita yayi a d'akin bayan ya karbi kudin yazo ya zura takalminsa,sai Kuma ya cire da sauri,ya ringa laluben bakin dakalin Amma wayam baiji takalminsa ba



Sumayya!!ya k'wala Mata Kira



"Na'am"Sumayya ta amsa tana fita a d'akin itama



Sumayya Banga takalmina ba pls ki duba mini Mana?



"Ba gashinan a gefenka ba" tace tana kallonsa



Wannan ba nawa bane



"Nawa kenan?kadaisan banda takalmi irin wannan soson"?



Amma ni sai inaji Kamar ba nawa bane,nawa fa da laushi sosai ya kode



"Toh wannan in fa",ta tambaye sa tana mamakin fahimta irin nasa



Kamar sabo sabo,



"Hhhh lalle zaka tafi da kafa kenan tunda dai ga takalminka kace Wai ba naka ba"



Sumayya bafa Wasa nake ba Wannan ba takalmina bane



"Nidai naka na gani atoh"tace tana komawa d'akin



Al'ameen Kam ba yanda ya iya Haka ya saka takalmin Amma har ransa yanaji ba nasa bane.



Bayan fitar Al'ameen Sumayya aikace aikacen ta na gida ta Gama ta d'aura ruwan zafi a kittle.



Al'ameen Kam bakin kasuwa yaje ya musu sayaya ya kamo hanyar gida





Bayan Al'ameen ya dawo Sumayya ta soya dankali da k'wai sai ta hada musu tie, rufewa tayi ganin Al'ameen ya Shiga wanka



Al'ameen aban d'aki mamakine ya kamasa Jin sabulunsa na kamshi ,Amma baiyi magana ba bayan ya fitoh, d'aki ya Shiga a hankali ya bude bakkon sa jallabiya D'aya ya zare a ciki ya zaro gajeren wando da vest.



Sumayya na zaune akan kujeran tana kallonsa saka wando yayi da vest sai Kuma taga ya tsaya Yana tattaba vest in,Amma baiyi magana ba ya d'auki jallabiyar yasa,sai Kuma ya juye kayan bakkon duka a cafet Yana tattabasu.



Sumayya!ya kirata



"Na'am"tace tana kallonsa



Sumayya wa'innan ba Kayana bane?



"Akan me zakace haka"



Sumayya wa'innan Sabine kijifa kayan kamshin sabbin Kaya suke bama Turare ba kiji da karfi fa kayan ba masu laushi irin nawa bane?



"Nidai naka na gani"



Sumayya me Kika sayo jiya da naji laida na kayo kayo a hannunki?



"Ina ruwanka"ta basa Amsa



Indai baki fad'amin gaskiya ba toh bazan fad'a Miki wacece kamila, menene hadin mu da ita ba



Tabe fuska Sumayya tayi "Gaskiya n................











<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß *Albishirin ku Mata ku marmaso kuji sirrin,Koh kinsan mace sai da kamshi da gyara* =Ø Þ





<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß *Turare suna d'ayace Amma sun banbanta kowanne da ingancinsa kamshinsa da aikin sa*



<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß *Ina muku Albishir da UMSAD INCENSE Dan samun turaruka masu kamshi da* *gyara*



<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß *Tabbas Turare sirrine ga Koh wace mace*



<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß *Gamai bukatar turarukan UMSAD INCENSE*



<Ø@ß *Na tsunguno(habil)*

<Ø@ß *Na jiki (kwalaccam)* ( *khumra, black & white* )

<Ø@ß *Turaren turara jiki after birth* ,

<Ø@ß *Na d'aki(halud Al'oud)*



*UMSAD INCENSE suna kofar waika wajen Ado bayaro layout Kano State* =؃Ü<Øüß=؃Ü<Øüß



<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß *Suna bada d'aya Koh sare akan farashi Mai Rahusa*



<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß *Suna bada order kayansu Gamai bukata aduk jahar da yake a fadin Nigeria*



Contact them vie

>Ø€Þ08028827241 or 09033791049

IG @umsadincense



<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß

>ØÑÝ
>Ø¯Ý *MATAR MAKAHO* =ØhÜ
>دÝ

~ Na ~



<ØCß *Rukayya* *Ibrahim* <ØCß



('Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za'a ga mistake Koh typing error Amin afuwa=ØLÜ

free book >Ø'Ý



Page 3þã 8þã &3þã 9þã

"Ni Kaya na saya" ta basa amsa



Wani irin Kaya kenan?

sannan Ina Kayana?



"Nina yarda kayayyakin ka duka sabo na sai maka Naga nakan sun kode,Amma kayi hakuri bazan sake ba" tace tana Kama hannunsa dake kokarin zare jallabiyan jikinsa



Sumayya akan me Zaki sayamin Kaya bazaki fad'a mini ba saboda bani da ido saiki zo ki musanya mini,kamar wani yaro.



"Kayi hakuri kaga yanda jallabiyar nan ta karbe ka kuwa yayan khadija" tace ta ja maza zip in gaban jallabiyar,hade da d'aukar Turare ta fisa Masa,vayan ya shafa Mai



Nagode Allah ya miki albarka ya hanani Miki butulci a rayuwa Sumayya



"Ameen" tace tana jera abincin karyawan, Bismillah ta Masa suka fara ci cikin kwanciyar hankali



Bayan sun Gama cin abinci tattara Kwanukan yayi yakai waje,bayan ya ajeye, d'akin yadawo



"Toh yayan khadija wacece kamila"Sumayya ta tambaye sa



Nifa nayi Miki Alkawari ,ai basai kin Kara tambaya taba nida kaina Zan fad'a Miki kome Daya shafe kamila.



"Uhmm ba Dole na tambaya ba tunda sai jamin Rai kake yaufa da wure na Gama aiki Amma sai wani sham kamshi kake"



Nasha kamshin, kema saiki Rama.



"Wallahih ka Gama iyya jarabanka bazan biye maka ba sai naji lbrn nan ehen"



Toh zoki zauna a kusa Dani samun lbrn yafi Dadi,yace Yana zama akan kujera



Saboda tsabar sonjin lbr yasa Sumayya mikewa da sauri tazo Kan kujeran ta xauna kusa dashi



Hannu yasa ya matsota jikinsa a hankali ya rungume ta a jikinsa cikin sanyin hallintarsa murya a sanyaye yace Sumayya!



"Na'am yayan khadija"



Yau Zan baki labarin kamila Amma saikin ji labarina Nima kafun ki gane lbrn kamila dakyau.



"Yauwa Aiko Ina sonjin lbrn ka da dangan takarka da gidan ADARA duk da Ina tunanin dangin mahaifinkane Amma halayenku sun banbanta,hakan matsayinka da khadija a gidan nan na fahimci a kaskance kuke ba Kamar sauran Yan gidan ba"



Duk xakiji insha Allah Koh Nima Zan samu amsar dalilin auren mu Wanda har yau bansan dalili ba.



"Wai kana nufin ba Kaine kace kana Sona ba,aka aura maka ni "?ta tambaye sa cikin zare ido.



Nima ban sani ba Sumayya bansan dalilin auren muba Amma koma menene inaji a jikina insha Allah haduwar mu dake alkhari ce



"Insha Allah insha Allah yayan khadija" tace tana share hawaye Daya gangaro mata



Gyara zama Al'ameen Yayi a hankali ya fara magana................



*Shikaru Talatin da biyar da suka wuce baya* =ØbÝ

Malam Yusuf sumul, shine cikekken sunansa da aka Sansa dashi matashine Dan shikara 35,Yusuf mutum ne Mai Hakuri addini ga kawaici baid'auki duniya da zafi ba,Yana da tsananin zurfin ciki duk yanda zaka zauna dashi bazaka taba fahimtar wani abu a tattare dashi ba shiyasa ba Wanda yasan shid'an inane Koh daga Ina yake, duk da kowa ya gansa Kuma yaji yanayin hausar sa da maganar sa Dole yasan cewa ba D'an kasa bane .



Alhaji Rabi'u ubangari. Wanda akafi sani da ubangari,maikacin gonnati ne Kuma Mai rufin asiri sosai,Yana da Mata biyu.



shine Mai gidan Yusuf, saboda tsananin hankali da nitsuwar yusuf yasa ya d'aukesa Kamar D'an gida ya basa d'aki a cikin gidansa,Yusuf na Masa aikace aikace kamar zuwa kasuwa wanki da gugan kayan yaransa da NASA na kansa Yana Kai kananun yaransa makaranta ya dawo dasu,



Yaran ubangari guda biyar ne sai yaran Yan uwansa maza biyu Mata hudu,kenan yara goma Sha D'aya ne a gidan ubangari

Zainab Fatima Auwalu lukman Nasir,sune yaran ubangari na cikinsa



Haidar Umar khairat munira safara'u murja sune yaran Yan uwansa Dayake rikewa



Yusuf da ubangari akwai kyakkyawar fahimta a tsakaninsu duk da baisan Yusuf ba Amma da zuciya d'aya yake zaune dashi ganin tsawon shikaru Bai taba nuna wani mugun halinsa Wanda mutane zasuye Allah wadai dashi ba.



Yaran gidan na basa girmansa kasancewar duk yaran gidan ya fisu a shikaru,yanajin dadin zaman gidan sosai don tun kafun Alhaji yayi aure suke tare har Allah yasa yayi aure





Yaran suna ganin girman Yusuf saboda yanda mahaifin su ke tare tashi hakan yasa suke kiransa da bappa yusufa



Zaman Yusuf a gidan ya fara gunduran sane bayan girman Yar Alhaji Rabi'u ubangari zainab,wance Allah ya diga Mata son yusuf Mai tsanani duk da a lokacin tana da shikaru 14 yayin da Yusuf keda shikara 35



Tun tana boyewa har abin ya gagara ta tinkare Yusuf da maganar.



Sosai Yusuf ya ja Mata kunne akan zancen kuma ya tabbatar Mata shi bazai aureta ba donshi a matsayin diyarsa,ya d'auketa duk yanda tayi kokarin ganin tashawo Kan Yusuf abin ya gagara,taso fad'awa mahaifyarta zancen tanason Yusuf Amma khairat Yar bappanta ta hanata saboda tasan mundin maman zainab tasan zancen daker zainab ta aure Yusuf.







ADARA FAMILY HOUSE haifafun jalingo ne tun iyaye da kakanni anan gidan Adara suka tashi don duk fad'in sintali ba gida Mai dumbin tarihi da shikarun mazauna ciki irin family ADARA tun husul sai chanje chanjen gini da ake in zamani ya shude,

Tun husul ma haka suke mutane ne masu masifan tsiya ga fad'a kamar ahlin dambe shiyasa aka musu lakabi da ADARA



Aishan ADARA d'aya ce daga cikin yaran gidan adara ,macece Mai matsifa na bugawa a jarida duk yanda kaga mala'in yaran gidan ADARA Aisha ta damasu ta shanye saboda tsananin masifarta yasa Koh saurayi Bata dashi don a lokacin abin kunyane mace takai shikara 20 batayi aure ba Amma Aisha shikarunta 20 Koh saurayi Bata dashi saboda tsananin tsoronta da maza keye

Gidan ADARA tun asali haka yake har wa yanzun.



Aishan ADARA na Saida Dan wake a bakin kasuwan main market na jalingo



Sun hadu da Yusuf ne lokacin da yaje kasuwa sayayyan kayan Miyan gidan ubangidansa,ya saye danwaken ta by mistake robanta ya fashe a hannunsa,



Ba karamin bala'i Aishan ADARA ta sauke Masa ma kwando kwando da Kuma uzzurawa saiya biyata robanta



Yusuf Kam ba karamin mamaki yasha ba ganin irin bala'in da Mai danwake ke Masa akan robanda Bai wuce sule biyar ba sai bala'i take Masa Kamar ya Mata Satan jari



Sosai Yusuf yaji haushi kala baice Mata ba ya Kama hanya Yana tafiya itakam sai binsa take sayya Biya robanta



Yusuf kam yasha Alwashin bazai biya ba ganin jarabanda take Masa haka tayita binsa harya Gama cefenen ya Kama hanyar gida bayan ya tare machine.





Duk jaraban Aishan ADARA yau taga iyyakarta don ba zagi ba duka da Mannin hauka Yusuf ya rabu da ita



Bayan dawowar Yusuf gida Sam ya rasa sukuni,tunanin Mai danwake Kam ya hanasa sukuni Sam



Ta bangaren Aishan ADARA ma hakane Sam bayan tafiyar kyakkyawar mutumin da Bata Sansa ba gabaki daya ya hanata sakat a tsawon shikarun ta Bata taba bi takan soyayya ba Amma wannan Karo tayi tuntuben so a bakin titi Wanda Bata San inda zata sake ganinsa ba





Bayan sati biyu Sam Yusuf ya kasa sukuni ya kasa hakuri sosai Y'an kwanakin nan ya gane meke d'awainiya dashi,sai a lokacin yaji tausayin zainab Ashe haka takeji yake wulakanta ta,



Farga bansa d'ayane kar yaje gareta da soyayya ta tsigalesa don Tabbas daga ganinta Yar bala'i ce sosai Abu na biyu Kuma asalinsa kar rashin sanin danginsa yasa a hanasa auren ta.



A hankali Yusuf ya fara zuwa gun Aishan ADARA cin danwake Wasa Wasa harya kasance ba ranan da baya zuwa ci haka ba ranan da basa fad'a a tsakaninsu kafun su rabu ,har shakuwa yazo ya shiga tsakaninsu Mai tsanani Wanda a zahiri kowa son junane ke d'awainiya dashi,Amma ya kasa sanar da D'an uwansa



A hankali Yusuf ya fahimci masifar Aisha a tarbiyan gidansu yake a Hankali ya Soma nutsar da ita sosai yake nuna Mata abin Bai dace ma Abu kamar Wasa Aishan ADARA ta nutsu sosai sai dai fa har lokacin in ka tabota zaka Sha bala'i sai dai in abinda ba ruwantane Bata Shiga haka zalika ta daina dambe da kowa,abin harya fara bawa jama'a mamaki sauyawan ta



Lokaci da Yusuf ya bayyana ma Aisha soyayyarsa gareta Babu wani jinkiri ta amsa sosai suke zuba love



Yusuf ya samu Alhaji akan maganar Aisha ba karamin murna alhajin yayi ba dayaji Yusuf ya samu wance yake so don burinsa kenan,ya tambaye Yusuf danginsa don maganar aure Dole ana bukatan dangi na jini



Hankalin Yusuf ya Tashi matuka don har kwanciya yayi a gadon asibiti Akan zancen danginsa da Alhaji ya matsa Masa akai



Karshe dai fa ubangari yaga abin fa nayine yasa sa hakura da tambayar Yusuf shi yashiga maganar auren Yusuf



Da yake ubangari ya jima tare da Yusuf kowa gani yake kamar Yan uwane hakan yasa ba dogon zance aka basa auren Aisha don Suma sun Matsu tayi aure ganin ta girma a gida



Ta bangaren zainab Yar ubangari Kam in hankalin ta yayi dubu ya Tashi tayi kuka tayi kuka Kamar zatayi hauka Amma khairat ta taka Mata birki tare da Mata alkawarin sai Yusuf ya aureta amma tabare ayi auren taga matakin da zata d'aukar Mata



Bayan auren Yusuf sumul da Aishan ADARA, Alhaji yaki yarda Yusuf ya Kama gidan haya a gidansa sukaci gaba da zama, soyayya suke shimfid'a wa Mai tsafta sosai Aisha ta nutsu suna zaune da yaran ubangari da matansa lfy Sam bata nuna musu Yar Hali sai daifa basa shiri da zainab ganin kallon banza da take mata



Sai Bayan shikara uku da auren Aishan ADARA da Yusuf kafun Allah ya baiwa Aisha ciki sosai sukayi farinciki da wannan cikin da Allah ya azurtasu,sukaci gaba da rainon cikin cikin farin ciki



Bayan Aisha ta haihuwa sun samu d'a namiji Mai matukar Kama da mahaifinsa Kamar an tsaga Kara, mahaifinsa yasa Masa suna muhammad.

Mahaifiyarsa na kiransa Al'ameen.



Da sauri Sumayya ta d'aga ido tana kallon Al'ameen dake Bata lbr"kana nufin kace mini gidan n........"



Bai bare ta karasa ba ya girgiza Mata Kai Yana Kara kwantar ta ita a jikinsa,ki aje tambayoyin ki Inna Gama saiki tambaya



Kai kawai ta gyad'a Masa



Ya cigaba.....har lokacin zainab Bata saduda da soyayyar Yusuf ba don a lokacin ta kammala secondary school nata,Amma Taki aure Dole yasa babanta nema Mata wani makarantan gaba da secondary taci gaba



Bayan haihuwa Al'ameen da shikara uku Aisha ta Kara haihuwar wani da namiji yaci sunan Salim, tun daga lokacin Aisha Bata sake samun ciki ba,sukaci gaba da kula da yaransu don a lokacin Alhaji ya budewa Yusuf shago yabar aikace aikacen gida basuda wata matsala sai na d'ansu Salim Wanda ke fama da mummunan ciwon zuciya,duk bayan wata D'aya sai sunga likita Kuma sai anci kudi.



A hakan rayuwa tayita tafiya yau Dadi gobe akasinsa Al'ameen da Salim suna matukar samun kula daga iyayen su suna Isa shiga makaranta aka sakasu yarane da suka shagu da junansu matika Kamar wasu tagwaye Dayake Salim nada gaban girma tuni ya tsara da yayansa har lokacin Aisha Bata San cewa Yusuf ba Dan uwan Alhaji bane duk da tana yawan tambayan sa labarin Yan uwansa Amma Yusuf daga tayi tambar saiya hau hada Mata fuska



Bayan wasu shikaru lokacin Al'ameen nada shikara 11 Salim nada shikara 8 a duniya. Aisha na d'auke da karamin ciki.



wata ranan juma'a da zuriyan yusuf bazasu taba mantawa da ranan b a tsawon rayuwansu ba har Abada ciwon bazaibar zukatan su ba



Da misalin karfe bakwai na dare yusuf ya dawo gida,Yana kokarin shiga shashen su sai ga khairat taresa tayi cikin kuka Wai zainab ba lfy tana dakinta Alhaji yace yaje su kaita asibiti



Da gudu yusuf ya bi bayan kairan zuwa shashen Yan matan gidan,shiya fara Shiga d'akin Yana shiga khairat taja kofar ta rufe kofar ta waje da makulli.



Yusuf na shiga d'akin ya ware ido ganin zainab ba Kaya daga ita sai d'aurin kirji a zaune akan gado



Tambayar ta yusuf ya farayi, zainab menene haka Kuma ki nemi riga ki saka yace Yana Mai kokarin bude kofar



Dariya zainab ta sake hade da furta wallahih kaji na rantse maka Yusuf tunda ka hofantar da soyayya ta kasa kafa ka shureta Nima saina jazamaka bala'i inda zaisa ka aureni Dole wannan itace kad'ai abinda zanyi na mallakeka,ka 'dauka Koh shurun da nayi na hakurane?

Ah ah wallahih ban hakura ba tanadi nake maka.



Subhanallah shine abinda yusuf ya furta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login