Showing 72001 words to 75000 words out of 122551 words

Chapter 25 - MATAR MAKAHO COMPLETE HAUSA NOVEL

07 Sep 2024

16730

zan ganar dake



Yi hakuri muje



Haka suka nufi cikin kokon kamila kamar zata mutu tsabar wari ai bata gama ganin tashin hankali ba sai data shiga kokon taga tashin hankali mutum ne a zaune kamar an sassaka sa jikinsa duk kuraje sunyi ruwa sun cika sai doyi yake dagashe sai fata kawai ya d'aura a Gabansa ga gashin kansa sa tsitsige kamar shaid'an gashi jikin kokon kadangaru ne sunfi dubu a mamman ne koh ta ina bazama kaga jikin kokon ba tsabar yawansu gasu a shure waje d'aya



Kai ku dakata ku dakata nace, yafad'a da muryarsa mai amoi gata muryar yar irin jarirai cikin tsawa yayi maganar



Sosai kamila ta razana da gudu tayi hanyar fita



Karki kuskura ki fita a nan ba tare da an gama da bukatun ki ba Tabbas zaki sami Muhammad MAKAHO.......



Aijin ya ambace zata samu muhammad yasa ta dawo da sauri jiki na rawa ta tsunguna kamar yanda Harira tayi



Kallon ta bokan yayi sannan ya rufe idonsa yana wani irin magan ganun tsibbo na d'an wani lokaci kafun ya bude idanunsa kallon cikin kwaryar yayi nad'an wani lokaci kafun ya d'aga ido yana kallon kamila



Tabbas zaki samu muhammad amma fa rabasu da sumayya babban Had'ari ne saboda kaddarar su a manne take dana juna akwai makiya sama dake idanunsu kullum na kansu sannan asirin dake yawo akansu yafi wanda kike so a saka musu Amma akwai mafita d'aya



Jiki na rawa kamila tace kamar ya kenan Allah gafarta malam



Wani irin tsawa ya daka mata, keee ba'a kira mana Allah Anan kinsan akwai sane kika zo neman biyan bukata wajen mu(Wa iyyazubillah)



Tuba take na kan dutse sabuwa ce Amata afuwa



Ammata Harira amma ta kiyaye nan bama son shirme



Zan...z..nkiyaye..takara sa maganar cikin tsoro harga Allah mutumin razana ta yake



Yanzun ana tsaka da ibadan watan Azumi kuma sun tsaya dakyau wajen ibadah basu bada wani kofa da Za'a kawo musu farmaki ba sai dai akwai dama, nan da sati biyu zata Fara jini mundin tayi sake da ibadah zamu farmata



Kamar ya malam?kamila ta tambaye sa



Ranan juma'a 17 ga azumi da misalin karfe 1 na rana zata fara jini a lokacin zuwa kwana biyar kina da daman da maganin zai cita mundin tayi sakaci da ibadan da suke yanzun



Ok toh malam ni yanzun wani mataki koh ince wani aiki d'aya za'a mini



Akaf asirin da za'a musu don ganin yakita, bazaici ba don an musu bakin asiri na zama tare da juna abu d'aya zan miki shine Ama sumayya kurciya tabar kasan gabaki d'aya ta manta da NIGERIA a rayuwar ta kwata kwata da rayuwar da tayi a ciki,

Wannan damar xaki samu na auren muhammad, duk da hakan zai batawa wasu shirin su da suka dade sunayi



Na Amince wallahi na yarda ayi mata koma menene



Shikenan zaki kawo bakar tinkiya da jan tatabara sai rakuma biyar masu ciki



Malam ina zan samu wa'innan abubuwan sai dai in b

Da hali na bada kudin sai a nema asaya



Ba damuwa ki kawo



Nawa ne?



Bama yanke kudi biya kawai ake



Kudi kamila ta basa kusan 500k



Kije ki dawo gobe in mun had'a aiki sai kizo ki karba



Toh mungode



Fita sukayi da Harira sosai taji dadin jin za'a mata maganin yar iska



**************

Sosai sumayya da Al'ameen suka dage da ibada sallan dare ga sadaka duk yamma sai sumayya tayi kunu da kankara shi kuma muhammad yayi sadakar lemo ma Almajirai koh dabino



Khadija kam haryau basu kara haduwa da Ammar ba bata kuma san shiya bude ma yayanta shago ba taci gana da zuwa makaranta har azumi yakai 17 sumayya batayi sakaci da ibada ba kwanciya da Alwala in Muhammad ya tashi da dadare yana tada ta itama ta zauna tana lazimi sosai suke ibada Awatan koh bacci yanzun basu da lokacin sa sai bayan asuba



Ta bagaren kamila sun koma wajen boka washe gari a idanunsu ya kamo wata katuwar mujiya ya fade mata ciki layoyin da ya rubuta sunan sumayya ya saka ma mujiyar a cikin da Allura da zare yasaka ya dinke cikinta ya baiwa kamila tayi ta kula da ita a keji ta mata jinya nan da kwana 16 ranan da sumayya zata fara Al'ada kenan kuma ana son karta sake azumi daga ranan sai randa sumayya ta fara Jini saita saketa da tsakar dare tana mai Ambaton sunan sumayyar kafun gobe da safe zataji kyakkyawar lbr



Duk da kamila na tsoron mujiya Amma dayake shaid'an ya buga mata ganga haka ta cici a kwando tayi jalingo



Yau aka kai azumi 20 a daren ranan sumayya ta samu tsarki bayan isha'i tayi wanka



Al'ameen kam bayan ya dawo daga Ashan kwanciyan sa yayi don yau Tahajjud zasu shiyasa yake son kwantawa da wuri



Sumayya kam abincin asuba tayi sai kusan 9:39 ta kwanta



Da misalin karfe 12:10 Al'ameen ya farka Tada sumayya yayi sukayi Alwala kaya suka chanja daga na bacci zuwa jallabiya ita kuma tasa dogon riga sai hijab sallaya ya d'auka suka rufe kofar suka fita



Gidan goggo suka wuce don khadija tayi ta rokon su zata bisu itama bayan sun isa sumayya ce ta shiga gidan da sallama jin shuru yasa ta buga kofar d'akin khadija



tashe tayi Itama Alwalan tayi suka fita a gidan



Haka su uku suka kama hanya koh ina ka wuce group group ne na Al'umma musulmai suna tafiya manyan masallatai kamar rana ne ba dare ba



Sumayya da khadija da Al'ameen da kafa suka taka har macilin babban masallacin juma'a na Dr Ibrahim jalo jalingo



Sai 3 aka tashi Ana fifita a masallacin, ture ture tsabar yawan jama'a cunkoson ne yaraba sumayya da khadija



Bayan khadija ta fitoh daker tsaya tayi tana dube duben sumayya Amma bata ganta ba A haka ta fitoh bakin SINTALI GIOBAL ta tsaya saiga yayan ta don daman sunyi agun zasu hadu in An tashi



Bayan isarsa da mamaki jin muryar khadija kad'ai banda sumayya ya tambaye ta, ke khadija ina Aunty taki?



Wallahi yaya banganta ba tunda muka..............



<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß

08146017245 *hohoho wani Kaya Sai amale shin kunsan kayatattun magungunan Mata na maman haidar*

*Kayan maman haidar basuda matsala domin traditional medicine ne Kuma anahadasu da ingantattun itatuwa masu karfi da Basu da illah*



<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß



*1 Gumbar kankana da ayu* <Ø@ß<Ø@ß

2 *Gumbar ayu zallah* <Ø@ß<Ø@ß

3 *Gumbar Madara da kwakwa*<Ø@ß<Ø@ß

4 *Kaza mekwai* <Ø@ß<Ø@ß

5 *Zabo me zuma*<Ø@ß<Ø@ß

6 *Kaza me allurai<Ø@ß<Ø@ß sahihiyar mallaka ba boka ba malam*<Ø@ß<Ø@ß

7 *Kwallin idonka inadona*<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß

8 *Tauwadar mata*<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß

9 *ketar larabawa magani me kankarowa mace kima da daraja*

10 *Maganin sanyi me fatattakarsa duk kuwa nacinsa Koda bakya haihuwa indai matsalar sanyice gwada wnnn*

11 *Maganin nono. Sahihi*

12 *Maganin hips and bobbs*

13 *hodar. Ni I'ma koramar mata*

14 *nakasan Mara babban sirri*

15 *kafi jijjibi*

16 *daga Sha Sai wanka kasaitacce magani*

17 *Dan kwankwalati namata da mazajensu Kevin Mata*

18 *matsin kinfi budurwa dubu ko haihuwa nawa kikai Babu magana*





<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß

*Maman haidar Bata tsaya anan ba*

*takawomuku hadaddan sabulun gyaran jiki da hadin dilka Mesa sheki da laushin fata gaman kitso Wanda laraba ke amfani dashi inkin gwada saikin dawo kudai kunemeta awannan number* 08146017245

<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß



<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß

>ØÑÝ
>Ø¯Ý *MATAR MAKAHO* =ØhÜ
>دÝ

~ Na ~



<ØCß *Rukayya* *Ibrahim* <ØCß



('Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za'a ga mistake Koh typing error Amin afuwa=ØLÜ

free book >Ø'Ý



Page5ã 6ã &5ã 7ã

Tunda muka fitoh Banganta ba.



Wani irin baki gantaba kuma hauka kike ne khadija koh me?



Wallahi yaya da gaske nake banga Aunty ba.



Nashiga uku ni muhammad, yace yana kamo hannun khadija suka tsallaka titi zuwa cikin masallaci sosai suka dudu ba Amma basu ga koh mai kamada sumayya ba sosai abin ya gigitashi, ke khadija a daidai ina kuka rabune wai?



A kofar fitane fa yaya cunkoso yasa muka rabu.



Jingina kawai yayi da jikin ginin masallacin shikam dai ya shiga ukun sa ina sumayyar ta shiga ne wai?



Yaya koh dai aunty gida ta koma ne?



Wani irin gida kuma khadija bayan saida nace ku jirani a global xaki wanice ta koma gida nadai san sumayya bazata koma gida ba



Daga khadija har muhammad hankalin su ya tashi har hankalin yan agaji ya dawo kansu d'aya daga cikin su ya tambaye sa



malam lafiya naga kana ta zaga masallaci kaje ka dawo, tun dazun yanzun fa ana neman 4:00 bazaka tafi gida ba ga kanwarka ma naga kuna ta yawo tun d'azun lfy kam?



Ina fa lfy wallahi ranka ya dade da matata mukazo masallaci amma ban ganta ba gabaki d'aya na gama iyya dubata amma bangan taba



Wace irin magana ce wannan ita matar taka yar yayece koh jaririya da za'a nema a rasa koh hanyar gidane bata sani ba?



Ranka shi dad'e ni nasan bazata koma gida ba tunda nace ta jirani toh tabbas zata jiranin



Kaga malam karkazo ka d'aga mana hankali a wani unguwa kuke ne?



Sintali ne..



Sintali=Ø3ÞA koh B?



Sintali A ne ranka ya dade



Amma dai kai d'an rainin wayo ne ina sintali A ina macilin da bazata iyya komawa da kanta ba kazo kana kokarin daga mana hankali?



Kayi hakuri ranka ya dade



Na hakura amma ka fita kakama kanwarka kubar masallaci nan ya zakazo da maganar da hankali bazai d'auka ba matar ka ta bata, ina macilin ina sintali?da bazata koma ba



Kayi hakuri..



Kama gabanka malam?



Haka Al'ameen ya fita kaman k'wai ya fashe masa a ciki



Da sauri khadija tazo ta kama masa hannu haka suka fito a masallacin gwanin tausayi

Tsallake titi sukayi suna tafiya Gabaki d'ayansu inka gansu kaga wa'inda basu da nutsuwa gabaki d'aya zuciyar Al'ameen bugawa take kamar ance masa sumayya zata barsa



Sunzo daidai titin doruwa kamar daga sama khadija ta hango mace da hijabi tana tsallako titi Allah yasa akwai wutan sola shiya bata daman ganin wance ta tsallakon da karfi ta kwala ma sumayya kira Aunty!!!





Ai da wani irin mugun sauri Al'amesn ke magana, kee kin ganta ne ina sumayyar take tana ina?



Kafun khadija ta basa amsa da gudu sumayya ta karaso karesu"lafiya har yanzun baku koma gida ba"?



Kee sumayya kina da hankali kuwa banace miki kafun mu shiga masallaci, kujirani a gidan man sintali ba koh ba haka nace ba, shine zakisa kafa ki koma gida don tsabar kin raina min wayo gani d'an iska koh?



"Don girman Allah kayi hakuri, wallahi sace mini takalmi akayi shine na tsaya nema na jira mutane suka fifita duk ban gane ba dana fitoh wajen global, nan ma ban ganku ba shine nayi tunanin kun koma gida saina koma nima danaje kuma naga baku dawo ba, shine nabiyo ku"



Don Allah yaya kayi hakuri tsabani aka samu!



Na hakura khadija Amma sumayya karki sake mini haka Am warning you?





"Insha Allah" tace tana kama hannunsa dake cikin na khadija don baizo da sanda ba suka tsallaka titi



Bayan sun isa gida ganin sun kusa makara yasa sumayya hana khadija zuwa gida abincin sahur ta iba mata tuwo ne miyan kifi d'anye suka zauna a waje suna ci



Al'ameen kam tuwo kawai yakeci da miya baya cin kifin



Da mamaki sumayya tace "yayan khadija ya bakacin kifin gashi mun kusa makara fa"?



Sumayya bazan iyya cin kifi d'anye ba kar kashi ya makale min a wuya



" tarwad'a ne fa"



Nikam ah ah



Hannu sumayya tasa a kwanon miyan ta yago kifi tasa mai a baki"toh bude bakin nasa maka"



Da sauri khadija ta kauda kai kamar bata gansu ba don wallahi sun bata kunya



Al'ameen kam bude baki yayi sumayya sai da ta ciyar dashi kifi har yace ya isheshi kafun ta ci nata



Bayan sunyi sallan asuba khadija ta koma gida Al'ameen kam bacci suka koma suna ramakon na jiya



Yau koh tafsir basu samu zuwa ba saboda baccin dake idanun su har 12:00 suna bacci a d'aki



Assalamu Alaikum!! wasu yan matane guda hudu ke sallama sunfi minutes 8 suna buga sallama shuru



Al'ameen kamar a mafarki yake jin sallama akai akai mikewa yai hade da amsa musu



Ina kwana?



Lafiya, ya amsa



Am wajen sumayya mukazo



Ok lafiya kam?



Eh munzo tambayar lallen sallah ne



Ok bara na tada ta



Ah ah ka barta in bata tashi ba inyaso gobe sai mu dawo



Ok toh Allah ya kaimu



Ameen, in ba damuwa inta tashi kace yaran gidan Malam yunusa ne sukazo tambayar Lalle kar wasu suzo su riga mu?



Toh yace yana d'aukar boket bayan sun fita wanka yayi ya shiga dakin dayake yanzun yasan soket in kunna TV jin an kawo nepa ga fanka na hura d'akin danna soket in yayi daman jiya sunnah suke kallo aka d'auke, zama yayi yana sauraron wa'azi hannun sa d'auke da calbi yana ja



Sumayya bata tashi ba sai azahar nan ma shiya tashe ta kafun ya tafi masallaci



*******************

Haka rayuwa yayi ta tafiya axumi nata karewa a hankali hankali customers na sumayya suke zuwa tambayar lalle tun sallah saura kwana goma ita karan kanta batasan adadin wa'inda suka tambaye lalle ba ita dai ta amsa zatayi amma suzo da wuri, sannan tana musu tallan wanda zaiyi kitson sallah kanwar mijinta nayi ai kuwa khadija ma tatara customers sosai,



kayan sallah ma bana muhammad ne ya d'auke sumayya da khadija har kasuwa sukayi sayayyan sallah duk da sumayya taki yarda ganin tana da wasu zanunuwan a akwatin ta amma ina yace na akwati daban na sallah daban, ba laifi yasai musu kaya itama ta dad'a wasu da kudin ta haka ma khadija ta kara mata har kala biyu bayan wanda ya musu she karan kansa gezena biyu yasaya sumayya ta kara masa biyu duk sunka kai dinki.



Akwana A tashi yau dai saura kwana d'aya sallah kofar sumayya makil da jama'a daga masu kitso harda masu lalle, harda su suwaiban adara yau ana bin layi a kofar, sumayya na hango sanye da riga da wando baki tana ta fama da lalle sai khadija dake ma wata yarinya kitson brazil kulu da bit



Har yamma mutane ne makil ba ita ta rabu da mutane ba sai kusan goma na dare nan ba hakuri ta basu akan gobe su dawo da asuba



Al'ameen dake d'aki kwance yana lazimi shiya raka khadija gida



Yau sumayya koh girkin asuba bata samu tayi ba na bud'a bakin ma watace ta mata girki tana ma yarta lalle



Yauma bayan sunje tahajjud suna dawowa ne suka samu tuwo a bakin titi na asuba suka saya, dashi sukayi sahur



Sumayya suna komawa gida suna sallah ta kwanta ai koh gama d'aukarta bacci baiyi ba tafara jin sallaman mutane ga idonta duk bacci kin tashi tayi Al'ameen ne ya fita ya basu hakuri akan sumayya na bacci Amma haka bayin Allah nan sukaki tafiya taburma suka shimfid'a suka zazzauna>Ø#Ýsuna jiran sumy(masu lalle gaskiya kuna ganin abu a sallah har kwana ana muku a d'aki)



Surutun su shiya hana sumayya komawa bacci haka tanaji tana gani ta kasa bacci dole yasa ta fitoh jin jama'a sai dad'uwa suke



Ai tana fita saiga khadija da tawagar masu kitso sun tasata a gaba=ØÞ



Haka suka dukufa suna neman halal nasu,



Al'ameen fita yayi a d'akin sumayya! yakira sunan ta



"Na'am"ta amsa tana mai mikewa ta bisa d'akin ganin ya koma



Sumayya zan fita na karbo mana dinki, maganar zuwa kasuwan fa muna sa ran gobe sallah fa naga bamu shirya kome ba?



"eh kam gaskiya nima naso naje kasuwan nan da kaina amma yanzun ba iyya fita zanyi ba sai dai ku tafi da khadija in yaso sai na rubuta mata list"?





Ok nace na saya mana watanda ne?(naman shanu da ake yankawa a ranan jajeberi ana saidawa a unguwa)



"Ah ah ka saya mana kaji gaskiya tunda sallah ne"



Shinkafa koh tuwo zakiyi?



"Habba tuwo ranan sallah, shinkafa zanyi da miya sai coslow da kaji sanan zanyi masa da miya"



Ok daman so nake ranan sallan nan mu kaiwa gidan su Ammar abinci kuma muje mu gaida iyayen sa sai kuma nayi tunanin kar suce don kudin su yasa muke son rabansu fa?



"Ah ah yayan khadija in zakayi abin Alkhari kayi kawai karma ka bari shaid'an ya saka maka wani tunani daban a ranka kaji"?



Shikenan sumayya Allah ya kaimu goben kinyi lalle kuwa?yana maganar yana kama hannun ta



"Ina naga lalle daga ni har khadija ba lalle ba kitso"



Kai gaskiya nifa an takurani tun sallah saura kwana hudu ban sake cin abincin kiba ki taimaka ki mana girkin sallah da kanki



"Insha Allah la'asar nayi zan sallami kowa wanda ya samu da wanda bai samu ba duk sai suyi hakuri nima na samu nayi aikin sallah"



Ok kiramin khadijan inkin gama rubuta list in mu tafi



Haka koh akayi sumayya list ta rubuta ta baiwa khadija duk yanda jama'a masu kitso suka ringa roko sai da sumayya ta d'aga khadija suka tafi kasuwa



dinki suka fara karbowa sai cefenen da sukayi sosai sukayi cefene sai da ya cika bairo.



Bayan khadija ta dawo sumayya tashi tayi ta gyara kajin duk da wasu sunso karba mata Amma taki yarda soya kajin tayi daman guda biyar ya saya ta rabawa mutane d'aya sosai tayi ta ayyukanta wasu kamma ganin aiki take kuma ba karewa zaiyi ba, zuciya kawai sukayi suka tafi abinsu wasu kam kama mata aikin sukayi duk da ta nuna su bari amma kin bari sukayi wasu sun gyara mata tattasai wasu sunkai nika cikin kankanin lokaci ta kammala had'a abubuwan sallan ta miya ma ta soya amma bata sa ruwa ba saboda ba'a tabbatar anga wata ba vegetables ma bata yanka ba tadai sasu a firij ne



Bayan Ansha ruwa sumayya sallamar mutane tayi wa'inda bata musu ba ta basu hakuri wasu kuma sukace gobe koh jibi zasuzo Amusu



Yau kam saida muhammad ya saya mata matsala 8 tasha tsabar yanda bayanta ke ciwo amma fa gaskiya ta samu kudi bana wasa ba a sallan nan khadija karan kanta kudi ta samu sosai



Har dare ba'a sanar anga wata ba haka su sumayya suka kwanta da niyar inba'a gani ba zasu tashi da azumi



Aiko hakance ta faru don da asuba ji sukai ana atashi ayi sahur jama'a gobe ba sallah bane=Ø Þ



Ai yau kam sanin da sumayya tayi ba karamin mutane ne zasu zo ba yasa tana sallan asuba ta tattara boron lallen ta tayi gidan goggo Al'ameen ta bari a d'aki yana bacci tace masa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login