Showing 3001 words to 6000 words out of 122551 words

Chapter 2 - MATAR MAKAHO COMPLETE HAUSA NOVEL

07 Sep 2024

16728

ya kulata cikin mu biyun,



cikin bacin Rai tayi tsaki ta juya tafita. Koh ido ba mudu bane yasan kema ni ba sa'ar yinta bane kallo daya tamin ta gane ni ba kallan raini wayo bane Kamar yanda suka Saba Raina Masa,



**mamaki ne ya kamani, lallai sai nayi da gaske Zan iyya zama da Yan gidan nan. don dagani Basu da mutunci wallahi=ØÞ





Muna Gama karyawa ya mike ya dauki kwanukan da mukaci abinci harda nawa ha Hada ya fita dasu a kitchen ya Ajjye,



Dawowa cikin dakin Yayi cikin sanyin halinsa ya bude baki a Hankali ya furta Zan fita wajin sana'a Koh akwai abinda Zaki bukata,?



Kamar bazan tanka ba Amma na daure nace "babu"Koh zaka dawo kaci abincin Rana"? cikin natsuwa yace min ah..ah Zan saya naci sai yamma Zan dawo,



"har Ina ne wajen sana'ar taka" ? Cikin D'anjin Dadi jin Ina kulasa yace bakin titin kofar gida ta gefen shagonan, su haladu



** Ni Kuma Ina nasan wani Haladu bare shagonsa=ØÞa Raina nake fada



Amma a zahiri cewa nayi "toh Inna Gama ka tura yaro yazo ya karba maka abincin"



da zumudi yace toh ......toh Zan turo bayan azahar. Ya sa Kai ya fita



***Daki na koma na bubbude akwatunan Kayana na bubbude kayan Ina jirawa a whtdp wasu a dressed mirror kayane na alfarma atamfufe dinkaku da Wanda ba dinkaku ba takalma da jakunKuna gyeleluka abaya material duka na shirya Kayana a nitse make-up kit na aje sa a drowarn mirror mayuka da turaruka na jirasu saman mirror. sauran kayan da suka rage na mai dasu cikin akwaiti ba wajen jirawa duk ya cika ba fili na rufe na Mai dasu saman whdrp ",



yarane suka fara shigowa ba sallama ba gaisuwa suka shigo mini daki harda Yan matan gidan suka cika dakin Wai sunzo kallon daki ga makwanta nata shigowa da sunan ganin daki Koh gulma ne oho, ana haka aka kawo NEPA Daya Daga cikin Yan matan ta Mike ta kunna TV



haka aka sake cika Wai ana kallo har baranda nidai abin daya isheni kawai na dauki wayata na fita waje,



" kitchen na wuce kazar jiya nake son hada miya dashi Amma kayan miyar jiya tayi kadan dole na shiga daki jakana na hannu mai kyau na dauka na fito waje budewa nayi na dau gudan dubu daya na aiki yaro a cikin Yan kallo kayan Miya Mai Dan yawa na Kara Masa da dubu biyu ya sayo harda kaza, don so nake na Kara na jiya bazai isaba ga yara a kofar.



Yaron na dawo mini da kayan Miya na fara aiki ba wance ta taimake ni Koh da jijjigen kayan Miya ne



shinkafa da miya na dafa Ina Gamawa na zuba a sabon kula Mai kyau na saka a basket da shukali da plt, na Koma dakin na bude freezer na dauki ruwan gora, na hada Masa a basket in na Ajiye, d'aid'ai yaron da Zai aika ya shigo na basa.



sauran abincin na zuba a babban faranti na hadawa yaran daban na sawa manyan daban daya ke nayi abincin da yawa sosai, Mika musu nayi ba kunya suka amsa gabaki daya Koh kwanukan Basu daga ba suka barsa a Inda suka ci sun batamin daki da datti sosai,



na ibi nawa na zauna a baranda kan darduma nayi Bismillah na fara ci ban tashi agunba saiga wani yaro ya shigo da sallama amsa Masa nayi, "waalaikumu salam"ya gaidani, "amsa wa nayi don naji dadin gaidani da yayi kaf yaran gidan da suka shigo ba Wanda ya gaidani Koh sallama babu,



Wai inji inji MAKAHO Mai mangoro aban abinci,



Wani Takaici ne ya kamani Wai sunan sama da MAKAHO ake kira "shap wallahih bazaiyu ba watoh nima haka za'a na kwatantani da MATAR MAKAHO Ina bazaiyu ba" duk Araina nake zancen nan.



Mikewa nayi na dauko masa basket in, basa nayi ya wuce



azahar yayi Amma kaf yaran gidan ba Wanda yayi Haraman Sallah Nima bance musu kome ba, na mike na dauro Alwala na koma dakin Hijab na dauka na fitoh waje nayi sallah na kwanta a sallayan Ina Danna waya,



Mutane Basu bar mini kofa ba har na Gama Tuwon dare na kwashe sukaci tukun suka fara watsewa daya bayan daya. Har suka watse suna fita na share dakina na goge, dakin Yayi kaca kaca sosai chanja zanin gado nayi yara sun kakama mini na jikin gadon da hannu yayi daud'a na fesa Turarukan daki na wanke dakalin kafun naji kofar yamin dama daman shekan iska Mai Dadi, wanka na shiga a gurguje nayi alwala na fada dakin na shirya nazo daukan turare Naga an min satan Mai Harda turare,



Raina ya kara baci don na tsani mutun ya dauki abuna ban basa ba, na kudurta Araina bazan sake Basu wannan fuskan ba tunda basuda mutunci gobe ba shegen da zai shigarmin kofa=ØÞ( tab kofarki Koh na makaho) Kaya nasa na jona wayata a cherge da laptop duka,



**na koma gefen gado na zauna



tunani na shiga yi lallai rayuwa ba tabbas yau Koh mutun daya daga cikin dangina Koh kawaye, babu Wanda yazo. watoh tunda talaka na aura kenan,?



alhalin duk wance tayi aure zuwa ake washe gari kallon gida da masu sallaman Amarya, a ranan. Amma ni ba Wanda yazo kallon daki ma bare sallama uhmm,



Karfe biyar da rabi MAKAHO ya dawo gida da kwandon abinci a hannu sai sandar jagoransa da lalube yakai kulan kitchen ya aje, wanka yayi ya fada dakin Yana shiga na fita na basa waje ya shirya,



Tana fita ya lalube Ghana must go insa ya dauki Kaya yasa ya fitoh waji lalube yayi ya dauki buta ya Kama alwala. ya wuce masallaci,don har an Tada sallah,



**lokacin Nima sallah na Tayar ,Bai dawo ba sai da ya hada da isha'i Tukun ya dawo,



*** abinci na zuba Masa

***na Koma Kan gado na zauna TV na kunna na kamo Tashar Arewa 24 Ana cikin Shirin kaddaran rayuwa. bayan ya Gama cin abincin, kwanukan ya dauka yakai kitchen hade da wanke hannu ya Sha ruwan Randa, ya shigo dakin,



cikin lalube ya lalubo kujira ya zauna a hankali cikin magana Mai sanyi yace nagode da abinci yayi Dadi sosai Allah ya biya." Amin" nace hankalina nakan TV,



jawo laidar da ya shigo da ita baka yayi ya fitar da sabulu da omo. sai wata laidar mangoron yako, ya Miko mini ta inda yake tsammanin saitin nake,



Cikin sanyin jiki da zullumin zata Amsa kuwa?



Yace ga mangoro ba yawa



***ban gwatselesa ba na karba na mike naje na bude firij na aje.



fita waje yayi, ya hada kayansa daya jika a ban daki da safe da Wanda ya cire dazun ya wanke ya shanya ya sake dawowa dakin yayi cikin magana d'ari..d'ari yace Koh Zaki kawo kayanki Mai datti na wanke miki,



***cikin mamaki nake kallonsa Wai ya wanke mini Kaya, lallai da wani idon Zan basa Kayana na fada a Raina, Amma a zahiri nace "ah ah na gode Zan bada wanki inya taru" baice kome ba ya lalube kujira ya zauna kawai yayi shuru ya kurawa TV da yake aiki ido kamar Mai kallo,



***abin har yaso bani dariya Amma na maze. muna zaune har goma, bacci na faraji,

mikewa nayi na chanja kaya zuwa na bacci, kashe TV da glop nayi na Kara gudun fanka zuwa 3 Addu'a bacci nayi na shafa na kwanta,



a hankali ya Tashi yaje ya rufe kofar duk Ina jinsa dawowa yayi kwanta, kwanta a kujira addu'an bacci yayi shima ya shafa.



**Nima gyara kwanciya nayi,

Tun daga jiya zuwa yau, a Takure nake Sam ban Saba kwana da namiji a daki ba, Amma ya zanye, dole na kwanta tunda daki D'aya ne bare na koresa falo.



Misalin karfe biyu na dare ya farka.........





My WhatsApp number

<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß

>ØÑÝ
>Ø¯Ý *MATAR MAKAHO* =ØhÜ
>Ø¯Ý *

~ Na ~



<ØCß *Rukayya Ibrahim* <ØCß



('Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za'a ga mistake Koh typing error Amin afuwa =ØLÜ

Free book>Ø'Ý



Page 5þã

Dan a irin lokacin da yake tashi sallolin dare,



mikewa yayi ya riga ya gane ma'ajiyin Randa da buta fita yayi a dakin alwala ya daura ya dawo dakin,ya tada sallah sai uku ya koma ya kwanta, Kiran farko na asuba ya farkar dashi, Addu'a tashi daga bacci yaye.



A hankali ya sauka a kujira cikin sanyi ya lalube gadon ya tsaya a bakin don bazai iyya Hawa ba kar a maimaita irin na jiya a hankali yake kiranta



**sumayya!! sumayya!! *



**A hankali na bude idanuna cikin bacci nace "naji habba" baice mini kome ba ya daga kafarsa a hankali da lalube ya bude dakin ya fita **Niko waya na laluba a gefen filo don dakin ba haske na kunna hasken ya haska dakin sauka nayi Nima nayi waje don d'auro Alwala, **fitana yayi daidai da kammala tasa alwalan mikewa yayi Yana laluben sandanrsa,Harna kammala alwala Bai gane sandar ba.



*Ina kammala alwala na shiga daki daukar wayata nayi na fitoh na haska kofar aiko Naga sandar Ashe faduwa yayi a kasa, dauka nayi na zungure sa da sandar a hannu *



da sauri ya mika hannunsa ya amsa cikin sanyi sanyin sa yace nagode,



* batare da nayi magana ba don takaice waini sumy nice yau da miji MAKAHO shap wannan ai abin kunya ne ma Wanda ya sanni ya gansa a matsayin mijina, Tabbas nayi Wasa da Damata a rayuwa, shiyasa Allah ya jarabce ni a lokacin da ban taba tsammani Koh tunanin hakan ba,



**Da sauri nayi istigifari na kauda tunanin a Raina



* Koh amsa Masa banyi ba nayi shege daki na tada sallah, Ina idarwa Qur'an na dauka cikin jakansa Mai kyau na bude,



*nayi azkar in safiya, dana sabayi kullun na mike nabi lfyn gado bacci ya dauke ni,



sai shidda da rabi ya shigo dakin da sallama hannunsa rike da bakar laida na kayan shaye da kayan miya Jin ba'a amsa ba ya lalube kujira ya zauna, numfashi Daya ji kasa kasa hakan ya tabbatar Masa ta koma bacci a hankali ya mike,waje ya fita da lalube ya Isa kitchen aje laidan yayi ,



shanyar kayansa ya dauko a igiya ya nade ya shigo dakin ya lalube Ghana must go in sa Daya aje a lungun kujira da firij yasaka kayan,ya dawo Kan kujiran ya kwanta a hankali wani irin bacci Mai Dadi ya sauke sa,



**Ban tashi ba, sai Takwas na safe shima ihu da ashariya na dandazon mutanen gidan Wanda Koh tantama banayi tambe ake, shiya farkar Dani,mikewa nayi sanye da kayan baccina Wanda na saka jiya da dare riga da wando Mai taushi sosai sai hulan bacci d'uka farare ne tas.



* da sauri na dirko daga Kan gado nafitoh dakin naje na rufe kofar shashen mu don nasha Alwashe yau bamai shigarmin kofa kallo Koh ganin daki bare naji yau da tambe aka tashi* =ØÞ (Anya ba tsoro ba kuwa?)





*Kitchen na wuce, ganin laidan kayan Miya a kasa,



* dauka nayi na bude kayan miyane su tarugu albasa da tattasai sai dayan kayan shaye ne yau harda Madara, na laida da bouviter, bread, sugar, da Lipton,



ruwa na zuba a kettle nasa Lipton, don yau muntashi da NEPA na jona a socket bude caton indomie, na kayan garana laida biyu na dauka manya shap shap na daura na dau kwai na soya cikin 40 minutes na Gama hada breakfast na Kama shara,



(' (tabbas aiki a wajen mace ribace babba duk kudin gidan ku duk mulki Koh gata ilimi da kyau in har mace Bata iyya girki ba gtoh Bata cika macen da za'a kira Tauraruwa ba Yan Mata a Kara bada himma karki xamantu baki da aiki sai adafa a baki kici ki kwanta kina Danna waya.koh makaranta kike zuwa at lest ki ware wasu lokutan a Rana kina Taya ma'aifiyarki,



aikin da kika tsana kina ga ana matsamiki ana bautar dake wallahih ribarta na zuwa don bakisan inda Allah zai kaiki ba)(' *shawarace*







**Tun sa'ilin da aka fara Yar Hali watoh dambe, a tsakar gidansu ya farka Amma Bai Mike ba har **fitanta da rufe kofar duk akan kunnensa duk yanaji Yana kwance ,



a hankali ya mike ya fitoh cikin sanyin halinsa da nutsuwa ya bude baki yake gai Dani,





**shuru na Masa naki amsawa *



baiyi fushi ba ya kara tambaya ta, Koh Zan Kama Miki wani aiki ? Abin nasa harda rainin wayyo kenan, Wai ya kamamin aiki? da wani idon Amma saina maze nace "wanke-wanke nakeso kamin" ba musu ya lalube sandarsa da takalminsa shinyayye ya saka

Da lalube harya lalube boket, ya dauka ruwa ya Iba a Randa ya aje a gefe da laluba har yakai cikin kitchen nidai Ina binsa da ido kawai, ganin garajen sa,



cikin tsawa nace "kaiiii aje kulanan abincine a ciki"



" tsaya na nuna maka kwanukan da zaka wanke"



" Wai baka ganewa ne?



Hala banda rashin gani ma? harda rashin basira? zaka dauki kula kaje da nauye basiranka bazai baka abincine a ciki ba zaka zungumu??



Kala baice mini ba ya ajiye kawai ya jingina a gefen kitchen ya tsaya,



Zuwa nayi na dauki kwanukan nakai masa gefe na hada ruwan kunfa na aje kwando da kujira na tsaya agefe cikin masifa masifa nace gashinan Bismillah sai kazo ka wanke jiki a sanyaye yazo da lalube harya zauna Niko Ina saye a gefe ina ganin ikon Allah wanke kwanuka yake Kamar Mai ido tas suke fita Yana kifewa Kai Koh Mai ido albarka, mamakine y kamani Amma ban nuna Masa ba,



**Shara na kammala na gera daki na na jona kask'wan lantarki na zuba Turarukan wuta a dakin fita nayi Naga har yanzun Yana Kan wanke wanke



Kwanukan akwai Dan yawa na abincin jiya da yara sukaci ban samu na wanke ba Harda na dare,



*Wanka na shiga Ina fitowa na tarar ya kammala Yana zaune a kujiran tsugunne,



" Koh Mai ban shafa ba na zura kaya atamfa super Mai kyau siket da riga Mai k'wala da hannun roba* dinkin zamani



*abinci na zuba ina ci daidai lokacin shima wankan ya shiga yana fitowa wanka ya shigo dakin, Alhamdulillah Koh ba kome na Lura Yana da tsafta duk da bana rayawa a Raina Koh da Wasa zanyi rayuwar aure dashi Mai tsayi dole ya sake ni yaje ya nemi miskiniya irinsa Amma kafun lokacin bazan cutu da wari ba tunda Yana wanka ( lol=ØÞuhmm muje zuwa zakiyi bayani )



*Fita nayi na basa waje*



Kaya ya saka wani jimemmen t-shirt da wando jeas duk da tsofene Amma sunyi Masa kyau sosai ya laluben kujira yayi ya zauna,



Ina waje ban kulasa ba naci gaba da cin abinci na kammala zamana nayi A wajen naki basa abinci shi kuma Bai tambaye ni ba Danna waya nayitaye sai kusan goma na safe na iba Masa a plt da shaye a Kofi na shiga dakin na aje Masa na koma Kan gado na kwanta,



ya jawo plt in yayi Bismillah ya fara ci



Yana tsaka dacin abinci muka ji bugun kofar shashen mu mikewa yayi zaiji ya bude na dirko daka kan gado cikin fada fada nace "bazafa ka bude kofar nan ba don yau bamai shiga kofar nan ehen kaji na gaya maka don Naga alama Yan gidanku basuje islamiyya ba"



Baice mini kome ba ya koma ya zauna



Jin Mai bugun yaki barin kunne na ya huta,



hijab na dauka na zura na fita ,don gani wani isheshshine,



Bude kofar naye idona y sauka akan wata yarinya kyakkyawa sosai farace Mai Kama da MAKAHO sak banbancin ita mace Mai karancin shikaru 18 zuwa 19 she Kuma namiji ne sanye take cikin riga na kodadd'in shadda sai hijab wuyan duk ya sabule gashinta har ya leko ta gaban goshi,



*Tunda aka kawoni wanna kaddararerren gida ban ganta cikin yaran gidan da suka zo kofana ba,



Aunty Ina kwana tace



hanya na Bata cikin dakewa nace "lafiya shigo"



Shigowa tayi daidai lokacin shi kuma ya fitoh cikin dakin murmushe dauke a fuskarsa itama murmushin take da sauri tazo ta amshi kwanukan hannunsa hade da gaishe sa ya amsa,Yana tambayar ta ya su Goggo Aminar,



Ta basa amsa



Tace in nazo nace tana gaida Amarya,ta fada tana kallona



Amsa Mata nayi ba yabo ba fallasa "Ina amsawa"



Fita zaiyi hade da tambaya ta Koh akwai abinda za'a saya Kai tsaye nace "babu "sa Kai yaye ya fita hade da cewa Khadija in Zaki tafi ki biya ta guna, da toh ta amsa Masa



Nidai daki na wuce naje na kwanta sai da Naji fitarsa tukum na kwala Mata Kira " Khadija shigo daki Mana kina tsaye a waje" don haka kawai naji yarinyan ta kwantamin sosai a Rai duk da bansan Alakarsu ba amma nasan akwai alakar jini a tsakanin su,



Da sallama ta shigo dakin na amsa Mata tana kukarin zama a kasa nayi saurin cewa tahau kujira Amma Taki da kerta zauna, firij na bude na dauko mangoron jiya da yayanta ya kawo na hada Mata da drinks harda ruwa na aje mata hira take mini Kamar na saba da ganin akwai ta da surutu sosai tun Ina amsa Mata har bacci ya dauke ni,





Ban farka ba sai 1:30 na Rana shima kiraye kirayen sallane ya tashe ni sai a lokacin na tuna Ashe fa Ina da bakuwa,

A hankali na sauke idona akan kujiran da na barta akai da mamaki sai Naga wayam ba kome,



Sauka nayi a gadon na fita a dakin cike da mamaki nake bin kofar da kallo har idona ya sauka akanta cikin sabon mamaki ganin ta a cikin....................



Good morning fan's <Ø%ßþ



An gaishiku Yan free books=؃Ü<Øüß=؃Ü<Øüß=؃Ü<Øüß=؃Ü<Øüß



<Ø@ßMATAR MAKAHO FAN'S GROUP <Ø@ß

Naga comments naku naji Dadi Kuma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login