Showing 114001 words to 117000 words out of 122551 words

Chapter 39 - MATAR MAKAHO COMPLETE HAUSA NOVEL

07 Sep 2024

16754

jawa mutan masifa.



jin abinda mutumin da ya bangaje sumayya yace, yasa yaron da ya tarota ya taimaka mata ta zauna a bakin wani shago, da sauri ya nufi guy in, wanka masa mari yayi, ya cakumo wuyarsa cikin bacin rai yake magana, kai wani irin dabbane wawa kawai baka dubi halinda take ciki ba, ka tashi ka bangaje ta batare da ka dubi halinda zata shiga ba, kazo kana gayawa mutane maganar banza.



Hannu guy in ya d'aga zai rama marin sa, da sauri yaron daya taro sumayya ya kama hannunsa, wasa wasa fa dambe ya kaure a tsakanin su, yayinda sumayya ke gefe gabaki d'aya jikin ta rawa yake, don ita d'auka tayi ma yau innan dai sai abinda Allah yayi.



Da sauri jama'a suka shiga raba fad'ar, don gudun kada abin yakai ga yan sanda kuma ya zama babban magana, daker aka samu yaron ya hakura, guy in ya tafi, da sauri ya dawo wajen da sumayya ke zaune, sannu Aunty badai binda ke damunki koh?



Girgiza kai sumayya tayi a hankali, tana kallon laila data gaji da jiranta tabiyo baya, don ita bata ga abinda ya faru ba.



Kalamu-wahid!!!!!Daga nesa aka kwalama yaron kira da sauri ya juya, yana kallon mai kiran nasa,Na'am babayo ina zuwa pls.



Babayo dake tinkaro inda su sumayya suke, bakine kamar Kalamu-wahid sai dai kalamu ya fisa kyau, duk da shima ba tayan baya bane, kuma babayo nada zanen kanuri a fuskar sa, sabanin kalamu da baida zane sam.



Ke sumayya lafiya sayan mangoron ne, kika zo kika zauna?bata jira Amsar sumayya ba ta kalli kalamu, malam lafiya ka saya mata a kai?



Sumayya ce ta bata amsa, "Lafiya laila taimako na yayi, saura kad'an yau nasha kasa"



Sumayya dakin kashe kanki, shiyasa nake ta miki magana Ki tsaya na sayo miki, amma kememmen kika ki saurarata.



Yi hakuri Aunty laila ba laifinta bane, kalamu yace, yana tattara wa sumayya jakanta daya watse a kasa.



Kalamu lafiya mayya tsayar da kai kuma, ka barni a mota tun d'azun?



Yi hakuri babayo bara mu sauke wa'innan a gida.



"Ah ah ka bari kawai mun tare taxi harna saka kayana a ciki"



Ah ah aunty sumayya muje dai na kaiku, kuyi hakuri wallahi da zuciya d'aya nake son d'aukarku.



Shuru sumayya tayi tana kallon yaron da mamaki, bazai wuce shekara 19 zuwa da 20 ba, daga hadu d'aya har ya shiga jikinta ga Aunty sama Aunty kasa"toh shikenan sai muje ku d'auko kayan mu dake mota"



Ok toh muje ku shiga mota gashi shan, yace yana nuna wani had'aden mota dake tsallaken titi, babu musu sumayya ta mike da sauri ya karbi jakan nata, laila na binsu a baya sukayi wajen motar, baya sumayya da laila suka shiga, yayinda babayo da kalamu-wahid suke gaba, babayo ne mai tukawa kalamu na gefe, da nuniya sumayya suka nuna musu taxi in, tattara mata kayanta sukayi shida babayo suka zuba a boot, wasu kuma a baya don kayan yawane dashi, shiga sukayi hade da tambayar su unguwan da suke.



Da mamaki kalamu yace laaa ai unguwan mu d'aya daku wallahi, jin unguwar da laila tace.



Laila ce ta kallesa Au da gaske, ku a wani gida kuke kenan?



Muna kusa da gidan hayan Malam sale uba?



"Kai aimu a gidan hayan muke "sumayya ta basa Amsa.



Babayo ne yace, Ah lallai kam rashin ziyara ne babu, ace unguwan ku d'aya har ginin gidan ku a manne bakusan juna ba.



"Gaskiya kam"kawai sumayya tace tayi shuru ganin sun iso get na gidan su, sauka sukayi kalamu ya sauke musu kayansu, tare da bawa babayo umurni daya shiga gida, shi zai shigar wa da sumayya kaya, duk yanda sumayya ta hanasa kiyayi, haka ya kinkimi kaya shida laila sukayi cikin gidan su sumayya, yayinda ita kuma ke binsu a baya.



Khadija dake zaune a falo tana cin abinci, sannan ga laptop a cinyarta tana kallo,sai munira da kaninta a gefe, suma tasa musu abinci daban a plate, da sauri ta d'ago jin muryan namiji na sallama a bakin falon su, kafun ma ta Amsa har an turo kofar an shiga.



Laa Aunty kun dawo?sai yanzu, da sauri yaran laila suka mike sukayi wajen mamansu suna mata oyoyo.



Sai yanzu khadija sayayyar ce da yawa, yauwa kalamu aje mana kayan a falo.



Aje kayan kalamu yayi, laila ma ta aje nata, juyawa yayi zai fita yana musu sallama.



"Ah ah kalamu dawo ka zauna, ke khadija kawo masa sallaya, falon namu Empty ne ba kome sai katifa"



Kai Aunty dama kin bari wallahi nagode



Da sauri sumayya tace"Ah ah kalamu kadai zauna ta kawo maka abinci kaci don Allah karkace ah ah"



Gaskiya ne kalamu ka zauna mana kaci abinci, nima khadija ibomin abincin nan yunwa nakeji, kinsan na fita gida banci kome ba, laila tace tana nufar kitchen in sumayya, karban abincin kawai tayi a plate ta fita.



Zama kalamu yayi yayinda sumayya ta wuce d'aki abinta, zata watsa ruwa sosai taji dadin girkin da khadija tayi, don ita tama manta tace zata musu take Away.



Kawowa kalamu Abinci khadija tayi da ruwa ta aje masa a gaba, komawa tayi inda ta tashi taci gaba da cin abincin ta, shukali kalamu yasa ya ibi abinci sai kuma ya kalli khadija da mamaki ganin tunda yazo falon koh gaidashi batayi ba, sai wani cin magani take kamar bata ga bako ba, damuwar ka da bawa kenan bai iyya samun yanci ba saiya zage.



Jin abinda yace yasa khadija gane kanuri ne, cikin dariya tace eh tsabar rashin yancin wasu koh gangan tarihi basu dashi a fada.



Kutt ke wallahi karyane kune bayi, kauyawa in banda kauyanci mutun yaga bako yaki gaidashi?



Baki ma ai iri-iri ne, akwai kalan gaisuwa akwai kalan kori.



Da mamaki yake kallon khadija, kutturu amma yarinyar nan ta iyya bakar magana, waike anya ba makarantan harshe kike ba?



Ah ah na kutare nake



Shuru kalamu yayi jin abinda tace masa, yaci gaba dacin abincin sa.



"Waini maganar me nake jine tun d'azun ina bathroom"?



Wallahi Aunty bakon kine da iyayi, harda zai gayawa fulani magana.



"Ke kuma sai kikayi me"?



Saina fad'a masa ba sugari, mudasu waza'a kira bayi.



Jin abinda khadija tace da sauri kalamu yace, kune dai bayin.



Wallahi badai muba.



"ke khadija ya isa haka, banason zagewa da yawa kinsan dai ummina kanuri ce koh?toh ki sassauta musu"



Dariya kalamu ya sake, shikenan Allah ya kamaku duka



Itama sumayyar dariya tayi," babu wani Allah ya kamamu nadai kwace ka kawai yaro"



Kai Aunty yaro kuma a gaban wannan yar rainin wayon?



kai wallahi ya isheka karka sake cemin yar rainin wayo, ni bance maka ba sai kai zaka fad'a mini.



Kunga ni surutun nan ya isheni haka, ibo mini abinci naci yunwa nake ji, habba kedai kullum fad'a da mutane ga kalamu yazo zai karbi Ammar.



Kai Aunty Allah suke shiga idona, tana maganar tana shiga kitchen



Zama sumayya tayi akan katifar ta, bayan khadija ta kawo mata abinci, cin abinta take koh a jikinta ta rasa me yasa ta sake jiki da kalamu sai hiransu suke da khadija, tana sa musu baki jifa-jifa in taga khadija na k'wararsa a magana, don daga gani ba sabo yayi da surutu ba, kawai yau saka kansa yayi, har suka gama cin abinci kalamu bai tafi ba sai da azahar yayi ya musu sallama ya wuce.



Yana fita bayan su sumayya sunyi sallah kayan sayayyan tasa khadija d'aukowa suka duduba, sosai khadija tayita yaba kayan don yayi matikar kawatuwa, kuma an kashe kudi kam ba karya.



Washe gari da safe principal insu khadija ya kira sumayya, akan baza'a zo d'aukar khadija ba, saboda drivern school buss insu ba lafiya, dole tasa yau khadija da kanta zata makaranta dayake yanzun tana da kudi, karywa kawai tayi tama sumayya sallama ta fita.



Takai minutes 20 a tsaye bata samu abun hawa ba, tun 7:00 ta fitoh gashi yanzun har 7:20 bata samu mota ba, gabaki d'aya ranta ya gama baci, gashi suna jarabawan second team, gani kawai tayi mota yayi packing a gaban ta, da sauri ta d'ago tana kallon wa'inda ke cikin motar, kalamu dake sanye da fararen uniform na nurses, yana zaune a kusa dame tuki, sai students na makarantan su, dake baya su biyune namiji da mace, dukansu fuskar su d'auke da zanen kanuri,sabanin kalamu da babu, murmushi tayi ta gaida mai tukin.



Amsawa yayi.



ba tare da ta kalli kalamu sau biyu ba, tajuya zata ci gaba da tafiyar ta.



In ance ma mutum bakauye yaji haushi, Amma bazai daina kauyancin ba, kinga mun tsaya a gaban ki, aikin san d'aukar ki zamuyi shine zaki wani juya kamar ana sarrafaki da remote.



Ba karamin haushi khadija taji ba, jin rashin mutunci da kalamu ya mata.



Kiyi hakuri kanwa ta, kizo mu wuce munyi late karki kulasa, mai tukin yace.



Babu wani karta kulani babayo, gaskiya dai na fad'a kalamu yace yana danna wayar sa kamar bashi yayi maganar ba.



Wallahi badon ana exam ba, yau da babu abinda zaisa taje makarantar ma gabaki d'aya, bare hawa motar su, amma ba yanda zatayi haka ta bude back seat ta shiga.



Kalamu suka fara saukewa a school of nurse, kafun aka sauke su khadija, babayo ya wuce aiki.



Wasa wasa shakuwa ya fara shiga tsakanin khadija da kalamu-wahid a boye don a gaban sumayya kam fad'a suke, don yanzun duk lokacin da yaso yake zuwa kofar sumayya, suyi hira ya tafi, duk da sumayya bata kawo kome a ranta ba, ganin cewa in yazo har falo yake shiga, kuma in suka zauna da khadija ma fad'a suke akai-akai.



Kamar yau khadija sun gama jarabawa tun Friday, zaune take a falo ita da sumayya, sai ga Kalamu yayi sallama a kofar falon su mikewa khadija tayi ta mikawa sumayya hijab nata kafun suka basa izinin shigowa, sosai sukasha hira yauma, dayazo tafiya bayan sunyi sallama da sumayya tsayawa yayi a waje get, kamar minutes 5 da fitar sa khadija ta mike zata fita a falon.



"Ina zaki kuma khadija"?



Aunty zan tattaro shanya nane naga garin da hadiri?



"Ah ah kidai tattaro shanyar, Amma garin nan kam ba hadiri bayan yanzun damuna ta wuce"



Jin Abinda sumayya tace yasa khadija sunkuyar da kai, ta fice a falon da sauri ta nufi igiya ta dauko hijab nata, tayi get, tana bude get in aiko kamar yanda ta zata inne Kalamu na tsaye, kai lafiya tun a falo sai ketket-ta mini ido kake?



Wallahi khadija magana nake so nayi dake daman.



Da mamaki da kallesa au yau kuma kunyar Aunty kake ji kome?



Ah ah ba haka bane kinsan next week zamu fara exam? so bazan samu daman shigowa ba shiyasa na kawo miki wannan, yace yana mika mata bakin laidar dake hannunsa.



Ba musu khadija ta karba hade da tambayar sa menene a ciki?



Wayace harda sim, na miki register sai muna gaisawa daidai na samu zama, don zan kwana biyu gaskiya bazan leko ba?



Kaga karbi abinka wallahi babu ruwana?



Kamar yaya ba ruwanki khadija?



Kamar yanda nace maka, so kake Aunty taga rashin kyauta wata gareta? tayi mini dukkan kyautatawa baika mata na nuna mata rashin godiyan Allah ba.



Yanzun khadija karbar wayar ce rashin godiyan Allah?



Kayi hakuri Amma bazan iyya karba ba sai dai in zaka kaiwa Aunty da kanka ka bata?



Babu damuwa muje na batan.



Ah ah wallahi ka fara zuwa dai kaikad'ai kar tace mun had'a baki, tana maganar ta koma cikin compound in tana tattara shanyar ta.



Ba musu Kalamu ya koma kofar sumayya, da mamaki take tambayar sa lafiya kuwa ya dawo?bayani ya mata akan waya ya baiwa khadija taki karba shine ya kawo mata koh khadijan zata yarda ta karba?



Da mamaki sumayya ta karbi wayar ta bude, wayane sumsung Galaxy S9+" Kalamu nima karan kaina nayi tunanin saya wa khadija waya, Amma nafi son saita kammala secondary ta mallaki hankalin kanta"



Aunty yanzun ma khadija tayi hankali fa, shekara 19 take nema wasu a shekarun tan nan ma, suna jami'a don Allah aunty ki barta ta rike wannan in?



"Au haka ta fad'a maka kenan bazan barta ta rike ba, kuka had'a baki kazo waje na koh"?



Ah ah aunty kawai dai na fahimci khadija nada biyayya ne.



"Shikenan Allah ya sanya Albarka, harda shekarunta ta fad'a maka kenan"?



Ameen Aunty Amma nidai kiyastawa nayi bata fad'a mini ba, yace cikin murna ya fita ganin Aunty ta karbi wayar, yana fita a falo yakusa cin karo da khadija dake makale a kofar falo tana sauraron su, cikin murna tace Aunty ta yarda?



Kai kawai ya d'aga mata ya wuce get ya fita, Khadija kam kasa komawa cikin falon tayi, taci gaba da tsayuwa a bakin kofa.



Sumayya dake jiran Khadija ta shigo, shuru shuru bata shigo ba, yasata mikewa fuska a had'e ta nufi kofar falon.......



*************

Jikin muhammad sai rawa yake yaje ya karbo wasu kayan, ya karbo sabon shayi, ya sake shigowa falon wannan karon tsohowar ce da yara biyun, wanda d'ayan bai manta sunan taba muhibbat sai karamar , gaida tsohowar yayi ya wuce falon sarki, Wannan karo sarkin baya falo yana ciki, aje masa shayin yayi a table ya tsaya a gefe, kusan 30 minutes kafun ya fitoh yauma kamar kullum fuska a rufe,, a take gaban Al'ameen ya soma bugawa da karfin gaske, zama sarkin yayi a hankali akan d'aya daga cikin kujerun falon, da sauri Al'ameen ya dukar da kansa a hankali ya matso da table in ya siyaye masa shayi hade da gaidashi, hannu kawai sarki ya d'aga masa ba tare da yayi magana ba.



Yana gama had'a shayin, ya fita a falon, direct kitchen in shayi ya koma, yama abokan aikin sa sallama duk da lokacin tashi baiyi ba, ya kama hanyar gida, cikin hanzari yake tafiya har ya iso bakin titi tare abin hawa yayi.



Yana isa gidan cikin hanzari ya bude kofa bakin sa d'auke da sallama, baikara saba sallamar ya makale masa a wuya, ganin baba tsaye akan kafafunsa...........



('Ruqeenjalal('



<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß

>ØÑÝ
>Ø¯Ý *MATAR MAKAHO* =ØhÜ
>دÝ

~ Na ~



<ØCß *Rukayya* *Ibrahim* <ØCß



Page8ã 6ã &8ã 7ã

Babane tsaye akan kafarsa yana gyara yayin dake kan bukkar sa, da mamaki Al'ameen yace ikon Allah baba menake ganin nan?



Da sauri baba ya juya da mamakin ganin Muhammad ya dawo daidai lokacin nan, Alhalin ba lokacin ake tashi aiki ba, lafiya ka dawo yanzun?



Kai zan tambaya dai baba, na ganka tsaye akan kafafunka, kaida ka karye?



Zoka zauna muhammad muyi magana?yace yana zama akan taburma.



Ba musu Al'ameen ya zauna a kusa da baban.



Muhammad ina fatan kaga abinda nake so ka gani koh?



Da sauri Al'ameen ya warware rawanin sa, kamar ya baba kuma me kakeso na gani?



Muhammad Abinda yasani yin haka badon kome bane, illah don naga kaje da kanka gidan sarkin nan, tunda na ganka jikina ya bani wani abu, kamar dake tsakanin ka da muhibbat da muwaddat ya baci sosai, haka sarki ma duk da rabona dana ga fuskar sa, bazan iyya tuna ranan ba Saboda dadewar da nayi bana gani, Amma fa ka sani nasan sarki tunkan yahau mulki, yanda kaga fuskar ka, haka fuskar sa yake sai dai ka nuna masa yaranta?



Me kake nufi baba bangane ba, wai sarkin da naga fuskar sa a rufe kana nufin yana kama da yara biyu dana gani innan?



Kwarai muhammad duk da dai akan samu mutum, ya samu mai kamar sa a duniya Amma kaman ku dasu Akwai alamun jini.



Baba ni bani da kowa a nijar fa bansan kowa a nan ba.



Toh Amma kaman nin ku, ku hudun nan yayi yawa muhammad?



Bamu hudu bane mu biyar ne, da kanwa ta.



Muhammad niba yaro bane, Amma tunda kace haka shikenan, amma dai zaka cigaba da zuwa aiki har lokacin da na yanke akan zancen kafata, tunda ba kariyar gaske nayi ba baikamata na koma ba yanzun?



Shikenan baba zan cigaba da zuwan,har randa zaka koma aikin, ina su gidado ne tunda na shigo ban gansu ba?



Sunje kasuwa yi mana sayayyan kayan abinci.



Tashi muhammad yayi ya ibi ruwa ya shiga band'aki wanka yayi ya shige d'aki ya kwanta, tunanin duniya ya dame sa, duk sanda ya lumshe idanunsa yaran nan yake gani wanda baba yace masa muwaddat da muhibbat wai suna kama da sarki, kenan suna kama dashi, kai shikam bai gane kan Al'amarin nan ba, wani zuciyar na kawo masa wani tunani, amma kokarin tunkude sa yake don yasan abune da kamar wuya.



Yana kwance har gidado da badaru suka dawo kasuwa, yana jinsu suna ta girki da jido ruwa Amma bai koh fita ba.



Har suka kammala aikin dare abinka da gidan gauraye, bayan sunci abinci suka wuce masallaci.



Daren nan sukutum muhammad baiyi bacci ba, sai kusan asuba bacci ya d'auke sa.



Washe gari muhammad yaje aiki kamar jiya bayan sun gama shayin safe, yaukam had'a masa akayi da yawa a tire, ya wuce dashi falon , da sallama ya tura kofar falon ba kowa a falon sai kamshin turare dake tashi aka tsakar falon, wucewa falon maimartaba yayi a hankali ya tura kofar da sallama.



Sarauniya ce cikin Alkimba a zaune akan kujera hannunta dauke da kumshen lalle ja abinka da farar fata sosai yayi kyau, sai sarki dake kujeran sa na special kamar kullum fuskar sa a rufe, sai muwaddat da muhibbat dake zaune akasan kushin sai tsohowar nan dake zaune a kujera tana magana da nabila, ke nabila nafa fahimci babu wanda ya bata ku sai lawiza(sarauniya) ace mutum ya dage sai yayi turanci abinda bama amfani muke dashi anan ba?



Kai mahmah karfa ki manta a abroad nake karatu kuma ashan basu san wani abu wai French koh buzanci ba, da turanci kawai ake Amfani kinga kuma nan gaba muwaddat da muhibbat suna gama secondary suma chan zasu, shiyasa nake saba musu tun a gida mahmah, nabila tace.



Murmushi sarauniya lawiza tayi tana kallon mijinta da kwata kwata hankalinsa baya wajen su, hankinsa bama a wajen su yake ba, hawaye ne ya cika mata ido, ta rasa yaushe ne ita da yaranta zasu samu lokacin sa? abu tsawon shekaru abu d'aya, tun yaransa na kanana suke korafi har yanzun sun girma har yabi jikinsu, Abban muwaddat......bata karasa ba sukaji sallamar muhammad.



Amsa masa mahmah tayi, ya karaso cikin falon yana gaidasu da turanci lawiza da su muwaddat ne suka amsa sarki kam koh d'ago kansa baiyi ba bare Amsa gaisuwa, mahmah kam baki ta kama sai kuma tayi shuru

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login