Showing 57001 words to 60000 words out of 122551 words

Chapter 20 - MATAR MAKAHO COMPLETE HAUSA NOVEL

07 Sep 2024

16746

Yana samun na abinci da biyawa Khadija D'an hidindimun makaranta





Zancen kamila Kam baiyi fushi ba duk da Bata Masa ta'aziyar D'an uwansa ba haka ya sake Kama Khadija don lokacin ta d'anye wayo sukaje gidansu kamila.



Kamila ce tsaye da kawayen ta a waje tare da wasu samari uku A bakin mota



Al'ameen suna Isa kofar gidansu kamila,yaji hayaniyar maganar mutane Kamar harda ta kamila hakan yasa cikin murna yau dai zasu gana, tunda ya jima Yana zuwa baya samun ganin ta



Da saurinsa yace wa Khadija suye wajen da Yake jin muryan mutane



Ba musu Khadija na rike da sandar sa suka nufi wajen, Assalamu alaikum



Waalaikumu salam D'aya daga cikin samarin ya Amsa Masa



Ina wunin ku, Al'ameen ya gaidasu



Lafiya samarin suka amsa d'ayan ya zare kudi a Aljuhunsa Yana mikawa Khadija,ungo Yan mata



Khadija Kam kin karba tayi don bata Saba bara ba koma yayanta ya hanata roko Koh karban abin hannun Wanda Bata sani ba



Karba Mana yarinya D'aya daga cikin kawayen kamila ta fad'a don Bata San Al'ameen ba



Yayana ya hanani karban kudin Wanda ban sani ba, Khadija ta fad'a musu tana noke kafad'a



Da mamaki samarin ke kallon su Al'ameen mutum ya fitoh bara abasa yace bazai karba ba,toh lfy meya kawo ku gun mu inba bara ba



Am don Allah Ina da tambaya ne? Al'ameen yace



Allah yasa mun sani



Yauwa Kamar muryan kamila nakeji d'azun a cikin ku?



Eh ganinan lfy?kamila ta basa Amsa



Lafiya kamila in ba damuwa inason magana dake ne



Ina jinka,tace tana Masa kallon banza



Don Allah mu koma gefe



Kai MAKAHO akan me zaku kebe da matar da Zan aura Kai asuwa d'aya daga cikin samarin yace



Wani abune ya cake zuciyar Al'ameen shikenan kamilar ma ya rasata shikam yaushe zai samu farin ciki ne duk mai kokarin faranta Masa wata Rana gudu yake ya barsa



Kamila aure zakiyi?yace Yana kokarin faduwa tsaban shock



Eh aure zanyi Koh kana da matsala da hakan ne



Kamila Ina Alkawarin mu?



Alkawari kana nufin na aure ka kana MAKAHO Kuma talaka da wanne zanji da ciyar dakai Koh da ciyar da yaranka Koh da maka jakora Koh d'awainiya?Zan dai iyya auren ka a Talaka Amma banda kana MAKAHO kam.



Sosai zuciyar Al'ameen ta tsinke



Dariya matasan da Y'an Matan suka sake na shekeyanci,Kai kamila bakida mutunci wallahi = soyayya ce fa saikuje kusha love da lalube D'aya daga cin Yan matan ta fad'a tana dariya



Budurwar da ke gefe sanye da hijab itace kad'ai Bata ma Al'ameen tozarci ba



Kama hannun Khadija taye hade tacewa Al'ameen su tafe



A hankali Al'ameen ke tafiya Kamar k'wai ya fashe Masa a ciki Bai d'auka Koh nakasa zaisa kamila gudunsa ba Koda kowa zai gujesa



Suna sharan kwanan nayin, kawar kamila ta dube Al'ameen,kaga bawan Allah don Allah Ina Mai rokon alfarma a gareka shine ka rabu da kamila Koda itace autar Mata ka barta duniyace ai Koda zata rabu dakai bada tuzarci Koh kushen halitta ba Amma ita Bata dube hakan ba y

Ta wulakanta ka kaima ka barta bari na har Abada,Kaye hakuri Allah Yana tare da musu hakure.



Insha Allah baiwar Allah na rabu da kamila Nima na hakura da ita Allah ya had'a kowa da rabonsa,



Ameen ta basa amsa tana Mai komawa layinsu tabarsa tsaye da Khadija



Wannan shine Ranar da Al'ameen ya fita a Rayuwan kamila.



Bayan wasu shekaru karatu ya fara zama sai da kudi, a hakan yake ta faman ganin Khadija tayi karatu Koh ba kome zata tallah fawa kanta, Amma Ina kudi ya gagara don yanzun mangoron ma sai a hankali Bai wuce a Rana yayi cinikin 200 Koh kasa da hakan. Gashi a ciki Kuma yake ciwa cikinsa hakan yasa karatun Khadija tsayawa iyya Junior.



*An dawo labari* ...........

Khadija Kam kuka take kaman me,haka ma Sumayya Allah sarki Ashe haka rayuwar wa'innan bayin Allah yake, tasu kaddarar kenan,a cikin Yan watanni nan da mahaifinta ya juya mata baya taji kamar tafi kowa matsala,ashe itakam ma in an had'a kaddarar ta dana Muhammad nata ba kome bane tunda har tayi karatu ta tashi cikin kudi da lfyr ta Amma shifa ga maraici ga kuncin rayuwa da Talauci.



D'aga ido tayi tana kallon Al'ameen dake zaune a kujera fuska tayi ja"yayan khadija baka bani lbrn auren mu ba"?ta tambaye sa



Khadija tashi ki tafi kinji kukan ya isa haka, Al'ameen yace batare da ya amsawa Sumayya tambayar taba



Mikewa Khadija tayi zata fita a d'akin cikin kuka abin g'wanin tausaye"Khadija"Sumayya ta Kira sunan ta



Na'am Aunty



"Khadija kiyi hakuri kome na rayuwan duniya Mai karewane Sannan Yana da iyyaka kinji"?



Toh Aunty tace tana share hawayenta



"Ki d'auki doyan nan ki tafi dashi gobe da safe sauki kawo mini ducuments naki kinji Khadija"



Toh Aunty kawai tace tana d'auki laidan doyan ta fita



"Yayan khadija na tambaye ka shine kaci no face"



Sumayya nagaji wallahih ki barni nad'an huta Mana waima me zakiye da ducuments in Khadija ne?



"Oho ba'a sani ba Ina maka magana kana tambaya ta Nima naki fad'an"



Shuru ya Mata tare da lumshe idanunsa



Itakam ganin ya Mata shuru tasan dai akwai abinda bayason fad'a matane,tashi taye a hankali ta Isa garesa faduwa tayi a kansa da gangan



Washhhh yace yana gyara Mata kwanciya



"Don Allah ka fad'amin Mana"



Kinga Sumayya nifa banason na fad'a Miki abinda zaizo Yana d'aga Miki hankali.



"Allah bazan d'aga hankalina ba kawai ka fad'a mini"



Ok toh shikenan Amma sai da dare Zan fad'a Miki



"Gaskiya Nina gaji da abinda kake minin nan wani irin sai dare Kuma Wannan ai Jan Raine"



Banace Zan fad'a ba ki barni Mana zuwa Daren in ban fad'a Miki ba saiki Tuhume ni



"Uhmm toh yanzun me zakayi"?



Bacci,ya Amsa mata



"Bacci a hakan"?



Eh.....



Tashi Sumayya tayi taje ta d'aura abincin dare ta barsa a d'akin



Bayan fitarta sosai yake tunani akan ya fad'a matane Koh karya fad'a Mata karshe dai ya yanke shawaran ya fad'a matan kawai



Bayan isha'i Sumayya ce da Al'ameen kwance akan gado Sumayya taye matashe da cinyar Al'ameen sunfi minutes 20 a haka,tunda sukaci abincin dare sukayi sallah, suke a haka Amma Al'ameen baice mata kome akan labarin ba abin sosai ya dame ta Amma ta danne tunda yace zai fad'a zata barsa ya fad'an da kansa.



Sumayya!!ya Kira sunanta Yana Mai shafa gashin kanta mai tsawo da kamshi



"Na'am"ta amsa Masa



Sumayya banso fad'a Miki dalilin auren mu ga ganin cewa kece kikafi kowa sanin hakikanin gaskiya don bana tunanin har yanzun ana cikin zamanin da za'a ma mace aure batare da tasan miji Koh miji ya santa ba.



"Me kake nufi"? Sumayya ta tambaye sa fuskar ta a hade Jin abinda yake fad'a Mata



Yanzun masifa Zaki mini Koh Jin lbr zakiyi?



"Aiba labarin kake bani ba sukata kake"Sumayya tace,tana kokarin sauka a gadon



Sorry toh, yace Yana kamota



"Nikam ka sake ni "



Kin saketan yayi yana rungume da abarsa, naki sakin kin in kajimin mata fa



"Allah ni ka sakeni nace maka"tace tana kokarin xame kanta a jikinsa



Fushi kikayi ne Gimbiya?



" waye Gimbiyar"?



Sumayya mana.



"Gimbiyar wa"?



Al'ameen...



Uhmmm kawai tace bata kara magana ba



Kinga na miki Alkawari, zan fad'a miki gaskiyan abinda na sani akan auren mu?



"Nima nafasa ji yau sai gobe"ta fad'a tana mai sa hannu ta d'auko wayarta dake gefen filo, airp inda ke makale a jikin wayar ta manna a kanne



Sai magana yake baiji ta amsa masa ba hannu yasa yana tattaba ta, Gimbiya ina magana kin mini shuru



Duk da sumayya taji Al'ameen ya taba ta Amma taki koh sauraransa



Shikam gane fushi take yasa sa dagota sama daga jikinsa ya jefata gefen gadon



Ihu sumayya ta sake bawai zafi taji ba don laushin katifar dana blanket bazai bari taji zafi ba tsorata kawai tayi don bata tsammaci hakan ba" wayyo wuyana ya karye"



Nashiga uku sumayya inga wuyan da gaske kinji zafi dan Allah kiyi hakuri ban dauka zakiji zafi ba, yace yana matsowa kusa da ita



Sumayya kam langobewa tayi wai wuya ya bugu"wayyo wuyata shikenan ya kasheni jama'i



Don Allah kiyi shuru muga wuyan wallahi bada niya nayi ba



Sumayya kam kara lafewa tayi jin ya cicibeta ya daura a cinya kamar wata baby



Sannu sumayya koh muje asibiti ne?



"Nidai goyona nakeso kayi"ta karasa maganar da make murya



Jikinsa na rawa yace, toh... toh... hau, yana dukawa a kan gadon



"Nika d'agani bazan iyya tashi zaune ba"



Cicibar sumayya yayi ya goya haka ya ringa lalube yana zaga d'aki zuwa baranda da ita sai kusan 10:00 sumayya taji gyangyadi kafun tace masa, " ka kwantar da ni bacci nake ji"



Ai da sauri bawan Allah yayi d'aki da ita da lalube ya shimfid'ata a gadon duk ya gama gajiya ba kad'an ba shiyasa daya samu taye bacci ba karamin dadi yaji ba gudun fitina ma koh tabata bayyi ba a gefe ya kwanta yanata tunanin wuyan sumayya don harga Allah ya d'auka da gaske ne





Da asuba ma hakan take sashi tayi ya d'auketa har waje tayi alwala ya dawo da ita d'aki kafun ya tafi masallaci.



Misalin karfe 9:12 na safe Al'ameen ne ke bacci a d'aki bayan dawowar sa sallan asuba



Sumayya data gama aikinta a nitse tayi girki duka don bata tashesa ba saida ta gama harda wanka tayi kafun a Hankali tashigo d'akin wayanta ta d'auka ta danna play in waka ta kara volume, ta saka Eirps kunnen Al'ameen ta mannawa



Ai kam yana cikin baccinsa yaji abu tibbbtibb ga waka kamar a kwakwalwarsa, da sauri ya mike zaune hade da furta, innalilahi sumayya wuyank........sai kuma yayi shuru jin dariyan sumayy a kusa dashi



Hannu yasa sosai ya damkota kwantar da ita yayi a gefensa yahau kanta sosai yayi lamo yana daidaita bugun zuciyarsa har lokacin abin na kunnensa



"Wayyo menene haka"?



Shikam koh jinta bayayi, sai dad'a lumshe idonsa yake jin wakar da ke tashi a kunnensa sosai yatafi dashi



Da sauri sumayya ta zare eirps in jin sai magana take baya kulata



Da sauri ya bude ido, tare da kamo hannunta data cire masa abin kunnensa, mena cirewa? wakarfa bai kareba



"Inata magana kamin banxa badole na cire ba"



Toh mekike son na miki kenan guda daya? tunda jiya ma ai magana nake miki kika saka abinnan a kunnenki kika manna mini nima, duk wai akan maganar jiyanne kiketa fushi koh?



Shuru sumayya tayi



Dalilin auren mu.......

nidai bazance Miki nasan kome akan auren mu ba illah dai bazan manta ba wata Rana wani mutum yazo ya sameni agun sana'a ta yasai Mangoro ya tafi bayan kwana biyu Kuma sai gashi ya dawo Amma baifita a motarsa ba aika yaro yayi ya kirani nakai masa mangoro bayan naje ne yace na Shiga motarsa, Yana da magana Dani,ni kuma naji tsoro gudun kar Amaimaita na baya(Randa aka makantar dashi) shiyasa naki Shiga motar duk yanda yayi Dani ki nayi,karshe dai agun mukayi magana,Kamar haka



Ni sunana mamman Ina da yarinya Naga hankalinka da nutsuwarka shine nayi maka kwad'ayin Koh zaka Amince in baka auren ta?



Sosai naji mamaki nida bana gani ad'auki yar Mai mota sukutum a bani gani Talaka haka kawai sainaji Raina Bai Kama zancen ba, shiyasa nace Masa bana bukata batare da Kuma sauraransa ba nayi tafiya ta



Bayan sati D'aya kawai bappa sulaiman yakirani Wai za'a mini aure,sosai abin yaban mamaki za'a mini aure kuma kamar mace,bappa aure Kuma Kamar Yaya?na tambaye sa



Kamar yanda kaji bappa sulaiman ya bani Amsa



Duk Azana Yar gidan nan za'a bani Amma bappa yace Wai Yar shugaba family ne tunda naji haka kawai nasan lallai wannan aure mai dalili ne ba auren Angani anaso ba,da farko naso nunawa bappa illan auren nan Amma ya murza ido yace sai anyi daga karshe ma cemin Yaya Wai yarinyar tanada Wanda zata aura matsala aka samu bayan anyi test shine aka samu tana d'auke da c................









<@<@<@<@<@<@<@ *Albishirin ku Mata ku marmaso kuji sirrin,Koh kinsan mace sai da kamshi da gyara* =





<@<@<@<@ *Turare suna d'ayace Amma sun banbanta kowanne da ingancinsa kamshinsa da aikin sa*



<@<@<@<@ *Ina muku Albishir da UMSAD INCENSE Dan samun turaruka masu kamshi da* *gyara*



<@<@<@ *Tabbas Turare sirrine ga Koh wace mace*



<@<@<@ *Gamai bukatar turarukan UMSAD INCENSE*



<@ *Na tsunguno(habil)*

<@ *Na jiki (kwalaccam)* ( *khumra, black & white* )

<@ *Turaren turara jiki after birth* ,

<@ *Na d'aki(halud Al'oud)*



*UMSAD INCENSE suna kofar waika wajen Ado bayaro layout Kano State* =؃<=؃<



<@<@<@ *Suna bada d'aya Koh sare akan farashi Mai Rahusa*



<@<@<@ *Suna bada order kayansu Gamai bukata aduk jahar da yake a fadin Nigeria*



Contact them vie

>؀08028827241 or 09033791049

IG @umsadincense



<@<@<@<@<@<@<@<@<@<@<@

>
>د *MATAR MAKAHO* =h


~ Na ~






('Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za'a ga mistake Koh typing error Amin afuwa=L

free book >'



Page 4 6 &4 7

Wai yarinyar tana d'auke da ciki shiyasa sukeso na rufa musu asiri na aure ta



Sosai nayi mamaki kuma zuciya ta takasa Aminta akan zancen cikine kawai ba, tunda yaran masu kudi da yawa suna cikin shege Amma ba'a bawa talakawa saini MAKAHO sam nakasa yarda.



Dana matsawa bappa da tambaya ma cemin yayi koh naki koh naso sati mai zuwa d'aurin aure



Harga Allah banso auren ba sam, don inaji a jikina ba batun ciki bane, imma cikin ne taya za'ayi a d'aura aure da ciki a jikin budurwan kenan, koh an zubar?karshe fa akafi karfine kafun sati d'aya ba wanda baisan zancen auren mu ba saidai sam ba wanda yasan dalili kuma duk wanda yaji batun auren saiya digawa auren ayar tambaya



Amma ke sumayya menene dalilinki na aure na?



"Auren ka, ina ma na sanka kajimin mutumi fa" ?ta fad'a cikin kuka sosai abin ya mata zafi watoh bayan auren kaskanci da akaso mata har b'atata akayi a wajen mijin don aga abinda yafi wanda suka sata=-muni



Sumayya nifa tambaya kawai nayi kuma abinda nayita gujema kenan, kika ga nake gudun fad'a miki gaskiyar abinda na sani, ya karasa maganar da kara rungumarta jikinsa



"Shikenan yanzun koh inada cikin sai ka yarda ka zauna dani" ?



Indai har cikin babu a jikinki koda kin tabayene zan zauna dake a hakan ma naji dadi ai, na samu mata



Kuka sumayya ta sake sakewa watoh duk zaman da suke da Al'ameen na kokonto ne tayi ciki koh batayi ba kai wai meta tsarewa dangin mahaifintane, na mahaifiyarta kamma bata sansu ba bare



Kiyi shuru sumayya mundin bakece kika gaji da zama dani ba ni bazan taba juya miki baya ba a duniya, bayan khadija da ke sai goggo bayan ku banida mutanen da suke sona tsakani da Allah, ke kuma kin nuna mini tsantsar hallaci a rayuwa, don wata koh da gaske tayi ciki aka aura matani bazatayi hakurin zama dani ba bare ta taso cikin kudi yanzun kuma tana fama da rashi harsai ta nemi na kanta



Da sauri sumayya ta rufe masa baki cikin kuka tace"karka kara fad'ar haka banaso nima a yanzun kaine kad'ai Garkuwa ta kaine bangon da zan jingina ya rikeni, insha Allah kome zai wuce kamar ba'ayi ba.



Allah yasa toh yanzun ya maganar kamilar?



"Bazan koya mata ba gaskiya kartazo tana shigewa mijina don yanzun kai ba tsaranta bane"



Yanzun shikenan saboda ni saiki rasa makudan kudi haka?



"Wani makudan kudi kuma bayan jiya ma na samu mutum uku da zasu fara zuwa, shiyasa yau zamu fita dakai muje bank zan bude Account maganar kudin koyar, shiyasa zan bude Account transfer zasu mini ta bank kuma yaran manya ne sosai fa, inaga anya ma bazan bude shago ba"?





toh Allah ya bada sa'a, Amma banda maganar shago kam banyarda ba matar aure da shago kamar wata inyamura.



"Ayya koh a shagunan kofar gida saina kama d'aya tunda bakin titi ne"



Sumayya ban Amince ba, yace yana tashi akanta hade da karban eirps in hannunta ya mayar kunnensa kawai ya kwanta



Ganin ya kwanta yasata tashi ta d'auko musu karyawa jejjerawa tayi, ganin bai sauko ba yasa a hankali tahau kan gadon agadon bayansa ta kwanta luf ta lumshe idanunta "breakfast is ready"



Shuru taji bai amsa ba Amma dai yasa hannu ya tabata,hannun ta buge hade da cire masa abinda yasa a kunnen san ta makala a kunnenta wakar umar m shareef ke tashi a ciki



Jin ta cire masa yasa sa mikewa da sauri ya Amshi abin a kunnenta, wakar dadi tamin don Allah ki maida mini, ya fad'a mata yana mai mika mata wayar hannun nasa jin wakar ta chanja



Hhh"waikai kam anya ka taba saka eirps a kunnenka kuwa"?ta karasa maganar da sauka akan gadon



Da sauri shima ya sauko had'e da cewa wallahi kamar kin sani inadai jin ana zancen sa Amma ni bantaba sawa ba ashe da dadi



"Hhh toh zauna kaci abinci sai na baka bluetooth harda wa'azi da karatun qur'ani zakaji a ciki ba waka kawai ba"



Menene bluetooth kuma, banda na waya?



"Baka san ana posted a waya ba? toh ai yakamata kasan bluetooth da mp"



Nasan mp mana, bluetooth ne bansani ba saina tura abu a waya inaji anacewa kai bude bluetooth naka na tura maka waka koh vedio.



"Kayi kokari wannan kuma na yayi ne a kunne zaka makala ba tare da igiya kamar eirps ba ka gane"



Eh na gane..yace yana zama



Abincin sumayya ta zuba musu mika masa tayi bayan ta damka masa shukali a hannu, wai nikam me kika maidani ne? an gaya miki bazan iyya d'aukar shukalin bane?



"Waya sani koh abincin ma saina fara baka"



Kwafa yayi kawai ya fara ci



Suna tsaka da karyawa sukaji sallamar khadija amsa mata sumayya tayi hade da bata izinin shigowa



Khadija bataso shigaba ganin yayanta na d'akin, Amma ba yanda ta iyya haka ta shigo, ina kwana Aunty?



"Lafiya khadija ya goggo"?



Tana lafiya ina kwana yaya, tana maganar tana kokarin zama



Lafiya khadija...ya Amsa mata



" khadija matso muci" sumayya tace wa khadija



Ah ah Aunty nagode, daman takarduna ne na kawo miki duka kamar yanda kika bukata.



"Lallai ma khadija bansan yaushe zanna baki abu kisa hannu ki karba ba tare da kin mini filako ba"tace tana mikawa khadija plate na abincin data zuba mata sabo



Ba musu khadija ta karba



"Yayan khadija"



Na'am sumayya..



Inaso zamu fita da khadija, zanje na sama mata makaranta tunda yanzun muna first time bazamu sha wahalar samun aji ba, Amma yakace ka Amince koh yaya"



Sumayya bazance miki kume

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login