Showing 18001 words to 21000 words out of 122551 words

Chapter 7 - MATAR MAKAHO COMPLETE HAUSA NOVEL

07 Sep 2024

16743

Naga hannunki na motse Kamar kin tashi bara dai na Kira nurse, yana yunkurawa zai Mike hannun nasa na rike cikin nawa hakan yasa shi komawa ya zauna Yana Mai cigaba Damon sannu tunda dai yanzun Kam ya fahimci na farka maganar nedai bazanyi ba, daidai lokacin Khadija ta shigo falon tana zazzare ido tana neman gadon da muke,har dai ta gan mu,



Isowa tayi bakinta a washe gani na ido a bude sai dai na Dan rame sannu Aunty Allah ya Kara sauki,



**nidai sai ido



Khadija jike Kira doctor kice ta farka, toh yaya tace tana fita









Karyawa Al'ameen yayi kafun ya ce zaije gida Khadija ta zauna Dani





Bayan fitar sa keke napep ya hau zuwa gida ,ya sauke sa a kofar gida, da sallama ya shiga gidan Jin gidan yayi yau kamar ya Bata hanya Sam Kamar ba gidan su ba, gabaki daya shuru ba hayani da suratai Kamar da don gidan su tun daga bakin kofa zakana Jin hayaniya na tashi Amma yau sit Keke ji lalube yake da sandar sa ya shiga kofar su,







Wanka yayi ya shanja Kaya ya kwanta don wani irin bacci yakeji Wanda Bai samuyi ba Daren jiya har kansa na ciwo, sai azahar ya farka massalaci yaje yayi sallah sai agun yake Jin abinda ya faru a gidan su sosai hankalinsa ya Tashi don shi mutum ne Mai son nasa duk wulakancin da suke masa in Abu ya samesu sosai yake damuwa daga massalaci police clinic ya wuce kamar yanda akace gun aka kaita,





Yana Isa ya hadu da Rabin Yan gidansu a farfajiyar asibiti gaidasu yayi yaukam ya samu amsa ya tambaye jikin inno ance masa Basu Bari a ganta har yanzun,,,



Zama yayi shima a asibitin duk hankalin sa nakan Sumayya sai la'asar ya koma FMC,





Haka Al'ameen da Khadija suka ringa jinyata a asibiti har muka Kai sati sosai Khadija ta tallafamin itace girki itace kaikawo tsakani gida da asibiti yau satin mu daya aka sallame mu, kudin hannu na ya kare Daman dubu d'arine abokin abie ya damka mini lokacin da naje ma abie sallama a falon sa ranan da za'a kawo ni gidan su Al'ameen,



na kashe kudi a gidan Al'ameen kafun naje asibiti na biya kudin aiki nasai madara da bonvita gongomi manya su sugar shi nayi ta Sha a asibiti da Abubuwan da aka bukata a asibiti shi Karan kansa naira d'ari shida ya rage agunsa,



**Keke napep muka hau dukan mu uku sai sintali har kofar gida ya sauke mu Khadija ta taimaka mini muka shiga cikin gida shi Kuma ya biya Mai keke ya dauko Mana kayan mu ya shigo,





Kofar mu Muka wuce nikam sai mamaki nake ganin gidan shuru babu hayaniya kamar an musu kulle Amma ban tambayi Khadija ba, kofata muka nufa Yana binmu a baya da kaya muna shiga nabi kofar da kallo kamar ina nan gaskiya Khadija yar arzikice har raina yanzun nake kaunar yarinyar sosai daki muka shiga na kwanta a Kan gado,



shima shigowa yayi da kaya ya aje "khadija kunna mini fanka"nace Mata,



Wallahih Aunty babu nepa an yanke muku wuta,





"Anyanke wuta kuma Daman wake biya"



Hada kudi ake duk wata a biya wannan watan inno ba lfy ba Wanda ya saurare Yan NEPA,



Allah ya bata lfy nace ina mikewa waje na fitoh Khadija ta shimfida mini darduma da filo na kwanta abina,



"Khadija kije gida kinji kije ki huta yau basai kin Mana abincin dare ba yayan ki zai sayo Mana yaukam ki huta abinki kinji"



Badon ranta yaso ba ta amsa mini da toh ta juya zata fita,



"Khadija dauki taliya uku a caton in kinje gida ki dafa muku kinje akwai Maggi da Mai duk ki eba,"



Toh Aunty ta shiga kitchen in ta dauka ta tafi,



shikam fita yayi ya rasa Meka Masa Dadi yanzun Sam baida jarinda zai Kama sana'a sai d'ari shidan nan koma dashi ya biya kudin Keke 200 saura d'ari 400 gashi yanzun abinci zai Saya Kamar yanda nace Masa Khadija taje ta huta zama yayi a kofar gidan ya zuba tagumi abin duniya ya damisa,





****Nikam bayan fitarsa tunani na hauyi tunda na kwanta rashin lfy babu yan gidansu Koh namu da yazo dubani hatta Yan unguwan makwanta basuje ba sai Goggo Amina kawai itama sau daya taje, lallai rayuwa abin tsorone,



Sai da yaji ana Kiran sallan mangariba kafun ya mike ya tafi masallaci daga nan ya wuce bakin first bank dake D'aya tsallaken titin kofar gidan su ta Gefe ya sai abinci plate daya naira dari uku ba nama haka ya sai plate daya aka Masa take away ya dauka yayi hanyar gida,



Nima sallah nayi naci gaba da k'wanciya a inda nake, naji shigowar sa da sallama amsa Masa nayi, ya karaso Kan darduman ya zauna a gefe na Dayake yanzun ya daina shakkar rabar inda nake tun zaman mu a asibiti,



Ga abinci nan na sai Miki shinkafane fried rice ,



Toh nace na karba budewa nayi na fara ci Ina tambayar sa nasa" Ina take away in ka Kai Kuma" agun naci ya Bata Amsa,



abinci rabi naci,nace yaban. ruwa dauka yayi ya kawo mini nasa" sai da akayi Kiran isha'i yayi Alwala ya wuce masallaci yayi sallah sai karfe 9:00 ya dawo lokacin nikam na gigice ga zafi ka sauro sai fifita nake da caton in taliya,

Dolen sa ya fita yaje yasai maganin sauro na ishirin,kudin hannunsa saura 80 kacal ya rage,



Yauma a darduma daya Muka kwanta shiya rigani tashi da asuba ,,,



Vayan fitarsa nayi Sallah sai 7:00 ya dawo wanke wanke yayi ya jawo ruwa yakai kafa biyar yasa a randa nikam bacci nake a daki



Khadija ma tazo ita tayi shara ta shiga kitchen zata daura mana karyawa sai dai babu kayan miya,fita tayi tazo ta same sa,



Yaya ba kayan miya aban kudi na saya,



Me Zaki dafa?



Shinkafa ne



Sai dai Khadija ki Mana shinkafa da wake da Mai da yaji don bani da kudi sai 80 innan ,gasu nan ma kije ki sai Mai da borkono da Maggi,



Yaya akwai Maggi kam da Mai da manja galam ma babba a kitchen in sai dai na sai borkono na talati kawai yaya,



Toh yace ya Mika mata Yana cewa tayi abinci gabaki daya harda na Rana direct, hamsin ya Bata,



ta karba ta koma kitchen in ta daura shinkafa a gas da wake,taje ta sayo barkono ,





****Sai 8:30 na tashi na safe fita waje nayi Naga Khadija na aiki a kitchen shi Kuma nata Jan ruwa,gai Dani tayi na amsa shima gaishini yayi amsawa nayi na ibi ruwa a buta na Kama brush,



Sai karfe 9:00 ta kammala abinci ta zuzuba Mana karba nayi na fara ci Sam ba cimana bane shinkafa da wake Amma ya zanyi ni Karan kaina nasan Basu dashi Dole na koyawa kaina cimar su ,



Yana Gama cin abinci ya Mana sallama ya fita wajen Yan sarin kayan fruit ya wace inda yake saya yazo ya kasa,da sallama a bakinsa ya karasa gun dukansu suka amsa masa suna tambayar sa lfy, baya zuwa kwana biyu Koh ya chanja sana'a ne,





Lafiya Alhamdulillah Ina zama agun mara lfy ne a asibiti shiyasa bana fita, Yana fada ya karasa wajen customer in sa, Dan Allah malam Hafizu nazone ka taimaka ka bani bashin mangoro na dubu daya inje in kasa in Allah yasa nayi kasuwa sai na kawo maka kudinka ka bani wani, wallahih bani da Koh sisi sai naira talatin,



Chap gaskiya bazan iyya wannan kasuwan cin dadawan kauye ba ,



Habba malam Hafiz mun saba da Kai shikara nawa Ina sayan kaya a gunka don yanzun jarina ya karye bazaka iyya tallafa mini in mike ba,?



Bazan iyya ba,yace cikin masifa ,kala Al'ameen baice masa ba yaje kusa da table in dayan makwancin malam hafizu Amma yaki yarda haka ya zagaya Tashar kayan marmari Anki Vasa duk da sun Saba dashi Amma haka suka ki basa jiki a sanyaye ya kamo hanyar gida,..







Muna zaune da Khadija a kofa tana mini kitso Ina kwance a Kan darduma a baranda Hira muke akan bikin kawarta Yar wani Mai kudin unguwan saura wata Daya da sati biyu,



Aunty kinsan Allah Asma'u tana sona da kawance Amma mamarta Bata so shiyasa yanzun bana zuwa gidan su itama Bata zuwa namu sai dai mu hadu a hanya mu gaisa da auren ta ya kusa ma kaninta ta aika ya fadamin date na auren ,





Kuma ,, kawayen ta suna wulakantani tun muna makaranta basaso na da Asma'u,sai nake ji Kamar kar naje bikin,



"Don me bazakije bikin ba"?



Saboda banaso.a wulakantani Aunty,



"Ai.in bakije ba baxataji Dadi ba Kuma basai kin kulasu ba zasu wulakantaki ,"



Shikinan Aunty Allah ya kaimu,..



"Ameen Kenan in anyi bikin da wata Daya azumi"?



Wallahih Aunty yanzun bakiga sai aure ake ba akai akai azumi yazo,



"Toh Koh kema za'ayi nakine kafun azumi tunda ba karatu kike ba"? na fada Ina dariya,



Shap aunty aini Koh saurayi bani dashi ban ma tabayi ba,



"Kutt don me Amma dai Inaga ke kike kinsu Koh Amma duk kyau inkin nan kice baki da saurayi"



Aunty Kenan ai samarin ma Yan Mata masu kwalisa suke so ba Irina ba,



"Karki Kara cewa haka ki gode wa Allah wata ma batasamu gata kamarki ba kinji insha Allah wata Rana sai lbr ",



Insha Allah Aunty





tsayuwar mota mukaji a kofar gidan ba'a jima ba sai Muka fara Jin Ihu da salati na dandazon Yan gidan sai koke koke ake dagaji bana lfy ba ne,,,,....



Khadija ce ta Mike da gudu ta fita a kofar tayi cikin gida Koh takalmi babu ni karan kaina na tsorata,



Koh minutes uku batayi ba Sai gata ta dawo da kuka tana haki ta Fadi a kasa kusa dani cikin gunjin kuka ta bude baki tace Aunty I.................







<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß *Albishirin ku Mata ku marmaso kuji sirrin,Koh kinsan mace sai da kamshi da gyara* =Ø Þ





<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß *Turare suna d'ayace Amma sun banbanta kowanne da ingancinsa kamshinsa da aikin sa*



<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß *Ina muku Albishir da UMSAD INCENSE Dan samun turaruka masu kamshi da* *gyara*



<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß *Tabbas Turare sirrine ga Koh wace mace*



<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß *Gamai bukatar turarukan UMSAD INCENSE*



<Ø@ß *Na tsunguno(habil)*

<Ø@ß *Na jiki (kwalaccam)* ( *khumra, black & white* )

<Ø@ß *Turaren turara jiki after birth* ,

<Ø@ß *Na d'aki(halud Al'oud)*



*UMSAD INCENSE suna kofar waika wajen Ado bayaro layout Kano State* =؃Ü<Øüß=؃Ü<Øüß



<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß *Suna bada d'aya Koh sare akan farashi Mai Rahusa*



<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß *Suna bada order kayansu Gamai bukata aduk jahar da yake a fadin Nigeria*



Contact them vie

>Ø€Þ08028827241 or 09033791049

IG @umsadincense



<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß<Ø@ß

>ØÑÝ
>Ø¯Ý *MATAR MAKAHO* =ØhÜ
>دÝ

~ Na ~



<ØCß *Rukayya* *Ibrahim* <ØCß



('Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za'a ga mistake Koh typing error Amin afuwa=ØLÜ

free book >Ø'Ý



Page1þã 4þã &1þã 5þã

Aunty' inno ta rasu tace tana Kara karfin kukanta,



"Innalilahih wainnailaihir rajuun" Allah ya jikanta da rahama yasa ta huta" nace



Ameen Aunty tace tana mikewa tadau hijab inta ta nufi cikin gida,



**Banyi niyar zuwaba saboda jikina Amma ganin mutuwa ne Kuma Abu da gida babba hakan zai iyya zama abin magana, yasa na mike na fita zuwa cikin gidan,



Ai ban tashi sanin Yan gidan ba sai da Naga manya da yara Suna kuka harda na tashin hankali kuka suke ba manya ba yara Mai makon a ma mamaci Addu'a sai ihu da kuka nidai Ina zaune a Gefen matan makwanta da suke shishigowa Ina kallon ikon Allah



Al'ameen da wannan sanyin jikin ya iso kofar gida ya tarar da jama'a makil, inno ta rasu mutuwar ta dake sa sosai don alokacin sai da mutuwar mahaifiyar sa ta dawo Masa sabo,ganin yanda iro ke kuka Wanda yasan halin iro ba kome ke tsorata Sa bama Amma yau kuka yake,



tabbas mutuwar iyaye akwai ciwo,(Allah kajikan iyayen mu)



Ankai inno gidan ta na gaskiya yau har anyi sadakar bakwai gida ya koma kamar yanda yake kowa na sha'aninsa sai yaranta da sukayi sanyi kadan na rashin uwa,



A tsawon satin nan na fahimci yayan Khadija baida aiki haka zaije yayi ta yawo Koh sisi bazai samuba ya dawo Yana kame kame taliya Koh Maggi Koh indomie nake iba na bawa Khadija takaima masu shago su Saya da araha kafun mu samu na shifenen Miya,..

Duk da Al'ameen baisan Ina Saida garana ba,



karshe dai ajesa nayi nace ya fadamin me ke faruwa, dashine yanzun,duk lokacin da ya zauna baida aiki sai tunani,



Tukum yamin bayanin bashi da jari yaje tashan kayan marmari sun hanasa bashi duk inda yaje su taimaka Masa sunki,



,"Amma menace maka in Abu ya taso ta wajenka bance ka ringa fada mini ba"?



Hakane Sumayya Amma ni sai Inga Kamar ni ya dace in bukatar ki ya Tashi ki tambayi ni ba Zan ringa daura Miki nauyi ba,



"Au aini ma nufina bashi Zan baka Amma Ina ni Ina baka kyautar kudi sai dai bashi "



Duk da haka dai Sumayya....



Ban Bari ya karasa maganar Saba na tare sa "na baka bashin ne ka rufawa kanka asiri Koh na rike kudina ka cigaba da yawo ba aiki ga azumi saura wata biyu"



"Kuma bara na gaya maka in azumi yazo kayan Dadi zakana sai min Kuma kamin kayan sallah harda Khadija kaji dai na fada maka"



Toh shikenan abani yace Yana gyara zama alamun dai baida mafita,



"Ka Bari sai gobe Zan baka"



Washe gari Khadija na tura yaro yace tazo, ba'a jima ba sai gata aikanta nayi *say* *box* ta Kira mini Daya daga cikin yaran masu shagunan sai da wayoyi da laptop's suzo tare tace Masa amarya ce ni Kuma ban fara fita ba,



Don nasan in na Bata laptop innan za'a Mata cinikin wulakanci ne kawai Koh ma wani ya Mata wayo ya gudu da laptop in don nasan say box ba irin mutanen da babu a ciki,



Munyi ciniki da Mai sayan system in ganin yanda Yama laptop in cinikin wulakanci yasa nace na fasa sayar wa,



Buhun flower na dauko a kitchen Daman ban taba bude Saba nace wa Khadija taje gun Haladu tace Masa xai Saya buhun flower Zan Masa sauki,



Bata jima ba ta dawo tace min yace ta kawo flowern ya gani, Bata buhun nayi taje shagon Haladu ta sayar mini shima naira dubu bakwai ya Saya ba yanda na iyya haka na sayar Masa Amma ni Karan kaina nasan ba haka kudin yake ba,



Yayan khadija na baiwa dubu uku yayi jari na rike dubu hudu na D'an Yi sayayyan abin bukata nayi irin su pad omo sabulu na baiwa Khadija dubu D'aya, tunda har yanzun Basu gyara Mana NEPAn kofar muba don sun biya ganin mu bamu biya ba sai suka yanke wayar kofar mu Khadija na baiwa dubu daya ta mikawa bappa sulaiman kudin wutan NEPAn mu aranan sukasa aka hada mana wayar aka gyara, na baiwa Khadija dari biyar itama =Ø Þ





Haka rayuwa tayi ta tafiya Rana ya wuce sati ya shude yau Dadi gobe Akatsen sa har Muka cika wata Daya da sati biyu da aure, ba abinda ya taba shiga tsakanin mu Koh da kuwa hada gado ne, in munkwana waje D'aya toh ana zafi munyi kwanan waje ba nepa,



A y'an kwanakin nan na fara fuskantan matsen rayuwa Wanda ban Saba ba,



Dole sai abinda ya samu zamuci wani sa'in ma in Bai samo kome ba haka zamuci indomie d'anye wani a dafe da ruwa, in ya samu D'an ciniki Kuma muci shinkafa da Mai da yaji,Inda Allah ya sumuma garana Bai kare ba akwai taliya Mai Maggi kefe shinkafa, Amma duk da haka na D'an fada na chanjin yanayi, saboda yanzun ya hanani Saida Kayana don har Yan unguwa sun fara gulman ya kasa rikeni Kayana nake sai dawa,maganan har kunnen da yashiga shiyasa ya nuna mini baya so ,



yau na shirya da niyar zuwa gidan Goggo Amina, da gidan mu tunda safe na kammala aikina yau mun Sami kudin kayan shaye mukasha da safe' bayan ya fita na kammala aikina dake na sanar dashi Zan fita gidan Goggo Amina ( marikiyar Khadija ) Zan bi gidan mu d'uka Bai Musa ba saboda mun Riga munyi maganar dashi, dari da hamsin ya bani kudin Keke,



Khadija zata rakani kasancewar yaune Zan fara fita, unguwa tunda nayi aure bayan asibiti ba inda naje,



Sai goma Khadija tazo lokacin na fitoh wanka, Muka gaisa ta shiga Wanka Dayake tun jiya ta zo ta guge kayanda zatasa d'aya Daga cikin Wanda nake Bata,



Shiryawa nayi cikin lufaya Mai tsada fari Mai Flowers brown NASA riga long sleeve brown NASA takalmi fari na dau jakama fari fuskata ba kome sai powder da man baki, Khadija dake gefe na tsaye baki bude tana kallona,



"Rufe bakin ga guda zai wuce ciki"nace Mata cikin murmushi Mai karawa fuskata kyau,



Hmm Aunty na gaskiya ke Mai kyauce Allah ne kadai yasan dalilin da yasa ya bawa yayana wannan k'yakk'yawar hallintar nan Ina ma Yana kallo yaga yaran da za'a Haifa Masa =ØÞ



Murmushi kawai nayi bance kome ba don na lura ita ta yara ma take,



" Khadija kiye sauri kisa kaya don Allah na masu na ganni a gidan mufa Naga abie na"



Toh Aunty tace tana saka dogon riganda na taba Bata,tayi shafe shafen ta tana Gama shiryawa, Muka fita"



Yaune rana na farko Dana taba karewa unguwan sintali kallo unguwa ne da ya hada ruwa biyu masu kudi da talaka wa Yan kasuwa da ma'aikata da masu zaman banxa unguwan nada kyau sosai da fasali,..



Gidan Goggo Amina mukaje da kafa ,



Mun samu tarba Mai kyau ba laifi matar nada kirki sai dai na Lura ita mace ce da Bata shiga abinda Bai shafe taba Sam babu ruwanta,mun D'an jima a gidan kafun Muka Mata sallama na aje Mata laidan Turare Wanda na d'auka a kayan aure na,



ta rakomu har waje Muka tare keke napep ,



Hajiya Ina kukayi? Ya tambaye ni



"Specialist" zaka kaimu,

Ku hau muje yace,



Dukan mu Hawa mukai yaja machine insa muka nufe unguwan specialist,



Muna shiga unguwan mu na Masa kwatancen inda zai sauke mu,



"Yana sauke mu na tambayi sa "nawane kudin ka"



Naira dari da hamsin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login