Showing 93001 words to 96000 words out of 116224 words

Chapter 32 - Maciji ne book 1

28 Aug 2024

25313

kukan,In kuma ba haka ba saidai asakeyin irin na dazun,shine zaki daina jin zafi"Adeeb ya faɗa cike da zolaya fuskarsa ɗauke da murmushi.

Da sauri fattu ta ɗan zabura tare da buɗe idanunta ,da suka ɗan yi jaaa, tace "a'a wllh baza'a ƙarayi ba har abada,bana so "ta fada tana turo masa baki.dariya yayi har fararen haƙoransa suka bayyana reras kwanin sha'awa.kafin yace "shikenan Hulwa yanzu bari na taimaka miki kiyi fitsari sai kiyi alwala ko?In yaso saikici abinci da magani ki kwanta,shikenan zakiji ki garas kin warke "ya fada yana ƙoƙarin kamata dan ta mike tsaye.

"Ni da kaina zan tashi,karka rakani ko ina,ba nace mun bata ba"fattu ta faɗa tana turo baki.

Kallonta Adeeb yayi tare da sakin murmushi,ashe Hulwa ma ta iya rigima haka?ji yadda take turo masa wannan dan karamin bakin nata,kamar ba ita bace Sarkin tsoron nan da kunya,lallai yau Hamma yayi laifi.adeeb ya faɗa cikin ransa yana murmushi,sosai take burgeshi idan tana masa wannan shagwbar, yakanji kaso casa'in na damuwarsa ya goge.
Fattu kuwa cikin karfin hali ta sake yunkurawa zata mike,amma ina,wani sautin ƙara da bayanta ya bada shine yasa ta komawa da sauri tare da riƙe ƙugunta"wayyo Allah ƙuguna,wllh Hamma ka karyamin ƙugu bazan yarda ba saika biyamin"ta fada tana ɗan kukan shagwaba.

Da sauri Adeeb ya tarota yana faɗin"yi ahankali hulwa,bazaki iya tashi bafa, ki barni da hamman nan tunda ya karya miki ƙugu ko,saina hukuntashi,dan yayi babban laifi wa hulwata"ya faɗa yana janyota jikinsa.da gyar take takawa suka nufi toilet,ko wajen fitsarin ma da gyar ya samu tayi,dan tace idan tayi gurin zafi zai mata .
Ruwan zafi ya bata tayi tsarki ,sannan tayi alwala suka fito.
Bayan ta isar da salla ne ya bata abincin da aka shirya musu akan daining,farfesun kayan ciki ya bata,mai zafi da dan yaji.kuma ta ɗan ci sosai .sallar ishsha tayi ya bata magani ta sha da gyar,sannan ya kwantar da ita akan gado tare da lullubeta.
Zama yayi bakin gadon yana shafa kanta tare da rarrashinta cikin malamai masu dadi har tayi barci.

Murmushi yayi tare da sumbatar kumatunta sannan ya fita zuwa gurin ammi,bayan ya kulle part din nasa da security.


Ammi kuwa tana can garden ɗinta,inda suka saba haduwa da mai nannaɗaɗɗiyar fuska,to yauma dai shine yazo,dan haka suna zaune acan cikin garden ɗin.
Magana yake wa ammi fuskarsa arufe kamar kullum"ki tabbata kin aikata kamar yadda na faɗa miki,dan kuwa wannan gubar idan har yaci abinci da ita,to saidai wani ba shiba,kuma ba wanda zai zargi wani abu,dan kuwa zata lalata masa kayan cikinsa ne ahankali, ta yadda badaga cin abincin gubar zatayi aiki ajikinsa ba,kinga da zarar ya mutu,zuciyar ubansa zata buga,bugawar da na tabbata zata zamo ajalinsa ne,shikenan mun jefi tsuntsu biyu da tarko daya"mutumin nan ya fada cikin salo na kwarewa a mugunta, yana mai jingina bayansa jikin kujerar da yake kai.

Ajiyar zuciya ammi ta sauke,tana jin wani irin farin ciki aranta."lallai kayi tunani mai kyau,shikenan idan akayi haka ,burin kowa zai cika,daga Ni har kai.shikuwa wancan ya riga ya zama marar amfani,ahaka zaiyi ta zama cikin ƙunci da tashin hankali,dan haka bana jin ta tashi"ammi ta fada tana mai kallon kwalbar da mutumin ya bata mai dauke da guba.

Adeeb kuwa koda yaje part din ammi bata nan,kai tsaye ya wuce garden,Dan yasan bata wuce can,tunda bata bangaren abie,amma kuma me takeyi a garden da wannan daren?kasancewar garden ɗin akwai wadataccen haske,kana iya ganin komai tar tar kamar rana.can Adeeb ya hango ammi zaune da wani mutum,cike da mamaki yake kallonsu ,yana yawan ganin wannan mutumin mai fuska arufe,waye shidin?me yake kawoshi gurin ammi?kuma duk zuwa sai da daddare?
Ƙara sauri yayi dan yaje ya cimma mutumin nan yau kam saiga ko waye shi.

Da sauri yaga mutumin ya mike tare da bin wata hanyar yayi waje yana gyara rufin fuskarsa.
Ammi kuma tana boye abu cikin rigarta.dan mutumin shine ya hango Adeeb yana tahowa,shine ya sanar da ammi ya mike da sauri ya tafi.

Cike da tuhuma Adeeb ya karasa gurin da ammi ke zaune tana wani muzurai,zama yayi shima tare da kafe ta da Mayun idanunsa,waɗanda ke cike da tuhuma.

Murmushin karfin hali ammi tayi tana mai faɗin"Prince kaine da daren nan?aida kayi zamanka ma zuwa gobe saikazo,bana son kana wahalar da kanka"ta fada cikin basarwa tana kallon gefe guda.

Adeeb kam kallonta kawai yake,dan duk wasu alamu na rashin gaskiya ya bayyana akan fuskarta.cikin dakakkiyar murya yace "ammi waye wancan mutumin daya bar gurin nan yanzu?meye alaƙarki dashi?meyasa Aduk lokacin dana ganku tare yake saurin barin gurin kafin na iso?Adeeb ya jerowa ammi waɗan nan tambayoyin ,da suka matukar firgitata.tunda suke dashi bai taba mata tambaya makamancin haka ba,duk lokacin da zai ganta tare da wannan mutumin baya taɓa tambayar ta waye wannan mutumin,amma yau tambayar ta yake,hakan yana nuni da cewar kiri-ƙiri Adeeb ya fara zarginta kenan.
Cikin dakiya da son basarwa ammi tace "wannan wace irin tambayace Prince?wannan mutumin yana zuwa karbar tallafi ne na gidauniya,bayan wannan ba wata alaƙa tsakanina dashi "ta faɗa cike da bugawar zuciya tana kallon Adeeb.
"Amma me yasa kullum sai dare yake zuwa?ammi Please karkisa zuciyata ta fara aminta da abinda ke kai kawo cikinta akanki,Please ammi don't disappointed me "Adeeb ya fada kamar zaiyi kuka,dan kuwa zuwa yanzu sosai yake jin zargin ammi cikin zuciyarsa.

Kallonsa ammi tayi cike da tsoro da fargaba,me zuciyar tasa ke raya masa akaina?kodai yasan wani abu ne game dani?ko yaji me muke fadine yanzu?kai bai iiba ,dan kuwa da yaji hakika da bazai tsaya yana min wannan maganar ba,na tabbata wani abune dai da ban.
Cikin salo da iya kissa ammin ta sanya kuka tare da kamo hannun Adeeb ta rike gam cikin nata,kallonsa take idanunta na zubda kwalla "yanzu ashe akwai ranar da zata zo ace kana zargin amminka?akwai ranar da maƙiya zasu sanya maka kokwanto akaina?nice fa amminka ,nice wacce na kula da rayuwarka fiye da yadda na kula da tawa,me yasa kake son sanya kokwanto akaina ?bazan taɓa cutar da kaiba Adeeb kasan da haka, dan Allah kadaina sanya komai cikin ranka, yin hakan zai zame mana damuwa "ammi ta karasa cikin kuka tana ɗora kanta agefen kafadun Adeeb.

Shiru Adeeb yayi yana sauraronta, wani sashen na zuciyarsa na tausayinta,wani sashen kuma ya kasa gasgatata,abubuwa da dama suna masa yawo akwakwalwarsa.

Ahankali ya sanya hannunsa yana mai ɗago ammi ,kallonta yayi cikin tausayawa yace "kiyi haƙuri ammi I don't mean that,kawai bana son kina hulda da irin wadan nan mutanen ne,amma bana zargi ki da aikata komai"ya faɗa yana share mata hawaye.

"Shikenan dana,ka tashi ka shiga ciki dan akwai sanyi awajen da safe zamuyi magana,sannan ya kamata ka dawo da fattu gurin nanny,Dan gudun zargi ko"ammi ta fada tana share hawayenta.
Jinjina kai Adeeb yayi kafin ya mike yace "saida safe ammi"ya fada yana barin gurin ba tare da ya su ɓaci hannunta ba,kamar yadda ya saba.

Binsa ammi tayi da wani shegen kallo cike da tsana ,kafin ta furta"kayi kuskure daka fara zargina Adeeb,dan kuwa zaka tafi lahira da damuwar rashin samun gamsashshiyar amsa akaina."

Koda Adeeb ya dawo part dinsa ,wanka yayi tare da dauro alwala,sannan ya fito,kayan barci da ya sanya ,bayan ya feshe jikinsa da turaren barcinsa. Sannan ya kwanta kusa da hulwarsa ya rungumeta tsam! Ajikinsa. Wata ajiyar zuciya ya sauke mai ƙarfi yana jinsa cikin wani irin nutsuwa,kaso da yawa na damuwarsa ya kau.

Kissing din wuyanta yayi sannan yayi musu addu'a tare da ja musu bargo ya kunshe idonsa.
Ya jima yana nazari akan abubuwa da dama kafin barci ya dauke shi.

Tunda yayi sallar asuba,bai kona barci ba,karatun Alqur'ani mai girma yai tayi,har zuwa lokacin da gari ya fara haske.
Cak ya dauki fattu yayi toilet da ita,sai jinta tayi cikin bahon wanka,kukan shagwaba ta fara masa,shikuma yana lallabata, tare yayi musu wanka.tunda fattu ta rufe idonta bata budeba tsabar kunya,dan bazata iya ganin hammanta ahakaba,shikuwa ko ajikinsa,sai tsokanarta ma yake.

Bayan sun shirya ne kuma ya kamo hannunta zuwa falo,dan yasan zuwa wannan lokacin,an gama shirya breakfast.

Zaunarta yayi sannan shima ya zauna.abincine gasu nan kala kala na larabawa dana turawa.tea ya fara hadawa sannan ya matso kusa da fattu yace" Bismillah amaryar Hamma Adeeb "ya faɗa yana nufar bakinta da tea ɗin......


Masu karatu me zai faru?
Shin fattu zata sha tara ɗin na ko yaya?

Muje zuwa anty mammynku ce

Mrs babi💘💘

Share and comment fisabilillah.

More comment
More typing.
[30/08 14:58] %Faiza%: 🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄



MACIJI NE🪱🪱🪱



Na mammy kabeer
(Anty mammy)



Elegant online writers📚📚



Free book

Page 71/72




_______________Cikin kuka da rawar murya ,fattu ta fara magana "wa...ce...ce .ma...haifi.......yata?kuma ina ne take ?sannna me ya faru da Hamma na bayan rasuwar momma?"ta fada cikin kuka mai ban tausayi.

Saida Nanny ta share hawayen idanunta kafin taci gaba da fadin" lokacin da labarin hadarin nan ya iske mu,mun shiga tashin hankali bana wasa ba,dan kuwa nan take mai martaba ya yanke jiki ya fadi asume,gaba ɗaya faɗa ta rikice da kuka da alhinin rashin mutuniyar kirki kamar Momma, wacce ke son talakawa da taimakonsu.

Lokacin da Adeeb suka dawo daga makaranta,ya ji labarin mutuwar Mommansa da kannansa,shima sumansa uku,saida gyar aka samo kansa,tun daga wannan lokacin Adeeb ya kara komawa shiru shiru,bashi da aiki sai tunani haka zaki ganshi zaune shi kadai yayi tagumi yana zubda hawaye,saida aka tashi tsaye akansa da addu'oi kafin ya dan warware.

Mai martaba kuwa,ciwon zuciya ne ya kamashi, saboda tsabar damuwa da tunani.
Yana matukar kaunar Momma,Dan macece mai hakuri da shiga rai.
Tana faranta masa rai,duk abinda yace tayi bata ko musu akan umarninsa.

Bayan sadakar bakwai ne ,aka fara bincike akan abinda ya sami motar tunda kai tsaye motar ta kama da wuta, kai tsaye aka gano bomb aka sanyawa motar.dan haka wannan hadimin mai kula da harkar motoci shi aka fara kamawa.
Anyi -anyi ya fadi abinda yayiwa motar amma yaƙi,shidai yace tabbas bomb ɗin ne ajikin motar,saidai idan ya fadi wadanda suka sashi,to zasu kasheshi ne.
Dukan tsiya akayi masa tare da kulleshi akurkuku.

Cikin dare muka shirya zuwa gareshi,dan ya faɗa mana wadanda suka sa sashi,akan idan ya faɗa zamu sakeshi ya gudu.
Amma saidai me?lokacin da mukaje, tuni Ammi ta riga mu zuwa,tana tsaye ita da wani mutum wanda ya nannaɗe fuskarsa da bakin gyalle.ta yadda ba wanda zai gane fuskarsa.

"Wato so kake ka tona mana asiri ko?lallai kayi babban kuskure,dama ko kafada ko karka faɗa dole ne ka baƙunci lahira, tunda har kashigo hannu, kuma kasanar dasu da gaske bomb ɗinne ajikin motar,to watarana idan kaji azaba zaka sanar dasu mune muka saka ka sanya bomb din Dan haka yau zaka bi su Nazli kaima"Ammi ta fada tana mai dagowa daga sunkuyon da tayi tana yiwa mutumin magana.

"Kuyi min rai, ranki ya dade,wllh bazan ce kune kuka sani na aikata wannan aikin ba,dan Allah karki kasheni" mutumin ya faɗa galabaice dan yaci duka dazu.

"Kai!!! sakaran bawa, rufe mana baki, mu zakayiwa magiya mu gyaleka?wllh baka isaba,dole ka mutu dama baka da wani amfani agaremu, tunda kasan sirrinmu dole ka mutu"yana gama faɗin haka ya shaƙe bawan nan ,tun yana turje turje har ya daina alamun rai yayi halinsa.

Gaba dayanmu dagani har Amma kuka muke jikinsu na rawa,tsabar tsoro da razani.wanene wannan wanda ke taimakawa Ammi wajen aikata ta addancinta?ta yaya zamu gane shi ?shine abinda ke ta yawo cikin kwakwalwarmu.amma bamu da amsa. Ganin yadda amma ke kuka kamar ranta zai fice ,gashi jikinta sai rawa yake,yasa nayi saurin janyeta dan barin gurin.
Saidai agarin guduwa muka bigi wani bokiti ya fadi kasa yayi kara sosai.wanda ya jawo hankali su Ammi.
Gudu muka farayi tun karfinmu, dan kuwa akwai tazara sosai tsakanin cikin faɗa da kuma sijin ɗin.
Suma basu fasa ba kuwa suka biyo mu.
Ganin zasu cimmana yasa Amma ta ce in buya,karsu ganni, ita zata tsaya ayi wacce za'a .
Dan Ni zasu iya kasheni nan take ,amma ita tasan yadda zatayi.

Haka na buya jikin wasu bishiyu.ta yadda bazasu ganni ba,amma Ni ina hango su dajin duk abinda suke fadi.

Koda suka cimma Amma tana zaune tana numfarfashi, tsayawa sukayi akanta suna kare mata kallo.
Ammi ce cikin ɓaci rai tace "dama nayi tsammanin kece,dan kuwa nasan ba wani dan kasadar da zaiyi yunkurin bin bayana ɗan ji da ganin sirrina.to kingani, kuma kinji,hankalinki ya kwanta,amma wllh idan naji wata magana akan abinda kika gani na rantse da Allah saina kashe danki da adeeb,kisa mafi muni,kuma na lakamiki kisan, nace ke kika kashesu, kuma kinsan zan iya.
abinda yasa bazan kashe kiba yanzu, ina son kiga yadda zan lalata rayuwar yaranku ,insanya kiyayya atsakaninsu,ta yadda wataran daya shi zai zamo ajalin daya.
Kuma kinsan menene ke nake so kizabi wanda zai zamo ajalin wani acikinsu"Amma ta kare maganarta tana dariya da kallon Amma.

Kuka kawai Amma keyi, tana jinjina rashin imani irin na Ammi,mace kamar kafura?sam ba Allah cikin ranta.Amma na kuka take rokon Ammi akan ta gyale musu yara ,taji tsoron Allah,duk abinda take yana kallonta.Amma cikin rashin imani Ammi ke cewa "shikenan Ni zan zaba da kaina,nasan kina son danki,dan haka zan miki adalci yazamo shine zai kashe Adeeb "ta fada tana wani ware hannu da daga gira.

Cikin sauri Amma tace "a'a karki kashe Adeeb,gara Rashad ya mutu amma dan Allah karki cutar da Adeeb Maraya ne,zuciyarsa akarye take karki illatashi na roƙeki"Amma ta faɗa cikin kuka.

"Wow zabi mai kyau,kin zabi dan kishiya akan danƙi ko?lallai kin ciki shashasha,shikenan duk abinda zanyi akan su, naki idone ,daidai da rana daya kika yi min wata magana saina kashe Adeeb kinsan banda asara,bansan ciwon makida ba"tana gama faɗin haka ta karasa kusa da wannan mutum da suke tare,wanda dama yana tsaye dan nesa dasu yana kallon hanya.

Saida suka bacewa ganinmu sannan na ƙaraso gurin amma,wacce ke kuka sosai.haka na kamata muka koma cikin fada,zuciyoyinmu sam ba dadi.

Tun daga wannan lokacin Adeeb ya daina yiwa amma magana ,sai harara da bakaken maganganu,masu nuni da cewar yana zargin tana da hannu wajen kashe Momma.kuma nasan duk sharrin Ammi ne.kuma
Daidai da rana daya Amma bata taɓa kula Adeeb ba saidai tayi ta kuka.
Adaidai lokacin ne kuma suka tafi Singapore karatu.inda Adeeb yayi karatu bangaren likitanci,tareeƙ yayi karatun sa na koyon aikin jirgi,shikuma Rashad injiniya ne.

Bayan dawowarsa daga karatune kuma babban tashin hankali ya samemu, na rasa Adeeb da akayi sama ko kasa, kwanansu uku da dawowa daga Singapore akawayi gari ba Adeeb ba labarinsa.duk inda ya kamata aje nemansa anje amma babushi,lokacin kuma da ya dawo daga Singapore,yana da tarin dukiya wacce shi kansa baisan adadinta.dan dan kasuwane mai neman na kasan,bai damu da matsayi ko mulkin gidansu ba ,yana da kamfanoni da dama akasashe da yawa,ciki harda nigeria.hakan yasa Adeeb ya iya Yaren Hausa sosai,dan darasi yake dauka na musamman akan bangaren.
Dan haka lokacin da aka rasa Adeeb,tareeƙ shine yaci gaba da kula da duk wasu al'amura na dukiyar Adeeb .har Allah yayi dawowarsa ta silarki,
Ashe kema rabon ki sadu danaki iyayen ne,kuma ba kowa bace mahaifiyarki, face sarauniya suhaimat"

Baki buɗe fattu ke kallon Nanny ,Tana jinjina kai cike da jinjinawa ƙudirar Ubangiji,yanzu dama innar yan biyu itace mahaifiyarta? ashe shakuwar da sukayi ta lokaci ɗaya ba banza ba?waɗan kyawawan yaran kannantane?wayyo Allah na gode maka Allah mai yadda yaso ga bawansa.

Allah Sarki hammana yaga rayuwa,ya hadu da ƙaidin matar uba.wacce yakewa kallon muguwa itace masoyiyarsa. Ita kuma wacce ya dauka uwa itace ke son ganin bayansa.lallai yazama dole In fahimtar da hammana.
Cikin kuka da sarkewar murya fattu tace "amma waye yayiwa Hamma asiri ya zama maciji?

Ajiyar zuciya Amma tayi ta fara magana akaron farko,tun zamansu aɗakin, tace "wannan ne har yanzu muke son sani,dan bamu da tabbacin Ammi ita tayi masa asirin, saidai muna zargin wannan mutumin da muka kasa sanin ko waye yana da hannu akan al'amarin"Amma ta faɗa tana share hawaye.

Hannunta fattu ta kama cikin kuka,tace "lallai Amma kincika mutum mai halacci, kin sadaukar da rayuwar danki,dan ki ceci dan kishiya,nayi miki alkawarin in Sha Allah komai zai dai daita. Hamma zai dawo gareki matsayin uwa da data,sannan rashad zai zamo abin alfahari gareki.
Sai yanzu na gane wannan abinda ya faru dani itace ta shirya komai,dan kuwa ita ta kaini bangaren da kanta,kuma ta kulle ƙofofin, sannan ita ta dauke sarkata wacce baffana yace itace shaidar da iyayena zasu gane Ni da ita."
"Na sani ƴata,nasan itace ta shirya komai, sannan tun ganin farko da nayi miki nake ayyana ke yar sarauniya suhaimat ce ,dan kuwa akwai kamar ta atare dake .ina fatan Allah ya bamu sa'a akan abinda muke shirin aikatawa na alkairi "cewar amma.

"Nanny kema kiyi haƙuri komai zai daidaita in Sha Allah"fattu ta faɗa tana rungume nanny cikin kuka.
Kukan nanny ma keyi,tace "Allah ya amince ƴata.

Kallon tareeƙ tayi tace" Hamma tareeƙ kayi hakuri in Sha Allah abokinka ,kuma dan uwanka,zai dawo gareka"jinjina kai yayi tare da saurin share hawayen daya gangaro masa,yana murmushi.

"Amma kibi komai ahankali yata,hammanki ya aminta da Ammi sosai ,ta yadda baya ganin laifin ta ko kaɗan"amma ta faɗa tana shafa kan fattu.
Jinjina kai fattu tayi tace "In Sha Allah Amma zan kula"

Adeeb kuwa,gaba ɗaya ya duba ko ina baiga fattu ba ,hankalinsa ya tashi sosai,ina kuma taje?ko wani abune ya faru da ita?"ya Salam"ya faɗa yana mai fitowa daga part ɗin nashi cikin sauri. Kicibis sukayi da fattu tana shirin komawa bangaren nashi,dan Nanny ce tace ta koma kar Adeeb ya ganta anan yayi wani tunanin,
Kallonta Adeeb yayi idanunta sunyi mugun jaaa, cikin hanzari ya kamo kafaɗunta yana girgiza kai,gabanshi na faduwa"me yasameki? Wani ne yayi miki wani abu? Ko Rashad ne ?"ya faɗa cikin ruɗu yana duba jikinta.

Ita kuwa fattu kallonsa kawai take cikin tausayawa,yana cikin matsala babba,amma shi Sam baigani,zuciyarsa da idanunsa sun rufe,ya rike azzulamar uwa matsayin mai kaunarsa.jikinsa ta fada tare da sakin wani sabon kukan mai tsuma zuciya.
Hankalin Adeeb gaba ɗaya ya tashi,jikinsa har rawa yake ,tana rungume ajikinsa ya bude part dinsa suka shige ciki,sai kuka fattu keyi harda shashsheka.

Kai tsaye cikin daki ya wuce da fattu,bakin gado ya samu ya zauna tare da rungumeta ajikinsa ,yana jin damuwarsa na kara yawaita,zuciyarsa kamar zata fashe .
"Am sorry Hulwa ki sanar dani abinda ke damunki zuciyata na min zafi,bazan iya jurar ganinki cikin damuwa hakaba "Adeeb ya faɗa kamar zaiyi kukan shima.

Fattu dai taki cewa komai sai kuka take tare da kara kankameshi.ganin irin kukan da takeyi ne ,kuma baisan me zai mata tayi shiru ba ,ya sanya Adeeb ɗago kanta,ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login