Showing 30001 words to 33000 words out of 116224 words

Chapter 11 - Maciji ne book 1

28 Aug 2024

25289

gidan,dan haka da sallama tashi ga cikin dakin,juyowa fattu tayi da sauri tana kallon matar.

Murmushi matar tayi tare da kama hannun fattu ta miƙar da ita tsaye tana murmushi,
Kallonta kawai fattu keyi cikin tsoro da rashin sanin ko itaɗin wacece?
Cikin harshen larabci matar ke cewa" kai masha Allah yarinya mai kyau da daukar hankali,gaskiya kina da sihirtaccen kyau,ƴata, zanyi Mali kwalliya mai kyau kamar ke" ta kai karshen magannarta tana murmushi. ita dai fattu kallon matar take tana tunanin wannan ɗin kuma daga ina ?wacece?kodai itace hulwar?

Ahankali matar ta kama fattu ta zaunar da ita bakin gadon,gashin fattu ta fara warwarewa, " kai masha Allah,kina da gashi mai tsananin kyau,samun irin gashinki ba kowacce mace ba,larabawan ma" matar ta faɗa cikin harshen labarci,

Ita dai fattu tayi gurum cike da tsoron matar,gashi kuma ta kasa koda yunƙurin gudawa ne bare ta tsere.haka matar ta kama fattu sukaje toilet ta wanke mata kanta tass,sanann suka fito.

Gaban madubi ta kai fattu tare da ɗauki handryer ta busar da kan na fattu,mayuka kala-kala ta shafawa fattu akanta,kan kame tuni kan fattu ya ɗauki wani sheki da ƙamshi, ita kanta fattu wani sawai takejin kan nata.
Gyara mata kan tayi sosai sannan ta ɗaure mata shi da wani ƙaton ribom mai kyau.
Kwalliya tayiwa fattu cikin nutsuwa ba mai yawa ba,daga powder sai lips da kwalli ta sawa fattu a idonta,irin sakun nan da larabawa keyi,kusan rabin ido.
Kai fattu fa tayi mugun kyau fuskar nan Tata kamar farin wata dan haske,kwalliyar ta karbi fuskarta sosai,kodan ba tabayin kwalliyar tayi ba oho?
Ledojin nan mata ta buɗe tare da ɗauko wata bakar doguwar riga,dama kuma kayan duk dogayen riguna ne masu kyau da sutura jiki.
Har zata dauko su bra,sai taga wata akan gadon ,dan haka sai bata daukoba.

Wani ƙaton towel ta ɗauko ,dake gefen kofar bandakin asaƙale ,mikawa fattu tayi tare da cewa ta cire kayan jikinta ,saita sanya bra ɗin sannan tasa kayan nan.cikin harshen larabci matar ke magana.dan bata san cewa fattu bata jin larabci ba,dan kuwa ita tayi tunanin fattun ƴar Misran ce itama.

Kallon fattu tayi gurum! Kamar kurma,dan bata san me matar ke faɗi ba.ganin fattu bata karɓi towel ɗin ba tana zaune kawai yasa matar tunanin kodai kurmace?
Kwatance ta farayiwa fattu da hannu,cikin ikon Allah kuwa fattu ta gane wai rigar zata cire ta ɗaura towel din .karɓa fattu tayi tare da daura towel din asaman ƙirjinta.murmushi matar tayi tare da ɗaukar bra ɗin ta mikawa fattu.kallon brar fattu tayi tare da kallon matar" tab Ni nasan me zanyi da wannan abun da kina wani mikomin" fattu ta faɗa cikin ranta tana mai turo baki tare da kauda kanta.

Murmushin matar tayi tana mai rayawa aranta ,kodai fattun kunyar saka bra ɗin take?dan ga dukkan alamu wannan ne karonta na farko asaka bra ɗin.

Cikin hikima da dabara matar ta sakawa fattu bra bayan sun sha artabu,dan fattu sam ƙin yarda tayi da farko, aganinta wannan hulwar so take ta gane mata abubuwa,amma cikin hikima matar tayiwa fattu munin ba ganin jikinta zatayi ba tana son rufe mata jikinta ne,sannan ta dagawa fattu rigar jikinta tare da nuna mata itama ta saka irinta.sai lokacin fattu ta fahimci inda ake saka bra ɗin.ikon Allah wato suma waɗannan abubuwan harda jakar da ake boyewa?lallai zakaga abu da yawa idan baka mutuba.

Aikuwa tsif bra din tayiwa fattu ajikinta,Dan dama koda tareeƙ yaje karbowa cewa yayi budurwa yar kimanin 16 za'a haɗawa kayan,
Saidai fanties ɗin duk sun mata kaɗan sosai,da gyar matar ta samo mata wani mai kama da gajeren wando sannan tasaka.

Da kanta ta sanya rigar ajikinta,masha Allah masu karatu duk wanda yaga fattu awannan lokacin zaiyi tunani wata fattun aka sake,dan tayi kyau har ta gaji da yin kyan.
Tauraruwa matar ta fadawa fattu ajikinta masu daɗin ƙamshi,sannan tayi mata rolling ta ɓame da wani kyakykyawan abinda ake riƙe mayafi dashi dan gudun zamewa.

Sosai matar ke yaba kyan da Fattun tayi , ga sarƙarta sai walwala take,matar sai kallon sakar take cike da jinjina irin kuɗin da aka batar wajen siyanta,kafin ta kama hannun fattun ta juya da ita gaban madubi.saida gaban fattu ya faɗilokacin datayi arba da kyakyakywar fuskarta jikin madubi,hannu tasa tare da shafa fuskartata,dan tabbatarwa itaɗince kuwa.
Ƙuri!! Fattu ta kure kanta da kallo ta jikin madubi,wai dama haka take ko kuma dai ba ita bace wannan ɗin?anya matar nan ba sake mata fuska tayi ba ?dan dan ita bataga tsohuwar fuskarta ta da ajikin madubin ba.
Murmushin tayi lokacin data ɗan mintsini hannunta kadan,kuma taji zafi.
Wllh nice ,nice fattun baffa, gaba daya na zama ƴar gayu aradu zan tsula tsiya, wayyo Allah na ,ina Hamma yazo ya ganni ,yaga yadda na koma fattu ƴar gayu.
Juyowa fattu tayi tana kallon matar nan, fuskarta dauke da murmushi, itama matar murmushin tayi tana yaba kyau da Allah ya ba faytu.
Wayar matar ce tayi ƙara hakan yasa ta dauka ba tare da tace komai ba ta kara akunnenta,
"To yallaɓai ganin nan"
Shine abinda matar ta faɗa tana mai haɗa jakarta ,sallama tayi fattu bayan ta rungume fattun.

Koda matar ta fita tsayawa fattu tayi jikin madubin nan tana ƙara kallon kanta,tajita nan ta juya can tana dariya ƙasa -ƙasa.

Adeeb ne ya shigo ɗakin sanye da farar jallabiya mai tsananin kyau da ɗaukar ido,kansa kuma hiramine sai wannan baƙin abun da suke ɗorawa asaman hiramin, ba ƙaramin kyau yayi ba sai sheƙi fuskarsa keyi.

Tsak !ya tsaya abakin ƙofar yana mai faɗin "masha Allah,watabarakallahu fi ahsanil kaliƙin" lokacin da yayi arba da ƴar gayu fattu,wacce Bama tasan yana gurin ba,kallon kanta kawai take ,ta taɓa nan ta taɓa can.
Saida yayi gama ƙureta da kallo,yaga dai idan ya biye ta kallonta to zasu kwana anan ba tare da ya gaji da kallon nata ba,dan haka sai yayi ɗan gyaran murya kafin yace " idan kin gama kalle madubin zo mutafi.

Sai lokacin fattu ta an kare da Hammana nata na gurin" cikin jin daɗi ta nufeshi tana murmushi," Hamma kalli yadda matar nan ta sauya min fuska? Wllh gani nake kamar bani ba "fattu ta faɗa tana dariyarta mai burge wa da ban sha'awa.

Kallonta kawai Adeeb yake ,dan shikam ya rasa bakin magana ma,gaba ɗaya fattu ta sanya shi cikin wani yanayi na ruɗewa da zallar kyanta.
Ita kuwa tana tsaye gabansa sai rangaji take ,jinta take kamar sarauniya yau ɗin nan.

Ahankali Adeeb ya kai kallonsa kan waɗan nan abubuwan na fattu, ajiyar zuciya ya sauke ganin yanzu kam ta saka wannan abar.dan haka hannunta kawai ya kamo sukayi waje.

Sai lokacin fattu ta sami damar kallon tsarin falon,sama gidan baki ɗaya .
Suna tafe amma fattu na waige waige,ikon Allah Allah garin daɗi na nesa,ashe su amaƙabarta suke,anya kuwa wannan gidan ba aljannar duniya bane.ahankali tace " kaikuwa Hamma dan Allah wannan gidan na waye?"ta faɗa tana kallon yadda yake danna nonbibin bude ƙofar.


Kallonta yayi bayan sun fito farfajiyar gidan,kafin ahankali yace "nawa ne"
Baki fattu ta buɗe cike da mamaki kafin tace " ikon Allah, to Hamma a ina ka sami kudin gina wannan gidan, dan nasan aradu zai kai kusan dubu saba'in ko tamanin " ta faɗa tana irin jinjina kan nan na ta kwaso kudi da yawa.
Dariya ce ma ta kama Adeeb ,saidai kasancewarsa ba mai yawan dariya ba yasa yayi murmushi kawai ,kafin yace " ki tara kuɗin da kika faɗa kibani na baki gidan" ya faɗa cikin nishadi,haka kawai yake jinsa cikin wani irin nishaɗi dajin daɗi

Kama baki fattu tayi cikin zato ido tace"woooooh Ni ɗiyar baffa,ina zanga wannan uban kuɗaɗen? saidai idan kaina san siyar insamu, Ni wllh bazan gina gida irin wannan ba ma,haba saikace wanda zan zauna da aljanun duniya acikin" ta faɗa tana wani dan taɓe baki irinna rufamin ashirin nan.

Kallonta Adeeb ya ɗanyi, yadda take ta zuba masa surutu,ashe dama tana da surutu haka?yanzu ta sake dashi sosai,kuma ya fuskanci idan suna tare sam bata fiye lura da wasu abubuwan da zata gani taji tsoroba.

Dai dai nan suka kawo wajen ajiye motoci,kafin su karasa saiga tareeƙ ya fito daga cikin wata rantsatstsiyar mota Black,mai baƙin gilasai,motace yar ubansu wacce kana gani kasan anyi barin kuɗin agurinta.
Bude musu motar yayi yana ɗan satar kallon fattu,wai zuƙi haka yarinyar take dama,gaskiya yana fatan Allah yasa wanan alherin da suka ƙalla karya kunce .

Harararta Adeeb yayi cikin jin haushi yadda ya kafawa fattu idanu yace " to yi da gaske ka cinyeta" ya faɗa cikin harshen larabci yana hararar tareeƙ .

Dan sosa kai tareeƙ yayi yana murmushi,azuciyarsa yana faɗin lallai yallaɓai irin wannan kishi haka kiri-ƙiri?hmmmmm .


Shiga motar sukayi fattu na ta kallon yadda motar take wani sukuf da ita ,kamar siffar wani kwaron,
Kallon Adeeb tayi wanda ya jingina kansa da jikin kujera as usual idanunsa alumshe.
"Hamma wai a wannan duniyar da mukazo, acikin kwarya ake yawo ne?"ta faɗa tana mai riƙe haɓa.

Idonsa daya ya buɗe tare da kallon ta ,yana rasa mai zai ce mata dan takaice wai motace ƙwaro,kai fattu sai gyaran Allah.
Ganin yayi shiru ta kuma cewa "Hamma yanzu kuma wace duniyar zamu?"
Kai Adeeb ya dafe cike da gajiya surutu yace " duniyar cinye mutane masu surutu" ya faɗa yana harararta.

Allah Sarki fattu dagalo!!tayi tana kallonsa cikin mutuwar jiki ,kafin ahankali ta ɗan matsa kusa dashi tare da kamo hannun rigarsa ta rike tayi kalar tausayi sosai ,ashe duk murnar da take dama duniyar cinye mutane zasu koma,?shikenan bazata ƙara ganin baffanta ba?
Ahankali tace "Hamma baffa....

"Hihhhhhhhh" Adeeb ya fada yana mai ɗora danyatsarsa akan bakin fattu,sannan ya kwanto da kanta zuwa kafaɗarsa.

Kwanciya tayi lamo cike da tunani kala kala aranta .

Tafiya sukayi mai ɗan nisa kafin naga sunzo gaban wani irin makeken gida mai matukar girma da ƙasa,girman gidan yayi haɗa anguwanni manya guda uku,get suka nufa ,suna idan akaga tareeƙ sai abude masa cikin girmamawa,ba wanda ya kula da Adeeb dake bayan motar,dan glass ɗin bakinsa sosai.

Saida suka wuce manyan get bakwai ,kafin suka nufi wani get mai matukar kyau da girma,wani irin walwali get ɗin keyi kai kace da zallar kwal akayishi.

Daga samansa kuma wasu danjojine masu ruwan kwal ke rubuta,

Well come to the King palace cikin manyan baki.

Ahankali get din ya buɗe bayan wata doguwar na'ura ta danno kai ta haske ko ina cikin motar .
"Yallaɓai mun karaso" tareeƙ ya faɗa yana ɗan juyowa kadan.

Shiru Adeeb yayi yana mai jin wani irin kewa da damuwa azuciyarsa." Tareeƙ how long na dauka ba'asan inda nake ba?Adeeb ya tambaya cikin sanyin murya.

"Yallaɓai 5 months 3days" tareeƙ ya faɗa cikin jimami.

Runtse idanu Adeeb yayi tare da budewa ,da sauri kuma ya yunƙura tare da dauke kan fattu daga kafaɗunsa,wacce tayi lamo kamar mai barci tsoro duk ya gama cika mata ciki.

Fitowa yayi daga motar kafin ya fara takawa cikin nutsuwa da jin kewar iyayensa.
Da sauri fattu ta fito daga mota ita ta riga da gudu tabi bayan Adeeb,Allah yasa flat shoe ne akafarta.saurin kamo gefen hiraminsa tayi ta riƙe gan cikin hannunta.yana jinta baice mata komai ba ,har suka kai bakin ƙofar.

Ahankali ya nuna fuskarsa jikin wani dan madubi,wani dogon layine naga yana zagaye fuskar tashi,kafin kofar ta buɗe da kanta,yana sanya kafa cikin wani tafkeken falo ,naji wata murya ta dauki
Magana," Well come home prince Adeeb Muhammad Ashraf ,your hinest you have a big surprise to see "

Masu karatu fattu fa gaba ɗaya ta tsure da ganin irin duniyar da suka shigo,wani irin mahaukacin falone ,wanda ta ko ina matsalar benece acikinsa, ga wani dan banzan sanyi da ƙamshi dake dukan hancin ta.nan da nan jikinta ya kama rawa.
Ta rike hannun Adeeb gam-gam cikin nata.

Kamo hannun nata yayi tare da kanta zuwa cikin tsakiyar falon,wanda da gyar fattu ke taka ƙafarta dan wani irin kaishi da taji a ƙasa dakin.
Zaunar da ita yayi yana mai kallonta,
"Ki zauna anan, za'a shigo dake yanzu."
Adeeb ya faɗa yana mai kallon yadda jikinta ke tsuma.

Hannunsa ta kara damkewa kafin tace "Hamma tsoro nakeji sosai" ta faɗa cikin rawar murya.

Hannun nata ya kama ahankali ya kai bakinsa ya sunbata, kafin ya shafa gefen fuskarta ,yace kijirani kinji " yana faɗin haka yabi matakalar dake tsakiyar falon yayi sama.
Kallo fattu tabishi dashi cike da tsantsar tsoron wannan guri.hawayene ya zubo mata sharrrrr!! Daga idanunta,ahankali ta sanya hannu ta share wahayen .

Shikuwa Adeeb wani haɗaɗden part ɗin naga ya nufa asaman,hadimaine birjik farfajiyar gurin kowa da abinda yake ,tafiya yake cikin sauri da sassafar,ba abinda yake so da buri illa yayi ido hudu da abinsa.wata baiwa ce ta ankare da Adeeb,cikin hanzari ta zube ƙasa tana faɗin
Takawarka lafiya ,dan sarki jikan sarki,yarima mai jiran gado,alherin Allah ya kai maka.
Da sauri duka suka ankare da abinda baiwar nanke fadi,cikin azama da tsantsar farin ciki sauran ma suka zube ƙasa suna kwasar gaisu da murnar ganin Adeeb,ba wanda Adeeb ya kula kai tsaye dakin mahaifinsa ya nufa.
Ahankali ya buɗe kofar cikin sanyin murya yayi sallama.
Wani farin Balarabe dattijone kwance akan wani lafiyayyen gado irin na sarakuna masu ji da kansu,gefensa kuma wani likita ne ke ƙoƙarin daura masa ruwa ahannunsa,
Sai wani mata guda biyu dattijai, sunsha ado da gwala-gwalai na alfarma ,ko wacce tana inbakiyi bani guri,
Sai wani farin matashi zaune kusa da dattijon nan,ya riƙe hannunsa.

Cikin azama dattijon ya wani zabura tare da sauƙowa daga kan gadon yana mai goge idanunsa,kafin cikin rawar murya yace " habeebee Adeeb "
Ya faɗa tana nuna gofar dakin ,inda Adeeb ke tsaye ,cikin shaukin ganin mahaifin nashi.

Gaba dayan yan dakin ne suka biyo suna kallon ƙofar dakin,aikuwa Adeeb ne ya dawo,prince Adeeb ya dawo gida.

Da gudu Adeeb ya karaso cikin dakin tare da rungume dattijon nan ajikinsa tsantsan yana mai faɗin," habeebe rurh cikin kuka"
Shima kuka kawai dattijon nan yasa tare da ƙanƙame Adeeb ajikinsa.

Matan nan kuwa kallon kallo naga sun fara cikin rudewa da shiga kokwanto.



Masu karatu muje zuwa yau dai ga fattu cikin gidan sarautar Masar,koya zata kasance?


Ga kuma Adeeb jikin mahaifinsa .
Sai mun hade next page.

Anty mammynku ce

Mrs babi💘💘💘

Share and comment fisabilillah

More comment
More typing.🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄


MACIJI NE🪱🪱🪱




Na mammy kabeer
(Anty mammy)



Elegant online writers📚📚




Free book

Page 35/36





_______________Kallon- kallo naga matan nan nayi atsakaninsu, ko wacce tana jifar ƴar uwarta da mugun kallo, yayi da zuciyoyinsu ke buga cike da mamaki .

" Habeebee ina kashiga? Me yasami rayuwarka? Na shiga damu matuƙa lokacin da muka wayi gari an nemeka anrasa ba ƙasashen da bamu zagaye ba wajen nemanka, na sanya ƙudede, kadarori,dama kanfanunuwa na ga duk wanda ya kawo min koda labarin in da kake ne,amma bamu sami komai da ya shafeka ba,meke faruwa habeebee?"dattijon nan ya faɗa yana mai shafa fuskar Adeeb hawaye na zuba daga idanunsa.
Ahankali Adeeb ya kamo hannun mahaifin nashi ,tare da sumbatar hannunsa ,sannan yace " abie wasu abubuwan basu buƙatar afadesu,saidai kawai mubarsu cikin zuciyarmu, sannan muyi ta kallon azzaluman dake neman ganin bayanmu da bakin halinsu." Adeeb ya faɗa yana mai kallon daya daga cikin matan dake tsaye aɗakin.
Kallone irin na duk abinda kike aikatawa akaina, na sani kuma ki kiyaye ranar haduwarmu.

Ahankali naga matar cikin ruɗewa da irin kallon da Adeeb ke mata,ta sanya gefen mayafin dake kanta tana goge zufa daga goshinta ,kanta a ƙasa.

Ita kuwa ɗayar mata cikin sassarfa ta karaso gaban Adeeb ,hannu tasa akan kumatunsa tana shafawa, hawaye ya gama wanke mata fuska.
"Hayatee nayi kewarka fiye da yadda zan fadamaka, naji daɗi da Allah ya kuɓutar dakai daga sharrin mahassada" matar ta faɗa cikin kuka tana mai rungume Adeeb.

" Ammina" Adeeb ya faɗa cikin wata irin murya mai cike da kewa ,yana mai rungume matar daya kira da amminsa.

Matashinnan kuwa gaba daya ya haɗe fuska ,ba alamun fara'a ko murnar dawowar Adeeb gida atare dashi.zamu iya cewa ma bakin ciki yake da ganin Adeeb ɗin.

Zama sukayi abakin gadon ,shida mahaifin nashi,fuskokinsu dauke da mafificin farin ciki da ɗauki ganin juna.
" Habeebee ka bani labarin abinda ya faru" mahaifinsa ya faɗa yana mai kwantar da kan Adeeb ɗin akan cinyarsa.
Kwanciya Adeeb yayi tare da kamo hannun mahaifin nashi kafin yace " abie ,zan baka labarin komai daya sameni ,amma yanzu baka da lafiya ka huta kayi barci abie na" Adeeb ya faɗa yana sumbatar hannun mahaifin nashi.

Dariyar farin ciki abie yayi tare da shafa kan Adeeb yace " ai naji sauki yanzu kam ,wanda yayi silar kamuwa da cutar yazo ya bani magani,bana jin ciwon komai habeebee likita ,zaka iya tafiya" abie ya faɗa yana mai kallon likitan cikin fara'a .

Godiya likitan yayi cikin garmamawa ,yana mai taya sarki murnar dawowar Adeeb ɗin gida,dan kowa yasan da batun bacewar Adeeb ɗin.
Dubawa nayi cikin dakin naga ya rage daga sarki sai Adeeb da ammi,amma ɗayar matar da saurayin nan tuni sun bar ɗakin.

Fattu kuwa tana nan zaune afalon wannan matar ta sauko daga saman sarki cikin wani irin yanayi ,dan ko lura da fattu batayi ba, sai ƙoƙarin kiran waya take .

Ba jimawa kuma,saiga wannan kyakyakywan saurayin shima ya fito cikin fushi da bacin rai,kallonsa fattu keyi taba dan hango yanayin kama da sukayi da Adeeb,saidai ko kama ƙafar kyan Adeeb baiyi ba.

Harya gota inda fattu ke zaune ,sai kuma ya dawo da sauri ya tsaya akanta.
Fattu kuwa da sauri ta mike tsaye tana kallonsa.ganin irin yadda ya tsaya mata akai ƙerere.
Shikuwa saurayin nan mai suna,Rashad ,wani irin. Shegen kallo yake bin fattu dashi,tunda ga sama har kasa,wow wannan kayan fa ?daga ina haka?ya faɗa cikin zuciyarsa yana mai kashewa fattu idanu.
Haɗe fuska fattu tayi tana mai turo baki tare da kawar da kanta gefe.

"Hi babe !" Rashad ya faɗa yana mai ƙoƙarin kamo hannun fattu.
Da sauri fattu tayi baya tana mai turo baki tare da biye hannunta abayanta.
Murmushin gefen baki yayi tare da shafa gefen fuskar fattu yace " yanzu ina cikin hanzari amma zan nemeki,dan kin kwanta araina kuma yawuna ya tsinke" ya faɗa yana mai wucewa bayan ya sunbaci hannun daya taɓa fuskar fattu dashi.
Duk zancen da yake da larabci yake yinsa,dan haka ba abinda fattu ta fahimta cikin zancen nasa.taɓe baki tayi tare da binsa da harara , tana faɗin" Allah ya isa taɓa min fuska da kayi" ta faɗa afili tana mai murguda baki,sannan ta koma ta zauna.

Tana nan zaune shiru -shiru agurin nan ,tunanin take

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login