Showing 105001 words to 108000 words out of 116224 words
kiyi kiba Yar dai dai ba Mai Muni ba
Dilkar amare sabulun amare sabulun dilka sabulun oray White da sauransu ,
Akwai maltinar Mata
Hadin karya gado
Sahihin hadin mallaka
Hadin Mai jego
Hadin sabon budurci
Butar tsarki
Dan goshi da mahadinshi
Dan goshi sabon salo
Sirrin tafin kafa
Kalolin humra
Hatsabibin turare
Dai dai sauransu ga Mai bukatar ganin kalolin kayan da muke dashi zai iya nemana ta wannan number 07034251528 call or WhatsApp karku manta da sunan *Mmn zarah sokoto.ina sokoto Ina aikawa kowane gari cikin aminci da yardar Allah*
07034251528
_______________Nan take sarauniya suhaimat da mahaifin fattu,suka shirya tahowa Misra,hankalinsu gaba ɗaya atashe yake ,barinma sarauniya suhaimat,burinta daya taji a inda aka sami labarin yarta,tayi alkawarin ko awace duniyar take zataje nemanta, fatan ta daya Allah ya nuna mata yarta,yasa ace Adeeb ɗin yasan inda take zaune.
Haka aka shirya musu jet,cikin lokaci kankani, su zayyad suna school dan haka ba'a taho dasu ba,Basu san da tafiyar Bama.
Ko acikin jirgin gaba ɗaya suhaimat ta kasa samun nutsuwa,fargaba da tunanin wane labari zata samu akan diyarta, ya cika mata ciki.
Ahankali mijinta ya kamo hannunta ya rike cikin nashi,kallonsa tayi cike da karaya,murmushi yayi mata tare da cewa"ki kwantar da hankalinki Fulani na In Sha Allahu alkairine yake kiranmu" sarki ya faɗa cike da kokarin kwantarwa da matar tasa hankali.
Jinjina kai tayi tare da faɗin "Allah yasa hakan mijina"
Cikin hikima da tsari Adeeb ya tsara musu yadda zasuyi su kama ammi,sannan yana son abie yaji komai da kunnensa,kuma duji wanda ke taimakawa ammi akan waɗan nan abubuwa da tayi ta aikatawa.
Dan haka sun tsara akan amma zata tunkari ammi akan cewar me yasa ta karya alkawarinsu? Tasan cewar itace ta sanyawa Adeeb wani abu yaci,dan gashican yana fama da ciwon ciki yana ƙoƙarin mutuwa. Sukuma zasu tsaya a waje ɗan jin duk abinda ammi zata faɗa da kanta.
Haka dai suka shirya abinda zasuyiwa ammi domin tona mata asiri.
Adeeb ne ya kalli tareeƙ yace idan jirginsu ya sauka kaje ka daukosu,ka kai su can guest house ɗina,idan lokacin shigowar su yayi,zan kiraka saika kawosu.
Amsawa tareeƙ yai da to,
Gaban fattu sai bugawa yake,tana jin wani irin tsoro da fargaba,wani sashen kuma na zuciyarta tana jin wani irin farin ciki,wai yau itace zata sadu da iyayenta?yau zataga ahalinta, hakika bazata taba mancewa da wannan ranar ba,ranace wacce zata sanyata cikin ranaku mafi muhimmanci arayuwarta.
Kallonta Adeeb yayi cike da ƙarfafa gwuiwa,ya riko hannunta,da sauri ta kalleshi tana ɗan marairaice fuska,lumshe ido yayi tare da sakar mata murmushi yana ɗan murza hannunta.
Ahankali ta sauke ajiye zuciya tana mai kallon hamman nata,tana jin sanyi cikin zuciyarta.
Cikin nutsuwa da dauriyar zuciya Adeeb ya mike,duk da zafin da jikinsa ke dashi na zazzaɓi,dan har yanzu akwai zazzaɓi sosai ajikinsa,amma sam baya jin zai iya kwanciya ahalin da ake ciki yanzu,faɗa musu yayi kan cewar zaije ya kira mai martaba,dan yajiyewa kunnensa,sannan yace amma yaje gurin ammi,tayi magana da ita,tabi duk wata hanyar datasan zata bi dan ammi tayi magana yadda mai martaba zaiji da kunnensa.sannan yace idan ya kira mai martaba ,,zai sanar da ita ta hanyar yi mata flashing awaya,Dan haka wayarta ya karba ya kira number ta kafin ya yayi saving din number nata.
Cikin sanyin murya da gajiyawar zuciya Adeeb ya kalli tareeƙ yace "tareeƙ ina buƙatar rashad ya kasance agurin shima"ya faɗa yana shafa kan Rashad,Wanda yake kallon dan uwan nashi,cike da tausayawa,dan yasan Adeeb jarumi ne na gaske,yaga rayuwa kala kala,wanda badan Allah yana kareshi ba,da tuni wani zancen ake ba wannan ba.
Bayan sun gama tsara yadda komai zai tafi yadda suke bukata,kai tsaye Adeeb ya wuce bangaren martaba,lokacin da yaje mai martaba yana shirin fita fada,gaida shi yayi cikin girmamawa sannan yayi shiru kansa aƙasa.cike da kulawa abie ya zauna kusa da adeeb,kansa ya shafa cikin ƙauna kafin yace "habeebee meke tafe da kai?me kake so ?dan naga akwai Magana cikin bakinka"abie ya faɗa yana mai ci gaba da shafa kan Adeeb .
Ahankali Adeeb ya sauke ajiyar zuciya tare da ɗago da kansa,hannun abie ya kama ya sumbata,sannan yace "abie akwai tarin damuwa atare dani, amma In Sha Allah yau komai zai zo karshe,ina son ka biyoni bangaren ammi,domin jin komai da kanka,amma inason dan Allah abie duk abinda zakaji,kada ka sanya damuwa aranka, kada ka bari abun yayi tasirin da zai tada maka ciwonka Please"Adeeb ya faɗa yana mai kara damke hannun abie cikin nashi.
Cike da tausayawa abie ke kallo Adeeb,hakika Adeeb yana cikin damuwa,dan kuwa kallo ɗaya zakayi masa kasan akwai gagarumin abinda ke samun zuciyarsa.dan haka cikin tattasan lafazin abie yake faɗin"In Sha Allah habeebee zan zama mai sanya juriya da tawakkali akan duk abinda kunnena zaiji,fatana daya ne ,Allah ya yaye maka duk wata damuwa dake damunka.
"Ameen abiena,na gode sosai"Adeeb ya faɗa yana ɗan ɗora kansa akafadun abie.
Wazirine ya shigo cikin ƙaton falon da sallamarsa,amsawa abie yayi kafin ya shigo ya kwashi gaisuwa.nan abie ke sanar dashi yana da uzurin da zaiyi yanzu dan haka ya kula da faɗa kafin ya fito. Da to waziri ya amsa kafin kafin ya nufi ƙofa,bayan Adeeb ya gaidashi.har zai fice Adeeb yayi tunanin waziri ma familynsa ne,kuma zai iya taimakawa agurin idan bukatar hakan ta taso,dan haka yace abie ya kamata uncle ya biyomu koba komai shima jininkane"
Jinjina kai abie yayi cike da kokarin don faranta wa Adeeb ɗin kafin yace "shikenan habeebee,ba damuwa idan hakan kake so"
Nan abie ya sanar da waziri akwai bukatar ya biyoshi bangaren ammi dan akwai muhimmin abu da suke son aikatawa acan.
Da to kawai waziri ya amsa sannan suka tashi gaba ɗaya suka nufi bangaren ammi.
Suna fitowa Adeeb yace yana son suje su duba rashad kafin su wuce can ɗin.
Dama kuma yau abie bai shiga duba rashad ɗin ba,dan kullum yana zuwa ya ga ya jikin nashi.dan haka sai suka wuce can.
Daidai lokacin da sukaje tuni rashad yana kan keken guragu azaune.
Sosai abie yaji dadin ganin cewar rashad sauki ya fara damuwa,tunda har sunan shi ya kira.
Adeeb me yace ya kamata su tafi part din na ammi yanzu,dan kammala komai cikin lokaci.shidai abie baisan me ke faruwab a,amma haka nan ya tsinci kansa cikin faduwar gaba.
Haka suka fito gaba dayansu suka nufi part din ammi.
Daidai wannan lokacin kuma,tuni amma tana part din ammi,
Zaune ta tarar da ammi kan kujera,tayi shiru da alama tunani yake,abin duniya ya isheta,tana tunanin idan aka san abinda tayiwa zulaihat,tabbas komai yana iya faruwa,tasan mahaifin Zulaihat ya fita iya shege,kuma bazai gyaleta ba in yasan abinda tayiwa yarsa. Dan haka kawai ta yanke shawarar ta sanya afitar da Zulaihat can jeji akashe ta ayarda gawarta ajejin.
Tana cikin wanna tunanin taji shigowar amma,kai tsaye ba tare da ko sallama ba,kuma da karfi ta buga kofar.
Juyowa tayi da hanzari dan ganin wanda ya shigo mata daki haka,ya ɓuga kofa da karfi.
Ido hudu sukayi da amma,cike da mamaki da kallon ƙasƙanci ammi tace "ke mahaukaciyar inace zaki shigo min daki bako sallama?ta fada tana kallon amma cike da raini da tsana.
"Baki da wannan matsayin da zanyi miki sallama,domin ke ɗin mushrika ce,azzalumai,maha'inciya kuma maci amana"amma ta faɗa cikin zafin murya tana nuna ammi da hannunta.
Daidai lokacin su Adeeb da mai martaba suka iso babban falon ammi,suna ƙoƙarin buɗe kofar da zata sadaka da falon da su ammin ke magana da amma.kuma duk abinda amma ta faɗa akan kunnensu.
Alamu abie yayi musu na su dakata anan gurin,ɗan jin abinda ammi ta fara faɗa.
Cikin dariya irin ta mugaye ammi tace"banda abinki menene na maimaita abinda kin riga kin sani?kuma nima na sani,ina mai gargadinki daki gaggauta fita daga dakin nan,kokuma yanzu ina aikata miki abinda zaki jima baki manta da wannan ranar ba"ammi ta fada cikin haɗe rai .
"Menene kuma ya rage ammi?duk irin zalumcin da kika aikata mana abaya, kina nufin akwai wanda zakiyi mana shi yanzu ya girgizamu? Kin kashe rayuka masu yawan da kema bakisan me suka aikata miki ba,dan haka karki damu barazanar ki ta daina tsoratani,nazo in sanar dake cewar ina sane da gubar da kika sanyawa Adeeb yau cikin abincinsa.
Darammm gaban mai martaba ya fadi da sauri ya nemi gurin zama sakamakon ji da yayi yana neman faduwa....
Manage plessa yau Ina busy ne
Mrs babi 💘💘
Share and comment fisabilillah.
More comment
More typing.
[30/08 15:01] %Faiza%: 🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄
MACIJI NE 🪱🪱🪱
Na mammy kabeer
(Anty mammy)
Elegant online writers📚📚
Free book
Page 85/86
_______________Ƙarar faɗuwar abu da sukaji,itace tayi sanadiyyar juyowarsu gaba ɗaya,ba komai bane ya fadi face tanfatsestiyar wayar queen suhaimat,Wanda shigowar su kenan ita da mijinta,dan tuni tareeƙ yayi musu iso zuwa dakin ammi,kuma gaba daya kalaman ammi akunnensu suka sauka,
Cikin rawar jiki queen suhaimat ta ƙaraso cikin dakin,zuciyarta kamar ta kamar ta tsaga ƙirjinta tafito, dan yadda take bugawa da ƙarfi,zaka iya juyo sautin bugun nata.
Gaban ammi tazo ta durgushe tana kallonta baki buɗe,kafin tace "uktee me kike cewa?me kunne na keji kina faɗa?Please kada kisa zuciyata ta buga,akan abinda kunne na yaji"queen suhaimat ta fada cikin rawar murya tana kamo hannun Ammi.
Cikin azaba ammi take kallon suhaimat,tana jin wani irin bakin ciki da ɓacin rai,yanzu shikenan, suhaimat tayi galaba akanta?shikenan suhaimat zata san wacece yarta,kuma ta ganta araye? Ina idan hakan ta faru shikenan ta zama marar nasara arayuwarta.dan haka cike sa tsana ta fizge hannunta daga cikin na Queen suhaimat,kafin ta yunkura da gyar ta tashi zaune,jingina tayi da jikin bango tana maida numfashi kafin ta fara magana"tabbas abinda kunnenki yaji suhaimat,to haka yake,nice nan narabaki da ƴarki,tun tana karama,Ni nasanya baiwarki ta satomin ita,kuma nasa aka jefar da ita acan wata ƙasar,ta yadda har abada bazaki ganta ba,domin ajeji nasa aka yardata, wanda nasan,ba wani mahaluki da zai ganta agurin,kuma ko namun dawa basu cinyeta ba,yunwa zata kasheta, sannan na kashe baiwarki da hannuna dan rufuwar asirina"ammi ta faɗa cike da rashin imani tana wani zazzaro kunburarrun idanunta.
Da baya Queen suhaimat ta koma ta zauna dabass.kunnenta yana amsa kuwwar maganar ammi,ko amafarki bata taba tsammanin jin wanan bayanin daga bakin ammi ba,she can't believe ace ƴar uwarta ita ce silar batan yarta,amma me tayiwa ammi haka da zafi?me ta tsare mata da har take burin ganin bayanta?
Cikin muryar kuka queen suhaimat tace"uktee,me nayi miki?wane laifin na aikata agareki, da har na cancanci wannan aika aikar agareki?nifa yar uwarkice ta jini,amma kika zabi ki cutar da Ni da abinda nafiso fiye da duniyata"
Cikin zafin rai ammi tace "saboda bana kaunar ki,bana sonki,na Tsaneki,ban taba sonki matsayin yar uwa ba,domin kedin mai nasarace,akan komai, ke kekiyin nasara akaina,an fifita sonki akaina,bayan haka kikazo kika auri mutumin da na ƙwallafa rai akansa,wanda nake fatan aura,amma aka aura mikishi,Ni kuma aka aura min wanda bashine cikin raina ba.suhaimat na Tsaneki,kuma nayi alƙawarin ganin bayanki, keda zuri'arki,dan kuwa ko su zayyad Allah ne ya tseratar dasu daga kaidina, da tuni na hallakasu sun bar duniyar nan"ammi ta fada tana jan numfashi da gyar,tsabar yadda take jin jiki.
Kuka sosai queen suhaimat keyi,tana jin wani irin ciwo da radadi cikin zuciyarta,yanzu yar uwar ta itace ta cutar da rayuwarta haka?wannan wane irin son zuciya ne,
Cikin kuka ta kalli ammi,yadda take fidda numfashi da gyar,ga ƙafarta ta dama sai jini take.
Tace "amma me yasa baki sanar dani kina son habib ba? Wllh Dana bar miki shi kin aura ,meyasa kika yi haka yar uwata?ina yata take ?ina kika kaita?na rokeki ki sanar dani inda kika kaita,zan tafi neman ta, koda zan rasa raina akan hanyata ta zuwa neman ta ne,hakan shine kadai zai sanya Ni farin ciki"queen suhaimat ta fada cikin matsanancin kuka,
Shi kuwa Sultan Habib tsabar kaduwa ya kasa koda matsawa daga inda yake,kallon ammi kawai yake yana jin kamar yaje ya shaketa ta mutu tabar duniyar ma kowa ya huta.
Ahankali Adeeb ya riko hannun fattu,wacce take bin iyayen nata da kallo,tun shigowar su,wani irin shauƙi da farin ciki ke dibarta, ji take ko ahalin yanzu ta koma ga mahaliccinta,tabbas tayi nasara tunda har ta ga iyayenta,wayyo Allah baffa ko kana ina ?dagaka wannan ranar da kake burin zuwanta.
Da sauri ta kalli Adeeb hawaye na zuba cikin idanunta,lumshe ido yayi tare da girgiza kai alamun kar tayi kuka,sannan ya sanya hannu yana share mata hawayen idonta,kafin yayi mata nuni da taje gurin queen suhaimat.kallonsa tayi gabanta na tsananta faduwa,amma ya jinjina mata kai tare da sakin murmushin da zai kwantar mata da hankali.
AHankali ta fara takawa,cikin hikima da fargaba,kasancewar ba wata cikakkiyar lafiya gareta ba, hakan ya kara bata damar tafiya ahankali,kallo su amma da nanny suka bita dashi,cike da tausayawa,saidai nanny tana son gano kamar wani abu ya faru da fattu,duba da yadda take takawa ahankali,kuma tana ɗan dingisawa.amma tunani da sanin da wa fattun ke tare dashi,yasa ta kawar da tunanin da takeyi,ta dauki hakan amatsayin fargaba ce kawai.
Queen suhaimat na kuka gaban,ammi tana faɗin "na roƙeki,ki sanar dani inda kika kaimin yata dan Allah "kawai saiji tayi andafa kafaɗunta .
Da sauri ta juyo tare da kamo hannun wanda ya dafata,
Fattu ta gani tsaye kusa da ita tana hawaye.
Kallon fattu tayi cikin kuka itama tace"dan Allah ƴata ko kinsan in da zan hadu da gudan jinina?wallahi itace rayuwata,bani da wani abinso sama da ita,ki taimaka min idan kina da masaniya akan ƴata"ta kai karshen zancen ta tana Dora goshinta cikin rafin hannun fattu.
Kuka fattu keyi sosai ,ganin yadda mahaifiyarta ke tsananin kaunarta,amma saboda zalunci aka rabata da ita,yanzu gashi suna tsaye tare da juna amma bata san ko wacece agabanta ba.
Ahankali Adeeb ya taka zuwa garesu,hannunsa ya sanya cikin aljihunsa ya ɗauko wannan sarƙar,domin tana tare da shi dama.
Kallonsa kowa keyi,harda queen suhaimat,ta bayan fattu ya tsaya tare da daura mata sarƙar nan.nan da nan sarƙar ta dauki walwali da haske ,tuni tambarin hoton zuciya mai dauke da harafin s&h ya bayyana jikin sarƙa.
Cikin kasalalliyar murya ammi tace "a'a Adeeb , a'a karka daura mata sarkar nan, nayi alƙawarin suhaimat harta mutu bazata ga yarta ba,me yasa ka je kasato min sarkarnan?ashe kaine ka ɗauke sarƙar Adeeb,ka cuceni,kai amanata wayyo ni ammi na shiga uku komai ya kare"Ammi ta fada cikin yanayi na fitar hankali,wanda zamu iya cewa kwakwalwarta ta tabu.
Wani shegen kallon tsana Adeeb ya jefo ammi dashi,kafin yace"kaicona rayuwarki ammi,kin cuci kanki,kuma tun yanzu kin fara ganin sakayyar Ubangiji akanki,Allah ya isa tsaninmu dake"
Adeeb ya fadi hakan cikin zafin rai da kumar zuciya.
Tareeƙ ne ya matso ahankali yana mai bubbuga bayan Adeeb,alamun rarrashi.
Cikin tsantsar ruɗu da wani irin farin ciki queen suhaimat ke bin sarƙar da ido,kafin ta kamo sarƙar tana kalla, da sauri ta fizgi sarƙar dake wuyanta,ta kara da sarka wuyan fattu,sak!!irinsu ɗaya komai da komai,
Hakan na nuna cewar fattu itace yarta?fattu itace gudan jininta wacce ta dauki tsawon shekaru tana nema?ya salam yanzu dama soyayyar da takeji azuciyarta ta fattu,tana da nasaba da kasantuwar fattu diyarta ta cikinta?wani irin kuka ne mai tsananin karfi ya kwacewa queen suhaimat,Tana mai kamo fuskar fattu,tana girgiza kai,cikin wata irin murya mai fidda amo tace "FATIMA ZARA, da gaske kece ?kece zarana diyata abin sona?"queen suhaimat ta fada cikin yanayi na rudewa.
Cikin kuka sosai fattu ta jinjina kai tana kallon mahaifiyarta,da wata irin kalar soyayya mai narkar da zuciya.
Kankameta queen suhaimat tayi tare da kara sakin wani irin kuka mai rikitar da mai sauraro,tana faɗin"Alhamdullah ya Allah,Nagode maka ubangiji, kaine mai juya farin ciki ya koma bakin ciki,bakin ciki ya koma farin ciki,yau kukana ya ƙare ka nuna min yata farin cikina abin sona,ya Allah ka kara karemin yata karka ba azzalumai dama akanta,Fatima zata diyata,abin sona "irin kalaman da queen suhaimat keyi kenan,tana ƙanƙame fattu,kamar za'a kwace mata ita,wanda saida ta sanya kowa kuka agurin,
Cikin sassarfa Sultan Habib ya ƙaraso gurin tare da rungumesu gaba ɗaya shima yana kuka.
Duk mai imani idan yaga wannan bayin Allah ,dole ya tausaya musu,dan kuka suke bilhakki da gaskiya.fattu har neman shiɗewa take tsabar kuka.
Su sukuwa sai sum batar fattu suke tare da godewa Allah,daya bayyana musu ita cikin aminci.
Kusan minti biyar suna cikin wannan yanayi kafin abie yayi gyaran murya cike da alhini,yana jin zuciyarsa nayi masa zafi sosai,yace "Alhmdllh ba Abinda zamucewa Allah sai godiya,yanzu kam komai yazo ƙarshe,azzamar matar nan zata girbi abinda ta shuka,tsawon shekaru.dan haka akwai bukatar kowa yaje ya hutawa zuciya da jikinsa.Rashad kuyi hakuri,akan abubuwan da nayi ta nuna muka abaya kaida mahaifiyarka,sam hakan ba yin kaina bane,sharrin wanann makirar ne"abie ya faɗa yana nuna Ammi,wacce take kwance sharaf kamar gawa.
Girgiza kai Rashad yayi kafin yace "abie nima ka yafemin,domin nayi ta sanya ka cikin damuwa da tashin hankali,kuma duk sharrin ammi ne azzaluma"ya fada yana hararar gurin da ammi ke kwance sharkaf.
Matsowa gareshi Adeeb yayi tare da shafa kansa yace "Allah ya baka lafiya lilna, sannan ya kara tsaremi daga sharrin masu hali irin na ammi" da Amin suka amsa gaba dayansu.
Ko kallon inda ammi take Adeeb baisonyi,dan sosai yakejin haushin kansa ,na kasa fahimtar gaskiya da yayi tun dadewa,har ammi tayi wannan gagarumar nasara akansa.
Abie ne ya sanya wasu dakaru suka shigo dan fitar da ammi daga dakin,yace su kaita can kurkuku mafi tsanani da duhu su ƙullewa aciki.kafin ayanke mata hukunci.
Haka suka kinkimi ammi batama san inda kanta yake ba sukayi waje da ita.
Juyawa sukayi gaba ɗaya,Suna shirin barin dakin sukaji kamar motsi cikin dakin da aka kulle Zulaihat,dan haka cikin azama tareeƙ da Adeeb suka nufi ƙofar,da gyar suka balle kofar,dan sun rasa makullin.
Aikuwa suna budewa suka hangi Zulaihat kwance abakin ƙofar adaddaure, gaba ɗaya jikinta jini kaca -kaca.cikin azama suka fara kunceta,ta galabaita sosai kuma har lokacin kanta na zubda jini,
Da gyar ta buɗe idonta ta kalli Adeeb tace "my prince,karkaci abincin nan akwai guba aciki, kuma tare suka hada baki zasu kasheka"ta karasa da gyar,jini na zuba daga bakinta.
Abie ne ya ƙaraso gurin da sauri yana faɗin"Zulaihat Meya sameki haka?waye yayi miki wannan abun,kuma ammi ita da wa suka hada bakin"abie ya faɗa yana jin bugun zuciyarsa na kara tsananta,dan baisan kuma wa Zulaihat zata ce ba.
"Cikin mawuyacin hali,Zulaihat tace"Abba.....na,abba na ne,tare suke kulla komai shida ammi,karku barshi"tana faɗin haka idanunta suka kakkafe jikinta ya saki.
Cikin wani irin bugawar zuciya abie yace "w...a....z.....
Sai kuma ya kasa karasawa kawai ya zube agun asume.
Hmmmmm masu karatu wannan wace irin rayuwace ?wacce amana tayi karanci?dan uwa shine zai cutar da dan uwansa.
Allah kasa nufi karfin